Showing 78001 words to 81000 words out of 130249 words
hanya a jefar kud'in ashe tun a gida ne kuma wallahi kinga muka had'u da malam Habu zai kai 'yarsa makaranta shine ya bani kud'in yace na sai miki" d'an zaro ido tai tana ri'ke baki tace "oh Allah mai baiwa kai malam Habubakar baya gajiya da alkairi Allah ka bud'a arzikin sa ka tsole idon ma'kiya gaskiya Habubakar mutum ne na 'kwarai Allah ya biyashi da mafificin alkairi" Amin Dauda yace harya mike zai tafi yace "am babah tunda an samu kud'in inaga ki bayar a mayar masa abinsa ko" kallon sa tai tana cewa "eh kayi gaskiya kar'bi wannan din kace masa a gida a manta" kar'ba Dauda yai yana fita ya hau mashin d'in ya hango malam Habu ya sauka da jibgin kaya yasa da sauri ya karasa yana cewa "ashe kaga kud'in a gida na barshi ban sani ba na jefarshi" kallon sa malam Habu yai "haba Dauda kuma dan ka gani saika dawo min da kud'ina mayar mata dan Allah ta 'kara jari" cike da jin dad'i Dauda yace "to an gode Allah ya kara arziki" "Amin kai kam karka damu mayar mata" malam Habu ya karasa maganar yana fara d'iban kaya yana shiga gida dasu Saida gama sannan ya zauna kan tabarma a kofar mashigar d'akinsa cikin gajiya ya ce "Binta Kai min ruwa nai wanka a d'an fad'a yau garin da sanyi" to Binta tace tana mi'kewa cikin mamakin labarin abinda ya fad'a mata na had'uwar da sukai da mai girma Alhussain ya nuna mata rigar da Asad d'in ya baiwa Amatu saida ta gama komai ta dawo daidai zai tafi wanka tace.
"Malam amma dagaske ka bashi ita da aure kuma idan ya dawo fa yace yazo kar'bar ta"? Murmushi malam Habu ya "idan ya dawo yace yazo ne dan cika alkawarin sa wallahi Binta zan bashi" 'yar dariya Binta tai tana cewa "tab saidai a mafarki mezai dawo yayi yanzun ma sila ta kawoshi balle ya auri d'iyar talaka" "oh kina mamaki ne"? Kai Binta ta d'aga "eh 'kwarai ina mamaki sosai ma abin da kamar wuya" juyawa yai yana tafiya tare da cewa "ki daina jin mamaki babu abinda gagari mahalicci" da kallo Binta ta bishi harya 'kule sannan ta sauke ajiyar zuciya tana sake zubawa Amatu ido wacce gabadaya ta tattare hankalin ta ga wasan da take da 'kyar karamar Teddyn ta.
Mai nasara Alhussain sun koma gida lafiya saidai bai samu shiga gurin mai martaba ba sai bayan sallar isha yana part dinsa ciki ni'imtaccen 'kayataccen tsararran kyakkyawan falonsa wanda yaji kayan more rayuwa daga shi sai matansa biyu amma daya balarabiya ce da alama itace mahaifiyar Asad dan yana kama da ita zama Alhussain yai suna niyyar tashi domin basu guri su tattauna ya dakatar dasu "a'a kuyi zaman ku ba wani abun bane" komawa sukai suna zama shikuma ya fara bayyanawa mai martaba halin dayaje ya tsinci mutanen wannan kauyen amma yanzu alhamdulillah komai yazo karshe an taimake su da sutura kayan abinci da kuma kud'i su gyara gidajen su" fuskar mai martaba fal da annuri yace "masha Allah sai yanzu naji nutsuwa ta zo min hakan yayi kyau sannu da 'ko'kari d'an uwana Allah ya kiyaye gaba" Amin yace yana mayar da hankalin sa kan Mami yace "baki tambayi babyn kiba Asad gidan rigima" murmushi Mami tai "ai bansan kun dawo ba sai yanzu dana ganka ya hanya" "humm hanya lafiya amma suna bukatar gyaran ta nayi magana da wakilin da Governor ya tura cewa ayi musu titi suna shan wahalar abin hawa a hanyar rairayi yayi yawa" kai mai martaba ya d'aga"eh kayi gaskiya Allah ya taimaka" Amin yace da murmushi akan fuskarsa yace "babyn ki fa yayi budurwa kwanan nan zamusha biki" zaro ido Mami tai "to ikon Allah a ina ya ganta ko a garin take"? tabd'i shifa Alhussain sai yanzu ma ta tuna masa basu tambayi malam Habu sunansa ba balle ya fad'a musu wani abu game dashi yace "tanan munyi kuskure ni ko sunan uban yarinyar ban sani ba" dariya sultana Fatima tai "to harda gurin uban 'ya kukaje ko ro'kon arziki kuka kai daga can 😜" ta karasa maganar da rasha kowa darawa yai Alhussain yace "a'a ba ro'kon arziki mukaje ba ya taho ne fa zai rakota makaranta ya hango su shine yasa aka tsayar da mota yaje gurin su yarinyar shekararta shida😂" dariya Mami tai "tofa shekara shida kace ma karamar yarinya ce" kai Alhussain ya d'aga "eh yarinya ce sosai sunan ta Hauwa"..,...............,.....,.,...
