Showing 12001 words to 15000 words out of 130249 words
ya karasa maganar muryar shi na rawa saboda tsoro domin dazu a gaban sa ya fara dukan Kimiyyah jikinsa ma rawa yake kuma yana sauraron me zaice masa can ya tsinkayo muryarsa yana cewa "batu ne akan stockyard dina ina son ka kula min dashi kafin na dawo ya zama tamkar ina nan kuma koda Ajeeb ne ban amince ya shiga wurin su ba kaji abinda nace"? Da sauri Amjad yace "eh ranka ya dade za'ai yadda kake so Allah ya tsare ka ya dawo dakai lafiya" "Amin" ya fad'a can kasa kafin cikin taku ya wuce da sauri Amjad ya mike yana jan trolley yabi bayansa har mota da wadanda zasuyi masa rakiya zuwa airport batare da sanin kowa ba ko bankwana da kowa ko tunanin halin da Kimiyyah take ya wuce airport daga nan jirgi ya d'aga dashi zuwa Marshall islands.
Ummmhhππ SAFE JOURNEY ALIYU ASADπΉπΉ.
To yau kam anan zan tsaya sai idan Allah ya kaimu gobe a'a ba gobe ba sai jibi oh sorry it was a mistake ba jibi ba sai gata zaku samu typing kuyi hakuri kada ku gajiya da halina ni haka nake bani da haushin kowaπ
π€£π.
Mrs AL'AMEEN AHMAD CE π ta kowa.
Sannan ga wata sanarwa idan kuna so na yi muku typing gobe tofa saina ga sama da mutum dubu sunyi comments ππππ idan kuwa ba haka ba nayi fushi saina huci kafin na d'ora ehe bazan fatse aiki na nayi muku typing ba ku turo min sticker π€π duk wacce ta sake turo min sticker saina debo mata yan committee ko na kaita ofishin 'yan hisba π€£π
π€£ππ
.
Jinjina nake a gare ku masoya abokan arziki fatan samun rahmar ubangiji da amincin sa a duk inda kuke bazan ta'ba mantawa daku ba.
Naja'at Musa Abubakar
Zarah Musa d'an Adam
Hafsat Harees
Salmah Hayat
Suwaiba Yusuf
Fatima Idris
Khadija A Yusuf
Saudat Yusuf
Zainab Sunusi.
Mrs Al'ameen Ahmad ce ke gaida ku πΉπΉπππππποΈ.
YUSRAHMS WE WILL MEET AGAIN π€.
Tofa a'a abun yayi ashe ana son posting irin wannan comment haka na wani ma ban samu damar karantawa ba sai hakuri amma maganar gaskiya kun bani mamaki ai bansan haka littafin nan keda farin jini ba ya tara masoya da yawa masu min fatan aikairi TO IDAN KINJI DAD'I KO KAJI DAD'I KAI SALATI D'ARI GA MANZON ALLAH SAW RANAR JAMA'A ZAKA SAMU WANI HASKE RANAR ALKIYAMA WANDA DA ACE ZA'A RABAWA ABIN HALITTA ZAI ISHE SU SHIGA ALJANNAHπ².
TYPING π² FRI 01 March 8:18AM Yusrah Musa Abubakar na karaso kuzo kusha story.
πME KAMAR SARKI π
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION π« HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY.
YUSRAH MUSA ABUBAKAR)(Maman little Zaran aunty π)(*).
π
π π
π π π
ππππππ
π π
π π
ππππππ
πΏπΏπΏπΏπΏπΏ
πππ
It's Friday don't forget to recite suratul al-khaf may Allah open the door of success for all of u may Allah accept our du'as may Allah bless nd help us Amin π.
Dedicated to
MR HAUSA EBOOKS π
ππππππππππ
STORY AND WRITTEN BY
βοΈYusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty π.
07~ AL-MUHAIMINU
The dominator
08~AL-AZIZ
The almighty.
4~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Khaifina.
πMe kamar sarki π
By
πΉ Yusrah Musa Abubakar Mrs Al'ameen Ahmad ce πΉ.
