Showing 15001 words to 18000 words out of 130249 words
kan tabarma ya kunna radio yana saurara takaici ne ya kama A'i tayi kwafa tana daukar kwarya ta shige d'aki sai balbali take "wai kayi magana kaida gaskiyar ka a mayar ka mahaukaci nikam wannan abu ya na 'kona min rai maigida guda ba sana'a wallahi da sakal dole ka tashi ka nema malam Habu idan ba haka wata rana zaka budi ido kaga gidan ka ya zama kango duk mun watse mun barka wazai iya zama cikin irin wannan ba'kin talauci haka" ita kadai take wannan tace wancan.
Yadda zata jiyo shi ya d'aga murya yana cewa "aike A'i tun ba yauba na fahimci kin samu matsala a kwakwalwarki shiyasa nake miki usuri dan da kinsan abinda kike baza ki rika kallon cikin idanu na kina iya fad'a min dukkan maganar data zo bakin ki ba" fitowa A'i tai tana cewa "yo malam tsakani da Allah inda talauci ma fa da laifin ka ka mike ka nema inace ko majalisar zaman taku kowa da abin sana'arsa kai kadai ne kake zaman kashe wando labarin rariyar hannu ce dakai ya zaga ko'ina har wajajen kauyen nan gashi ko samari babu wacce yarka take dashi mutane suna cewa kada su aure su suna debe kayan abinci suna kawowa gida....................
"A'i ya isa haka" malam Habu ya fad'a yana nuna ta da yatsa shiru A'i tai domin ganin ta fusata shi yasa ta debi 'yan siraran kafafunta tabar gurin tana cewa "kai kuma malam akwai son yiwa mutum tsawa har kasa naji shakkar ka" ko kula ta baiyi ba ya cigaba dajin radiyon sa.
Gidan ilyah Amatu ta fara zuwa amma dai kamar kullum ba maraba ba 'karaso balle a nuna anji dadin zuwanta tana ta tsaye kamar kafaffiyar bishiya har Nafisa ta fito tana cewa "umma nifa gaskiya yunwa nake ji wai har yanzu ba'a sauke ba" kallon ta Bara'atu tai "eh ya kusa kidan kara hakuri juyawa Nafisa tai tana komawa bayan ta gasawa Amatu harara tace "wai nikam dama har yanzu ana maula ne lallai kud'i sunyi" Bara'atu batai magana ba domin haka nan taji tana kunyar Amatu.
Itakam Amatu maganar da Nafisa tai ko kadan bata ta'ba taba saima d'an kyakkyawan murmushi data saki tana cewa "sai anjima" a yangace Bara'atu tace "a'a bazaki shiga ku gaisa ba yana ciki fa" bata ce komai ba ta juya da sallama ta shiga d'akin sa yana zaune gaban sa fal da kayan marmari ga wani yana sha gefe gashashshan naman balangu ga kwaryar kindirmo dukka anyiwa yan birni tanadi durkusawa Amatu tai tana gaida shi a ciki ya amsa yana hade rai tare da zaro d'ari biyu ya mi'ko mata kaita girgiza tana mikewa tace "a'a dama kawai nazo gaida ku ne sai anjima" mayar kudin sa yai da sauri yana cewa "to to sannun ki da kokari tun kina yarinya kinsan zumunci ki gaida yan gidan naku" to tace tana fita Bara'atu ta tsayar da ita da cewa "Amatu har kin fito ki tsaya na sauke miya kici abinci ga kaji nasan kila yau bakici komai ba tun dumamen safe" juyowa Amatu tai da sauri ta na kallon Bara'atu da mamaki saidai batace komai ba kuma bata nuna ta damu ba tace "a'a nagode sai anjima" ko magana bata bari Bara'atu ta sake yi ba tai waje tana mamaki wato haka baba Ilyah ya koma amma ya taimaki mahaifin ta koda jari ne ya'ki.
