Showing 102001 words to 105000 words out of 130249 words

Chapter 35 - ME KAMAR SARKI

  

04 Oct 2024

17602

ba ta dawo gurin su Shaukiyyah duk mi'kewa sukai suna fita anan yake tambayar su ya sukai da doctor Amar akan jikin Khimiyyah Ameer yace.

"Wallahi Abba babu wani sau'ki tana nan a yadda take gara mu fita da ita India muje akwai wani babban asibiti a Chennai mercy hospital ina ganin haka zaifi akan zaman nan ba cigaba, amma me kace Abba"? Kai mai martaba ya d'aga cike da gamsuwa yace "shikenan ranar monday saiku tafi kaida Ajeeb da Annur tare da Hauwa'u Allah yasa a dace kaje a yau zan had'a ka da wani mutum kuyi maganar shi masanin India ne sosai yayi zama acan shekaru da yawa yasan ko'ina zan baku numbarsa zuwa an jima kuyi abinda ya kamata" to Abba Allah yasa idan muka je Khimiyyah ta samu lafiya koda yaya ne amma Abba zan Kira Asad na fad'a masa ya same mu acan saidai kasa baki idan ba haka ba nace nine zan fad'a masa bazai zoba" kai mai martaba ya girgiza "a'a Ajeeb babu ruwan ka dashi kuyi abinda ya kamata kawai" to Abba insha Allahu.

Bayan kwana biyu kamar yadda mai martaba Alhassan yace haka ne ya faru sun shirya tsaf zuwa India amma fa Sultana Hadizah ta dage ta rufe ido tai ruwa tai tsaki akan wallahi bazata yarda a tafi da Sultana Hauwa ba idan kuma ya zama dole tafiya da ita to saidai su tafi tare haka kawai za'a tafi mata da 'ya kuma a rasa dawa za'a had'a su tafiyar ma saida ma'kiyanta taje su 'karasa kasheta acan su dawo mata da gawa saita bisu, shima mai girma Alhussain yace wallahi ya rantse da wanda ya halicce shi bazataje ba idan kuma ta nace saitaje a bakin auren ta Sultana Hadizah ta shiga tashin hankali tayi kuka tayi ihu da kururuwa lokacin da zasu tafi amma haka tana kallo jirgi ya tashi๐Ÿ›ซ ba ita koda suka dawo gida ita kad'ai a d'aki sai yage yage take duk ta birkita d'akin harda gwara kanta a bango tana tsinewa Mami uwa da uba๐Ÿคช.


๐Ÿ—ฃ๏ธHummm duniya mai cike da abinda mamaki๐Ÿ˜ฏ Sultana Hadizah babu wanda yasan inda rana zata fad'i๐Ÿ˜ ๐Ÿ˜ฌ mental ur selfโ˜น๏ธ๐Ÿ˜–๐Ÿ™„ if u go to the river๐ŸŒŠ๐ŸŒŠ don't swim๐ŸŠ it can carry u away๐Ÿƒ๐Ÿ„

๐Ÿ•๏ธ'KAUYE๐Ÿ•๏ธ
Malam Habu yana zaune akan tabarma a kofar d'akinsa yaro ya shigo da sallama yana cewa "wai malam Habu yazo inji Malam Sadi yana waje" malam Habu yana shirin magana A'i tace "tofa Malam nesa tazo kusa inkaji Kira an samu amma banda kiran d'an sanda Malam kayi sauri karya wuce ka Allah yasa zakkar shinkafa ko dawa ya kawo maka muma mu samu canjin d'an wani lokaci mu huta da wannan ba'kin cikin cin gero da muke fama dashi kullum mu ba kaji ba koda yaushe mu tabbata a tsatstsagar tsaba" wani kallo Malam Habu ya mata zaiyi magana Saude tace "Malam dan girman Allah karka kulata batasan me take ba ka mata uzuri" kai kawai ya girgiza bai ce mata 'kala ba kamar yadda Sauden ta ro'keshi yasa takalmansa ya fita mi'kewa Saude tai bayan ta gama wanke shinkafar saidawa zata zuba a wuta tace.