π VIXENS ND ABSENT MINDEDπ
Episode 07 & 08
Lokacin da Mami ta isa asibiti duk suna zaune shiru sauke ajiyar zuciya tai tana cewa "ya jikin na Kimiyyah fatan babu abinda ya sameta"? Kai Ajeeb ya d'aga "eh Mami muna dai fatan hakan amma har yanzu bamu da wani gwarin gwiwa akan komai domin tana ICU likitoci suna iya bakin kokarin su ganin sun ceto ranta amma dai abun yaci tura Mami kita addu'a Allah yasa kada ta silar Asad ace Kimiyyah ta mutu" wani irin juyawa kan Mami keyi hajijiya na dibanta baya tai luuu da sauri Ajeeb ya taro ta yana cewa "sorry Mami kiyi hakuri" muryarta a hankali tace "ina Sultana Hadizah"? rike hannunta Ajeeb yai "muje na kai ki" fita sukai suka bar saura mikewa Ameer yai yana zura hannun sa cikin aljuhu ya fara zagaya gurin dakatawa yai yana d'aga kansa sama yace "nifa na kasa ganewa"? Kowa kallon sa yai da mamaki cikin alamar tambaya Annur yace "kamar ya"? Komawa Ameer yai ya zauna yana cewa "kamar yadda nace maka abun tambayar anan shine me Kimiyyah taje yi part din Asad me ya kaita laifin me tai masa wannan tambayar na bari a raina nake ta so mu koma na tambayi Asad" kai Annur ya jinjina yace "haka ne Ameer tunanin mu yazo daya wallahi nima abinda ke raina kenan Asad nada zuciya amma a banza Asad bazai yiwa Kimiyyah irin wannan ba'kin dukan mutuwar ba" da sauri Khaldiyyah tace "ya Annur nima abinda nake tunani kenan" kallon ta Annur yai yana cewa "wai ke ni sa'an wasan kine ko tare aka haife mu fad'a min inji yawancin lokata kina min shishshigi duk ranar dana rike ki ni kuma saina miki dukan shiga 'kabariπ²" zaro ido Khaldiyyah tai baki bud'e take kallon sa dariya sauran suka ri'ka yi kamar ba Kimiyyah ce ke ICU ba.
Waya Ajeeb ya dauko daidai zaiyi making call yace "to ai mutumi na in kaji kare yana shinshina takalmi hausawa sukace dauka zaiyi" wani kallo Annur yaiwa Ajeeb cikin had'e rai yace "meeeh d'an sake fad'a domin ban jika sosai ba"? Da sauri cikin tsokana Ameer yace "cewa yai in kaga kare yana shinshina takalmi hausawa sukace dauka zaiyi to nan din ma haka abun yake" sakon harara ya samu daga Annur yana cewa "kai kuma ban sako dakai ba saboda haka can you be quietπ€«" sannan yana kallon Khaldiyyah wacce ta kau dakai yace "ke da gaske ne"? Shiru tai ta kasa bashi amsa wanda hakan ya tabbatar masa wato da gaske son shi take tabb lallai ta kira ruwa bata da lema cire lips yai yana maida kallon sa kan Ameer wanda ya dage gira zaiyi magana jin Ajeeb na waya yasa yai shiru.
Da mamaki suke kallon Ajeeb daya dage yana zazzagawa Asad fad'a cewa duk suna hospital bayan shine ya daketa amma ko leko su baiyi ba balle ya damu da halin da take ciki tsit Asad yai yana sauraron sa saida ya bari ya tsaya sannan yace "ka gama" shiru Ajeeb yai cikin takaici yace "ban gama ba" tsuka Asad yai yana cewa "ok continue Abba, ba kira na kai kamin fad'a ba mezai hana kazo ka kama ni da duka I think zaifi wannan ihun da kake min" da karfi Ajeeb yace "ASAD" "what up Ajeeb"? Asad yai maganar slowly cikin 'kulewa Ajeeb yace "wallahi idan muka dawo masarautar nan saika gane Allah da girma yake" Ajeeb na rufe baki Asad yace "ok what do you mean? wato so kake kace min ni bansan shiba kaine zaka nuna min ya sheik" "kasan Allah ko Asad ka jira dawowa ta saina baka mamaki" tsaki Asad yai yana cewa "me kake cewa ne magana kake ko bakin ka ne a haka? Meyasa lokacin da kazo ka tarar ina duka ta kaima baka rufe ni da duka ba, ka godewa Allah da sauran kwanan ta a gaba amma da yanzu na kaita kabari" haushi ne ya gama cika Ajeeb yace "maimakon ka risina kayi nadama ai haka kace ko"? Kai tsaye Asad yace "eh nace hakan idan akwai wani abu da kake tunanin zaka iya ina jiran ka babu tantama akan bugun danai mata" cikin alamun tambaya Ajeeb yace "me"? Cikin son tura masa haushi Asad yace "akuya zaka cewa me ba mutum ba" rai bace Ajeeb ya sakar masa ashar yana cewa "uban akuya zan cewa me wai Asad meke damunka ne" "babu kaga wani abu sa'banin hankali a tattare dani"? "Ban sani ba" "kada Allah yasa ka sani banza uban yan shishshigi kada ka sake kira na idan kuma ba haka ba daga nan inda nake zan saito ka da bindiga na harbeka" zaro ido Ajeeb yai yana cewa "ji d'an iska inka fasa harbi na kaci ubanka" d'if yaji Asad ya datse kiran tsaki yai yana aje wayar kafin ya soma magana.
