Showing 39001 words to 42000 words out of 130249 words
da sanyawar albarkarsa da samun zuriya ta gari sannan ya ro'ki Baffah akan zai tafi da Lami su Naja'atu sun damu ta koma tunda hutu ya rage saura sati daya a koma Baffah kuwa dad'i yaji a take yace ta dauko kayan ta su tafi itama Lamin taji dad'i sosai da sauri kuwa ta had'a komai bata ta shirya ta bisu suka tafi.
Bayan tafiyar su Ramatu ta dawo batasan me ake ba hakkinta na uwa itama dole ya fad'a mata tasan abinda ke faruwa bazai biye halinta ba zata wuce yace.
"RAMATU" da sauri ta waigo ganin kaya turus a gaban Baffah yasa ta washe baki tana cewa "na'am malam gani nazo ne"? "Eh magana zamuyi" kamar an jefota yaga taxo ta zauna tana le'ken babbar ledar dake gaban sa yace "to malam gani nazo in kaji kira an samu amma banda kiran dan sanda".
Shiru Baffah yai yana kallon ta ganin baice komai ba tace "malam ka kira ni kuma kayi shiru"?.
Sauke ajiyar zuciya yai yana cewa "ina fata yanzu kam zaki fahimce ni duk da nasa ke baud'addiyar mace ce wacce ba'a gane inda al'kibilar ki take amma ya zama dole na fad'a miki yau dazu bayan fitar ki Musbahu yazo tare da wani mutum wanda d'ansa yake son Lami sunzo nema masa aurenta kuma na basu duk da banyi shawara dake ba amma ya kika ce kema mahaifiyar tace kina da hakki a kanta ga dai kayan da suka kawo nan da kud'i".
Zaro ido Ramatu tai gani kud'i daure a kyaure dami guda baki washe tayi tana cewa "ayya malam ai bakai laifi ba meye a ciki basai kai shawara dani ba ai kaida kaya mallakar wuya ne" ta karasa maganar tana dauko 'kwallelan goro daga cikin ledar ta soma garza tana cewa "yaushe zasu sake dawowa ne nifa ban gane cewa mutumin nan yana son Lami ba saiyau kace gara daya dauke ta suka tafi gashi harda abin arziki ta samo saurayi d'an birni" kai Baffah ya jinjina lallai kam wato idan akace mutum nada son zuciya sai a hankali yayi mamakin ganin yadda Ramatu ta amince Shi dai farin cikin sa daya Lami zata bar kauyen nan taje ta zurfafa karatun ta tayi ilimi ta cika burinta.
"Malam me kake tunani"? Ramatu ta fad'a tana sake cewa "malam aban nawa kason zan rabawa dangi" .
Cikin mamaki Baffah yace "kason me"? Kud'in dake gefe ta nuna tana cewa "garin su Mariya zanje in an jima nasan kayan lambu sunyi na saro Lami ta fara min talle" "telle kuma"? Baffah ya fad'a yana kallon ta "eh talle saita tara kud'in da za'a saya mata yan kayan d'aki da kayan katako" "a'a indai dan wannan ne ki barshi ni zanyi mata komai".
Daina cin goron Ramatu tayi bakinta daya sauya kala zuwa ja ta bud'e shi tana cewa "amma dai malam zilama ce tasa kace haka"? Wani kallo Baffah ya mata tare da maimaita kalmar "zilama"? Ba kunya Ramatu tace "eh zilama nace kake dashi malam bada zilan zilan irin taka ba da had'ama taya zakace kaine zakai mata kayan d'aki dan karka bani ko sisi shine kace wani kaine zakai mata to wallahi bazan yarda ba domin nice nayi na'kuda na haifeta na fika iko da ita wato dan ka je ka sayi ru'babbun Kaya shine kace a barmaka ragamar komai a hannun ka".
"Ramatu meyasa ko kadan baki da tunani? Ni kike cewa haka? Bansan ranar da zaki hankali ba shiyasa kullum nake godewa Allah da bai sa Lami tayo halinki ba" mi'kewa Ramatu tai "malam me kake nufi kenan karya nayi"?.