Duk abinda ya faru a gurin ya fad'a musu har kyautar riga da yai mata mamaki ne ya kama Mami tace "to abin nasa babba ne kam gaskiya zamusha biki amma inba shirmensa ba taya zaice a take zaku taho tare" "eh kinga laifinsa ne sone ya kawo haka ni nayi mamaki ma Asad da magana bata dameshi ba amma a gurin bakiji tambaya ba salo salo kamar wani d'an jarida".
Murmushi mai martaba yayi "nidai nafi tunanin ganinta da uniform dayai ne yasa yace ku tsaya nasan waye Asad akwai d'auke kai" yar karamar dariya Alhussain yai yana cewa "ai yaya Asad nada hankali yanzu shekara sha takwas baza ace yarinta ce tasa kawai uniform dinta ya burgeshi ba da gaske na hangi son yarinyar a idanunshi" kai mai martaba ya jinjina "shikenan bamu da ja koma wacece ita muna maraba ta shigo familin mu matsayin 'ya kuma suruka garemu zanso naga yarinyar data sace min zuciyar jarumtaccen jarumin sadaukin yarona miskili kyakkyawan gaske".
Hhhhhh tab dariya su Mami suka fara dan indai aka zo bangaren Asad mai martaba da kansa yake kurara abinsa yayi masa kirari ya kambama shi yaace Asad sawun giwa ne 'badda na ra'kumi saraki sadauki mai gyararran gashi, Mami na murmushi tace "uhm idan da sabo mun saba babyn Mami ya d'aukaka da yawa" kai mai martaba ya jinjina "eh toda ya kikace kina da jane" ri'ke baki Mami tai "a'a masu yaro mukam yan kallo ne" "eh na yarda ku zama yan kallon yayin dazan baku mamaki akan Asad d'ina tun daga yanzu ya fita zakka a cikin su rana daya aka haife su amma fa ya girme musu yanzu domin yahau turbar da babu wanda ya hau".
"Eh wannan gaskiya ne yaya kaima Kazo da magana domin nine shaida bari na tafi dare yayi sha daya ta kusa saida safenku" to Allah ya tashemu lafiya ka huta gajiya" fita Alhussain yai ya barsu suna ci gaba da tattaunawa.
Asad na zaune a bedroom misalin karfe sha daya na dare Ajeeb na kusa dashi sai sharar barci yake shikam yana tsaye jikin window ya d'aga labule yana kallon waje gabadaya tunanin ya hana shi sakat ya kasa nutsuwa balle ya samu runtsawa waya ce kawai a hannunshi ya zubawa photon da sukai d'azu ido yana kallon fuskarta da dariyar datai juyowa yai ganin Ajeeb yai juyi yana magana da alama mafarki yake yasa yaja tsuka yana fita daga bedroom din ya fice a part din nasu ma gabadaya ya kama hanyar shiga garden babu kowa gidan yai shi ji yai wata murya tace.
"ALIYU ASADULLAH🦁".
