Showing 18001 words to 21000 words out of 130249 words
ya cewa liman yai shela duk wanda yake neman mace sadaka yazo ya aure masa ita" dafe kirji Aliyah tai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un yaushe hakan ta faru wai Balarabe meke damunsa ne da dai ba haka yake ba amma yanzu gabadaya ya gama canzawa kamar mai aljanu lallai da alamar tambaya kinga ki daina kuka Fatima tashi kije ki sallah maza kizo na aike ki gurin Kande ki ce ta bada kudin adashen nan ita kadai ake jira" to Fatima tace tana mikewa yayin da Aliyah tai tagumi cikin tausayawa yar uwarta Dalah da kuma halin da Indo ke ciki saidai tana fatan Allah yasa Dauda ya dawo da wuri insha Allahu tana sa ran zai auri Indo yarinyar nan ta huta da kuncin rayuwa.
Suna tafe a mota Nurain dake kallon photon Nafisa daya dauka bata sani abokinsa Yazid ne yadan daki kafadarsa yana cewa "kai mutumi na kaji tsoron Allah idan har kasan ba son yarinyar nan kake ba karka yaudare ta kaga kuna yi da mahaifinta" dariya Nurain yai yana kallon sa yace "amma ai kasan nima da yaudarar ce bazan ta'ba furtawa ba tunda tasan yadda Daddy suke da babanta kawai haka nan naji ina sha'awar ta domin tana da kayan aiki kuma zan aureta" kai Yazid ya jinjina yana yana mayar da hankalin sa kan tuki yace "amma fa baka da kirki ko kadan kasan madam din ka akwai bala'in kishi tasan da wannan maganar saita kusan kone maka gida" tabe baki Nurain yai yana cewa "dama ai ba da ita kadai zan zauna ba ni mijin mace hudu ne innaga dama a yau naso auren Nafisa zanyi" "umh umh fa Nurain banda cika baki" "to zuba ido kasha kallo muna dawowa daga tafiyar da zamuyi da ita zan auri Nafisa" Yazid dai jinsa yake amma yasan karya ne saidai kawai zai kyale shi kada yai masa magana yaga kamar ya takura shi.
Har suka isa cikin gari kai tsaye gidansa ya wuce a parlor ya samu yaransa guda biyu suna zaune da littafi a gaban su babbar tana koyawa karamar zama yai yana cewa "Amnah ina momyn ku"? D'agowa Amnah tai tana kallon sa tace "u're welcome Dad Mom na gurin aiki bata dawo ba" sauke ajiyar zuciya yai yana mikewa ya shiga part dinsa baifi minti biyar ba ta shigo cikin parlon ganin yaran basu lura da ita ba yasa tace "auta na karatu kuke ya school" duk d'agowa sukai suna kallon ta da gudu suka je suna rungumeta cikin shagwaba karamar tace "ni momy yunwa nake ji" kallon fuskarta tai "oh sorry dear ina Falmata batai lunch bane"? Ta karasa maganar tana kallon dining ga kuloli nan alamar an gama rike hannun ta tai tana cewa "muje nayi serving dinki" kafada ta ma'ke tana cewa "ni mom biscuits da ice cream nake so" daukar ta tai suna zuwa gaban fridge ta bud'e ta dauko mata kafin tace "Daddy ya dawo daga kauye ne" kai Amnah ta d'aga "eh mom ya tambaye ni ma kin dawo office nace a'a" jin haka yasa ta wuce gurin sa tabar yaran anan baya bedroom ya shiga wanka dan haka fita tai zuwa nata part din itama ta shirya kafin ya fito.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE ๐
Yau kam nayi muku typing da yawa dan haka bazan sake yin posting ba sai ranar monday idan Allah ya kaimu da rai ya bamu aron numfashi da kwana.
YUSRAHMS.
Be good be helpful than everybody will like u to be a happy child like my daughter Fatima Ilham.
Mrs al'ameen Ahmad ce
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
Ai littafin me kamar sarki bangarori ne daban daban zaku Sha labari kudai kawai ku taya ni da addu'a Allah ya bani dama da lafiyar yi muku typing da posting.
Mu kwana lafiya gaskiya zanyi kewar ku masoya ina mi'ko sakon godiya da gaisuwa ta gareku.
