Showing 114001 words to 117000 words out of 130249 words
ka tsaya kallo ne kaje saiya tafi aikin banxa d'an sakalai kawai" Balarabe baice mata 'kala ba ya fita a gidan kan Indo ta mayar da hankalinta wacce take wanke kwanuka kamar bataji abinda suke cewa ba dariya tai tana jan 'kwafa tace "hummm d'auke kai dakyau lokaci yayi ubanki zaki ci wallahi dan bazan 'kyale kiba har a gidan auren ki bazan bari kiji dad'i ba ai Indo tunda kika shigo hannu na kin shiga uku" banza Indo tai mata bata sake magana ba ta baiwa iska ajiyarta wucewa Asabe tai tana zage-zage ta shiga d'aki murmushi Indo tai tana cewa "humm akwai ranar nadama zata zo a lokacin da bazan saurari d'aya daga cikinku ba keda baba bazan iya yafe cutar dani da kike ba kisa ya dakeni ya zageni ya munana min kamar ba shine ya haife niba hummm babu komai wata rana sai labari Allah yasa 'karshen wahala tane yazo nima nayi matukar damuwa dason barin gidan nan kodan na samu canji nayi rayuwa mai kyau da 'yanci kamar kowanne d'an Adam yake yi.
Shigowar Balarabe yasa ta d'ago tana kallon sa shima itan ya zubawa ido nadan lokaci kafin yace.
"Ina fata kinsan Iluh ba'kon d'an bulani mai turin baro na gidan malam Garbah mai sa'a"?.
Kai Indo ta d'aga jiki a sanyaye tace "eh na sanshi"?.
Sauke ajiyar zuciya Balarabe yai yana cewa "to shine yazo nan yasa akai sallama dani akan yazo nemar auren ki kamar yadda na bada sanarwa a masallaci duk mai son sadaka tun ba'aje ko'ina ba gashi kin samu miji da kina ja'be a cikin gida baki da motsi daga d'aki sai band'aki kin daiji abinda nace ko Iluh ba'kon d'an garuwa na gidan malam Garbah mai sa'a yazo tambayar aurenki kuma na bashi dan haka zai koma gida yaje ya turo iyayensa ayi magana d'an wajen Wudil ne kuma saura tsautsayi yasa ki bari Dalah da 'yan uwanta suji wannan labarin saina kusa kasheki".
Fitowa Asabe tai ta riski karshen zancen da suke caraf ta cafe da fad'in "yo malam tsoron me kake ta fad'a man Dalan banza ta isa hanaka abinda kai niyya 'yarka ce Indo ka fita mu'kami da ganin dama dole sai yadda kace ko abinda ka yanke shine suke kai".
Kai Balarabe ya jinjina "to aini kinsan wanda nake tsoro malam Sa'idu yayan Dalan kinsan tsinannen mutum ne akwai masifa yanzu yana jin wannan labarin sai kinga tsiyar da zamu kwasa dashi".
Ta'be baki Asabe tana cewa "shid'in banza ya isa jada ni? Kaga kabar min komai ahannu na ni kuma nayi maka alkawarin sai Indo ta auri wannan d'an garuwar nan da 'yan kwanaki".
Kai Balarabe ya d'aga "to shikenan na baki wu'ka da nama dama kai da kaya mallakar wuya ne sai yadda kikace".
Murmushin mugunta Asabe tai tana cewa "Yayi ina so zan fita in anjima idan na dawo zamu karasa maganar".
Da alamar tambaya Balarabe yace "zuwa ina"?.
"Zuwa oho tunda so kake sai nace ga inda zanje wai Balarabe zargine ya fara shiga tsakanin mu ko kuwa me?".
"A'a kiyi hakuri niba zarginki nake b...................
"Kai dallacan gafara kaban guri zan fita duk inda nake so a lokacin da naga dama kuma kai baka isa ka hana ba dan Naga yanxu wani sabon raini kake ji dashi🙊 fad'a min uban waye yake hure ma kunne a waje cewa idan ka dawo gida ka wulakanta ni? Kazo tsayar da idonka cikin nawa saboda ga sa'arka tana magana ko"?.