Dakatawa yai cike da mamakin waye yai masa magana amma ba kowa ya sake duba gabansa da baya babu ko 'kwaro bai fasa ba ya tunkari bud'e kofar shiga garden ya shiga jiyai an sake cewa " 'Dana Asad" da sauri yakai kallonsa 'karkashin wata bishiyar tsohuwa ya gani zaune akan wani farin abu mai walwali tasha kwalliya da murmushi a fuskarta gabanta babban littafi mai girma da tudu" mamaki ne ya kama shi ya tsaya cak yana kallon ta bawai dan ya razana ba sai tunanin wace wannan tsohuwar bai ta'ba ganin taba me takeyi anan? Tambayar dake ransa kenan yaji ta sake kiran sunansa a karo na uku tana masa alamar yaje gareta babu fargaba ko wani tsoro a tattare dashi ya soma takawa zuwa inda take.
"Bismilllah zauna"? Tana rufe baki yaga kujera mai kyau a gefensa zama yai batare da jin ko d'ar ba yana kallon ta ta soma magana "sunana Innah Habibati na sani kai yaro ne mai hankali kuma da akwai tambayoyi a ranka game dani wace ni ya akai nazo nan ni mutum ce ko a'a? To maganar gaskiya ni aljana ce a Duniyar aljanu ni sarauniya ce ina da 'ya'ya guda d'ari shida da hamsim sannan mijina ma yana nan muna rayuwa a cikin daula kamar ku kuma har gobe kasan wani abu? 'Dazu lokacin da kai rakiya wa 'kanin mahaifin ka kun tsaya inda kaje gurin mutumin da yake ri'ke da yarsa kunyi zance a fadata kuma na yaba da hankalin ka shiyasa naji bazan iya barinka ba dan akwai 'kalubale a gaban ka saidai nayi maka alkawari zan zame maka garkuwa bazan bari a cutar dakai ba, d'an shiru tai tana kallon sa sai kuma tace "kalli nan" kallon littafin yai saiya gansu lokacin da suke tsaye a gurin inda yake tambayar Amatu shekarun ta nawa tace talatiin da goma da d'ari" d'an murmushi ya sake wanda baisan yayi hakan ba tare da d'agowa ya kalli fuskar tsohuwar exactly women sak babu wani abu dazai nuna maka cewa aljana ce ta fito a kyakkyawar sura zaiyi magana ta katseshi "a'a basai kace komai ba na sani kaidai karka damu kuma kada ka fad'awa kowa yanzu zan tafi amma zan dawo gareka kwana kusa idan na samu lokaci ka huta lafiya" tana fadin haka ya nemeta ya rasa ga mamakin sa maimakon ya ganshi a garden saiya ganshi a bedroom kusa da Ajeeb lullu'be cikin bargo shiru yai yana zurfafa cikin tunani har zai tashi ya le'ka garden din ta window sai kuma ya fasa tare da gyarawa Ajeeb rufar dayai shima ya rufe jikinsa gabadaya har kansa yana rufe ido.
Washe gari makara yai sosai har gari yai haske Ajeeb nata tashinsa amma saidai yai juyi ya gyara kwanciya haushi Ajeeb yaji sai kawai ya bud'e fridge ya dauko ruwa mai sanyi ga sanyin gari yana zuwa ya watsa masa a firgice Asad ya tashi zaune cikin magagin barci tare da goge idonsa da yai ja zubasu kan Ajeeb wanda ya aje saura ruwan yana cewa "wanne irin barci ne wannan Asad ina ta tashin ka'ki sai sake gyara kwanciya kake"? Harara Asad ya maka masa jin sanyin ruwan na ratsa shi batare dayai masa magana ba ya mi'ke yana shiga toilet zama Ajeeb yai yana cewa "hum lallai yaron nan ka gama raina ni".
Saida Asad yayo alwala ya fito yana kallon Ajeeb kamar bazai kula Shiba sai kuma yace "waye yaron naka"? Dariya Ajeeb yai "ina wani bayan kai a tunani na mu biyu ne kawai a d'akin ba mu goma ba balle kace da wani nake" daidai Asad zai tada sallah yace "liar" zaro ido Ajeeb yai "kanbu nine ma'karyacin"🙄? Asad bai sake tanka masa ba ya fara sallah Saida yayi sallama yayi addu'a ya shafa kafin ya mi'ke yana sake shigewa toilet ya banko masa kofa da karfi har Saida Ajeeb ya toshe kunne jin zai kumanta shi yabi kofar da kallon mamaki yana cewa "amma wallahi baka da mutunci Asad in mace me ciki ce ai sai kasa tayi 'bari......................
