Showing 75001 words to 78000 words out of 130249 words

Chapter 26 - ME KAMAR SARKI

  

04 Oct 2024

17629

yake har tasa malaman sukai sabo dashi suka sanshi sosai sune silar da aka dawo kiransa da malam Habu yan gari na masa isgili wai kodai yana cusa kaine dan su d'auke shi koyarwa.

A wannan garin kuma da akwai wani mahauci ana kiransa 'kwalisa yara suka samasa sunan sakamakon idan yaje rafi yayi wanka duk sai jikinsa yai farin ta'bo da farar kasa kuma idan ya dawo gari saiya ri'ka tafiya irin ta yan gayu yana doro yara suna tsokanarsa kullum idan d'aliban sun tashi shi kuma nan ne gurin zaman sa wata ranar har kwana yake kuma gashi a lokacin sanyi ne yana kwance da dare sanyi ya dameshi ya kasa barci sai juyi yake yana ma'kyar'kyata tashi yai akwai wani guri ta bayan makarantar da aka jibge kara da yawa kawai yaje abinka da mahaukaci ba hankali ya dauko ashana a aljihunshi ya kunnawa karan wuta dan ya samu yaji d'umi tun wutar tana ci kad'an kadan hartai karfi yadda shima ta dameshi gashi dare yayi babu mutane jin zafi a jikinsa yasa shi matsawa daga gurin yana dariya yace "ina yara kuzo muyi 'kwalisa na kunna haske kun ganshi yana yawa kuzo muyi 'kwalisa na iya had'a haske" ya karasa maganar yana rawa da tafi shi kadai sai shirmensa yake yayin da wuta taci gaba da tsiri har farfatsi take haka ta fara kama makarantar nan ga gidajen garin kusan duk dangan kara yafi yawa ga iska da ake mai karfi watsuwar da wutar take yasa ta fara kama ko'ina gidanjen kusa da gurin farkawar wani mutum ganin hasken daya sa'ba hankali yasa ya fito da sauri daga d'aki zaro ido yai yana raraka wani uban ihu.

"Subahanallahi innalillahi wayyo Allah jama'a ku tashi wuta ta kama shikenan tamu ta 'kare" da gudu yayo waje yana kara zunduma wani ihun "ihuuuuh jama'a ku tashi gobara ta kama kara dan Allah ku farka" nan da nan mutane suka fara tittid'owa suna fitowa gari ya rud'e da salati kowa ya rasa inda zaisa kansa sai ruwa suke de'bowa suna watsawa amma kamar basa zubawa sai kara tsiri take kamar zata ta'bo sama ruwan gidaje ruwan rafi ruwan rijiyoyi haka suka ri'ka kwararawa da'kyar suka samu wutar ta mutu bayan tayi musu mummunan ta'adi duk ta kone gidajen dake makotaka da gurin babu abinda ya tsira sai mutanen gidan da yan kayan da suka samu nasarar fitowa dashi.

Washe gari haka gurin ya zama ba'ki'kirim bayan makarantar ma da rufin ta duk ya 'kone jama'a ta taru an cika guri sai kallo ake babu wanda yasan ya akai wutar ta tashi dole suna bukatar taimako amma basa da wani tsayayye a garin me shige musu gaba haka suka dauki tsawon lokaci suna fama shan wahala musamman wadanda gidajen su ya'kone makaranta ma haka suka cigaba da karatun ba'a gyara ba yau da gobe tafi karfi wasa ganin zasu shiga tsaka mai wuya domin akwai kayan amfanin gonakin su da suka 'boye a cikin karan gashi ya kone sun dawo fama da 'karancin abinci yasa liman din garin sukai hadu sukai shawara aka za'bi manya a garin suka kai kokensu karamar hukuma cewa ga abinda ya same su suna neman tallafi daga can aka d'ebo wakilai domin suzo su gani harda 'yan jarida aka zo suka danyi tambayoyi daya wutar ta tashi sannan sukai wa gurin video da makarantar sannan bayan su koma suka fad'i dukkan abinda suka gani lallai mutanen garin na bukatar taimako ba karamin 'barna wutar tayi musu ba, dole aka dakata dayin makaranta harsai an gyara kafin aci gaba domin gyaran zaici kud'i sosai ga 'konewa gidajen mutane.