"Gaskiya A'i ki gyara halinki wannan d'abi'ar da kika d'auka bazata amfanar dake da komai ba kar ki zama butulu man mai manta kyautar jiya meye baki samu ba meye Malam bai bamu ba lokacin da yake da wadata har iyayen mu da dangin mu sun moreshi shin ke bakya jin kunya idan kina fad'a masa magana? ki canza kullum dai ina fad'a miki".

Wata uwar harara A'i ta sakar mata tana cewa "ah sannu da 'ko'kari Saude wato nan d'in wa'azi kike min kome"? Kai Saude ta girgiza "a'a ni bance miki haka ba amma dai ina gargad'in ki ki gyara" a masife A'i tace "bazan gyara ba na fad'a ai da ta wuce gaba ake hange kowa yana jin dad'i a 'kauyen nan amma banda mu ko gidan biki muka shiga zakaga ana kallon mu kamar wanda mukai abun kunya saboda mun fita dabam matan fa'kiri๐Ÿ˜ณ kowa da sutura mai kyau banda mu sai kod'dd'un kaya da matattun gyale da hijabai kowa da 'kibarsa mu kuwa a 'kai'kashe kamar 'kanzo hum wannan ce rayuwa kuma a hakan har zakice min bulutu? Na butulce d'in kiyi abinda zaki aikin banza kawai" ta karasa maganar tana jan tsaki babu wanda ya sake mata magana daga Saude har Binta sai takaici daya rufe su Asma'u da suke gefe suna d'inkin hula domin tunda Amatu taje Mopal-Base ta koya da zata zo gida ta sayo musu yanki da zararrika tana zuwa ta ri'ka koya musu yanzu da wannan hular sukan taimaki iyayen su harma su d'anyi abin kansu.

Suna nan zaune Malam Habu ya shigo da fara'arsa yana cewa "ina kuke Saude Binta A'i kuzo nan yanzu ina son magana daku ga dama ta samu" A'i ce akan gaba da kujera a hannunta da gudu tazo ta zauna tana cewa "nesa tazo kusa meye yazo kusa Malam irin wannan fara'a kodai kasar zaku bari"? Ta karasa maganar cikin sha'kiyanci kai ya d'aga mata daidai sauran su zauna yace "eh 'kasar zamu bari idan Allah ya kaimu jibi da rai nida mutumina Sadi" har had'a baki sukai wajen cewa "kasar waje dai Malam amma wacce kasar waye ya biya muku kud'in jirgi"? Murmushi malam Habu yai yana kallon su dad'i ya gama cika shi yana hasko yadda rayuwar su zata canza kwana kusa su dawo jin dad'i kamar da yace "ba'a jirgi zamu ba a mota ne" da mamaki Binta tace "amma Malam wacce kasar ce a mota daga nan ko Niger"? Kaiya girgiza "a'a Binta ba Niger zamuje ba Camaron ne".

"Amma Malam sana'ar me zakuyi"? "Nima ban sani ba yace dai ana samowa kud'i sosai acan saimun je komeye zamuyi fatana Allah yasa muje a sa'a na samu kud'i kona rufin asiri ne saboda ku kunyi ha'kuri ni nasan da haka amma kusa ranku a inuwa ku taya ni da addu'a Allah ya kaini a sa'a idan naje ko nima na samu d'an wani abu nawa harna manta rabo da naga biyar a hannu na wai da sunan tawa humm" ya fad'a abun na masa ciwo arai kafin ya sake d'agowa yana kallon su yace "amma shikenan nan babu komai kowanne irin aiki na samu duk wahalar sa zanyi saboda ku addu'ar ku nake nema kuyita min Allah ya dafa min ya zama shine jina da ganina da kafafuna sannan ya zama hannuna dazan ta'ba abu dashi zanyi kokari zan jajirce nasan ba'a maraya๐Ÿ˜ฃ sai rago".