Ransa a had'e yace "ban sani ba ban guri" wucewa Ramatu tayi tana cewa "wallahi kome zai faru bazan yarda malam ehe idan kuma ba haka ba saidai a fasa auren" Baffah bai sake kulata ba ya tattare kayan da kud'in ya shiga d'aki.
Nan labari ya kardad'e gari ko'ina sai gulma ake wai Lami tayi saurayi d'an birni zata koma can tabar rayuwar kauye lokacin da labari ya iske Tanko hankalin sa ya tashi haka nan yaji yaji bayaso ta auri wani nan ya fara shiga da fita ya rasa inda zaisa kansa yaji dad'i dan haka ya yanke shawarar zai samu iyayen sa suje nema masa auren Lami ba haku yai ba.
Abokin Tanko Mudi wanda ba'a ganin tsakanin su shi Tanko ya samu yana fad'awa matsalar sa yace kuma ya bashi shawara Mudi yace masa kawai suje su samu Lami idan suka hure mata kunne tuni zasu rusa ala'kar ta da d'an binnin saiya aureta Tanko ya yarda haka zaiyi idan ya samu ya shawo kanta saiya lalla'ba ya saki Karime tunda d'akin sa daya ne.
Lokacin da Tanko ya samu iyayen sa da wannan maganar sunyi mamaki kuma ransu ya 'baci cikin fad'a Delu tace "a lallai Tanko ka raina mana hankali wa ma naji kana zaka aura Lami ko? To wallahi ko Ramatu ce baka isa ba aidai itace ta haifi Lamin ko? gaskiya Tanko ka cika mara tunani Lamin data za'bi birni ta share ka ta manta dakai shine yanzu saboda baka da zuciya kai kuma kake kokarin rufa mata asiri bayan ta tona maka kai kuma sakarai kawai".
Shiru yai yana sauraren su malam balah shima da haushi ya gama cika shi yace "kai Tanko kada ka kuskura naji ka sake firta sunan Lami a gidan nan baka da hadi yanzu da ita ko mutuwa zakai baka isa ka auri Lami ba kuma abinda na yanke kenan" tashi kaba mutane guri shashashan banza shashashan wofi" tashi Tanko yai yana fita a majalisar su ta matasa masu shaye shaye yan iskan gari yaje ya zauna ba sukuni kowa yana harkoki suna ta busa haya'ki amma shi yayi shiru ransa a mugun'bace.
Ta'bo shi Mudi yai yana bashi sigarin dake kunne yace "mutumi na kadan busa ko zaisa ka kadan ji dama dama" kai Tanko ya girgiza batare daya kalli Mudi ba 'kara matsowa kusa dashi Mudi yai yana yin kasa da murya saboda Ilyah na gurin yace "aboki na ko akan maganar Lami ne su baba sun amince"? Kai ya sake girgizawa yace "taya zasu amince sai fad'a suke min da ihu wai ban isa ba kuma wallahi idan kaga ban aure taba to numfashi nane ya yanke domin ina son ta bazan yarda ta auri wani bayan niba ko meye zai faru har kisa zan iya yi" kasa da murya Mudi yai yana cewa "kaga Tanko ka daina d'aga harshen ka dole ne na taya ka cika burinka ka shirya gobe zamuje gurin ta muji ta bakinta in ta amince saika dauketa ku gudu kaje can wani gari ka aureta daga baya kamar shekara biyar sai ku dawo nasan duk tsiya idan kuka dawo baza suce komai ba dole su barku kuyi rayuwar ku wai mutum da ransa da lafiyarsa a hani shi jin dad'i"?.
Tsaki Tanko yai "gane min hanya makaho yaso gulma amma ai su ba komai suke ganewa ba nabar haka a gigin tsofa ke damunsu amma zan saita musu zama" kai Mudi ya d'aga "yauwa aboki gaskiya suna takura maka gara ka nuna musu kaima na zamani ne d'an duniya ne shiyasa ni nake murna da nawa suka gangara tun ba yanzu ba gashi ni kadai suka haifa ba wa ba 'kani ga gadon gonaki sai fanjan fanjan nake da kud'i kaima ina maka fatan haka" kai Tanko ya jinjina yana cewa "idan mutum ya'ki mutuwa sai a 'karasa shi" dariya Mudi yayi yana cewa "kai mutumi na kana wuya ina binka da fetur haka ake so ka nuna kai d'an zamani ne me zama kan uwar d'an yaro, kaga karbi haya'kin nan ka d'an ja zakaji dad'i" karba Tanko yai yana sawa a baki Mudi ya sake dauko wata ya kunna.
