Showing 45001 words to 48000 words out of 130249 words
Amin Amin harya gama suka shafa sannan Baffah yace.
"Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu".
Duk amsawa sukai "Amin alaika salam wa rahmatullahi wa barakatuhu".
Kafin Baffah yace Ramatu tayi farat tace "nifa na gaji bacci nake ji, meye ne na tara mu haka abinda ban ta'ba gani ba sai yau ko wata sabuwar tsirfarce ta samu"?.
Ba wanda ya kula Baffah dake kallon sauran yace "to alhamdulillahi ina godiya ga Allah daya nuna min wannan rana duk da banyi tunani ba na sani zakuyi mamaki zakuyi ta tambayar zuciyar ku meya faru akai kiranku ba komai bane dama na tara kune akan naji meke faruwa meke damunku kowa ya fad'i matsalar abinda ke ransa ina sauraron ku Salamatu mu fara daga kanki domin kece uwar gida kece babba"?.
'Dan shiru Salamatu tai tana tunani na 'yan mituna kafin ta d'ago tana kallon kowa tace "eh to gaskiya nikam ta bangare na babu komai ina wa kowa kallon kima da mutunci yara kuma na rikesu daya bana bambantawa ina yabawa da nagartarsu da kyakkyawar tarbiyyar da suka samu a gurin malam bani da bakin godiya gareka saidai nace Allah ya saka da alkairi kayi mana komai matsayin ka na me gida baka ta'ba gajiyawa damu ba ta bangaren abinci sutura harda kud'in kashewa na ihsani ka biya dukkan komai nauye nauyen dake kanka ka sauke ka karemu mu da karfinka da jarumtar Allah fatana a koda yaushe Allah ya kyautata ka kamar yadda ka kyautata mana" ta karasa maganar tana share hawaye.
"Amin nagode sosai Salamatu da shedar arziki da kikai min ina da ya'kinin cewa ko bayan raina zan samu yabo a gareki" juyawa yai saitin Ramatu yana cewa "Ramatu saura ke na dawo gareki kema meke damunki me yake faruwa akwai abinda ake miki wanda bakya jin dad'in sa".
Gyara zama Ramatu tai "nikwa ni akewa abinda raina baya so dan duk gidan nan babu wanda aka rainawa hankali kamar ni Kowacce bola aka d'ebo ni za'a lodawa saboda an tsane ni bansan me nai maka ba gara daka za'bi a zauna aji matsalar kowa sannan Ilyah ma yana da matsala domin munafikan yaran ka Sabi'u da Habu sun ware shi suna nuna masa 'yan ubanci komai su biyu suke babu ruwan su dashi".
Wani kallo Habu yaiwa Ilyah yana cewa "shine yace miki ba ruwan mu dashi sau nawa muna binsa yana zamewa ko abinci da kike ganin muna ci mu biyu ga Ilyan nan ki tambaye shi har gobe idan zamuci sai mun masa magana amma yace Allah ya sauwake to ya kike so muyi iya so muna nuna masa baya gani kema bakya gani bari kiji wata magana daga yau baza mu sake...........................
Katse shi Baffah yai "Habubakar bari kayi shiru haka Ramatu uwa ce gareka".
"Ah dole malam ka gama 'kwarkwance su cewa su wulakanta ni kuma yanzu dan kar nace da hannunka shine harda wani kayi shiru ni uwarsa ce tab Allah ya suturu bu'kwui inji kishiyar 'konanna nikam ban haifeshi ba yaje can kabari ya nemi uwarsa na haifi wanda na haifa".
Kowa kallon Ramatu yake da mamaki duk da dama ba ba'kuwarsu bace amma cewar Habu ba d'anta bane yaje ya nemi uwarsa a kabari bai kamata ba bata kyauta ba.
Baffah yaji zafin hakan da tace amma ya share cikin kaiwa zuciyarsa nesa yace "Ramatu wannan shine abinda yake damunki sun ware Ilyasu a cikin su babu ruwan su dashi haka ne"?.
"Eh haka ne basa kaunarsa kuma idan sharri na musu ko suna ganin na musu karya ka tambaye su basa kaunar Ilyah sam".
