Showing 9001 words to 12000 words out of 130249 words
yasa wasu sabbin hawayen sake gangarowa da sauri tasa hannu ta goge bude baki tai kamar zatai magana ganin Bintan na tsaye a kanta tana jiran amsa sai kuma ta kasa cewa komai a karo na biyu Binta tace "mamar gida tambayan ki fa nake me akai miki kike kuka"?.
Kai Amatu ke girgizawa da'kyar tace "umma shin bazan iya taimakon baba ba"? Da mamaki Binta tace "kamar ya"? Cigaba Amatu tai da cewa "umma zan koma gurin su Abba Bashir 'kanin ki na fara kasuwanci domin na taimaki baba wannan damuwar dake damunsa na gaji da gani bazan iya ba a iyasani na mahaifi na mutum ne me annurin fuska amma yanzu koda yaushe baya ciki walwala ki tuna yadda ya ri'ka kula dani ya taso dani a cikin gata ya bani komai da nake bukata a rayuwa idan na zuba ido yaci gaba da zama a haka na yaudari kaina na cuci kaina bazan iya yafewa kaina ba umma ina bukatar taimako" ta karasa maganar cikin kuka sosai wanda ke fitowa daga asalin ainishin cikin Zuciyar ta".
"Kinga mamar masu gida kiyi hakuri haka kinji karki jawo hankalin mutan gidan a kanmu" rufe bakin umma keda wuya caraf sukaji A'i na cewa "aikin banza kenan rigar bayan salla meyi ake cewa tai shiru kar muji za'a boye mana ko saurayi tayi ko kuma wani laifin tai ba'a so mu sani iye a fad'a min domin idan baku fad'a ba kun barni cikin zulumi" juyawa Binta tai tana kallon A'i dake wanke kwanuka batare datai magana ba tace "Amatu tashi ki koma kinji ina zuwa" mikewa Amatu tai tana shiga kamar yadda umman ta umarce ta.
Tabe baki A'i tai tana cewa "oh ni Indo yanzu Binta abin har yakai ga haka kin fara hurewa yarki kunne dan ta raina ni ina matsayin matar ubanta saboda kina kishi dani".
Kallon ta sosai Binta keyi cikin mamaki wato ta fahimci A'i ba 'yar neman zaman lafiya bace wa ya sako da ita har zata dauka..........
Katse mata tunani A'i tai "dake fa nake Binta"? Wani kallon umma ta kuma aika mata dashi batare datai magana ta wuce uzurinta dariya A'i tai tana cewa "ahahaha hayye kai ni yar gidan baba gaskiya akwai tantirai a gidan malam Habu gashi kuwa sun fara bayyana Allah ya tonu asirin su suna shirye shiryen zuwa gurin boka to naji ku sai ku sake shiri ku taka a sannu idan ba haka ba yanzun nan na garzaya na sanar da mai gari" ko kula iskar ta umma batai ba balle tasa ran ta mayar da ita mutum kawai aikin gabanta take.
π₯π»MRS AL'AMEEN AHMAD CE π MAI TAMBARIN YMA DUTSE ποΈ''YAR MUSA JIKAR ABUBAKAR MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY π.
Mrs Al'ameen Ahmad ce mai tambarin yma dutse sabuwar duniya πnew world new life π and new style π.
πΉ Yusrah Musa Abubakar ta kowa ce kuma ni I have no girman kai if you are fushi dani tofa you are just 'batawa kan k lokaci π.
Manzon Allah mai Makkah mai birni da 'kauyuka.
A gaskiya naji dad'in comments dinku yan uwa matukar jin dad'i da yadda kuka gwada kauna ga littafin nan hakan da kukai ya faranta min kuma na sake samun sabon confident na gwarin gwiwa daga gare ku kuma albishirn ku insha Allah zan dage kamar yadda kuka bukata naga kullum nayi muku posting koda kadan ne ngd da yabawaπππ.
Wannan page din naku ne yan uwa ina matukar kaunar ku soyayya ta a gare ku bata kwatantuwa hasashe bazai ta'ba iya hangowa ba Allah ya bar mu tare.