Kwana uku da zuwan su Musbahu Ramatu ganin babu Lami babu alamarta yasa tace "malam nifa kwana biyu banga Lami ba ina taje ne"? Kallonta Baffah yai "au sai yanzu zaki tambaye ni inda take duk da baki lura ba? Ta bi ubanta sun tafi" so'ko'ko Ramatu tayi tana kallon Baffah tace "waye kuma ubanta bayan kai"?.
"Musbahu ranar da suka zo ro'kon arzikin ta yace an kusa komawa makaranta kuma yaransa sun damu da rashin ganinta shiyasa nace kawai ta shirya su tafi".
Zaro ido Ramatu tai tana mi'kewa tsaye tace "meeehhh😲 sun tafi kuma? Wai komawa gurin sa ta sakeyi kenan lallai Lami ta raina min hankali tabdijan wallahi bazai yuwu ba sai naje na taho da 'yata bana son harkar gidadanci dan yaga wancan karon daya dawo da ita na share shi shine yake neman tashin hankali aiko ya sameshi tunda ya ta'bo ni".
'Daki ta wuce tana masifa ko kayan jikin ta bata sauya ba du'kun du'kun haka ta dauko kud'i ta fito tana cewa "malam nayi wudil zan taho da 'yata tunda naga idan na zuba ido za'a raba ni da ita ayi min haifi in mora ina zuwa zan wuce ofishin 'yan hisba sai an mana iyaka dashi babu shi ba 'yata har abada ehe".
Ci kanki Baffah baice mata ba tayi hanyar fita da sauri da wasu ru'babbun takalma a 'kafarta da kallo Baffah yabi ta baice mata kar kije ba ko dawo ko bada yawu na ba ya share ta tayi gaban kanta "malam bakace min komai ba"? Ramatu ta dakata tare da juyowa tana kallon sa dauke kai yayi daga saitinta bai tanka ba, "malam kana jina kayi shiru wato baka so naje na taho da 'yata ko"? Jin har lokacin yayi mata banza yasa tace "malam ko zakace daga wudil idan na dauko Lami na zarce gidan mu wallahi bazan fasa ba sai naje ballantana baka tanka min nikam nayi gaba malam sai ayi zaune ayita jiran tsamani" tana kaiwa nan tayi gaba.
Shiru Baffah yayi yana sake kallon kofar gidan gashi magriba ta kusa ya tabbata kafin taje anyi sallar isha ba sanin anguwar tayi ba kawai saboda neman rashin zaman lafiya ta d'ebi kafa ta tafi........................
"BAFFAH" jin an kira sunan sa yasa ya d'ago ganin Sabi'u yayi tsaye da murmushi a fuskarsa yace "zauna man" zama Sabi'u yayi yana cewa "Baffah ga tsire inji Habu yace a taho ma dashi daga kasuwa ba yanzu zai taho ba ni kuma ga kayan marmari na sayo maka Baffah kasha" kallon Sabi'u Baffah yayi yana cewa "to sannun ku da kokari Allah ya muku albarka ya 'kara bud'i ya haskaka lamarin ku" "Amin Baffah kuma na had'u da malam Yahuza yace na gaishe ka" "ina amsawa sosai Allah yai albarka" mi'kewa Sabi'u yayi yana cewa "Amin Baffah" kafin ya dauki buta ya d'ebo ruwa yana mi'kowa yace "lokacin sallah yayi Baffah" kar'ba yai cikin jin dad'i yace "Allah yayi albarka abun da kuke min Allah ya baku 'ya'ya masu hali irin naku su rama muku Allah yasa su faranta muku" "Amin Amin Baffah mun gode da addu'ar ka garemu" "a'a ba komai Sabi'u jeka maza kayi alwala ka taho masallaci kar lokaci ya 'kure" to Sabi'u yace yana shiga d'akin Salamatu itama ya bata nata sannan ya fito yana daukar butar da sauri jin ana neman shiga sallar.