Kamar yadda 'yan jaridar nan suka dauki video suna zuwa suka yad'a shi a gidajen television da radio mai martaba yana zaune yana ganin labaran hankalin sa ya tashi wannan abun ya faru amma bai sani ba taya zai zauna lafiya indai irin wannan abubuwan suna faruwa ransa ya 'baci sosai don gani yake maybe sakacin Governor ne domin ai duk tsiya yasan da garin tunda a campaign yaje ya musu za'kin baki gari ko gida daya ne indai lokacin campaign ne ana zuwa dan haka yasan da garin amma ace harsu shafe tsahon watanni takwas da gobarar babu wanda ya tallafa musu abar ta batun makaranta amma magidanta fa wadanda gidajen su ya 'kone a ina suke kwana? A layi ko kwa a ina? 'Daga waya yai fuskarsa babu alamar walwala ko wasa yana bada umarnin lallai yau d'in nan yana son ya gana da gwamna, yadda ya bada umarni haka ne ta faru da dare misalin goma suka samu ganawa mai martaba da Governor ya nuna 'bacin ransa sosai yayi fad'a gwamna ya nuna masa cewa ba laifin sa bane shima bai sani ba wakilan 'kananan hukumomi ne basa aikinsu yadda ya kamata dan haka mai martaba yace lallai gobe ko shi bazai samu damar zuwa ba ya tura wakili zaisa 'kaninsa Alhussain su tafi tare a kai musu tallafi na kud'i sutura da kayan abinci amsa masa gwamna yai sukai sallama tare da alkawarin zai tura wakilin sa gobe suje garin tare.

MRS AL-AMEEN AHMAD CE๐Ÿ˜˜.

See u next time, nagode masoya we will meet again ๐Ÿค—๐Ÿค—.

Sai Allah ubangiji mai duka mai yau da gobe jallo mafi girma ya kaimu gobe da rai da nisan kwana ๐Ÿ˜Ÿinai wa dukkan masoyana barka da wuni da fatan alkairi ๐Ÿ’“๐Ÿ’•๐Ÿ’ž.

YUSRAH MUSA ABUBAKAR ๐ŸŒน๐Ÿค™๐Ÿ‘Œ MAI TAMBARIN YMA DUTSE NEW WORLD ๐ŸŒ NEW LIFE ๐ŸŒŒ ANDA NEW STYLE ๐Ÿ‘Œ SABUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DAD'I YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN LAFIYA JIGAWA๐Ÿž๏ธ๐Ÿž๏ธ๐Ÿ—ป.

See๐Ÿ‘€ u next morning ๐Ÿค™.

Mrs Al'ameen Ahmad ce ๐Ÿ˜˜
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

TYPING ๐Ÿ“ฒ Thus, Jun5/6/24 YUSRAH MUSA ABUBAKAR ๐ŸŒน๐Ÿค™.


๐Ÿ’ŽMe kamar sarki ๐Ÿ’Ž



WhatsApp no:234 905 527 3614.
Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ.

๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธIna kake d'an uwa rabin jiki ha'ki'ka ka cancanti jinjina ๐ŸŽ‡๐ŸŽ‰ ina maka barka da wannan lokaci fatan alkairin Allah yakai maka duk inda kake Amin ๐Ÿ‘๐Ÿ‘.
๐Ÿ’•SALEEM MUSA ABUBAKAR ๐ŸŒนโœŒ๏ธ.

Sulaiman Ibrahim Usman
Usman Ibrahim Usman
Abubakar Musa Abubakar
Ibrahim Musa Abubakar
Fatima Musa Abubakar
Husnah Ibrahim Usman.

KU TAHO MASOYAN 'KWARAI๐Ÿคฃ๐Ÿคฉ๐Ÿ˜œ.

MARUBUCIYA๐Ÿ“š๐Ÿ’ถ๐Ÿ‘‡
โœ๏ธ Yarima Abdul-maleek
โœ๏ธ Rayuwa biyu
โœ๏ธ Safreeyyah
โœ๏ธ'Dan millionaire
โœ๏ธMinah-Umer
โœ๏ธDama kece
โœ๏ธ Royalty
โœ๏ธ Husnah ko Badiyat
โœ๏ธ Zuciyar Aliyu
โœ๏ธ Haskena Sauban
โœ๏ธA gidan talaka
โœ๏ธKowacce 'kwarya
โœ๏ธMe kamar sarki.

35~As-shakur๐Ÿ’•
The grateful
36~Al-Aliyu
The Sublime ๐Ÿ’•

17~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Shakirnah .