Jikin Balarabe na rawar tsoro yace "kiyi hakuri ni ban d'auka da wata munufa ba" fad'in haka ya juya yana fita a gidan da harara Asabe ta rakashi tana jan tsaki sannan ta juyo da kallonta kan Indo tana cewa "ke kuma mujiya mai ba'kin hali kinji abinda ran'kwal'kwalin😔 uban naki yace sai kad'au shiri ki nemi kayan d'aki dan ko cokali bazai saya miki ba wallahi saina hana saidai daga gidansu Dalah akai miki ko tabarmace" tana kaiwa nan ta shige cikin d'aki" sunkuyar dakai Indo tai tana goge hawayen da yake zubo mata cikin razani da rashin samun madafa saidai da wannan rayuwar 'kuncin ta gwammaci zama da Iluh d'an garuwa ko hakan zai zama sanadin ba'kin cikinta ta za'bi zama cikin bare akan zaman gidansu.
GIDAN MALAM HABU
A'i tana zaune gaban murhu tana dama kunnu ita kad'ai sai magana take "oh ni Aishatu naga ta kaina wannan masifa har ina? Ace yau kimanin kwanakin malam ashirin da biyar da tafiya ace babu ko waiwaye ba d'an aike na tabbata duk tsiya za'a samu wanda zaiyo nan haka nifa shiyasa ban yarda nadau kud'ina na bashi ba da yanzu ya dira ni dan nasan muzai bari a wahala wa yasani ma ko guduwa yai ya barmu ba yanzu zai dawo ba koma har abada bazai dawo garin ba ba'kin ciki ne ya koreshi".
'Dan kallonta Binta tai ganin duk sauran yaran sun zubowa A'in ido suna kallonta tasan ciwon maganar sukaji har Jamilan dan sun tabbata ubansu mutum ne na 'kwarai bazai ta'ba guduwa ya barsu ba ya damu dasu fiye da tunanin mai tunani kafin Binta tayi magana Saude tace.
"Aike A'i yanxu na daina saki a sahun nasu hankali dan da kinsan abinda kike fad'a kodan kunyar 'ya'yansa kya raga masa wani abu malam mijinki ne ba abokin wasanki ba amma duk kalar shashashar maganar da tazo bakinki babu taunawa babu tunani babu ruwanki da 'ya'yansa suna gun tsabar rashin hankali saiki furta a tunaninki kina wa kanki adalci ko kina neman kima da martaba a idonsu? Gaskiya magana ta domin Allah ki canza halinki A'i malam ya mana komai a rayuwa kuma mukam bamu zama butulu masu manta kyautar jiya gareshi ba addu'ar mu a kullum Allah ya rufa masa asiri ya d'auke nauyinmu kamar yadda yake fata sannan matukar baki canza ba ina mai tabbatar miki a gaba zaki nadama".
Wani karkataccen kallo A'i taiwa Saude tana ta'be baki tace "wallahi 'karya kike babu ranar da zata fito wacce zanyi nadama a cikin ta bafa wata uwar nake d'auka ba a gidan nan ba sai wahalar rayuwa jira ma nake Allah ya dawo da malam d'in yasan yadda zaiyi Dani dan na gaji da zaman kitiko-koko kukan jakin matsiyaci kullum baci gaba sai tauyewa nake niba leda ba zai dawo ai nikam bazanci gaba da zama dashi ba sallamata zaiyi gara na koma rayuwa gidanmu tunda ga 'kanina Rabi'u yayi aure kuma Saminu ma zaiyi ko a jikinsu na laru nasan kwanuka biyu dai zan 'koshi kuma ace safe da rana da dare Allah ya dawo dashi daga tafiyar idan kuwa nan da 'karshen watan nan naji shiru zan had'a 'yan kayayyaki na nabar gidan tunda zaman ba dole bane ku da ya zame muku farilla sai kuci gaba da zaman jegon jaka".
Kai Saude ta girgiza tana kallon A'i tace "ai shikenan Allah ya rufa mana asiri mukam muda malam mutu ka raba kome ya zama baza mu gujeshi ba" .
"Hum kada Allah yasa ku gujeshi man waiku 'ya'yan masoya ko? Uhm kuje ku 'karata nikam kad'an nake jira bazan iya ba" A'i na rufe baki Dijeh ta shigo gidan da sallama kamar an jefota tazo taiwa A'i tsaye aka tana mi'ko mata hannu tace"
"A'i bani kud'ina zan tafi kasuwa"?.
Kallonta A'i tai tasan yau bata zo da mutunci ba tunda bata bari an gaisaba ta tambayi kud'i katse mata tunani tai "A'i nace ki bani kud'i na"?.