Ibrahim Musa Abubakar
Ummi Musa Abubakar
Salim Musa Abubakar
Yusrah Musa Abubakar
Naja'at Musa Abubakar
Fatima Musa abubakar
Aishat Musa Abubakar
Abubakar Musa Abubakar
Abdullah Musa Abubakar.
Banda kamar ku duk fadain duniya ku nake kallo naji dad'i kune jini na kune dangi na kune ahli na kune abun faharin na.
To 'yan uwa mu tsaya mu kwana anan sai mai duka ya kaimu gobe ya bamu aron rai da lafiya zanyi muku.
Think before you do π¨
Be good be kind people will like u.
YUSRAHMS
Mrs Al'ameen Ahmad maman little Zaran aunty πππ.
π Till we meet.
TYPING π² Thu 9:48AM Feb may Allah open the door of success for all of u.
πME KAMAR SARKI π
π« ANNURI WRITER'S ASSOCIATION π«.
HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY GIDAN KARBAR MUTANE HANNU BIYU DA ZAMAN LAFIYA ANNURI HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI'YA'YAN TA. TAKEN MU KENAN.
Dedicated to
MR HAUSA EBOOKS π
ππππππππππ
WHAT'S APP NO: 234 8160983083
Chat with me at always banda kira idan kasan kai na miji ne only female kawai ππ.
βοΈ Yusrah Musa Abubakar story and written dedicated to my mum mama na ta kaina Allah ya kara girman matsayi ya kiyaye min ke mama na Amin π.
05~ AS-SALAM
The source of peace and safety.
06~ AL-MUMINU
The guarantor.
Manzon Allah saw
Ya mai nasiha ga alumma muso juna mu rike gaskiya amana dan gudun kuna mu raya zuminci hanya ne na aljannah makiyin zumunci baya kusanci ceto ba.
4-Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Shahidina.
Wa alam anan nasra ma'as sabriπ wa annal faraja ma'al karbiπ’ wa anna ma'al usri yusrahπ€πΉπΉπΉ.
π£οΈπ£οΈπ£οΈπAYI HAKURI IDAN AN SAMU TYPING π² ERRORπ¨ MATSALAR KEYBOARD NE π€.
π EMPIRE ND RESEMBLANCE π
Episode 05 & 06
Babbar masarauta ce wacce ta shahara mai cike da dunbun tarihi da kafaffiyar daula da jajurtattun sarakuna wadanda sukai zamanin nika kuma har yanzu ake mulkin ta kamar da masarautar nada girma da tsari wanda bayan emire Aliyuddeen Abdulmalik mai mulkin ta ya kwanta dama sai babban d'ansa alhassan Aliyuddeen Abdulmalik yahau kuma ya jajirce kamar mahaifin sa har izuwa yau.
Emire Alhassan Sun kasance 'yan biyu ne shida d'an uwansa Alhussain kamar su daya sak ba'a bambance su kamar ma harta baci kuma da suka tashi haihuwa kowa Allah yake arzuta shi da 'yan biyu kuma masu kama daya saidai mai martaba Alhassan nasa dukka maza ne matansa biyu Princess Hauwa da princess Fatima suka haife su rana daya abin al'ajabi d'aya ta haihu da safe daya da dare farin ciki a wannan rana baya musaltuwa kuma abin sha'awa ya sanya musu sunan mahaifin sa marigayi Aliyuddeen duk su hudun sunan su Aliyu Aliyu an dauki lokaci mai tsawo a masarautar ana bikin murnar haihuwar su 'kasashe daban daban yanki iri iri anzo domin karrama Emire Alhassan da iyalan sa sai hussain shi kuma nasa 'yan mata su ma hudu 'yan biyu suna rayuwa ne cikin mulki daula da sarauta ga ilmi saima ka gansu kyawawa zarata masu kwarjini da aji.
Kuna ina ku fito ku kashe 'kaikayin idanuwan ku Kai tsaye ya kamata mu leka mu ganewa idanuwan mu abin yake faruwa cikin wannan kasaitacciyar masarautaππ.
Zaune suke a wani irin kyakkyawan siritaccen 'kayataccen parlor suna da yawa samari da yan mata kyawawa farare tarr jawur dasu sun gaji da kyau ta ko'ina sun hadu saidai ko tari babu a parlon kamar masu zaman makoki sunkai kusan minti talatin a haka kafin a samarin daya ya d'ago yana kallon na kusa dashi dake ta aiki cikin laptop yana cewa.