๐ŸŒ„ULCERATION ND ASTONISHED๐ŸŒ„
Episode 35&36
Washe gari Aisha da Jamila ba lafiya anyi cinye cinyen kayan mai'ko bayamma ta tashi Asma'u kuma bata nan sunyi tafiya ita da Saude sai sati mai zuwa zasu dawo iya Amatu yanzu malam Habu yake kaiwa makaranta dan haka baya kaita a mota saboda ita kad'ai ce mashin d'in haya yake hawa ya rakata kullum yauma kamar yadda ya saba yana zaune a kofar d'akinsa yana jiran ta ganin shiru bata fito ga lokaci yana dad'a 'kurewa kuma dama yau sun makara rana ta d'ago sosai kila ma period d'aya ta wuce d'an 'kwalla mata kira yai.

"Binta wai ina maman nawa ne bata fito ba? lokaci fa yana kara ja karta makara a dake mun ita bazan ji dad'i ba".

Fitowa Binta tai da cooler 'karamar irin ta basket d'in yan makaranta bayanta Amatu sanye da uniform lokacin shekararta shida d'an zuba mata ido malam Habu yai kafin ya sauke numfashi yana cewa "ubangiji Allah ya d'aukaki rayuwar ki mamana ina fatan ki zama wani abu nan gaba wanda bani ko Binta ba al-umma da yawa su 'karu dake" murmushi Binta tai cikin jin dad'i tace "insha Allahu addu'ar ka zata kar'bu amma irin wannan kallon haka da kake mata kamar akwai abinda kake tunani domin na riski lokuta da dama idan kuna tare da ita sai naga ka zuba mata ido meyasa"? Rike hannun Amatu yai yana kar'bar cooler breakfast d'inta ya mi'ke zasu tafi yana cewa "eh dalili shine idan ina kallonta zuciya ta tana samun nutsuwa da kwanciyar hankali shiyasa koda yaushe nake addu'ar Allah ya bata nisan kwana lallai soyayyar wannan yarinyar a cikin rai da jini na take yawo Binta ina son yarana kuma dukkan su daya suke a gurina amma fa maganar gaskiya nafi sonta" ya karasa maganar yana sake rike hannun nata dakyau yana sake jin sanyi yana ratsa shi 'yar dariya Binta tai cikin tsokana tace "soyayya tasa ka manta da fitar lokaci kar abinda kake gudu ya faru ta makara a mata bulala a gabanka" dafe kirjinshi yai yana mata hararar wasa yace "Aiko yau damun kwashi damben tsiya da malaman nan dan wallahi nad'e hannun riga da 'kafar wando zanyi mu daku dasu sai inda karfi na ya 'kare" dariya sosai Binta keyi tace "kai da anyi abun kunya kun saba dasu fa" jan Amatu malam Habu yai suka fara tafiya yana cewa "sabo da kaza๐Ÿ”baya hana a yanka ta ayi farfesun ta dan kawai mun saba saina zuba musu ido su dake ta wallahi ko an shiga aji haka zasuyi hakuri su barta dan yau d'aya dai, mu mun wuce" to Allah ya tsare" Binta ta fad'a tana shiga d'aki domin duba jikin su Aisha dan itama A'i bata gidan ta tafi dubiyar wani d'an uwan su da mota ta bugeshi ya fad'i a mashi yaji ciwuka.

Lokacin da malam Habu ya fito ba kowa shiru garin da yake dama tun wuri masu mashinan suke ficewa wajen 'kauyen dan sufi samun kud'i duba gabas da yamma yai nan dai ba kowa ga tsewa bazata kaisu ba indai ba hakura zatai da zuwa makarantar ba yau daukarta yai ya fara tafiya da ita dan yafi sauri da nufin idan ya samu me mashin a hanya sai su hau idan kuma bai samu ba nan da awa yaje bai bar anguwar tasu bama ya hango Dauda zai fita d'aga masa hannu yai amma bai gano shiba d'an tsaki yai yana cigaba da tafiya ya fito bayan gari ya sake had'uwa da Daudan ya shawo kwana da alama akwai abinda yake nema dan a hankali yake tafiya yana kallon kasa dakatar dashi malam Habu yai.

"Dauda lafiya ina zakaje haka ina d'ago ma hannu baka ganni ba"?.