Kai Baffah ya jinjina "shikenan naji matsalar ki bari nayi magana dasu" kallon Sabi'u yayi yana cewa "Sabi'u meye matsalar ka matsayinka na babba cikin 'ya'yana kaine jagoran gida".
Fara magana Sabi'u yayi "ni Baffah damuwa ta rashin biyayyar da Ilyah yake maka da zama cikin samari yan shaye shaye da yake bugu da 'kari kullum idan muka ce yazo muci abinci ko kallon arziki baya mana matsayin mu na 'yan uwansa baida kamar mu a duk fadin duniya ko me zaiyi saiya yi shawara damu Baffah ka fahimtar dashi ka farkar dashi ka tuna masa matsayin mu a gunsa".
Yana rufe baki Ramatu ta wurga masa harara tana cewa "dama har wani matsayi kuke dashi a gurinsa in kuna tunanin kuna da mahimmanci ku daina Ilyah ba sa'an shirmenku bane abinci kuma bazai ci daku ba wannan doka tace dana kafa masa har abada".
Cikin 'bacin rai habu yace "to saime dan kin hana shi hakan bazai rage mu da komai b.....................
"HABUBAKAR kayi shiru dan Allah ka bari Ramatu uwace a gunka" Salamatu ta fad'a tana d'aga masa hannu huci Habu keyi ransa duk babu dad'i amma sakamakon Salamatu tayi masa magana yasa dole yai shiru bai amayar abinda ke cin ransa ba.
Baffah baice 'kala ba ya kalli Ilyah dake gefe kamar ba babu shi a gun yace "saura kai Ilyasu muna sauraron ka meye matsalar ka".
'Dan tsaki Ilyah yaja yana kau dakai kamar bazai magana sai kuma yace "ni bani da matsala kalau nake rayuwa ta idan akan haka ka tara mu ni zan fita dan ina da gurin zuwa daya fi min wannan zaman".
Kaiii duk kallon sa sukai a hasale Habu yace "Allah ya wadaran ka Ilyah wallahi kaji kunya kayi asara wannan d'abi'ar daka dauko sam babu inda zata kai ka sai halaka tun wuri ka gyara kafin lokaci ya'kure maka".
"Ban sako dakai ba Habu kada na sake jin bakinka yace min wani abu idan ba haka ba ran kowa da yake nan saiya 'baci" Ilyah ya fad'a tare da mi'kewa ya kalli Baffah dake binsa da kallo kafin yace.
"Kaja masa kunne ya fita harkata kafin ayi 'batacciya sai nayi abinda kowa zaiyi danasani".
"Yau d'an halak haka nake son ji karka ragawa kowa" Ramatu ta fad'a tana hararar Habu.
'Diban takalmansa Ilyah yai zai fita Baffah ya dakatar dashi "kada ka fita Ilyasu bamu gama magana ba ka zauna ban baka izinin tafiya ba".
Batare da Ilyah ya juyo ko ya dakata daga tafiyar da yake yace "dama umarnin ka nake nema saika sani abu zanyi basan zauna ba na fita zaka iya sawa a taro ni".
Da kallo suka bishi yana fita Baffah da gabadaya zuciyar sa ke masa zafi take masa shiru yayi ya rasa me zaiwa Ilyah ya dawo kan hanya addu'ar nan kullum yi yake ba fashi amma abun na Ilyah gaba yake saidai bazai 'kosa ba zaici gaba da nema masa shiriya...................
"To nima dai zan tashi dan na gaji bacci nake ji" Ramatu ta fad'a tana mikewa ta shige d'aki tare da rufo kofa.
Har lokacin Baffah yana shiru ganin yanayin yasa Sabi'u cewa "kayi hakuri Baffah mun 'bata maka rai ka yafe mu na dauka idan muka samu zama zamu fahimci juna ashe saidai mu fahimci damuwa munyi kuskure bansan me zamuyi yanzu ba na kasa gane komai".
"Me zamuyi kuwa daya wuce hakuri da addu'a dan Allah Baffah kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka insha Allahu komai zai setu" Habu yai maganar.
Ganin dai jiya iyau Baffah baice komai yasa Sabi'u cewa "BAFFAH ka gafarce mu dan Allah idan mun saka a wani hali".