"Ajeeb wai ina Asad ne tun shigowar mu banga yazo ba lafiya dai"? Batare daya d'ago ba yace "gaskiya ban sani ba domin nikam tun asuba muka rabu dashi a masallaci maybe yana part dinsa ko kuma gurin su Mami" ya karasa maganar tare da dagowa ya kallo yan matan yana cewa "ga Khimiyyah ma ban ganta ba uwar shashanci ai dama halin su daya da Asad din" dariya Ameer yai dan kowa a masarautar yasan jinin su baizo daya ba har bayi idan ka tambaya zasu ce maka haka.
'Daukan waya Shaukiyyah tai zatai Kira da sauri Khaldiyyah dake gefen ta tace "ke me zakiyi"? Kai tsaye tace "oh Asad zan kira naji inda yake"? Zaro ido Shaukiyyah tai da mamaki tace "ki kira shifa kikace? kin manta laifin da kikai masa jiya kenan zai miki dukan mutuwa Mami ta hana shi shine kuma yanzu kanki na rawa kike son taso mutuwa daga bacci ko? Allah ya taimaka mukam yan kallo ne da sannu yayin daya sauya miki halitta" ta karasa maganar tana kallon Annur wanda shi kuma hankalin sa sam baya kan maganar da suke Ameer yace "ai dakin barta taje ina tasan yana tattare da ita" shiru Shaukiyyah tai tana kallon su daya bayan daya domin ita badan sun tuno mata ba ta manta da tai masa laifi jiya.
Mikewa Ajeeb yai yana cewa "bari mu gani tsaya naje part dinsa" fita yai ya barsu duk inda ya gifta du'ka masa bayi suke cike da girmamawa tun daga nesa.
Ya nufi wata iriyar kyakkyawar kofa mai she'ki zaka iya jiyo kururuwa da ihu na mace tana kuka cikin tashin hankali da dana sanin abinda ta aikata.
Sanye yake cikin kayan sojoji kana ganinsa balarabe sak fari ne tarr kyakkyawan jarumtaccen sadauki wanda ba kamarsa a karfi kwarjini fuskarsa kamar ba'kin hadarin da yake gaf da zubar ruwa ransa a mugun 'bace idanuwansa sunyi ja kamar rana taje faduwa cikin tsananin bacin rai da tsantsan fushi yake kallon fuskarta da saitin inda yatsunsa suka fito da 'karfin gaske cikin taku yake yin wajen inda take kwance ganin ya kuma nufota kamar zakin daya hango nama yasa a zauce ta yunkura cikin dimuwa da gigita tana neman hanyar tsira daga hannun sa wani irin dan'ko gashin kanta yai yana jawo ta baya tare da wurgi da ita ta bugi jikin wasu kafaffun karafina tayo kasa ji kake tim ihu ta zunduma tana dafe kanta saiga jini ta hanci yana malala ko a jikinsa ya sake dan'ko wuyanta yana mikar da ita tsaye ya kuma sharara mata wani marin daidai Ajeeb ya bud'e kofar katafaren gate din part din yaga abinda ke faruwa da mugun gudu ya karaso yana cewa.
"Kai ASADπ¦ are you out of your sense baka da hankali ne ka sake mata wuya saika kashe ta mitai maka? ka bari fa nace ka sake ta" ko inda yake bai kalla ba balle yasan wai mutum ne ke masa magana sai kara matse wuyan nata da yake idanuwan ta duk sun fito waje sunyi jawur jini kuwa sai ambaliya yake ta hanci da baki ganin da Ajeeb yai idan ya zuba masa ido zai kasheta yasa da karfi ya soma kokawar kwaceta muryar Asad da tsananin fushi yace "AJEEB let's not get into thisπ π‘" shima Ajeeb cikin fushi yace "I won't spare you bazan 'kyale ka kashe ta ba wallahi ka saketa nace" a banza Ajeeb yake magana domin ko sauraron sa Asad baiyi ba kokarin kwatar ta Ajeeb keyi amma maimakon yai nasara sai ya jawo Asad din ya sake mata mugun rikon daya fi nada a susuce Ajeeb ya zaro pistol 'karamar bindiga dake aljihun wandon Asad ya harbeshi a hannu ko zai sake ta tuni jini ya wanke hannun amma tsabar tsaurin rai Asad bai sakar mata wuya ba "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda Ajeeb yake maimaitawa kenan cikin azama a guje ya fita ya nufi sashin mahaifansu dan yasan banda su ba wanda ya isa ya dakatar da Asad daga yunkurin kashe Kimiyyah duk bayin dake aiki a part din Asad kuwa kowa ya shiga taitayinsa sun rasa abinda yake musu dad'i tsoro ya hana suje su fad'a yanzu kuma sun san dole a hukunta su akan haka.