Had'a baki sukai suna masa addu'a harda su Aisha dake gefe tuni suka aje d'inkin hula suna sauraren su farin ciki ya gama cika su ji suke dama Amatu tana nan da zatafi kowa nuna murnarta sun tabbata sai tayi kuka.

Cigaba malam Habu yai da cewa "to sai maganar kud'in mota kunsan dole zaiyi tsada ni kuma dai biyar ban ajiye ba a cikin ku akwai wacce take da kud'i ko dubu biyar ne ta ara min kafin na dawo inyaso ko gurin yaya Ilyah sai naje na ro'keshi da Allah ko zanji tausayi na ya bani 'yar dubu goma shima na rage".

Zaro ido Binta tai tana kallon malam Habu tace "amma Malam kana da tabbacin zai baka"?.

Kai ya girgiza "a'a nima ban sani ba sai naje bana ji a jikina zai bani amma ya zanyi marar abu baya zuciya๐Ÿ˜” da inada gurin wanda zanje na kar'bo wallhi ko kallon yaya Ilyah bazanyi ba to amma yanzu idan nace bazanje gurin sa ba gurin wa zanje duk garin nan bani da kowa sai shi sai 'ya'yan yaya Sabi'u su kuma suna marayu abin kunya ne ina 'kanin ubansu ban basu ba nake nema a gurin nasan ba iya garin nan ba har 'kauyukan dake kusa damu sai sun taru sun tsine min".

"Ayya malam ka daina cewa haka insha Allahu yaya Ilyah zai taimaka maka".

Sauke ajiyar zuciya malam Habu yai yana cewa "umh Allah yasa amma banga alama ba, yanzu anan zan samu a gurin ku ne"?.

Da sauri A'i tace "a'a nikam gaskiya malam ta yara ina olo (tsoro) kar nace na tafe d'an kud'in da nake juyawa kazo tafiya batai kyau mu shiga uku mu sake dulmiya cikin wata azabar talaucin kuma nidai kud'i na baifi dubu sha biyar ba kuma wani duk yana gurin 'yan bashi baza ka samu guna ba" ta karasa maganar tana soke d'aurin kwali.

Kai malam Habu ya jinjina yana cewa "ai dama bake na tambaya ba" shiru A'i tai tana murgina kai Saude tace "wallhi malam kud'in gurina yanzu baifi dubu biyu ba jiya yaya Saleh ya turo matar Ladiyo da dare yace na ara masa dubu ashirin na d'auka na bata gashi yau kana so rashin sani yafi dare duhu"

"A'a karki damu babu komai Saude Allah ya miki albarka magana mai dad'i ma sadaka ce".

"To malam me kake nufi ni kuma Allah ya tsine min kome"?.

"Ni bance miki haka ba, ke dama Binta nasan baza'a samu a gunki ba tunda ba komai kike ba shikenan dai bari zuwa goben muga abinda zai faru Allah yasa na samu ina son barin garin nan kodan ku naje nayi aiki tu'kuru na samu kud'i na faranta muku ranku".

Kallonsa suke cikin girmamawa domin gaskiya Malam Habu mutum ne na 'kwarai baya so yaga wanda yake 'kar'kashin sa cikin 'kunci suna haka Asma'u Aisha da Jamila da suke dur'kushe kowa ta tashi tana shiga d'akin su kamar sakan biyu suka fito suna sake dur'kusawa a gabansa kowa da kud'i a hannunta kallonsu yai da mamaki cikin sanyi Asma'u tace.

"Baba ga wannan kud'in ka kar'ba na tabbata zai isheka kud'in mota basai kaje gurin baba Ilyah ba dan Allah".

Hannu biyu Malam Habu yasa yana kar'bar kud'in cikin mamaki yace "a Ina kuka samu kud'i Asma'u"? Asma'u kanta na sunkuye ji take kamar ta fara zubar da hawaye tsananin tausayin babanta ya kamata muryarta tana rawa alamar ta fara kuka tace "baba jiya ne muka sayar da hulunan mu da muka gama d'inkawa gashi munsa wasu kayi kud'in mota da wannan d'in".