'Dagowa Baffah yayi yana kallon su tare da girgiza kai yace "Sabi'u Habu Allah ya muku albarka baku ta'ba 'bata min ku farin ciki nane ina alfahari da samunku ina fata ku kasance cikin farin ciki har abada Allah ya tsare min ku ya shiga al'amarin ku ya baku 'ya'ya da matan aure na gari yasa ku gama da duniya lafiya duk abinda kuka san zaisa naji dad'i kuna kokarin yi min Allah yasa kuma ku samu masu yi muku".
"Amin Baffah mun gode sosai".
"Karku damu kuje ku kwanta" mi'kewa sukai suna masa saida safe ya rage daga shi sai Salamatu da Lami kallon Lami yai yana cewa "kiyi hakuri ke ba'a tambayi taki damuwar ba ko"? Kai Lami ta girgiza tana share hawaye cikin takaicin abinda taga Ilyah ya masa tace "ka gafarce ni Baffah ka yafewa yaya Ilyah abinda yake maka ka bishi da addu'a ka masa fatan gamawa da duniya lafiya shine fata na".
Kallonta Baffah keyi yarinyar nan za'a tona kafin a samu irinta zai wahala shiyasa koda yaushe yake farin ciki da samunta matsayin 'ya gareshi sake kallonta yayi yana cewa "kada ki damu indai wannan shine burinki zan cika miki tashi kije ki kwanta" mi'kewa tayi tana masa saida safe ta tafi, numfasawa Salamatu tai tana kallon Baffah tace.
"Malam na sani kana cikin damuwa a gidan nan mun gaza gyara zamantakewar mu badan bazamu iya ba sai rarrabuwar kai nayi tunanin a yau zamu magance matsalar mu amma sai naga abun yaci tura dan Allah malam kayi hakuri" kai Baffah ya girgiza "babu komai Salamatu tashi kije Allah ya mana sutura" Amin tace tana mikewa itama ta shiga d'akinta aka bar iya Baffah a tsakar gida yana sa'ka da warwara ya dad'e kafin ya mi'ke yana daukar buta yai alwala ya shiga d'akinsa ya fara nafila yana rokon daidaituwar al'amari a tsakanin zaman zuriyar gidan sa.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘 MAI TAMBARIN YMA DUTSE 🏞️🏔️ JIGAWA STATE.
TYPING 📲 SAT, MAR 23/24 Yusrah Musa Abubakar 💞🌹 maman little Zaran aunty.
💫 ANNURI WRITER'S ASS💫 HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY GIDAN KARBAR MUTANE HANNU BIYU 🌹🥀 DA ZAMAN LAFIYA ANNURI HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI 'YA'YAN TA KIRARIN MU KENAN.
Ya mai nasiha ga alumma muso juna mu rike gaskiya amana dan gudun kuna mu raya zuminci hanya ne na aljannah makiyin zumunci baya kusanci ceto ba ga wassu baitukan soyayya maula na daga masoyiyar ka Yusrah ta dumus yar Musa.
_______________________
Allahu dan isar bawan nan da ka Aiko shine Muhammad rasulullah daya sauko me sansa ka fad'i ba shakka zai karko albarcinsa bani basira me fad'i ka bani hikkimar sarrafa waka alhadi idan nayita bata ga buri aji dad'i a kara kankame soyayyar manzo na.
💋YUSRAH MS ABUBAKAR MUHAMMAD💋.
23~AR-RAFI'U
The exalter
24~AL-MU'IZZ
The giver of honour
12~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Khaidinah.
🌄THREAT ND TREASON🌄
Episode 23 nd 24
Bayan kwana biyar da faruwar haka Tanko ya dawo daga d'an yawon shashancin daya je ko hutawa baiyi ba Mudi ya munafirta masa cewa Lami fa ta dawo ya kamata suje su lallameta kafin wannan d'an birnin ya biyota idan sukai sa'a ta amince zata aure shi yarda yai da shawarar Mudi yace gobe zasuje.
Washe gari da magriba suka je kofar gidan Baffah suka sa aka yiyo musu magana da Lami tayi mamakin ganin Tanko har mamakin nata ya'ki boyuwa ranta a'bace tuna wulakancin dayai mata a dandali kwanan baya tace "meye ya kawo ka Tanko ko 'batan kai kayi tun wuri ka saitawa kan ka hanya".