Jitai zuwa gidan baba Sabi'un ma ya gundureta ya fita a ranta amma haka ta daure tabi ta gidan su Fatima domin ta rakata duk da gaban ta na fad'uwa batasan me zata tarar ba acan tunda shikam ya riga ya rasu sai matar sa da 'ya'yansa a gidan biyu sunyi aure da daya mara aure da mata uku a d'aki Kowacce da yaranta da sallama suka shiga Innah Rakiya tana zaune gaban murhu tana aikin girki da mamaki tace "a'a mamar kowa da gaske kece kamar a mafarki kai maraba lale sannunku da zuwa keda Fatima ne yar gidan malam Mato can kusa da dandali" tabarma ta dauko ta shimfida musu tana cewa ku zauna zama sukai suna gaida ita cikin fara'a ta amsa musu tana tambayar su can wajen anguwar har ta 'kare tuwan shinkafar da take tai kunu suna zaune domin sunyi yunkurin tafiya itace ta hana su saida suka ci suka koshi ta zuba musu wani tace Amatu taje gida dashi godiya sosai Amatu tai mata cikin jin dad'i da karramawar datai mata domin ta matukar burgeta shimfidar fuska akace ta wuce ta tabarma.
Daidai zasuyi sallama manya manyan motoci guda biyu sukai parking a kofar gidan Ilyah yana tsaye ya fito taryar su sai kancara ha'kora yake dan tabe baki Amatu tai tana kallon Fatima tace "amma ba anan zamu rabu ba zaki karasa gidan mu ko"? Kai Fatima ta girgiza tana cewa "a'a anan zamu rabu zanje gidan baba dala ne" kai Amatu ta d'aga "to shikenan Fatima na gode" sallama sukai ta shiga gida Fatima kuma ta wuce.
Da mamakin ganinta da katon kwano yasa malam Habu cewa "mama na daga ina"? Ya mata tambayar ne duk da shima yasan daga inda take kuma yasan ba kwanon gidan Ilyah bane saukewa tai a gaban sa tana zama kusa dashi tace "baba Rakiya ce ta bani na kawo muku" ta karasa maganar tana bud'e murfin kwanon fuskar malam Habu da fara'a yace "Aiko Allah yaiwa Rakiya albarka ya bata abinda take nema duniya da lahira kamar tasan a yau banci komai ba tun safe haka na wuni"😔 kallon sa Amatu tai jin abinda yace sunkuyar dakai tai saiga hawaye shar yana zuba a idonta da sauri ta mike tana shiga daki ta dauko kwano tazo deba masa tana ajewa gaban sa tace "baba kaci" kallon ta sosai malam Habu keyi cikin tausayawa tare da ri'ko hannunta yace "Mamana ki daina kuka kinji komai yai farko zaiyi karshe insha Allahu bazan tabbata a haka ba" kai ta d'aga tana daukar sauran ta kaiwa umma kafin tadau kofi ta debo ruwa mai sanyi a randa tana ajewa malam Habu daya nade hannun riga yana kai lomar tuwo sai kallon sa kawai take tana share hawaye tuna abubuwan data gani a gidan baba Ilyah ya tanadarwa ba'kin sa ga d'an uwansa jini daya uba daya amma ya'ki taimakon sa............
Muryar A'i ce ta dawo da ita daga d'an gajeran tunanin da take kallonta tai tana zaune kan kujera a bakin kofar d'akin ta sai cewa take "haba da Allah malam kaji fa wani irin tuwo me mugun dadi amma ace kullum daga gero sai gero ni Allah Allah nake ma dawa tazo mu huta da wannan 'kuncin kullum girki iri daya babu canji kaga kaima malam yadda ka karkace hula kana aiki amma ka noma shinkafar a gonar ka ka'ki kodan ina kaga gonar wata miyar sai a ma'kota" ta tafar sauke ko ci kanki malam Habu bai ce ba sai Amatu dai da take ta jin d'acin maganganun A'i.