Dukkan ahlin gidan a gigice suka shigo domin mai martaba ko takalmi babu a kafarsa tsabar tashin hankali Mami dake gaba ganin halin da Kimiyyah ta shiga na rai ko mutuwa yasa da gudu taje tana kasarawa ta wanka masa mari sau biyu tare da fashewa da kuka tana rike hannunsa dake wuyan Kimiyyah tace "Asad ba ita ya kamata ka kashe ba nice ka saketa Asad ka rike nawa wuyan innalillahi wa inna ilaihi raji'un Asad ka sake mata wuya kada ka kashe yarinyar nan bazan yafe maka idan ka zama silar mutuwarta" ta karasa maganar tana sake jan hannun sa da karfi jin kukan da take da abinda tace yasa Asad sakin wuyan Kimiyyah tilas ba hakura ba hannunsa na tsiyayar jini inda Ajeeb ya harbeshi da bindiga Kimiyyah kam yana sake mata wuya ta 'kame tare da zunduma uban ihun tsananin azaba kafin ta yanke jiki ta fad'i kasa da sauri sukai kanta yayin da Mami ta fad'a jikin Asad tana kuka sosai.
Gaba daya jikin 'yan gurin rawa yake an rasa mai kwarin gwiwar cewa komai sai salati da ake ganin yadda Kimiyyah ke wata iriyar mi'kar tana sankarewa irin na mai 'ka'karin mutuwa hankali tashe Ajeeb yace "Abba muje asibiti dan Allah karta mutu" kasa magana mai martaba yai sai mikewa kawai dayai ya bar gurin da sauri Ajeeb da Ameer suka dauketa suna fita sauran suka bi bayan su har lokacin Mami bata daina kuka ba ta kasa shiru ga jikin ta sai rawa yake kamar maijin sanyi ko mai zazzabi da'kyar ta d'ago tana kallon fuskar jarumin d'an nata da har lokacin yana cikin mood altering ganin jini duk ya bata mata jiki yasa ta kalli hannun sa zaro ido tai ganin harbi da sauri tasa hannu cikin aljihunsa ta dauko wani d'an karamin towel fari ta daure masa hannu gabadaya ta kasa nutsuwa kuma tasan ba magana zaiyi ba amma dai tace "Asad mai Kimiyyah tai maka kake kokarin kashe ta meya kawota part dinka ya naga harbi a hannunka"? Shiru yai kamar kurma kuma dama haka take tunani rike hannunta yai yana fita da ita saida ya mayarta har part dinta kafin ya dawo ya cire bullet din hannunsa ya nad'e hannu yana tattare kayayyakin daya tarwatsa domin tun daga parlor ya soma dukanta har harabar part dinsa Saida ya gama sannan ya mike yana shiga bedroom ya cire kayan jikinsa ya shigo toilet saboda sanin irin zafin Zuciyar sa yasa ba mace ko daya da take aiki a part dinsa mazan ma sai taka tsantsan suke.
