Showing 33001 words to 36000 words out of 130249 words

Chapter 12 - ME KAMAR SARKI

  

04 Oct 2024

17615

"shikenan Musbahu na amince ku tafi da Lami wudil ta zauna a hannun ka tayi karatu mai zurfi kuma karka dawo da ita kwana kusa..................


Kamar anyi wani abu na firgici ko tashin hankali haka suka ji muryar Ramatu tana rafka salati "la'ilaha illallahu kaito na, na lalace ni za'a munafinta? To Allah ya tonu asirin ku naji komai kuma wallahi tallahi babu inda Lami zata je talla nai niyya tayi ba karatu ba" nuna Musbahu take da yatsa tace "kai kuma daka d'ebo gemu kamar bunsuru da gurma gurman ido baka isa raba ni da 'yata ba munafiki d'an mafiya hatsabibi kawai harda wani ya amince maka ku tafi tare sai naga idan kaine ka haifa min 'yar..........

"RAMATU"!!! Baffah ya fad'a cikin tsawa da nuna bacin rai rike kugu tayi tana kallon yadda Baffah ke huci tace "malam dallacan ka rufe min baki fad'i Ramatu ka kara da babbar murya suna na kenan Lami ce kuma nace babu inda zataje babu shegen da zata bi ko'ina idan lokacin auren nata yazo shi munafikin naka mai zugaka tayi karatu zai siya maka gado ne ko kana tunanin zai taimake ka to ba dani za'ai rakiyar asara ba kaji dai na fad'a maka sai abar maganar Lami ku kama wata tashar na yanke hukunci".

"Amma ke kam Ramatu bansan wacce irin mace bace ke sam kin girma amma baki da hankali ko bakisan Musbahu baza kimin haka a gabansa balle kinsan d'an gidan amini na ne munyi kyakkyawan zama da mahaifinsa".

Ta'be baki Ramatu tai tana cewa "af daga baya kenan anyi sadaka da karuwa yo malam tsakani da Allah bazan fad'i gaskiya ina gani a cuce ni d'an yana d'an gidan amininka kawai saika dauki yarda ka bashi a wannan zamanin ba lallai mutumin arziki bane kana ganin idonsa kaga ri'kekken d'an tasha wanda yasan duniya yake jujjuyata".

"Ramatu ya isa haka ki iya bakin ki bana son shashancin banza ki barnan tun kafin ki fusata ni kisa na yanke miki danyen hukunci wanda zai miki zafi" wucewa Ramatu tai domin tasa saki Baffah yake nufi kuma dama saura igiya daya anyi biyu tana tafe tana maganganu 'kar 'kar da 'ku'kuni "eh 'yata ce nace babu inda zata kuma haka bazai ta'ba sauyawa ba ko ana so ko ba'a so ko maye zai faru ba matsala ta bace ta mutum ce" kasa magana Musbahu yai domin yasha mamaki tunda yake a rayuwa bai ta'ba haduwa da mace irin Ramatu ba kasa cewa komai yai sai binta da kallo kawai yake yana juya maganganunta...........

Katse shirun nasa Baffah yai da cewa "Musbahu kayi hakuri kada ka damu kaji kai ba'ko da taiwa haka kaine zakaji mamakin ta amma ba wanda ya saba ba dan Allah kazo da farin ciki ina fata ranka bai baci ba"? Murmushi Musbahu yai yana kallon Baffah yace "babu komai Baffah banji rashin dad'i ba abinda ta fad'a daidai domin yarta ce kowa sarki ne akan kayansa ina fatan kaima kayi hakuri da zuwa na domin ni na jawo hakan ta faru" .


"Kai haba Musbahu ba kai bane ka barshi a nine da bance maka komai akan Lami ba duk da baza'a zo ga haka ba" sauke numfashi Musbahu yai tare da sake kallon Ramatu dake faman hararar shi kafin ya mike yana ajewa Baffah kud'i yace "to Baffah sai wata rana ni zan koma gida Allah ya kaddara saduwarmu" mi'kewa Baffah yai zai masa rakiya yana cewa "Amin Musbahu Allah yai maka albarka ka gaishe min da amini na sosai kace in Allah ya yarda wata rana zai ganni nazo masa ziyara" har waje gurin motarsa ya raka shi sukai sallama ya tafi.