Fatima na shiga gidan su Dalah tai turus ta tsaya ganin yadda Balarabe ke surfa bala'i ga Indo
a gefe ta kifa kai tana kuka Asabe data fito a d'aki cikin tabe baki tace "yo ai malam wannan kaso kanka iya dan dukan da zakai mata kenan ni na dauka zaka karya mata 'kafar da take zuwa kwartancin da ita ai anzo har gida an fad'a ranar talatar data wuce karfe sha d'aya na dare wani me mota yazo ya sauketa malam idan bakai a hankali ba Indo zata fi karfin ka kawai ka aurar da ita kafin ta jawo maka abin kunya" cikin fad'a Balarabe yace "to wa ma zai sota a haka kalli fa duk kowa yasan tana bin maza nidai ba gado na kikayo ba saidai dangin Dalah kuma wallahi bari kiji duk ranar da tsautsayi yasa kikayo cikin shege saina kashe ki a gidan nan".
Dad'i ne sosai ya kama Asabe tana kallon Dalah datai tagumi tace "ai malam ga shawara kawai yau da asuba bayan anyi sallah a masallaci ka fad'awa liman ya sanar kana da 'ya zaka bada ita sadaka ka wanda keso sadaki kawai zai biya" shiru Balarabe yai a zabure Asabe tace "tunanin me ka tsaya yi ko shawarar tawa batai ba nasan tayi saidai kace baka so" da sauri Balarabe yace "a'a shawarar ki tayi zanyi hakan yanzu bari na fita majalisar mu shima malam Habu muyi wacce zamuyi ya karasa maganar yana yin kofar fita yana tafe yana magana shi kadai kamar ta'babbe la'bewa Fatima tai tana jiran Saida ya wuce sannan ta shigo gidan da sallama hankalin ta nakan indo wacce har lokacin kanta yake duke tana shar'bar kukan damuwa da takaicin 'kuncin rayuwa.
Kanta taje ta tsaya rai 'bace tace "Indo" da sauri Indo ta d'ago ganin Fatima yasa cikin kuka tace "Fatima me naiwa mutane ne meyasa bani da farin jini kamar wacce mujiya ta a ina fatan mutuwa a wannan lokacin da rayuwa ta" kai Fatima ta girgiza cikin tausayawa tace "a'a Indo kada kiyi sa'bo ki dauka hakan kaddararki ce kiyi kokarin cinyewa sai ki samu mafi alkairin sa".............
Asabe ce ta katse su da cewa "ke munafika uban me kika zoyi gidan mutane"? Ko inda take Fatima bata kalla ta d'ago Asma'u y suka shiga d'akin Dalah mikewa Dalah tai tana bin bayan su sakin gud'a da shewa Asabe tai tana rawa "ahayye nanaye ayuriiiiiiiii abun yazo kaga munafikai zaku fito ne kome kuke kitsawa to wallahi nidai nafi karfin ku idan ma ku mayu ne kurwata tai muku nisa nama na yai muku daci kuma Dalah kisa ido ki gani saina hana ki shan ruwa a gidan nan muje zuwa daya Kenan kuma idan akai munafirci na ban yafe ba" d'aki ta juya tana rera wakar munafirci kunun kanwa uwarku ta fara damawa.
Ba'kin Ilyah sun sauka lafiya kuma yai musu kyakkyawar tarba jiki na rawa daga shi harsu Bara'atu sai son yin gwaninta suke wannan karon Kam Nafisa kwalliya aka yi aka sa kayan 'kure ajiya itace mai kai musu komai idan ta ajiye saita kalli fuskar saurayin dake gefe amma shi ya'ki d'agowa ya kalleta sai zuwan karshe ta mike zata tafi gyalen ta ya zame ya hango breast dinta Dan lumshe ido yai ya sake budewa akan fuskarta daidai ta d'ago suka hada ido ya sakar mata murmushi mamaki ne ya kamata da sauri ta fita yayin daya cire lips dinsa yana sake bin kofar da kallo.