Batilah Abdullahi
Rakiya Abdullahi
Ruwaina Abdullahi
Surayyah magaji
Sadiya Khabeer
Ummi Ibrahim
Asma'u Abdullahi
Bintu 'Dalha.
Sai iyaye masu daraja girma hakuri kwazo Allah ya kara ri'ka muku ya tsare ku daga sharrin dukkan abun 'ki ya bamu rahmar sa duniya da lahira amin.
Mama Hauwa
Umman fati
Umman Basiru
Umman Suraj
Umman Huzaif
Umman usman
Maman baby
Maman Fadilah
Maman Maryam
Umma Habiba
Umma Addah
Sai kuma kaka mai kamar uwa kimin komai a rayuwa ta fatan Allah swt ya tsare ki ya kiyaye ki ya barmana ke ki kara tsahon kwana.
AISHATU SHU'AIBU๐คฃ
SHU'AIBU MAI ALEWA๐น๐๐
๐น๐น๐น๐น๐นโจ๐น๐น๐น๐น๐น๐น.
โ๏ธJinjina nake gareku yan group din mu na ANNURI marubuta Allah ya taimaka ya rikar ido yai karko basira ta karu hannu kada ya kosa alkalami yaita zayyanowa.
Safiyyah Aliyu wakili
Hajjara Abla's Glam
Rahmat A Abba Jada
Rabi'at bichi
Mrs Abubakar
Chp~ melody
Indo ce kano.
Mrs AL'AMEEN AHMAD CE mai tambarin yma dutse Jigawa new world new life and new style ๐.
5~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil 'Da'ina.
################
##############
###########
#######
####
###
##
#
TYPING ๐ฒ {9:44AM 18/24}โจโจโจโจโจโจโจโจโจโจ
๐ME KAMAR SARKI ๐
๐ซ ANNURI WRITER'S ASSOCIATION ๐ซ.
09~ AL-JABBAR
The irresistible
10~ AL-MUTAKABBIR
The majestic ๐น.
Dedicated to
Mr HAUSA EBOOKS ๐
SHURAIHU CEO๐๐๐๐
โ๏ธYUSRAHMS ABUBAKAR
Mrs Al'ameen Ahmad ce๐
๐SESSION ND REASSURE๐
Episode 09 & 10
Marshall islands misalin'karfe daya da rabi na dare ko'ina da haske ๐ gari yayi tsit ba motsin koda tsuntsu zaune Asad yake da phone a hannun shi tun karfe bakwai yake kiran wayar Mami amma bata daga ba karshe yanzu daya kira sai yaji switch up gabadaya ya damu ya sani dama za'ai haka Mami tayi fushi dashi wurgi yai da wayar daidai Isham ya fito daga bedroom cikin zafin nama yai tsalle yana cafe ta tsuka Asad yai yana zamewa ya kwanta kan lallausar cushion din tare da rufe ido.
Mamaki ne ya kama Isham me Asad keyi har yanzu bai kwanta ba zuwa yai kansa ya tsaya cikin alamun tambaya yace "buddy what is it? Said you wanted to talk, but haven't said a word, what happened"? Shiru yai bai bashi amsa ba duk da dama haka yake tunani "Asad ka fad'a min meke damunka ko akwai wani taimako dazan iya yi maka"? Batare daya d'ago ko ya bud'e ido ba yace "don't know how this happened" da mamaki Isham yace "haba buddy kamar ya bakasan me ke faruwa ba? me ne ya hana ka bacci? shine abinda nake son sani".
Tashi zaune Asad yai yana barin wurin ya koma jikin window ya tsaya yana kallon waje da ko'ina ya mamaye da haske kafin ya fara magana "nayi kiran Mami a waya amma ta'ki d'aga min" "ta'ki d'aga maka kira maybe bata kusa ne" kai ya girgiza "no tana wurin" "to kenan laifi kai mata"? Isham yai maganar yana karasawa inda yake ya dafa shi yana cewa "meyasa baka tsaya saida ka bata hakuri ba ka taho"? "Wai Isham wa ya fad'a maka laifi na mata kawai an samu sa'banin fahimta ne tsakani na da cousin dina" cikin tsokana Isham yace "tofa ashe harka fara soyayya bamu sani ba ko aure zakai n...................