'kirgawa malam Habu yai na Asma'u duhu hud'u na Aisha uku na Jamila dubu biyar da yake ta fisu iya d'inki tata har dubu biyar da d'ari biyar ko shida da biyar tana yi haka malam Habu ya had'a kud'i dubu goma sha uku daidai yasan duk da haka bazai isa ba amma ya 'kyale ya ha'kura da zuwa gurin Ilyah tambayar ya taimaka masa kamar yadda 'ya'yansa suka bukata albarka da addu'a mai kyau ya musu kafin suka tashi suna komawa can gaban d'akin su sukaci gaba da d'inka sabin da suka saka dama Amatu da yawa tayo musu yankin da zaren ta bayar akai fulo kawai saidai subi su tisa zubi da ciko A'i dai ta cika tayi fam saboda tun jiya take lallamin Jamila ta bata kud'in ta kara akan jarinta ta'ki ashe rabon malam Habu ne dukkan 'yar 'kwafa tai tana kallon Jamila ji take kamar ta tashi taje ta rufeta da duka kota huce haka ta tashi kamar mara lafiya ta shige d'aki harda hawayen ba'kin ciki tai ta kasa zama tayi nan tayi can sai hasko sanda Jamila ta mi'kawa Malam Habu kud'in take.


Tabdijan A'I kina da abun fad'a bawan Allah yana kokarin yaga ya faranta muku๐Ÿคจ ke kina wani tunani daban akan dubu biyar mstttt๐Ÿ™„ aikin kawai ki turo account number d'inki zansa FANS d'ina kowa ta tura miki 10k๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ ina shikenan? an wuce gurin FANS kada ku bani kunya ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธina sis Zarah Musa d'an Adam๐Ÿคฃ maza fito ko takan ๐Ÿ—ฃhajia ๏ธNajat Musa Abubakar maman baby nasan akwai money๐Ÿ’ฐ๐Ÿ’ฐ๐Ÿ’ฐ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ yana nan a 'boye a banki๐Ÿฆ dila-dila๐Ÿ™…๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ wallahi karma kice min baki da kud'i ehe๐Ÿ™„ matar nan kwanan nan kika sake sabuwar mota๐Ÿš˜๐Ÿคธ๐Ÿคธ fil a leda kin barmu da kwanan gida wunin gareji๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜๐Ÿ˜€๐Ÿ˜†๐Ÿคฉ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜๐Ÿ˜›๐Ÿค“๐Ÿคญ๐Ÿคซ๐Ÿ˜‡๐Ÿ˜น๐Ÿ˜ป๐Ÿ˜บ๐Ÿ™ˆ๐Ÿคธ

Tofa reader's ayi hakuri typing ๐Ÿ“ฒ din yau ba yawa ba kamar na kullum ba na gaji ne ku lalla'ba zuwa gobe idan Allah ya bamu aron rai da lafiya saimu karasa.

MRS รƒL'ร…Mร‰ร‰ร‘ รHMรƒD CรŠ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜.

MAI TAMBARIN YMA DUTSE๐Ÿž๏ธ ๐Ÿ†•WORLD๐ŸŒ ๐Ÿ†•LIFE๐ŸŒŒ ๐Ÿ†•STYLEโ›ฒ๐ŸŽก๐Ÿš„๐ŸŽข.

JIGAWA DUTSE Sร€BUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DA'DI YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN LAFIYA JIGAWA ๐Ÿ‡๐Ÿ‰๐ŸŽ๐ŸŒน๐Ÿฅ€๐Ÿต๏ธ.


๐Ÿ’‹YUSRAH MUSA ABUBAKAR๐Ÿ’‹

We will meet again๐Ÿค— na gode๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™ much appreciated ๐Ÿ‘Œ yabonku gareni ni๐ŸคŸ๐Ÿค.