Ruwa mai matukar sanyi yake kwararawa jikinsa idanuwan sa a rufe hannunsa nakan kyakkyawan pink lips dinsa ya ma rasa mai tazo yi part dinsa uban waye ya turo ta mai take nema har ta samu damar shiga d'akin sirrin sa tai amfani da na'urarsa ta tura sako ta goge masa abubawa masu mahimmanci wanda yadau tsawon shekaru yana tarawa yau daya tasa yayi losing dinsu duka bude idonsa da har lokacin babu fari ko kadan yai tare da furzar da zazzafar iska ya dunkule hannunsa ya kaiwa mirron toilet din naushi take ya tarwatse ko'ina numfashi ya sauke cikin zafin Zuciya bad temper yafi awa biyu yana tsaye shower πΏ na zubar ruwa a kansa kafin ya daura towel ya fita zama kawai yai gaban mirror yana zubawa had'ddiyar kyakkyawar fuskarsa ido mikewa yai a gurin yana komawa kan katafaren katon bed dinsa Wanda ya 'kawatu da kwaliyar zinare kwanciya yai yana kallon sama tare da lulawa cikin tunani har ya bata lokaci a haka karfe daya da rabi tayi bai sani ba kuma a yau yake son komawa domin isham ya kirashi a waya tun jiya ya yi masa albishir cewa ya kusa gano abinda ya dade yana nema amma yau d'aya Kimiyyah ta wargaza masa tanadin dayaiwa shekaru da dama runtse ido yai da karfi tare da cusa yatsunsa cikin lallausan gashin kansa tuni yaji ransa ya kara baci fiye da da jiyake dama zai hadu da Kimiyyah yanzu babu abinda zai hana ya d'aga bindiga ya harbe ta, tashi zaune yai a tsakiyar gadon yana tan'kwashe kafafunsa kamar daga sama idanuwan shi suka sauka akan wani photo wanda ya kasance anyi shi da dadewa zai kai shekara sha takwas sau'ka gadon yai yana zuwa gaban photo yasa hannu ya dauka yana kallo ko ba'a fad'a ba shine ya dauki wata karamar yarinya a hannunsa zatai shekara biyar da uniform a jikinta yana murmushi ita kuma tana dariya kuma da gani photon a waya akayi shi ya bayar aka wanka fuskar yarinya kadai yake kallo a ranshi yana tunanin shi da ita har abada bazai sake ganinta ba domin dama bai santa ba saidai yana fatan ya sake haduwa da ita ko sau daya ne a rayuwar sa aje photon yai yana barin wurin yaje ya fara tattara kayansa yana sawa cikin trolley ya zuge kafin yayo alwala yasa kaya yai salla ya shirya cikin kayan soja anan tsantsan asalin kyansa ya kara bayyana fili 'karara gaskiya ya matukar haduwa fad'a batawa fita yai a bedroom din,
yana yin hanyar wata kofa da aka rubuta STOCKYARDS anyi masa launin golden sai haskawa yake kamar ba rana ba password ya rubuta kafin kofar ta bud'e ya shiga iya ganinka dabbobin daji ne kamar gidan zoo fili ne mai girma an kawata shi da ado kyansa baya faduwa saidai hasashe wani 'katon 'ka'k'karfan zaki na ganinsa ya nufo shi yana kukan su na zaki da matukar gudu yana zuwa gabansa ya taka wani irin burki mai burgewa dukawa Asad yai yana shafa gashin zakin cikin so can ya jiyo kukan wata 'yar karamar giwa yana dubawa yaga har tazo inda suke amma babarta tana d'an nesa dasu itama shafa jikinta yai a yau baiji sanyi a ranshi ba sai yanzu daya shigo nan mikewa yai zakinπ¦ na biye dashi ya soma zagaya gurin yaga lafiyar su kafin ya fito yana fita a part din nasa gabadaya yayi tunanin zuwa gurin Mami saidai yasan ba lallai itama ta zauna ba maybe ta bisu asibiti yana tsaye a katon katafaren kofar shiga fadar mahaifin sa yasa anyi masa Kiran wani bawa wanda ya kasance duk masarautar shi kadai ne jininsu yazo daya gano Asad din tsaye yasa shi karasowa da sauri cikin girmamawa ya du'ka yana cewa.
"Ka gafarce ni shugaba na ka kira ni ne"? Kallon sa Asad yai nadan mintuna kafin ya bud'e baki cikin zazza'kar muryarsa da baiyi magana da ita ba tun dazu yace "Amjadd will you work for me if I ask you"? Sake dukawa Amjad yai yana cewa "Allah ya taimake ka Allah daukaka ka zanyi kowanne irin aiki daka sani amma ranka ya dade kamin bayani da hausa dan nafi fahimta ba sosai nakejin turanci ba"