Bai karasa abinda yake son cewa ba sakamakon naushin da Asad din ya kawo masa da sauri ya goce yana cewa "which rubbish is this"? Har lokacin hannun na nan a dun'kule yana kallon Isham din amma baice 'kala ba ya baro window yana dawowa tsakiya parlon yace "dan nace maka cousin dina ce kawai zakai min hauka a duniya akwai wanda naji na tsana irinta" hararar sa Isham yai yana cewa "ba wani ni fa bana son cika baki shi so ba anan yake ba Asad ka daina fariya" "Isham indai akan Kimiyyah ne zan bugi kirji nace Allah ya sauwake domin wallahi badan Mami ba jiya da yanzu tana kabari" zaro ido Isham yai "kaii Asad cousin din taka guda zaka kashe lallai na jima banga mai zafin Zuciya irin ka ba dole Mami tai fushi dakai" tsaki Asad yai yana cewa "wa ya fad'a maka fushi tai dani ban ta'ba aikata laifi Mami tayi min fushi ba saidai tai min nasiha" "to ai baka ta'ba irin wannan a gaban su ba kisa fa kaso yi Asad a gabansu dole kasan Mami tayi fushi dakai" kai Asad ya girgiza yana cewa "Mami bafa irin wacce ka dauka bace baza tai fushi dani ba akwai dalilin dayasa bata d'aga min kira ba na sani na bari zuwa gobe zan sake kiran ta".
"Shikenan buddy, amma baka fad'a min ba taya ka samu sunan wannan 'kungiyar da location dinta sannan mene shirin su me suke aikawa a sirrince dahar kowa da kowa yake kokarin ganowa asirin su shin da akwai wata alama da zamuyi amfani da ita"? Kallon sa asad yai batare daya bashi amsa ba sai rufe ido dayai a iya sanin Isham yasan yadda Asad ya kwallafa ransa da sai ya gano asirin 'kungiyar nan ya hana kansa bacci ya daina sukuni shekaru da dama ya 'bata yana tara bayanai akan ta har zuwa jiya domin a shekaran jiya sunyi waya Asad din ke fada masa ya gano sunan 'kungiyar da wasu bayaninnika amma yanzu ya masa tambaya game da haka yaga bai tanka masa ba.
Sake d'agowa Isham yai yana kallon Asad da mamaki yake "buddy what happened? Please tell me what your problem? Har lokacin Asad bai bud'e idonsa ba balle yace wani abu mamaki ne sosai ya kama Isham har yana tunanin to ko Asad din bayaso ya fad'a masa, saidai ya sanshi sani na ha'ki'ka bazai ta'ba boye masa wani abu ba balle da babu shi a cikin masu neman gano 'kungiyar shima da nashi bangaren da aka tura shi sojoji masu jarumtaka aka za'ba na dukka duniya su miliyon daya da dubu d'ari biyar da hamsim da biyar wada'nda aka basu dama suyi binkice akan 'kungiyar saidai mafi yawan sun halaka saura ne suka rage sakamakon cin wannan gasa duk wanda ya gano ta da inda asalin kafin tushen ta yake da mutanen da suka kafata da abubuwan da suke aikatawa a boye wanda yai nasarar sanin wannan kuma ya bada cikakken bayani da za'a gamsu dashi da 'kwararan hujjoji to zai samu babban matsayi zuwa matakin 'karshe na mu'kami a soja wato Bgs ya zama shine jagaban kowa duk ana bayansa shine mai fad'a aji.