TYPING ๐Ÿ“ฒ FRI, JUL 12/24 7:13PM YUSRAHMS ABUBAKAR๐Ÿค™๐Ÿค™๐Ÿค™๐Ÿค™.


๐Ÿ’ŽME KAMAR SARKI ๐Ÿ’Ž

AWA
๐Ÿ’ซANNURI WRITER'S ASSOCIATION ๐Ÿ’ซ HOME OF HOSPITALITY ๐Ÿค— AND HARMONY๐Ÿ•Š๏ธ๐ŸŒด๐ŸŒฒ.

WANNAN PAGE DIN NA SADAUKAR DASHI GA DUKKANNIN ๐Ÿ‘‰๐Ÿ‘‰MASOYAN ANNABIN MU MASOYIN MU SAHIBIN MU ABIN ALFAHARIN MU MANZON MU SHINE RAYUWAR MU SHINE MUTUWAR MU SHINE GATAN MU SAYYIDINA MUHAMMADIN RASULULLAH๐Ÿ‘ˆ๐Ÿ‘ˆ ๐Ÿ’• MUNA SONKA FIYE DA RAI๐Ÿ‘Œ DA IYAYE๐Ÿ˜˜ DA DUKIYA๐Ÿ’ฐ MUNA SONKA FIYE DA DUKKA MURADI NA ZUCIYA ANNABI MU MUGANKA SHINE BURI NA ZUCIYA LAMUNCE MU GANKA YA MAI SALSABIL DA KHAUSARA.

BANDA KAMAR KA YA RASULULLAH A DUNIYA BANDA KAMAR KA YA RASULULLAH A LAHIRA.
๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ
๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿ“ฟ๐Ÿ“ฟ๐Ÿ“ฟ๐Ÿ“ฟ
Hฤ€PPY JรšMรƒ'ร‚T MรœBร…Rร„K
๐Ÿ‡๐ŸŽ๐Ÿ‰๐ŸŒ๐Ÿ๐Ÿฅฅ๐Ÿฅ•๐Ÿ’๐Ÿฅ๐Ÿ“๐Ÿ๐Ÿฅ‘๐Ÿ†๐Ÿ
=_==_==_==_==_==_==_==_==_==_=

KUNA INA FANS KU FITO YAU RANAR MUCE MASOYAN MANZON ALLAH SAW.
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐Ÿ’“ANNABI๐Ÿ’“ ๐ŸŒน
๐ŸŒน S*A*W ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน
KUCE MINI SAI MANZON ALLAH๐Ÿค—
KUCE MINI SAI MANZON ALLAH๐Ÿค—
HABIBI HABIBI HABIBINA HABIBI MA'AIKI RASULULLAH๐Ÿ’•๐Ÿ’žโœŠ.

ANNABI NAKE 'KAUNA ABADAN BAZAN MAI KISHIYA BA ALLAH KA YARDA NAI YABO GURIN MAHMUDU SHA YABO WANNAN DAKE RABON RABO KYAUTA BA'AI YASHI BA.

YA MUSTAPHA ANNABI HASKEN IDANU NA YA MUNTAKA YARDA DANI YA MASOYI NA๐ŸŒน๐Ÿ’“๐Ÿ’—๐Ÿ’–.


๐Ÿ’žMANZON ALLAH S*A*W๐Ÿ’ž
You are the

YUSRAH MUSA ABUBAKAR INA YI MUKU BARKA DA JUMA'A FATAN DUK ALKHAIRIN DA YAKE A CIKIN WANNAN RANA ALLAH YA SADA MU DASHI DOMIN HASKEN MASOYIN MU๐Ÿ™ ALLAH YA GAFARTAWA MAHAIFAN MU๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ MUSULMAI MAZA DA MATA WANDA SUKA RASU ALLAH YA MUSU RAHMA YA LULLU'BE ZUNUBAN SU๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™.