Tanko na shirin yin magana Mudi yai gyaran murya yana cewa "haba Lami kamar baki le'ka birni ba zaki mana wulakanci sannan baki tsaya kinji abinda zan fad'a miki ba kawai kika yanke hukunci".
A fusace Lami tace "baka da wani abu da zaka fad'a min wanda zaisa na saurari Tanko kamar yadda ya tozarta ni a gaban kowa nima tun daga ranar na zubar dashi a rayuwa dan haka ka barni dan Allah naje nayi rayuwa ta".
Zata juya Tanko ya katse ta "haba Lami ki tsaya ki fahimce ni muyi maganar gaskiya nasan na aikata miki kuskure banyi dadai amma kiyi hakuri kinsan ina son ki".
"Na sani kuma na gode da soyayyarka gare ni saidai ka sani ka makara domin na riga na hakura dakai Tanko dan haka ka kyale ni nayi rayuwa ta".
"Bazan rabu dake ba Lami har sai kince zaki aure ni kin rabu da wancan shashashan tsigalallan birni".
"Kada ka sake zagin sa".
A hasale Tanko yace "na sake shi dambun uban sa wato kinje ya zuzzuga ki shine zaki min rashin mutunci" "ba rashin mutunci nayi maka ba Tanko kawai na nuna maka gaskiya ne kayi hakuri bazan iya aurenka ba na riga na hakura dakai dan Allah ka fahimta ka rabu dani".
Kai Tanko ya jinjina "shikenan na barki har abada kuwa jeki abinki" yana rufe baki Lami ta fad'a gida da sauri kai Tanko ya jinjina yana jan tsaki yace "lallai yarinyar nan ta kira ruwa saina gwada mata rashin imani na dan ko yayanta Ilyah bai isa jada niba balle ita" cikin zuga Mudi yace "to ai mutumi na kaine kayi sake taya zaka bari yar wannan yarinyar ta ri'ka kallon cikin idonka tana zazzaga maka rashin mutunci baka falleta da mari ba wanda saita ga wuta ba wallahi kada ka hakura ka dau fansar wannan abun da tayi maka" "fad'a batawa Mudi ai dole na sanyata bakin ciki kamar yadda ta sanya ni dole na rama cin fuskar da tai min kuma ta hanyar da kowa bazai ji dad'i ba muje kawai Mudi yau saina kora sosai kaina yadau zafi" wucewa sukai Mudi na sake zugashi da bashi shawarar yadda zaiyi.
Zaman Lami haka babu islamiya yana damunta tana son shiga tana tsoron masifar Ramatu ta kasa fad'awa Baffah gashi tun ranar da aka kawo ro'kon arzikin ta Ramatu ta sake bud'e mata wutar talla kamar jaka wai saita tara kud'in da zata sai mata kayan d'aki Baffah yayi fad'an har ya gaji ya 'kyale.
Lami na zaune a kofar d'aki tayi tagumi Baffah daya shigo cikin rashin jin dad'in ganin ta a haka yace "Lami lafiya meya faru"? Hawaye ne ya zubo mata tana kallon shi tace "dan Allah Baffah na rokeka ka sani a makaranta ko ta islamiya ce nima nayi karatu" sauke ajiyar zuciya yai yana rike hannunta yace "karki damu kinji share hawayen ki insha Allahu gobe da kaina zan raka ki har islamiya gurin malam Haruna yasa sunan ki cikin d'alibai ki fara zuwa daga baya saina dinka miki inifon tunda kinga Alpha din yace a 'kara masa lokaci bai 'karasa gini ba saiki fara islamiyar kafin lokacin ina haka kike so"? Kaita d'aga tana murmushi cikin jin dad'i tace "shima yace min zanci gaba da karatu na bayan bikin nagode Baffah Allah ya saka da alkairi" "Amin karki damu" Baffah na barin gurin Lami da murnarta ta tashi itama tana shiga daki tace.