Kashe mashin d'in Dauda yai yana sauka yace "wallahi kud'i na zubar dubu biyar kuma ba nawa bane kud'in babah ne ta bani na saro mata goriba a kasuwa bari nabi hanya a kafa ko zan samu" to malam Habu yace yana d'ora Amatu akan mashin d'in dake tsaye da kamar minti goma ya dawo da ganin fuskarsa bai samu kud'in ba kallonsa malam Habu yai "ka samu ne"? Kai ya girgiza "a'a wallahi ban ganshi kuma yanzu fitowa ta a gida kenan gari shiru ban ci karo da kowa ba balle na tambaya shikenan ya zama asara muje na kaiku" hawa suka ya tada mashin sukai gaba zuwa makaranta dama kuma yaune kasuwar garin shiyasa 'kauyen su malam Habu yai shiru kowa ya taho cin kasuwa sauke su yai a bakin shiga makarantar hannu malam Habu yasa a aljihu yana dauko kud'i ya bashi dubu biyar d'in yana cewa "ri'ke Dauda kaje ka sai mata goribar ka kai mata karka nuna kud'in ya fad'i sannan ga wannan kud'in aca'barka" ya d'ora masa d'ari biyu akai baki bud'e Dauda ke kallon sa da mamaki saidai ba abin mamaki bane tunda dama ya saba kyauta halin malam Habu ne ko ma'kiyi zai bada sheda saidai in baya tsoron Allah godiya sosai Dauda yai wa malam Habu kamar bazai daina ba murmushi malam Habu yai "karka damu kaji jeka abinka ai yiwa kaine" wucewa Dauda yai yana sake gode masa yayin da malam Habu ya ri'ke hannun Amatu suka fara tafiya zasu shiga makarantar.

Jin jiniya yasa mamaki ya kama malam Habu to yau kuma me akeyi a cikin makarantar bai gama tunani ba yaga motoci tsala tsala masu kyau da tsada sai she'ki suke suna ta fitowa a jere har daukar ido suke komawa gefe malam Habu yai yana sake ri'ke hannun Amatu dakyau kafin motocin su wuce wata farar mota data fito mai ba'kin glass 'katuwa tsadadda ce ta taka burki a daidai saitin su motar dake bayan farar aka bude murfin ta wani bafade ya fito da gudu yana bud'e murfin farar motar tare da durkusawa cikin girmamawa yace.

"Allah ya taimake ka akwai matsala ne"?.

Kai ya girgiza yana kallon fuskar kyakkyawan matashin saurayin dake hakimce zaune a gefensa ya d'ora 'kafa d'aya kan daya yana sanye da tsadaddun kaya ganin yadda ya had'e girar sama da kasa kamar ba shine ya bukaci su tsaya ba yasa Alhussain yai murmushin rigima irin tasa yana cewa "eh Harun akwai matsala" sake kallon fuskar saurayin yai bazai wuce shekara sha takwas ba amma fa kyakkyawa ne na kwatance kyau kuma irin na larabawa idan ba magana yai ba zaka rantse da Allah baisan meye wani yaren hausa ba.

Mamaki ne ya kama 'kanin mahaifin nasa har yana dafa shi cike da kulawa yace "Asad kana lafiya meke damun ka meyasa kace a tsaya kuma ka "ki magana"? Cikin aji da sarauta ya d'ago yana kallon sa na wani lokaci har Alhussain ya fidda rai bazai ce komai ba sai kuma yaji zazza'kar tsadaddiyar muryarsa mai sauka cikin tsari da dad'in sauraro a hankali yace.

"Ina son magana da wannan".

Inda yake kallo shima Alhussain nan ya kalla su malam Habu ya gani tsaye da mamaki ya kuma kallon Asad domin shi idan ba yanzu ba bai kula dasu ba da har zaice masa me zai masa sai kuma ya ce bari ya 'kyale yaga abinda Asad din zaiyi kallon sauran fadawan dake dur'kushe Alhussain yai yana cewa "ok Harun bud'e masa ya fita" da sauri cikin gaggawa Harun ya mi'ke da gudu ya zagaya 'bangaren ya bud'e masa tabd'i yafi minti goma bai fito ba kafin ya ziro 'kafa a hankali ya fito kai Masha Allah kamar babban saurayi akwai 'kira a tsaye yake zarrr jarumtacce sadauki 'kakkafa yana da manyan ido ga dogon hanci fari irin na larabawa ga pink lips kaiii ya gama had'uwa cikin taku ya fara tafiya cike da nutsuwa zuwa inda malam Habu ke tsaye wanda Alhussain jin hankalin sa bai kwanta ba shima ya fito yana bin bayansa ganin Alhussain ya karaso yasa malam Habu ya saki hannun Amatu yana dur'kusawa cike da girmamawa yace.

"Gaisuwa nake ranka ya dad'e Allah ya baka nasara".

Fadawan dake bayansa ne suka amsa masa "an gaisheka kaima mai nasara ya amsa gaisuwarka" kallon Asad Alhussain yai ganin ya zubawa Amatu ido kuma baiyi magana yasa ya mayar da hankalin sa kan malam Habu yana cewa "tashi" mi'kewa malam yai tsananin mamaki ya kamashi da yake ba iya bambance su ake ba baiyo tunanin ba mai martaba bane 'kaninsa ne lallai ya jinjinawa rashin girman kansu.