Tunani ne a ransa iri iri wato bai ta'ba karo da mace irin Ramatu ba a rayuwar sa sai yau amma yana daidai da ita zaiyi maganin ta idan bataja girman taba shima zai nuna mata iyakarta domin idan tanajin ita tantiriya ce shi zamani ma Saida ya sara masa.

Kai tsaye kasuwar garin ya nufa yana duba gabas da yamma ko zaiga Lami can ya hangota cikin samari sunata siyan gyada takaici ne ya kamashi karasawa gurin yai da mota yana sauke glass yace "mai gyada" da sauri Lami ta juyo duk da bata sanshi ba tasan daga gidansu yake ba'kon Baffah ne kuma akwai sanayya a tsakanin su.

Gurin tazo da fara'arta tane cewa "har ta fito tafiya zakai"? Kai ya d'aga mata "eh tafiya zanyi saidai tare dake" zaro ido tai "kamar ya ban gane ba ina zamuje"? "Garin mu wudil munyi magana da Baffan ki yace kina son karatu shine zan tafi dake na saki a makaranta kiyi ilimi ba haka kike so ba"? Kamar idonta zai fito waje dan mamaki tace "da gaske Baffah ya amince mu tafi daga nan ko saina koma gida"? Kai ya d'aga "eh daga nan basai kin koma ba" kashe motar yai yana fitowa ya kalli samarin dake gurin yana cewa "dan Allah idan akwai wanda yasan gidan su wannan yarinyar yakai mata farantin ya fad'awa babarta Ramatu cewa wannan d'an birnin daya zo dazu ya tafi da 'yarta zai sata a makaranta" yana fadin ya juya yana shiga mota ya bud'e mata dayar kofar itama da sauri kuwa ta shige ta zauna fuuuu yaja ya bar gurin.


Tanko da iya ganin tashin motar yai da lokacin da Lami ta shiga da sauri ya karaso yana cewa "kai wa na gani kamar Lami budurwa ta 'yar gidan Baffah ta shiga mota a nan"? Dariya duk gurin suka sa wani daga cikin matasan yace "wai kama ji da Allah ba kama bane itace watakila kaida ita har abada domin ta tafi birni zatai karatu kuma kaga idan ta dawo tafi karfin auren ka yaro"? Zaro ido yai "meeeh kenan kuna nufin...........

Duk hada baki sukai cikin tsokana sukace "eh muna nufin ta tafi baza ta dawo kwana kusa ba kuma ko ta dawo tafi karfin auren d'an kauye kasami irinka" jin sun kaure kowa da abinda yake cewa yasa a hargitse Tanko ya bar gurin da sauri yana tafi kamar zai kifa tsabar hankali ya fita daga jikin sa yana tsananin son Lami duk da iyayensa basa so domin ba wanda zaibar d'ansa ya auri jahila saboda gaba mai zata haifo masa 'ya'ya jahilai.

A kofar gida ya samu Baffah ya fito da tabarma yana zaune har lokacin rubutu yake guruff Baffah yaji an zube a gabansa ana haki yana d'agowa cikin mamaki yaga yadda Tanko ya birkice "meya faru Tanko na ganka a haka"? Muryar Tanko na rawa yace "Baffah wani mutum yaje da mota dandali ya dauke Lami ya tafi da ita" kallonsa sosai Baffah keyi yace "yanzu sun tafi kenan"? Kai Tanko ya d'aga "eh Baffah ya tafi da ita" murmushi Baffah yai yana sauke ajiyar zuciya da farin ciki a bayyane kan fuskarsa yace "alhamdulillah ba matsala Tankoo karka damu na san shi jeka abinka" jin abinda Baffah yace yasa Tanko fashewa da kuka kamar d'an karamin yaro ya mike da sauri yabar gurin da kallo Baffah ya bishi yana d'an girgiza kai.

Tanko na shiga gida mahaifiyar sa Delu dake daka a turmi tuni ta yada ta'barya tayo wajensa tana cewa "Adamu lafiya da girman ka kake irin wannan kukan meya faru haka fada min"? Kasa magana yayi sai shashsheka yake "waikai bazaka fad'a min ba"? Daidai baban Tanko ya fito daga bayi da buta a hannun shi yana wanke baki yace "subahanallahi Tanko kukan me kake haka"? Ya karasa maganar yana aje butar ya karaso inda suke tsaye cikin fad'a ya sake cewa "wannan iskancin banzan fa kana ji ina tambayar ka" ran Delu a bace tace "ai malam ya nuna mana bamu kai matsayin da zai fad'a mana matsalar saba sai kaje kayi tayi" komawa kan aikin ta taci gaba kawai ta share sa.