"Lallai ma Asad da tsaurin rai yake ji fa yadda yake magana hankalin sa kwance kamar wanda ya daki itace kuma na kirashi yana gasa min magana amma bari na barshi da Abban mu koma gida zanga da yadda zai Kare kansa" d'aga kafada Ameer yai yana cewa "da yadda ake karewa mana kaifa a banza Asad bazai ta'ba dukan Kimiyyah koda ma ace jininsu bai had'u ba" "ku dai yanzu baza kuce komai ba mu jira komawa gida koma mene ya hada su ai gaskiya zata fito" kowa na magana a gurin amma tunda suka zo Makiyyah batace ko alif ba saida ido take binsu da kallo yayin da Zuciyar ta tashiga kakkarwa domin a kaf zaratan samarin hudu Asad ne taji ya kwanta mata take son shi amma yau d'aya ta shiga kokwanto domin a ganinta koda yana son mace ya aure ta zatai matukar shan wahalar da ba'ai zato ba balle wacce ta kasance matar cushe aka 'ka'kaba masa ita wannan dama washe gari saidai ta waye shi a lahira domin zai tura ta bacci na har abada.
Batun Mami kuwa lokacin data shiga gurin da sauran matan suke tun kafin tayi magana Sultana Hadizah ta katse ta da cewa "babu abinda zaki ce min Hauwa gaskiya baki sa'ar haihuwa ba Asad bashi da tarbiyyah ko kadan yanzu me Kimiyyah tai masa dan tsananin tsabar tsagwaron mugunta irin tasa ta soja yasan ko namiji yaiwa wannan dukan iyaci kenan balle ita mace to wallahi bazan yarda ba ko kidau mataki ko na dauka da kaina dan na fahimci da sa hannun ki Asad yake duk abinda yaga dama a masarautar nan" mamaki ne sosai ya kama mami ba iya ita kadai ba harda sauran cikin rashin jin dad'in cin mutuncin da Sultana Hadizah kewa Mami yasa sultana Fatima cewa "amma dai gaskiya maman Khaldiyyah baki kyauta ba meye laifin sultana Hauwa'u a ciki zaki mata irin wannan wulakancin kamar wata bare ko baki santa ba kya yi kokarin ku fahimci juna ai ko amma daga xuwa baki bari tace komai ba kika hau fad'a gaskiya ki bata hakuri" a zabure sultana Hadizah tace "wa zan bawa hakurin bayan nice akai wa ba daidai ba wallahi I won't" ba sultana Fatima ba hatta abiyar sultana Hadizah taji babu dad'i itama saida ta magantu "haba ke kuwa maman Khaldiyyah ki bari mana dan Allah meye laifin ta a ciki ai baku bari ta farfad'o munji mai laifin ba ko"? Mikewa tsaye sultana Hadizah tai tana huci tace "waye mai laifi kuwa a cikin kowa ya sani bayan tantirin d'an nata da bataso a ta'ba niko fad'a ya zama dole tunda aka ta'ba min 'ya kuma wallahi bazan yarda ba 'kiris nake jira ta mutu na doka shi a kotu" ta karasa maganar tana jijjiga kamar wacce zasuyi dambe ba Mami data haifi Asad ba hatta sauran sultana Fatima da sultana Aisha sunji mugun rashin dad'in yadda Sultana Hadizahn ta rufe ido take ciwa Mami cin mutunci kamar bata ta'ba ganin taba ko irin bata santa ba" juyawa Mami tai zata fita a d'akin saida taje bakin kofa sannan ta juyo itama ba wuya idonta yai ja tana kallon sultana Hadizah tace "kiyi hakuri da komai duk ma abinda zaki fad'a min na bakar magana dole na dauka tunda d'ana ya miki laifi saidai ina son kisan wani abu you should stop spreading news with unreal source, be sure before you spread that's the right ba kuma ina nufin Asad bashi da laifi bane a'a amma mu jira farfad'owarta na barki lafiya Allah ya tashi kafad'unta" Mami na kaiwa nan tai waje cikin 'kunan rai da jin zafin kalaman da sultana Hadizahn ta fad'a mata amma ta 'kudura a ranta data koma zata samu Asad ya fad'a mata komai abinda ya hada su.