"Babah gobe Baffah yace zai kaini islamiya" Ramatu dake daurin gyada soyayyiya sai tumurmusa take jin abinda Lami tace yasa zatai magana ta 'kwaru tari ta ri'ka jerawa har shid'ewa da'kyar tace "kawo min ruwa" fita Lami tai ta debo mata bayan tasha tana numfashi tace "Kika ce gobe Baffah zai kaiki islamiya? Heeeeh lallai kam yau ake yinta to bari kiji wallahi baki isa ki makaranta ba abinda na yanke kenan wacce kika je ki kai a wudil din ma ba'a son raina bane talle zaki min kowa na neman kud'i ni kuma saboda da mutuwar zuciya gaki nan rid'ad'a ina kallon ki saidai kici kisha kije makaranta? Tab garama kisawa kanki salama babu wata makaranta da zakiyi idan ba haka ba lokacin aurenki saidai a kaiki daki hororo ba kaya".
Cikin kuka Lami tace "dan Allah babah ki barni nayi wallahi ina son makarant.................duka Ramatu ta kawo mata tana cewa "ubanki yahau baro🙊 ina magana kina musa min bazaki makarantar ba talle zaki kuma na fad'a zaki tashi ki dauka ki fita ko saina miki shege dukan da zaki kasa tashi shima malam din ina nan daidai dashi" mi'kewa Lami tai tana kuka ta dau farantin gyad'a ta bita Ramatu data bita da kallo tace "kuma saura kije ki zauna a guri daya idan kika dawo min da saura saikin gane" Lami dai bata sake tofa koda alif ba ta fice ta nufi matallata.
Bata fara ciniki da wuri ba sai jikin magriba kasuwa ta bud'e bayan sallar isha Lami ta baro dandali ta sayar gyad'ar tas sai farantin kawai a hannun ta jin taku ana bin bayanta yasa da sauri ta waiga ganin mutum yasa tace.
"Waye"? Shiru ba amsa a tsorace tasa gudu wanda shima ya rufa mata baya ga duhu ga matsatstsan layi tuntu'be tayi da dutse ta fad'i 'kara ta saki daidai ya iso waje da sauri ya toshe mata baki tare da kinkimar ta ya shiga wani kango da ita.
A tsautsayi ya daka mata tsawar cewa ta masa shiru cikin mamaki Lami tace "Tanko kaine me nai maka ka sake ni" kallon ta yayi "oh kin gane ni ashe aiko saina tabbatar ban barki kin kai labari ba yau babu me cetar ki a hannu na yadda kika haramta min auren ki shima wancan mayen da kika wulakanta ni akan sa saina tabbatar bazai same ki ba".
Cikin karfin hali Lami tace "Tanko wulakancin ya isa haka ka sake ni kuma wallahi bazan yarda ba gobe saina kai kararka gurin me gari" dariya yayi "ki kai karata gun wanne me garin? Basai na barki da rai ba balle ki kai labarin" jin abinda yace yasa ta fasa kara tana kai masa duka ta ko'ina shi kuma yana 'ba'bbaka dariya kamar zararre.
Ramatu na zaune lokaci zuwa lokaci ta kalli hanyar kofar shigowa ganin shiru babu alamar ta yasa ta mi'ke tana daukar hijab tace "a'a ni kalau kuwa Lami yau bata dawo ba bata irin wannan daren a dandali bari muga" fita tai ganin yar ma'kotansu abasiyya ta taho yasa Ramatu cewa "ina kika baro lami ko tana can"? Kai abasiyya ta girgiza "a'a ta ma riga ni tahowa saidai in a wani gun ta tsaya" jin haka yasa Ramatu wucewa ta nufi dandalin tana zuwa layin taga farantin da kud'i a baje a gurin salati tayi tana tattare kud'in tare da daukar farantin cikin mamaki ta kalli gabas ta kalli yamma babu alamar kowa da sauri ta fito a layin kamar zata kifa ta koma gida hankali tashe tan kururuwa azo a cece ina Lami tai nan gari ya hargitse aka d'ebo fitilu ana haska ko'ina tace ga inda taga farantin gurin suka je suka fara haskawa har cikin kangon gidan aiko sai gata kwance sharkaf bata motsi jikin ta harda jini da alama fayde akai mata innalillahi wa inna ilaihi raji'un guri ya kaure da salati Ramatu dake waje jiki na rawa tace "meya faru an ganta ne"?..........
Tana rufe baki taga Sabi'u da Habu sun fito dauke da ita ihu ta saki tana cewa "na shiga uku na lalace yau ranar tonon asiri tazo Lami wanne d'an diban albarkar wanda bazai gama da duniya