'karfe sha biyu da kusan rabi na dare Ramatu na cikin garin wudil tana bulayi tayi nan tayi can ta rasa inda zata sa kanta da wani mutum suka had'u da sauri tace "dan Allah kasan wani Musbahu"? Kai ya girgiza "ban sanshi ba zaki iya karawa gaba" yana fadin haka yai gaba da harara Ramatu tabi shi tana cewa "ji min mitsiyaci kada Allah yasa ka sani shashasha kawai mai ba'kin hali" cigaba tayi da tafiya sai tambaya take kowa yace bai san shiba takaici ne ya kama Ramatu ga gajiya ga yunwa harda bacci take ji ganin ta rasa mafita ga jama'a sun fara raguwa a layi sai ihun karnuka yasa ta samu wani bakin shago ta zauna tana zafga hamma ta kalli gabas ta kalli yamma.
Tsaki taja tana cewa "wannan wacce irin ba'kar jaraba ce ace idan mutum yazo gari baida kowa shikenan ya zama bola ba Wanda zai kula ka balle yaji matsalar ka ya taimake ka bari na tsaya na kwana anan din kar nayi gaba na had'u da kare gari na wayewa zan cigaba da cikiya................................
Ihu taji an kurma da karfi ana cewa "ihuuu jama'a ku fito 'barawo ku bishi gashi can yayi ta nan ku dauko abin duka haba da sauri Ramatu ta mi'ke tsaye tana gyara daurin zani tace "tofa yau nake ganin bankad'a iri iri wanne irin barawo kuma........ji tayi ana gashi can ku harbeshi kada fa ku bari ya tsere kallon gurin tayi aiko ta hango barawo yana cin gudu ana binsa ganin ya nufo wajen inda take yasa da sauri tayi gaba a guje taje shan kwana a bisa tsautsayi ji kake gammm!!!! Tayi karo da mutum tuni tayi baya rim ta fad'i cikin azama mutumin ya d'aga kokarar dake hannunsa ya buga mata a goshi yana saki ihu yace "kuzo da sauri ga barawon na kama shi" 'kara da kururuwa Ramatu keyi tana cewa "shikenan mitsiyaci ya kashe ni ya fasa min goshi Allah ya tsine maka bankad'adde mugu azzalumi".
'Duuuu jama'a sai tittid'owa suke kamar anyi kiranye tuni aka cika guri baka jin komai sai hayaniya wani daya dalle Ramatu da gitila irin ta kamun 'barayin nan yace "kai abin mamaki mace ce ai? Ke kuwa me zaki sata a daren nan kina mace"?.
Haushi ne ya kama Ramatu ganin zai raina mata wayo tace "sata? nayi maka kama da 'barauniya tsabar mugunta kun fasa min goshi daga zuwa na garin ina ruwa na da wani barawo da kuka biyo wallahi Allah ya isa ban yafe muku ba" mamaki ne ya kama su wani daya furmutso ya le'ko cewa yake "ga barawon can fa an kama shi yana hannun matasa ita kuma wannan me take anan naga an kewaye ta ga jini a gaban goshi"?.
Wata uwar harara Ramatu ta sakar masa tana cewa "au tambaya kake zakuyi bayani duk sai kun had'u da masifa bazan ta'ba yarda ba tunda kukai min rauni".
"Kunga kamar naga bata hayyacinta ku tafi da ita gidan me anguwa ta kwana da safe ayi komai" wani da yake rike da bindigar mafarauta ya fad'a yana kallon sauran mutanen.