Numfashi Isham ya sauke yana sake kallon Asad yace "buddy meya faru ne ka fad'a min dan Allah na sani tsakani na dakai babu boye komi" sai lokacin Asad yai magana "me zan fad'a maka Isham"? Mamakin tambayar Isham yaji amma sai yace "munyi waya dakai kace min ka fara gano wannan kungiyar ta mutanen banza ce masu dakushe 'kasa masu haifar da fitina da rusa rayuwa da farin ciki kuma sun kasance a wani kogo cikin daji ma'abota shan jini ko ba haka bane"? Kai Asad ya d'aga yana tashi zaune yace "but I've confirmed it haka ne abinda nace maka domin shi na gani saidai na makara Isham bana tunanin zankai wannan matakin duba da shekarun dana 'bata ina tattara bayanai rana daya shiri na ya wargaje na rasa komai" zaro ido Isham yai yana cewa "kamar ya I don't understand anything wani abu ne ya faru"? "Eh Isham a ranar dana fad'a maka washe gari na rasa komai before I find out kwana nayi a gaban na'urori kamar mahauci ina aiki ina tattara bayanai tun karfe bakwai da rabi na dare ban gano koda wata 'yar alama ba har karfe biyar na asuba sannan kamar a mafarki naga an watso min bayanai akan kungiyar da inda suke bayan nayi alwala naje masallaci da nufi idan na dawo na cigaba da neman information akan su amma kasan wani mamaki lokacin dana dawo zuwa nayi na tarar da Khimiyyah zaune a gaban laptop d'ina tana goge min komai abu biyu ne yazo min meyasa ta shigo part dina har cikin d'akin sirri na taya tasan abinda nake nema waye ya turo ta maye ala'kar ta da 'kungiyar dahar bata so a san asirin ta meyasa tamin haka wannan dalilin yasa tun daga d'akin na ri'ka dukan ta har zuwa harabar part d'ina banyi niyyar Khimiyyah ta sake rayuwa a duniya ba koda na sakan ne abu daya ne ya hana ni yunkuri na" shiru yai bai sake cigaba da cewa komai ba.
Isham dake ta faman binsa da kallo yace "meye wannan abu d'ayan daya hana ka kashe ta" "Mami ce Isham kuma da nasan idan tazo zata hana ni tun fitar Ajeeb zan tashi kanta da bullet Isham ka fad'a min waye za'ai wa haka ya hakura"? Kai Isham ya girgiza yana cewa gaskiya babu Khimiyyah bata kyauta ba tayi kuskure abinda ta aikata maka amma nafi tunanin tana da ala'ka da wannan 'kungiyar" kallon sa yai cikin alamun tambaya yace "meyasa kace haka"? "Saboda babu ta yadda za'ai tasan kana binciken kungiyar ka duba mana a cikin su akwai wanda yasan da haka balle har yai maka wata tambaya akai sai ita ba kace wata rana ta ta'ba tambayar ka wai ance akwai wata kungiyar matsafa da kake nema ba har ka nuna mamakin a ina taya ta sani tace ji tayi kana fad'a kuma kai kace babu wanda ka ta'ba fad'awa, shakka babu Asad lallai Khimiyyah tasan wani abu akan wannan kungiyar da ala'ka tsakanin ta da ita akwai abun da baku sani ba idan ba haka ba baza ta gano cewa kana neman 'kungiyar ba kayi tunani mana" Isham ya karasa maganar yana dafa Asad wanda yai shiru cikin zurfafa da tunanin hujjojin da Isham din ya fad'a yanzu wanda yake da tabbacin duka gaskiya abinda ya fad'a Khimiyyah tasan wani abu akan kungiyar ya tuna wata rana da take ce masa.
"Prince Asad dan Allah na maka tambaya? wai meyasa kullum baka da sukuni kana gaban laptop duk muna hira amma banda kai sai nayi sati banji muryarka kayi magana ba ka daina wahalar da kanka da yawa lallai na sani aikin da kakeyi me girma ne saidai zaka dade baka fahimci komai akan aikin naka ba domin abunda kake nema babba ne mai had'ari mai tarwatsa rayuwa mai halakarwa".
Asad baiyi niyyar kula ta ko kadan saida tazo daidai nan a bayanin wanda cikin mamaki ya kalli idanuwan ta daya juye ya zama wata kalar kamar ba idon mutum ba yayi baki 'kirim kuma yanayin siffar fuskarta ma ta canza gashin kanta yayi launin ja jikin ta ya fara mummurd'ewa yatsunta sun 'kara tsayi bata da kyan gani dai.