Jin ana kwankwasa musu kofa yasa Ajeeb tashi ya bud'e Ameer ya shigo yana kallon yace "barka da kwana bros, ina stubborn 'kaninka"? Kafin Ajeeb yai magana Asad ya kuma banko kofa ya fito daure da towel yana cewa "maimaita abinda kace, ina wa naji kana cewa"? Dariya Ameer yai yana cewa "barka da kwana bros Asad ina d'an uwanka Ajeeb"? Had'e rai Asad yai "I don't know" ya wuce zuwa gaban wardrobe "kada Allah yasa ka sani" Ameer ya fad'a yana aika masa hararar wasa juyowa Asad yai "me kace dawa kake" dariya Ameer yai yana cewa "not u da Ajeeb nake" "saidai Ajeeb din malamai zaku iya fita ina son sa kaya ne" da sauri Ameer yace "haba dai muje ina? Me ka mayar damu kwarata"😝? Ajeeb yace "gara kasa kayan ka dan wallahi Babu inda zanje uwar me zan kalla bayan..,..sai kuma yai shiru yana kwashewa da dariya kayansa Asad ya d'iba yana yin toilet murya kasa kasa yace "humm bastards" zaro ido sukai "kai waye yan iskan a cikin mu dakai"? Banza yai musu daya fito ma bai sauraresu ba yai gaba tashi sukai suna bin bayansa a parlor yaga Annur hannu ya bashi suka gaisa kai Ajeeb ya jinjina "lallai Asad wannan selfish din yayi yawa mu kuma me mukai maka da ka'ki bamu hannu mu gaisa"? Batare daya kalli inda yake ba yace.
"Do you want to know why"?.
Kai Ajeeb ya d'aga "eh tambayar ka nake ina son sani ka fad'a min yanzun nan ko jiki yai tsami🙄" wani kallo Asad ya watsa masa ta nuna cewa bismilllah kafin ya kara gaba daga nan yai bangaren mahaifansu dukkan su suna tare har mai girma Alhussain da matansa da kuma yaransa yan mata guda hud'u kowacce ta hakimce cike da sarauta da sallama ya shiga yana gaidasu ya samu wuri d'an nesa dasu kan wasu kyawawan cushions masu kalar golden and white ya zauna bai sake cewa kowa komai ba Alhussain yace.
" 'Dan gidana meya faru naga ka ware kanka kai d'aya ina sauran suke"? 'Dagowa Asad yai zaiyi magana suma suka shigo da sallama duk gurin sa suka nufa suna zama sai aiko masa da harara suke musamman Ajeeb kamar idonsa zai fito waje ya kalli Alhussain yana cewa.
"Daddy kayi masa magana ya daina harara ta dan naga yau tsokana yake ji tun muna part dinmu yake zagina 🙊".
Murmushi Alhussain yai yana cewa "babyn Mami meyasa kake harararsa".
Asad na yiwa Ajeeb kallon mamakin sharrin daya 'kuga masa yace "ni ban zageshi ba shine kawai ina barci na ya zuba min ruwan fridge mai sanyi a jikina wai hakan bai ishe shiba saina gaidashi kamar wani ubana".
Kallon Ajeeb Alhussain yai yana cewa "to kaji meyasa zaka zuba masa ruwa"?.
"Daddy ya'ki tashi ne gashi rana ta fito baiyi sallah ba shine naji haushi na zuba masa".