Kallonsa Ramatu tayi "ubanka ne baya hayyacinsa amma ni nasan abinda nakeyi" wanda ya bugeta kam yana gefe ya kasa magana shi wallahi da yake a rud'e yake ganin yai kamar naminji ya daka "baiwar Allah tashi muje a raka ki gurin me anguwa" mi'kewa Ramatu tai tana cewa "uban gurin me anguwa zaku rakani dama gurin sa akace muku nazo ni gurin Musbahu nazo wani ri'kekken d'an mafiya mai sace yaran mutane da sunan zasuyi karatu idan yaga kwana biyu abu ya tsirga saiya sayar maka da d'an ka shikenan idan kana jina ka fito da kai nake" mamaki ne ya kama kowa a gurin lallai kila ta samu ta'bin kwakwalwa dan haka babu wanda ya biyeta da'kyar suka lalla'ba suka kaita gidan me anguwa dan ta kwana kafin gari ya waye ayi bincike koda wanda ya santa.
Washe gari Musbahu na zaune a irin gurin me sayar da shayi yaji ana labarin yaji wani na cewa "kai jama'a ban taba ganin mace fitinanniya irin wannan matar ta jiya ba ta zage sai zagin mutane take" dariya d'ayan yayi yana cewa "humm kai dai bari kawai nifa nafi zaton mahaukaciya ce" me shayi dake tafaman shekawa yana mikawa yace "tab ba wani hauka daya sameta wallahi in kaga irin haka dama hali ne a jikin rai wazai yi fatan ace wannan uwarsa ce Allah ya kiyaye" Wanda yazo yanzu ya zauna ne ya tari zancen da cewa "ai abokai babu abinda zai baka dariya kamar da tace wai tazo gurin wani d'an mafiya ne mai sace yara da sunan zai sa su a makaranta idan kwana biyu yaji anyi shiru saiya sayar maka da d'an ka" dariya suka sa Musbahu dake zaune jin abinda suke cewa yasa ya shiga tunani kodai Ramatu ce ta biyoshi yasan zata iya ba karamin aikin ta bane kar abu yai nisa ma ta jawo masa masifa magana taje gurin hukuma bari yaje ya gano da mamaki fal a ransa ya kasa magana mi'kewa yayi yabar gurin dan yaje ya tabbatar abinda yaji suna fad'a gaskiya ne.
Gida ya koma ya samu mama a waje tana d'an ayyukan safe ganin sa haka yasa tace "lafiya naga kamar akwai wani abu da ke damunka"? Zama Musbahu yayi yana cewa "eh ba lafiya ba yanzu dana baro gurin baban Khairat me shayi naji wani zance wai jiya wata mata tazo tana neman gidan Musbahu d'an mafiya yana sato yaran mutane yazo ya sasu a makaranta bayan kwana biyu idan yaga iyayen yaran sun dauke kansu saiya sayar dasu shine tsoro ya kama ni kar naje ko Ramatu ce kinsan zata iya zuwa".
Zaro ido mama tai cike da mamaki tace "tofa gaskiya ne ma itace tunda kaji tace Musbahu kuma yana sato 'ya'yan mutane ai kasan itace yanzu tana ina" sauke ajiyar zuciya yai yana cewa "tana gidan me anguwa naji suna cewa" "to mezai hana kaje ka gani idan ita dince nifa bana son gayyar fitina sai a bata yarta mu samu salama tunda abun haka ne" kai Musbahu ya girgiza cike da damuwa yace "ina son yarinyar nan ta zauna a guna tayi karatu bana son ta koma wannan 'kauyen" "to ya zamuyi bamu muka haifa mata 'yaba dole mu ha'kura mu taba kayarta inda rabo tunda ga Alpha zai aureta kaga dai zata dawo kusa damu" mi'kewa Musbahu yayi "to shikenan bari naje na gani Allah yasa ba ita bace" "Amin mama tace daidai ya fita su Najat sun fito a d'aki suka ce "wace abban mu ke cewa Allah yasa ba ita bace"? Juyawa mama tai tana kallon su tace "ba kowa kuzo kuyi mana kayan karyawa" karasowa sukai Naja'atu ta dauki wu'ka ta soma firar dankali Lami kuma ta tafi kitchen zata dora tunkuyar shayi" Yusuf dake tsaye kusa da mama yace "to ni kuma me zanyi" kallonsa mama tayi "me zakai kuwa kana namiji aikin mata ne amma zauna ka taya ni d'aurayar kwanuka" kujara yaja ta roba yana zama suka fara.
A kofar gida