Da yake tun asali malam Balah ya 'bata Tanko da shagwaba sakamakon shi kadai ne gaba da baya shiyasa sau da yawa a lokuta yakan tsula tsiyarsa son ransa duk abin maye babu wanda baya sha ya firnaci kowa duk 'yan matan garin tsoron sa suke ji don ba abin kunya bane ya wulakanta mace kuma babu wanda ya isa hana shi koda me gari ne jan hannun sa Balah yayi yana cewa "kaga kai shiru haka fada min abinda akai maka"? Tanko na karya kai mara lafiya yace "baba Lami ta cuce ni" "wacce Lamin"? Har had'a suke wajen fad'ar sunan cigaba Tanko yai "Lami yar gidan Baffah yau ta tafi binni wai karatu zatai ba yanzu zata dawo ba".

Ta'baryar hannun ta Delu ta saki tana cewa "kan uba mu zasu munafirta, ai dama tun farko kafin maganar ku tai karfi na hana ka saboda da halin uwarta wanda ko kare bazai kalla ba amma kayi kunnen uwar shegu ga irinta nan wa zaiso hada zuri'a da jinin Ramatu dangin tsiya kaf kauyen nan kowa yasan ta da fitina ni gara da hakan ta faru ma wallahi naji dad'i kuma nayi farin ciki kaga yanzu saika nemi budurwa mai hankali mai salahar uwa haba yaro kamar wanda akaiwa asiri duk idonka ya rufe naji dad'in hakan da akai kaima yanzu zaka sake kai 'kiba duk ka 'kanjame kamar wanda mayu suka rike masa kurwa" ta karasa maganar bakinta har kumfa yake.

Shidai Tanko shiru yai ya kasa magana ganin haka yasa Balah tashi tsam yaje har kofar gidan Baffah ya same shi dan yaji dashir da gaskiyar magana bayan sun gaisa yake ce masa "dama nazo ne akan wata magana da naji ta sa'banin hankali a bakin Tanko wai 'yarka Lami ta tafi makaranta haka ne"?.

Shiru Baffah yai zuwa d'an lokaci yai numfasa yana cewa "eh haka abinda kaji Malam Balah ai Tankon yazo nan shine ma yake fad'a min sun tafi Musbahu ne dan gidan wani mutum alhaji Saboh daya ta'ba zuwa garin yai rabon shinkafa da zannuwa shekarun baya" kai Balah ya d'aga "eh na tuno shi mutumin kirki yana nan a raye kuwa"? "Eh yana nan sai aiki daya hana shi zuwa" mi'kewa Balah yayi yana cewa "ai shikenan bari na tafi to Allah ya dawo da ita lafiya" "Amin na gode Malam Balah".

Malam Balah yana komawa gida ya tarar har lokacin Tanko yana zaune inda ya barshi Delu tana tsaye a kansa tana balbale shi da fad'a ya karasa "malam ka dawo me yace maka" "yace min eh ya san da tafiyar karatu zatai to nidai shawara ta anan shine kai Tanko kayi hakuri ka sawa zuciyarka salama ka cire yarinyar nan a ranka ina ganin hakan zaifi zaman lafiya ka 'kyale batun Lami ka manta ka nemi wata ka aura in kuma rabonka ce duk ranar data dawo saika aureta" shidai Tanko tari dabai kamashi ba baiyi ba karshe ma tashi yai ya shiga d'aki kawai ya kwanta yana tunani lallai bazai yarda ba saiya dau fansa bari ta dawo wannan abinda Lami ta masa ta za'bi zaman birni sai tayi danasani.