Mi'kewa A'i tai tana shiga d'aki ta dauko ba magana ta bata 'kirgawa Dijeh tai ganin bai cika ba tace "ya haka ina sauran"? 'Dan tsaki A'i taja cikin takaici tace "bani dashi iya abinda ke gareni kenan d'aka da waje na d'auko miki bani da ciko nima yana gurin mutane" ri'ke kugu Dijeh tana cewa "Ina ruwana da wasu mutane dama nace ki basu bashine a hannunki nasan kud'i dan haka malama ciko min zan tafi"? Harara A'i ta sakar mata tana kau dakai tace "nace miki bani dashi sata kike so nayi na biyaki kome"? .
"Yo Ina ruwana kiyo satar ki biyani kayana meye damuwa ta"?.
Wani kallo A'i tai mata "nayo sata na biyaki kud'i? Saboda ga wacce batasan ciwon kanta ba ko to ki bari watan tsoron naki bai kamaba dan wallahi bazan takura kaina ba sai ranar dana samu zan biya da uban wa yace ki raba mana bashin"?.
"Au haka kika ce jimin tsinanniyar mace ni zaki jefa da sharri wato nai miki dare kinmin rana na rufa miki asiri ni kin bankad'a nawa na lullu'be ki lokacin da kike jin sanyi shine yanxu kin bud'e rufar zaki jefani a uku dama yarda da mutumin daya fito daga gidansu mai guga (baban A'i🤫) shirmen banza ne"
A fusace A'i ta mi'ke tana cewa "a'a kada ran kada han kada mai gani ya taka makaho Dijalle kinzo inda hankali na bazai dauka ba me kike nufi da cewa yarda da wanda ya fito daga gidanmu shirmen banza ne kina son nunawa duniya mu maciya amana ne kome"?.
A masife Dijeh tace "ashe kin gane abinda nake nufi shine dan gulma kike tada ha'kur'kura da jijiyoyin wuya a gaban kishiyoyinki dan karsu miki dariya to wallahi A'i bari kiji saikin biyani kud'i na".
Itama A'i cikin d'aga murya tace "wallahi bazan biya ba sai sanda na samu aikin banza aikin wofi matsiyaciyar mata kinzo kin dameni da masifa ki barni da abinda ke damu na".
"Kece babbar matsiyaciya bani ba tsinanniya wacce batasan halacci ba daga yau tayi kai bazan sake baki kayana ba".
"To kuma ni sai akace miki zan sake kar'ba saboda ga wacce kare ya lashewa zuciya tirrr da kayanki dama can 'kaddara ce tasa na d'auki bashin a gurin ki ga mutane nan da yawa masu daukowa saina canza she'ka".
"Ki canza man bai dameni ba nidai kawai kud'ina nake bu'kata kiban zan wuce kina 'bata min lokaci".
"Au ina 'bata miki lokaci danai me? Dama na ri'ke kine kalli ki gani ba tike nai a gun na d'aure kiba zaki iya tafiya".
"Wallahi tallahi kinji rantsuwa ko A'i bazan bar gidan nanba saikin bani cikon kudina ko kiga tsiya".
Ja A'i tai ta ture tana gyara daurin zani tace "wallahi bazan biya ba sai ranar dana samu a shirye nake mu dambu mu juya mu fidda raini dama na dad'e banyi fad'a ba jini na a daskare yake yau saiya tsinka shi".
"Kika ce bazaki biya ba"?.
"Eh bazan biya ba haka nace ko akwai wani abu da kika isayi"?.
"Niko nake da abunyi tunda ni 'yar kasuwa ce bana rasa abinyi" tana rufe baki ta fad'a d'akin A'i tana d'auko sabuwar tunkuya lamba sha biyar data sayo ta dafa abincin saidawarta tayo waje da ita zata fita a guje A'i taje tana kamata da kokawa ganin zata tafi mata da kayan kud'i tace.
"Gidan uban wa zaki kaimin tunkuya ajiye tunda ba tsofinki ne suka saimun ba" A'i na rufe baki taji saukar mari tasss a fuskarta 'kara ta saki dan batai zato ba kawai zafin marin taji kokawa suka fara sosai suna dambe-dambe da dake-dake baji ba gani da sauri Saude ta Binta suka zo suna rabasu sai fisge-fisge A'i tana da kururuwa "ku barni in rama akan me zata mareni na 'kyale ta wallahi saina fasa mata baki" huci Dijeh keyi tana kallon ta tace "dan Allah ku saketa naga da yadda zata fasa min bakin wallahi yau da saina targad'aki saidai ki kwana a asibiti".