Nafisa kam na fita da gudu ta karasa d'akin su tare dayin tsalle ta haye katifa tana fasa ihu a firgice Salma dake bacci ta farka tana kallon ta tace "lafiya meya faru kike ihu"? Dariya Nafisa tai tana cewa "ke Salma albishir dinki wannan zuwan anzo da wani saurayi naga sai kallo na yake yana murmushi watakila Sona yake kai wayyo Allah, Allah yasa da gaske ne dan ina matukar son zaman binni kinsan da dad'i kalli fa su yaya Hassan tunda suka tafi kin jisu shiru suna can suna jin dad'in su" tabe baki Salma tai tana cewa "umh umh fa kinga Nafisa ki kiyayi kanki yan binni wayo garesu wallahi kada ki saki jiki dashi ya saki kuka wata rana nidai na fad'a miki" had'e rai Nafisa tai tana hararar Salma tace "kinga goggo Salma idan bazaki bani karfin gwiwa ba kada ki karya min zuciya mu tsaya iya haka nikan yayi min ina son shi" cikin haushi Salma tace ai saiki je ki fad'awa baba ya aura miki shi inga karshe rashin kunya" gyara zama Nafisa tai tana cewa "meye abun rashin kunya bayan na gani ina so kinga kema ta dalili na zaki shiga binni kiga yadda yake" mikewa Salma tai zata fita a d'akin tace "Allah ya kiyaye kema dan bakisan ciwon kanki bane ina fata ki gane da wuri" shiru Nafisa tai tare da bin kofar da Salma ta fita da kallo saidai tafi tunanin ko Salma kishi da hassada take mata.
Tana nan zaune har Salma tayo alwala tazo zatai sallah ita kuma sai powder data kara daukowa tana sake fante fuskarta Salma na shigowa Bara'atu tai sallama tana cewa "ke Nafisa kizo baban ki na Kira baki zasu tafi an gama loda kaya daya daga cikin yace yana son zakuyi magana Allah yasa yace yana sonki ki fita zakka a kauyen nan ki auri dan binni mai kud'i" jiki na rawa Nafisa ta mike tana fita cikin zumudi bayan Salma ta shafa addu'a ta juyo tana kallon Bara'atu tace "amma umma wannan fa kuskure ne take aikatawa ya daga ganin mutun ba sanin sa akai ba kawai tace zata aure shi tasan halinsa ko baba nasan baisan komai game dasu ba iya kaci suzo da kud'i ya siyar musu Kaya su tafi dan Allah umma ku tsaya ku duba" wani kallo Bara'atu tai mata tanacewa "ke jimin yarinya da shishshigi me kike nufi dan kawai yazo daga binni kuma yace yana son ta saimu 'ki amincewa dashi"? "Eh ina tunanin abinda zaije ya dawo ne kuma ku idan yace zai aureta zaku bashi ne"? "maizai hana zai kashe tane"? Kai Salma ta girgiza "Amma umma a tsaya ai bincike kafin a amince masa" kallon ta Bara'atu tai "kinga Salma saurara meye damuwar ki ke ba kince kinfi son zaman kauye ba to saiki kyaleta itakam sai rayuwa a maraya" shiru Salma tai bata sake cewa komai ba itama Bara'atun haka.
Da sallama Nafisa ta shiga d'akin ba kowa shiru saishi zama tai dan nesa dashi yana kallon ta yace "barka da wannan lokaci kyakkyawa a gaskiya kin iya kwalliya kallon ki yasa na kasa furta kalma daya amma dai zanyi miki tambayoyi uku ki bani amsa, na farko mene sunan ki"? Ya fad'a yana kafeta da ido duk jitai ta takura da'kyar tace "Nafisa" a bakin shi kamar shine ya rad'a sunan ya maimaita "oh Nafisat nice ne, tambaya ta biyu kinji nai miki kina sona? tambaya ta uku zaki aure ni"? Ina jiran ki amsa hajiya Nafisa kece mace ta farko da naiwa kallo d'aya naji na kamu da cutar sonta kuma ina fatan kema zaki amince min"?.