"Ok to ka yarda bakai daidai ba ka bashi hakuri, meye abin d'aga hankali bayan kwanan nan zakuyi bankwana zai wuce Marshall islands ko duk fad'an karshen ne"? Ya karasa maganar da murmushi dan shiru Ajeeb yai sai kuma ya kalli Asad daya d'auke kai yace "kayi hakuri Bros" ya fad'a yana mi'ka masa hannu d'agowa Asad yai ya kalleshi dan kar yaje sha'kiyanci yake masa sai kuma yaga serious face dan haka shima ya mi'ko masa hannun sukai musahaba ya mi'kewa Ameer ma sannan yace "nima kayi hakuri" kai Ajeeb ya d'aga "ba komai ai mun saba indai rigima ce zuwa jimawa ma zamuyi wata jiki da jini kuma Asad nefa da Ajeeb" 'yar dariya yasa sauran sukai dan haka ne abinda Ajeeb d'in yace kullum suna cikin fad'a indai suna tare kamar Tom and Jerry 🤗 Alhussain yace "shikenan komai ya wuce Asad zai tafi tare da abokina abdul-kareem ranar Monday sai yayi shekara biyar zai dawo kuyi masa fatan alkairi da samun nasara" hannu Ajeeb ya bud'e yana cewa "a ro'ka da babban masaki nine mai karantowa" shiru kowa yai Ajeeb na zayyano addu'o'in nasara ga d'an uwansa saida ya gama kowa zai shafa yace "addu'ata ta 'karshe gareka Asad Allah ya baka mace jaruma mai ra'ayi irin naka amma banda fusata da son yin dambe da d'an uwa 🙉" Ajeeb na rufe baki khimiyyah da Makiyyah har had'a baki sukai kowacce na cewa "ai nice" kallon su Alhussain yai bayan sun shafa addu'ar yace "ai kune me"? Caraf khimiyyah tace "nice jarumar domin ina sonsa" zaro ido Makiyyah tai "kan bala'i kina sonsa a ina bayan na riga ki tun wuri kije ki nemi naki kafin lokaci ya'kure miki" a masife khimiyyah tace "wallh baki isa ba hauka ma kenan me kike nufi da na nemi nawa kar lokaci ya kure min? Humm Makiyyah kenan sorry yarinya wallahi Asad nawa ne gaba da baya gara kisan nayi" Makiyyah na shirin magana ganin shashancin da suke Alhussain ya d'aga musu hannu.
"Kai keep quite wanne irin shirme ne wannan kukeyi"? Khimiyyah na huci tace "Abba kana jinta abinda take cewa fa wallahi impossible na zuba miki ido yarinya wuce nan kinyi kad'an.............
Cikin tsawa Alhussain yace "zaki min shiru ko sai jikinki ya fad'a miki kada na sake jin irin wannan maganar a bakinku kowa ta ha'kura tunda ba dole bane dama ai kuna sonshi amma da yan uwantaka ba aureba karna sake jin haka dan gidana ba aure zaiyi ba aikinsa zaisa a gaba ku mayar da hankalin ku jikin ku yaushe kuka d'ago har kukasan miye duniya da abinda yake cikinta"?.
Fuskar khimiyyah ranta a 'bace take aikawa da Makiyyah mugun kallo tace "amma Abba.........,.......
"Ke ki rufe min baki nace tashi anan" mi'kewa Khimiyyah tai tana kumbura baki ta fice tana maganganu 'kasa 'kasa sauran ma mi'kewa sukai suna fita daga part din Makiyyah na shiga bedroom Khimiyyah ta sha'ko wuyanta tana cewa "ke har kin isa shiga tsakani na da muradi na wacece ke me kike ta'kama dashi"? Ri'ke hannun ta Makiyyah tai tana 'bam'barewa daga wuyanta tace "bakiyi karya ba Khimiyyah na isa ne tun farko inaji a jikina Asad nawa ne mijina ne shine mafarki na dan haka ta nuna Khimiyyah da yatsa taci gaba "kada ki kuskura ki koyi son wanda na gama mi'ka wuya sakankancewa da soyayyar ta idan ba haka ba kina tare da wahala".
Bige mata hannu Khimiyyah tai a fusace tace "hannu 'kasa yarinya kada ki sake gigin nuna min yatsa idan ba haka ba saina balla shi".
"Ke har kin isa kice zaki min wani abu"? Makiyyah ta tambaye ta itama zuciyarta na turiri.
'Kirji Khimiyyah ta buga "eh na isa harna wuce inda kike zato kuma kici gaba da shiga gonata wallahi wata rana za'ai babu ke dan saina 'badda ke".
Ta'be baki Makiyyah tai "humm gyara kalaman ki yan mata saidai mu 'badda juna tare dan baki isa na zuba miki ido ba nima ba kanwar lasa bace matukar kika fad'a min cuta ni kuma saina fad'a miki mutuwa😡😠".
Gajiya da shirmensa Shaukiyyah tai wani uban tsakin takaici taja tana cewa "wai dan Allah malamai maye haka ne kun ishemu da wannan