"Saidai ki targad'a uwarki wallahi saidai ki targad'a uwarki kisa tai kwanan asibiti amma badai niba inke mayyace nafi karfinki kurwata kurrr nama na yai miki d'aci" A'i tana rufe baki Dijeh ta sake kawo mata raruma da sauri Binta shiga tsakanin su tana girgiza kai tace.
"Kinga dan Allah Dijeh kiyi hakuri jeki tafi fad'a ba girmanku bane babu dad'i irin haka mu kanmu bama jin dad'in balle kuma kalli yaran nan suna kallonku dan Allah kije ki tafiyarki zata biyaki kud'inki".
Hayayya'kowa A'i tai tana cewa "wallahi bazan biya ba ta mari kud'inta".
Kallonta Dijeh tai zatai magana Binta tace "a'a basai kince komai ba kiyi hakuri dan Allah kije" hararar A'i tai ji take kamar ta sake sha'kota ta turmushe ta a 'kasa ta daki kud'inta "taya zan tafi kina jinta fa abinda take cewa danta raina min wayo" kai Binta ta d'aga "eh naji Dijeh amma nace dan Allah kiyi hakuri ki tafi zata biyaki kud'inki" "shikenan zan mata lamuni kamar yaushe zan dawo"? Tun kafin Binta tayi magana A'i tace "kefe ko uban lamani zaki wallahi tallahi bazan biya ba" kai Dijeh ta jinjina tana yin sama da tukunyar ta d'ora aka tana cewa "shikenan zan tafi da tukunya zuwa nan da ranar litinin idan baki aika min da cikon kudina ba zan sayar na d'auka na kawo miki sauran".
"Aiko wallahi kika kuskura kika sayar min da tukunya hukuma ce zata raba mu dan saina d'ebo miki 'yan sanda".
Hanyar fita a gidan Dijeh tai da tukunya aka tana cewa "yan kul'ke ko 'yan kokara zaki d'ebo min ba yan sanda ba kin dad'e baki d'ebo suba zanga tsinannan dazai tsaya miki banga shegen daya isa hana na sayar da tukunyar nan ba dama wanda nakejin kunya malam Habu ne dalilin sa nake d'aga miki 'kafa yanzu tunda baya nan humm mu zuba nidake d'an halak ka fasa" tana kaiwa nan tayi tafiyar yayin data bar A'i sai masifa take duk ta cika gida da hayaniya sai tsine tsine take ta kasa zama ta shiga d'aki ta fito tayi nan tayi can kamar wacce ta zare takaici ya gama cikata sukam babu wanda ya bata baki ko yace tayi shiru domin gamuwa tai da gamonta.
Aliyah na zaune da Dauda tana masa tsari Dalah tai sallama tana karasowa ta nemi gurin zama ta zauna da 'yar fara'a a fuskarta ta 'karfin hali tace "a'a Dauda yaushe a gari dama ka dawo ne"?.
Kan Dauda na sunkuye bai d'ago ba sakamakon a fusace yake da'kyar ya tattara nutsuwar shi cikin had'a ba'ki yace.
"Jiya na shigo da dare ina kwana"?.
"Lafiya kalau Dauda ayya kace jiya ka dawo cikin dare to sannu da dawowa 'yan Osun kuna can abinku kuna shan dad'i kin barmu a 'kauye 'boye cikin lungu mun zama kifin rijiyoyi".
Ganin wasan da take masa bai d'ago ba kuma a iya saninta da dane sosai zai biye mata suyi tayi yasa ta d'an kalli Aliyah tana cewa.
"Lafiya kuwa naga yayi shiru haka ban saba ganin irin wannan yanayin a tare dashi ba fatan ba wani abu bane"?.
Murmushi Aliyah tai daidai Dauda ya mike tace "Dauda karkaje gidan nan nasanka da zuciya yanxu sai kaje ka faffake shi dan haka ban amince kaje ba".