Zaro ido tai tana kallon sa tace "da gaske sona kake"? Kai ya d'aga mata "eh sonki nake irin ainun dinan fatan kema haka kina yina"? Cikin wawanci ta fara dariya wanda shi mamaki ma yasa ya tsaya kawai yana kallonta saida ta gama yace "yadai kiban amsa zamu tafi jira na suke" ko kunya balle kara haka Nafisa tana kallon idanuwan shi tace "eh ina sonka kuma zan aureka domin ba abinda nake so kamar zaman binni" wani kallo ya mata to maye abin son zama a birnin ko'ina ba gurin rayuwa bane gira ya dage tare da mikewa yace "shikenan to nagode da so zamu tafi" itanma mikewa tai suna fita tare saida tai masa rakiya har waje ya shiga mota suka wuce Ilyah sai yan'kare baki yake yana annaahuwa ganin dayai Nurain ya nuna yana son Nafisa yasan yanzu zai sake zama me dukiya fiye da da idan ya samu ta aure shi.
Gida suka shiga yana kiran Bara'atu d'aki gata ga Nafisa yace "to batu ne game da zancen Nafisa ga dai yaro Nura dan gidan alhaji Tajuddeen ya ganta ya yi maganar yana sonta to ni abinda nake so anan shine ku bani goyon baya d'ari bisa d'ari mu jajirce mu tabbata Nafisa ta aure shi ta fita daga kauyen nan ina da tabbacin wata rana sai munyi zaman binni mun bar wannan karkarar tun ta iyaye da kakanu domin ban aje kowa ciki ba daga ni sai ku iyalai na bani da wani 'kani ko d'an uwa Habubakar ne kuma shi gara kare ma dashi a gurina".
Dariya Bara'atu tai tana cewa "gaskiya ne malam ka fad'i gaskiya idan muka samu Nafisa ta aure shi mun samu kofar arziki ba karama ba mutanen dake da miliyoyin kud'i a banki a boye" cikin nuna son zuciya Ilyah yace "to kin gani dai nasan 'ya'yana suna da 'kashin arziki yanzu abinda za'ai shine ke Nafisa idan sun sake dawowa kice ya sai miki waya wacce zaku ri'ka magana kinji kuma ki tabbata kina tatsar sa kudade domin baisan ciwon su ba" "to baba" Nafisa ta fad'a tana mikewa ta fita sai murmushi take ita kadai farin ciki ya ishe ta har ji take wata sabuwar iska mai launin sanyi tana shigarta.
Karo sukai da Salma zata fita tare ta Nafisa tai "ke ina zaki je haka ko gurin wancan saurayin naki me kama da tuntu'be shine kike wannan saurin kamar zaki tashi sama anji kunya" wata uwar harara Salma ta sakar mata tana cewa "akwai wanda yaji kunya irin ki kawai tsabar gidahumanci daga ganin mutun ba sanin sa kikai ba babu binkice kawai kice wai kina sonshi" rama hararar Nafisa tai tana cewa "eh haka nake kuma son kayana kuma banga abinda zai hana na aure shi ba sai mutuwa" wucewa Salma tai cikin jin haushin ta tace "au aina dauka mutuwar ma bazata hana kiba nidai yar uwarki ce ta jini a matsayi na namai sonki nake fad'a miki kibi a sannu" da kallo Nafisa ta bita tana tabe baki tace "ji shegiyar yarinya waini zatai wa wa'azi bazan bi a sannun ba da karfi zanbi sainaga wanda zai hana haba Salma na fahimci ba'kin ciki kike dani kuma saidai ki mutu domin mijin dazan aura ya kere naki kyau dan dadai ne babu inda ya zarta ba irin naki ba tudu da gangare yana tafi kamar agwagwa zaki dawo ki same ni" ta karasa maganar tana shiga d'akin su ta kwanta tare da rufe ido kawai tana tunanin Nurain a ranta.
Fatima kam daga gidan Dalah kai tsaye gidansu ta wuce Aliyah babarta na zaune ganin yadda ta shigo yasa tace "Fatima lafiya naga kamar kinyi kuka"? Zama Fatima tai sai ajiyar zuciya take saukewa cikin takaici ta soma magana hawaye na zuba "yanzu tsakani da Allah umma babu wanda zaiyi magana sai baba Balarabe ya kashe Indo da duka yau ma baki gani ba yadda ya sata a gaba yana tsine mata da debe mata albarka wai Asabe harda zuga shi idan yaje masallaci