Baffah bai shiga gida ba sai bayan sallar isha da tabarmar sa a hannu ya aje buta a kofar d'akin Salamatu yana shirin wucewa Ramatu tace "Malam nifa ban gane ba har yanzu Lami bata dawo gida ba" Baffah na shirin wucewa yace "eh abinda dai da bakya so ya faru kuma ya zama dole na fad'a Musbahu yaje dandali dazu bayan fitar shi daga nan bai duba irin cin mutuncin da kikai masa ba haka ya tura miki aniyarki yaje ya dauki Lami ya tafi wudil da ita zai sata makaranta" a zabure Ramatu tace "meeeh ya tafi da ita aiko ya debowa kansa masifa da bala'i saina tabbatar ya gane ba'a ta'ba Ramatu a zauna lafiya dama hada baki kukai dashi malam badan haka ba ina zaisan inda ta tafi harya bita ya dauketa" kamar Baffah bazai magana ba sai kuma yace "Ramatu kina da abun mamaki duk wanda zai kyautata miki shine tsinannan ki amma ba matsala Musbahu dan Allah yai haka badan keba sannan bugu da 'kari yace idan kina bukatar ganin 'yarki duk lokacin da kika shirya kije ki ganota".

Cikin masifa Ramatu tace "bazan jeba dan malafar ubansa wallahi babu inda zanje hauka ma kenan yadda ya dauka min 'ya har gida haka zai dawo min da ita mara mutunci maye kawai ana gudun ka kai kana li'kewa aikin banza nasan malam da hadin bakin ya tafi da ita to sanka 'kanin 'kafarka kaje koma ina ne ka kar'bo min 'yata ehe wannan muguntar har ina"?.

'Daki Baffah ya shiga yana cewa "nidai na fad'a miki kada ki kuskura na sake jin wani batu" kuka Ramatu ta kama bayan wucewar Baffah d'aki "wai a dake ka a hanaka kuka nida 'yata a cuce ni amin mulkin mallaka na rantse da Allah sainaje har wudil din na dauko ta" ta karasa maganar tana face hanci da hucinta ta shige d'aki.

Sun isa wudil lafiya yayin da Musbahu ya kaita gidansa tare da dan'ka amanarta a hannun matarsa Halima tana yara guda biyu Naja'atu da Yusuf sunyi mamakin ganin Lami lokacin da suka dawo daga makaranta cikin alamun tambaya Yusuf yace "maman mu wannan daga ina tazo"? "Oh Yusuf kwai tambaya daga shigowa ko hutawa bakai ba"? "To ai maman mu naga ban santa ba ban ta'ba ganin taba"? "Eh haka ne Abban kune yazo da ita 'yar uwarku ce a makaranta zai sata zatai karatu saura naji wani yaro ance ya nuna mata wani bambanci kunsan Allah ko saina ma d'a shegen duka kuna jina"? Hada baki sukai "eh mama" "yauwa ku wuce maza ku shirya saiku dawo muci abinci" to suka ce suna wucewa.

Mrs Al'ameen Ahmad ce 😘 😘.

ZAMU KWANA ANAN SAI ALLAH YA KAIMU GOBE DA RAI ZAMU D'ORA.

Ina godiya πŸ’–πŸ’•πŸ‘πŸ€ sosai reader's da addu'ar ku gare ni Allah ya barmu tare amin.

Wannan page din naka ne dan uwa rabain jiki CPT. SALISU KOLI ABDULLAHI mai tambarin no going backβš”οΈπŸ—‘οΈπŸ‘ŠπŸ’£πŸ”«πŸ’₯🦁.

#VOTE
#SHARE
#COMMENTS
#FALLOW.

yusrahmusa65@gmail.com MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY πŸ’ƒπŸ‘ŒπŸ‘.


*Writer*
1πŸ‘‰Yarima Abdul-maleek
2πŸ‘‰ Rayuwa biyu
3πŸ‘‰ Safreeyyah
4πŸ‘‰ d'an millionaire
5πŸ‘‰ Royalty
6πŸ‘‰ Husnah ko Badiyat
7πŸ‘‰Haskena sauban
8πŸ‘‰ Minah-Umer
9πŸ‘‰ Kowacce'kwarya
10πŸ‘‰ Zuciyar Aliyu
11πŸ‘‰ Dama kece
12πŸ‘‰ Me kamar sarki
Loading A GIDAN TALAKA

Ga wanda yake bukata wadannan litattafan kofa a bud'e take kai tsaye ayi min magana tananπŸ‘‡.
08160983083
Chat with me πŸ’»πŸ“±πŸ–₯️.

19~ AL-ALIM
The all knowing
20~AL-QABID
The Restrainer.

10~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Raki'inah.