Shirun ne yai yawa gajiya Alhussain yai don yaga alama indai ba cewa yai su tafi ba Asad baida niyyar cewa 'kala kuma baida niyyar tafiya yace "Asad kazo mu tafi ko"? 'Dagowa idanonsa yai yana kallon Alhussain kafin ya mayar da hankalin sa kan malam Habu yana cewa "wannan 'yarka ce"? Kai malam Habu ya d'aga "eh 'yata ce" sake jefa masa tambaya yai "mene sunan ta"? "Sunanta Hauwa" d'an rufe ido Asad yai jin sunan mahaifiyarsa kai Alhussain ya jinjina yana cewa "shikenan fad'uwa tazo daidai da zama sunan maminsa ne" fuskar malam Habu da mamaki yace "masha Allah".

Bud'e ido Asad yai yana kallon malam Habu yace "zaka bani ita"? A tare Alhussain da malam Habu suka zaro ido Alhussain na cewa "to fa Asad kamarya zai baka ita matsayin 'kanwa ๐Ÿ‘ซ ko mata ๐Ÿง•"? Kai Asad ya girgiza yana cewa "mata" a d'ari Alhussain ya sake zaro ido da 'yar dariya yace "to mata kuma Asad? A lallai mun kusa daukar suruka kwana kusa muna komawa zani yiwa yaya albishir" kallon malam Habu Asad yai "zaka bani ita"? Fuskar malam Habu da murmushi yace "eh zan baka ita indai kana son ta"? A hankali Asad ya d'aga kai "eh ina son ta" "to shikenan na baka ita".

"Asad shirmen ya isa haka kazo mu tafi" Alhussain yai maganar kawai da murmushi fal fuskarsa juyawa Asad yai yana kallon sa kafin yace "ina son zamuyi photo" ya fad'a yana mi'ka masa wayar hannunsa "kayi mana" kai Alhussain ya girgiza yana amsar wayar matsawa Asad yai yana sa hannu ya d'aga Amatu sama yasata a kafad'arsa dariya Amatu tayi cike da yarinta daidai za'a d'au photon shi kuma yai murmushi daukarsu yai yana cewa "kunyi kyau kar lokacin shiga ajinta ya wuce ka ajeta mu tafi" ajeta Asad yai yana shirin bin bayan Alhussain wanda sukai sallama da malam Habu sai kuma ya tsaya yana cewa "shekararki nawa"? Cikin za'ki Amatu tace "talatiin da goma da d'ari ๐Ÿ˜‚".

*KAI ๐Ÿ™† AMATU SHEKARA 'DARI DA ARBA'IN ๐Ÿคญ๐Ÿ˜ฒTAB AIKO BAFFAH BAIKAI HAKA BA๐Ÿคฉ๐Ÿ˜‹*.

Dariyar da ba shiri malam Habu yai yana cewa "shekararta shida" "shekararki shida ni kuma sha takwas idan kika hada da nawa kina da shekara ashirin da hudu kenan" ya karasa maganar yana cire kyakkyawar rigar sanyin dake jikinsa da photon zaki kwance a jiki a 'kasan zakin an rubuta ALIYU ASAD da manyan ba'ki bata yai batare da ya sake magana ba ya juya ya soma tafiya da kallo suka bishi har ya shiga mota aka rufe suka bar gurin tun suna iya hangosu har suka 'bacewa ganinsu.

Sauke ajiyar zuciya malam Habu yai yana kallon rigar dake ri'ke a hannun Amatu sai tashin 'kamshi take yace "Mamana muje ko? Lokaci ma ya matukar 'kurewa da yake yau Juma'a gashi yara har sun fito inaga baifi nan da awa a tashi ba kawai ki barshi mu koma gida yau din kya zo ranar litinin muje a kasuwa na sai kayan miya mu tafi gida" kar'bar rigar yai ya zuge jakar goyon dake bayanta yasaka a ciki ya zuge kafin ya kama hannunta suka wuce.

Kamar yadda malam Habu ya baiwa Dauda kud'in gudun karya sake zubarwa sai kawai ya sayi goribar ya koma kai mata daga baya ya dawo yai hayar da mamaki babarsa ke kallon shi tace "sannu sarki shiririta na baka kud'in goriba saika tafi ka barshi anan ina shara na ganshi a inda ka zauna kuma da ya ka sayo goribar bayan kace baka da kud'i ko bashi ya baka"? Kai Dauda ya girgiza yana zama yace "aini babah na dauka a

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login