Dakatawa Dauda yai muryarsa a fusace yace "ba gurin sa zance ba" kafin Aliyah ta kara magana harya fice da sauri kai ta girgiza tana cewa "oh Allah kafi 'karfin abinda yafi 'karfinmu nikam wannan zuciya taka Dauda Allah yasa kar ku had'u da malam Balarabe nasan baza'ai ta dad'i ba".
Da mamaki Dalah tace "Balarabe dai? Amma ba wanda na sani ba"?.
"Shi dai Dalah".
"To meya had'asu daga dawowar sa jiya"?.
"Nice na fad'a masa cewa ga abinda Balarabe yake shirin yiwa Indo yana tallar sadakarta alhali baisan yaron ba kawai dan duk shekara yana zuwa shine zai mata auren dole dashi".
'Dan shiru Dalah tai ranta babu dad'i ta kalli yayar tata tana cewa "to ya zamuyi da 'kaddara yaya Aliyah a jiya da abun nan ya faru yaje gida ya sameni da maganar wallahi yaya Aliy da'kyar nai bacci".
"Zaki kasa bacci man Dalah abun kam da ciwo muma yake damun mu balle ke mahaifiyarta ni yanzu so nakeyi asan yadda za'ai Indo tazo gidan amma nasan tsinanniyar Asaben nan bazata barta ba matukar Balarabe yana gidan a ba'kin halinta ma kila ta jawo ya mata duka".
"Daya zata barta yaya Aliyah ba'kar wahala ce nasan tana can tana shanta tunda uban ta an gama dashi Allah masanin irin lalacewar datai yanzu ina gidan ma meye balle ba idona".
Kai Aliyah ta girgiza tana cewa "kada ki damu in Allah ya yarda bazata auri wancan yaron ba na gama magana da Dauda cewa shizai aureta domin bazan bari kawai ba'asan yaro ba a d'auki Indo a bashi yanzu taya zan samu Indo tazo nan gidan inason magana da ita".
Shiru Dalah tai cikin tunanin ta yadda za'ai tazo d'in zuwa wani lokaci ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Aliyah tace "gaskiya da kamar wuya Balarabe baya barinta taje ko'ina bawai dan kare mutuncinta ba yake haka a'a kawai dan Asabe ta mayar da ita baiwa a gidan shara girki wanke wanke dafa mata abincin sayarwa d'ebo ruwa kai abun ba'kin cikin na harda wankau d'in mutane yanzu naji Sahurah makofciyarsu ta fad'a min wai suna kaiwa wankin kud'i gidan kuma Indo ce takeyi".
Cizon yatsa Aliyah tai tana cewa "tabd'ijam amma Asabe kwai tsinanniyar mace insha Allahu 'karshenta bazai kyau ba saita girbi abinda ta shuka karki damu Dalah zansa malam yaje yai magana da Balarabe cewa ya soke maganar wancan yaron Iluh tunda iyayensa ba'a gari suke ba kuma dama ba wani saninsa akai ba za'a dauki yarinya kawai dan zalunci a bashi saboda rashin galihu to tana da mai tsaya mata Dauda zai aureta zata fita daga 'kunci da wahala".
Cikin jin dad'i da nuna farin ciki Dalah tace "na gode sosai yaya Aliyah Allah ya bar zumunci wallahi harnaji dad'i da kikace Dauda zai aureta jiya da'kyar nayi bacci shima ban samu nayi ba sai jikin asuba".
"Humm ke dai kawai bari komai yazo karshe Allah ya rufa asiri".
"Amin Dalah tace fuskarta wasai ji take kamar wani 'katon nauyi aka sauke mata akanta tsabar murna tasan indai aka ce Dauda ne ya aureta wahalarta ta kare itama yanxu zatai rayuwa irin ta kowa ta huta 'kuncin gidan uba.
MRS ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD CÊ😘.
Masha Allah alhamdulillah na gode sosai fans d'ina a gaskiya ina yinku sau ba adadi kaunarku gareni tamkar garkuwace ina son ku da dukkan zuciya ta💞🤙.
Sai Allah ya kaimu gobe darai da nisan kwana zamu tashi inda muka tsaya🙅.
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋🤟.
Banda kamarka ya rasulullah 🥀 a duniya banda kamar ka ya rasulullah a lahira 😢 ya sarkin dayaiyi sammai kassai gabadaya babu abinda babu ikonka jikinsa kulliya inkaso na raira wa'kar kobabu kafiya ga Manzon da kayyiwa wahayi ya hijrah.
TYPING 📲
LITTLE ZARAN