πŸŒ„TENSITY ND QUARRELπŸŒ„
Episode 19&20
Kwana uku da tafiyar Lami misalin 'karfe sha biyu rana akaji jiniyar motar yan sanda πŸš” ta danno kai garin batai fakin a ko'ina ba sai a kofar gidan Baffah Mamman na gaban motar yace "yalla'bai ga gidan nan" akwai mace yar sanda a cikin su saboda an fad'a musu mace ce za'a kama dan haka itace ta shiga gidan wanda Ramatu najin jiniya ta 'barka danga ko takalmi babu balle hijab ta fita da gudu sallama yar sandar tayi Salamatu dake shara ta amsa mata "akwai Ramatu a gidan nan"? Kai Salamatu ta d'aga "eh akwai amma ta 'barka danga ta fita tanan yanzu" "ok shikenan" ta fad'a tana fita da sauri tace "sir tada mota matar bata gidan wai ta fita da gudu ta bayan gida" tab 360 suka koma cikin motar da mugun gudu suka bi bayanta da yake damuna ce tuni ta 'bace musu sauka sukai a motar suna barbazuwa ko'ina dan binciko ta da wani yaro suka had'u yace "wata mata kuke nema? Gata can tabi wannan 'karamar hanyar tana gudu babu kwali a kanta" basu tsaya jin karashen zancen yaron ba suka bi hanyar tuni sukai mata kofar rago suka ritsata a tsakiya turus tai ta tsaya tana huci yar sanda da aka zo da ita ce ta karasa tare da danko ta dayar tasa mata ankwa kokawa suka fara sai harbe harbe Ramatu take da 'kafa tana burgima da fisge fisge "ku sake ni azzalumai mugayen banza" make mata baki 'yar sandan tai wanda yasa Ramatu sakin kara tana cewa "wayyo Allah na zaluncin yan sanda Allah ya isa ban yafe ba tsinanniya kin make uwark............ Sake make mata baki tai saiga jini cikin tsawa tace "rufe mana wannan ru'babben bakin zaki bayani yau saikin gane Allah da girma yake wallahi bari mu karasa bayan kantar zaki yabawa aya za'kin ta" har lokacin bakin Ramatu bai mutu ba ta harari yar sandan tana cewa "babu abinda kika isa kimin harda bari muje bayan kanta idan kin cika yar halak idan an kulle ni ki dau dan mubud'in kije ki jefa shi a kogi mai ambaliya kaina fito har abada" "shikenan zaki gani zuwa jimawa saikin manta inda kike wahala sai tasa kinje suma kin dawo" yar sandan na fadin haka ta jawota zuwa inda motar su take guri ya cika dam sai nuna ta ake ana gulmar Mamman ne ya d'ebo mata 'yan sanda wulla ta sukai a mota suka tafi sai ihu da tsine tsine take wani d'an sanda yana shirin bugarta da kulke ogonsu ya hana shi cewa ya bari idan sunje can wuya zatasa tai shiru.

Duk abinda ake Ilyah na ji yai banza a cewarsa itace ta jawo rigima ba inda zaije belinta kud'in sa ko biyar bazai ciwon kaiba saidai a sayar da tumakinta a belota amma indai dan ta shine tai ta zaune a bayan kanta😲😦.

Aiko suna zuwa suka hau jibgarta ihu kamar zata fasa ofishin cikin tsawa suka ce "rufa mana baki tunda ke kin zama annoba zamuyi maganinki a garin nan ba me gari shugaban ku ba amma kin raina shi bakya ganin girmansa bari yazo zaki bayani ba ke tantiriya ba"? Ramatu na haki ga gumi jikin ta ya ji'ke tace "a'a wallahi yalla'bai ban raina mai gari ba dan Allah kuyi hakuri na tuba" cigaba suka da tambararta zuwan ogansu yasa suka dakata kallon ta yayi yana Jinjina kai kafin yace "ku 'kyale ta haka ku fito nayi magana da me garin yace gobe zasu zo da mutanen da suke 'kararta" fita sukai suna rufeta Ramatu dake kwance da'kyar ta tashi zaune tana cewa "Allah ya isa na mugaye ban yafe muku ba wallahi kuma halina na nan babu abinda za'a fasa rashin mutunci bakuga komai ba yanzu na fara" ta fad'a tare da gyara zama tana kalle kallen gurin babu komai sai 'kura da datti haushi ne

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login