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
It's Friday don't forget to recite suratul Al-khaf may Allah bless you and your household may Allah open the door of success 4u all Muslims.
Juma'at Mubarak by Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ.

47~AL-WADUD
The Loving
48~AL-MAJID
The Glorious

23~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Munzirinah.

๐ŸŒ„ LEAVE TAKING ND WED๐ŸŒ„
Episode 47_48
_____Kwana biyu tsakani kamar yadda Sadi ya fad'awa Malam Habu haka ne ya faru sun tafi Cameron cikin 'kwarin gwiwa da zummar neman kud'i ta hanyar halal basu sare ba musamman Malam Habu tsabar farin ciki kasa ko shan ruwa yai har suka tafi nan labari ya karkad'e gari malam Habu da Sadi sun tafi neman kud'i Cameron kowa da abinda zai tofa wasu na fatan alkhairi wasu na fatan tsiya harda masu cewa kowa yai ta kansa kwanan nan malam Habu arzikin sa zai dawo ya manta da rayuwar 'kunci.

๐Ÿ™๏ธDUTSE MOPAL-BASE๐Ÿ™๏ธ
Cikin shiri Amatu da Maryam harda Nabilah suka fito harabar gida Maryam na d'auko musu mota zasuje Miyetti kar'bo d'inkin ashobi d'insu idan sun dawo zasuje benin galadima a musu saloon sunsha gyara kamar sune amaren Maryam ce ke driving lokaci zuwa lokaci tana kallon Amatu dake ta faman murmushi cikin mamaki tace.

"Amatullahi na tambaye ki"?.

Juyowa Amatu tai tana kallon ta har lokacin da murmushin ta akan fuskarta tace "eh meya faru"?.

Daidai Maryam zata sha kwanar asibitin police clinic ta shiga takur site zuwa gidan 'kanwar ummansu tace "nifa na kasa ganewa tun d'azu muna breakfast naga sai murmushi kike akwai abinda ya saki farin ciki ne"?.

"Kai Amatu ta d'aga tana cewa "eh akwai kawai na matsu sosai gobe tayi ne".

'Dan zaro ido Maryam tai har tana hadawa da dariya tace "saboda kece Aunty Lailah amarya"?.

Kai Amatu ta girgiza "a'a kawai na tuna gobe umma zata zo zan ganta ta ganni kuma na tabbata babanmu zaizo d'aurin aure Allah yasa domin ambatonsa danai har yasa naji ina kewarsa ke kuma har kikai min wata fassara daban wai amarya rufa min asiri ina zaune lafya amarya a gidan wa".

Le'kowa Nabilah dake baya tai tana cewa "amarya a gidan mijinki koba haka ba"?.

"Eh ba haka ba waye miji na"?.

"Mai sonki mana".

"Waye mai Sona"?.

"Hhhhh ji Amatu da wata tambaya dan Allah taya zan sani abu a duhu kodan banace ba ko wannan zuwa gidan da kikai wani yace yana sonki".

"Oh Nabilah zaki fara ko? Please kiyi shiru".

"Shikenan nayi shiru๐Ÿคญ Nabilah ta karasa maganar tana rufe bakinta parking Maryam tayi da mota suna fitowa suka shiga gidan da ya kasance gate ne amma ba mai gadi kuma ba laifi gidan Masha Allah ya matukar had'uwa matar gidan tana zaune a parlor tana kallo suka shiga da sallama ganinsu yasa ta d'au remote tana rage 'karar vidion tace.

"Tofa Antin gida (Maryam haka take kiranta saboda sunan yayar mijinta ce) yau kune a cikin namu sannunku da zuwa bismilllah ku shigo man kuke ra'bewa kamar wasu ba'ki" zama sukai suna gaishe da ita ta amsa da fara'a taba kallon Amatu tace "wannan yarinyar ce 'yar gidan Binta yayar Bashir ko"? Kai Maryam ta d'aga "eh itace Aunty Umma munzo kar'bar ankon mu a gurin telan momy shine nace bari mu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login