Baiyi magana ba ya mayar da kansa ga aikin da yake murmushi tai wanda harshenta ya fito da wata iriyar wuta mai balbali ta nufi 'kone masa fuskar laptop din Wanda shi kuma ya ankare da ita da abin da take aikatawa duk yana kallon ta da sauri a sukwane cikin zafin nama da nuna kwarewa ta soja da iya ya'ki ya janye laptop din wutar ta sauka akan kujerar nan wuta ta kama fuuuu ta ko'ina kayan jikin Khimiyyah ya canza kala zuwa ja siffar ta ta 'bace kansa ta nufe gadan gadan da shar'beban takobi yana walwali gaba daya babu alamar falon sai wani ba'kin guri mai duhu Asad yake gani tun daga nesa tai wani irin tsalle tana dira a gabansa tare da kai masa sara da karfi rike takobin yai da hannu daya tare da fisgewa yai jifa dashi gefe ya sha'ki wuyanta ihu ta kurma tana fito da macizai ta baki da hanci nan gurin ya cika fal dasu harda masu kai goma kowanne kokarin kawo masa cizo yake duk sun kewaye shi d'aga ta yai da hannunsa daya wanda ya shake mata wuya dashi yai jifa da ita nan ta tarwatse kamar an watsa ruwa sama ganin haka yasa Asad daukar takobin ya soma saran macizan nan duk wanda ya sarewa kai sai yaga kan ya koma jiki kuma jinin daya zuba wasu macizan na sake fitowa ta gurin yana cikin faman kashe su wasu murd'a murd'an mutane su biyar masu fika fikai baka'ke wuluk abin tsoro marasa kyan gani suka bayayyana kowa da takobi a hannun sa suka kewaye shi.
Asad na tsakiyar su da takobi shima a hannunsa wanda ya kwace a hannun Khimiyyah dukkan su biyar din wata irin kara suka saki mai firgitarwa suma suna ambaliyar wuta nan macizan suka fara had'iyar juna sai gashi sun had'e gu daya sun zama wata bakar katuwar macijiya mai koran ido jikinta duk gashi saiga mutum ya bayyana yana kanta a tsaye fuskarsa a rufe da'kyar kake iya hango jajayen idanuwan sa masu yanayi da garwashi.
Mutanen biyar na farkon dake zagaye da Asad tuni suka sha jinin jikin su suna risnawa bisa gwiwoyinsu wanda Asad yai amfani da wannan damar a zafafe cikin tafasa ya d'aga takobi ya fiffille musu kayuwa sai gasu kwance a kasa jini yana kwarara kamar ruwan kogi cikin mamaki Asad yaga mutumin dake kan macijiyar ya diro tare da kifa kansa ya soma shan jinin kafin wani lokaci babu komai a gurin sai iya gawarwakin su umarni yaiwa macijiyar ta debe su ta hadiye sannan muryarsa kamar tsawa ya soma magana.
"ASAD kayi kokarin da baza a samu wanda zai iya koda kwatan kwacin saba na jinjina maka kaidin jarumi ne sadaukin da ba tamkarsa lallai zaka iya fad'a da koma waye kaine mutum na farko daya shigo tarkon mu akai kokarin bada jininsa amma ya tsira ya haye ya tsallake rijiya da baya saidai ka sani cewa bazaka iya gano kungiyar mu ba har abada kaiwa sauran yan uwanka sojoji masu son gano mu albishir cewa sunyi kadan ba wanda ya isa jada mu a halin yanzu da nake maganar nan dakai mun hallakar da sojoji d'ari biyar masu neman wannan kungiya tamu ciki harda babban abokinka wanda kayi matukar damuwa dashi kuma baza ku kara haduwa ba har abada kaima na barka ne kawai dan ka bada labari ka fad'awa masu neman wannan kungiyar irin ka cewa su dakata kafin su rasa ransu domin kungiya ce ta matune masu had'ari zan barka kaje kayi nazari hhhhhhhhhhh ya karasa maganar yana shekewa da wata mahaukaciyar dariya.
A fusace Asad yai tsalle yana hawa kan macijiyar ya damko mutumin suka yo kasa nan dambe ya kaure tsakanin su kowa naji da 'kuwwa da karfi duk gurin ya rude kamar mutum dubu ke fad'a so mutumin yake ya kwace sakamakon da fari ya dauka yafi karfin Asad zaiyi nasara a kansa sai daga baya yaji Asad din