Tun kafin su 'karasa gida Mami zazzabi ya rufeta da'kyar ta iya karasawa part dinta ta kwanta bayin dake mata hidima basu sani ba saida Rabi'at taje kai mata madara ta ganta kwance cikin katon bargo tana makyarkyata da sauri ta karasa tana cewa "subahanallahi ranki ya dade meya faru"? Jin bata amsa mata ba yasa ta fita da gudu domin kiran mutane tare da jakadiya suka shigo d'an kwalinta a hannu tace "ranki ya dade sannu baki da lafiya Allah ya 'kara sauki yanzu wa zan kira miki ko me martaba"? Kai Mami ta girgiza alamar a'a sannan muryar ta na fita da'kyar tace "jakadiya ki duba drawer ki dauko min magunguna" da sauri jakadiya ta mike jiki na rawa tace "to ranki ya dade" duba drawer tai ta debo su gabadaya daga kwancen Mami ta nuna mata wadanda zata ballo mata ta hada da ruwa ta bata saida tasha jakadiya ta tattare ta mayar inda ta dauko tana zuwa gaban ta tadurkusa tace "ranki ya dade ko akwai wani abu dazan miki"? Kai Mami ta girgiza "a'a nagode jakadiya zaki iya tafiya" "to ranki ya dade Allah ya sauwake" jakadiya na fita Asad ya kira wayar Mami saidai bazata iya tashi ba balle ta dauko haka yai miss call kusan biyar tana ji ba damar dauka har shi yai zaton ko fushi tai dashi ya bari sai dare ya hau online nan ma ta saba suyi magana bai ganta ba dole ya hakura zuwa wani lokaci.
Basu baro asibiti ba sai kusan karfe sha biyu da rabi na dare suka dawo masarautar babu wani labari mai dadi game da Kimiyyah domin likita yace bashi da tabbacin zata sake rayuwa idan kuma ta rayu maybe zata samu tabin kwakwalwa lamarin daya susutar da kowa haka suka dawo jikin su a mace kowa da abin da Zuciyar sa ke fad'a masa tana sa'ka da warwara.
Mu dawo 'kauye tushe da asalin kowa wanda baida 'kauye baida asali tsintaccen kan hanya neπ.
Gidan ilyah zaune Bara'atu take a gaban kayayyaki tana ta lissafi da maimwitawa ta kasa total din kudin gashi tasan ba'kin sun kusa karasowa d'aga murya tai ta soma kwalla kira "Maimuna Maimuna kina ina zo dan Allah taho da sauri taki ta sameki" da saurin kuwa Maimuna tayo waje daga d'aki tana gyara daurin zani tace "lafiya Barah irin wannan kira haka duk kin hargitsa min ciki"? Dariya Bara'atu tai tana cewa "ke kam dai wallahi ba wuya kice an d'aga miki hankali dama lissafin kudin wannan shinkafar zaki taya ni da buhun wake biyar ga na gyad'a can Mara 'bawo buhu biyu ga barkono dan Allah muyi sauri da Ilyah ya dawo zai fara fad'a kin sanshi da hararrami" zama Maimuna tai suka soma lissafi har suka gama daidai Ilyah ya shigo yake tambayar nawa ne kudin ta fad'a masa ledar hannunsa ya mika mata yana cewa "na sanki da nawa kiyi sauri ki dafa musu kajin nan sun kira ni a waya yanzu sun kusa isowa" to Bara'atu tace tana karba shigowar Nafisa da markaden kayan miya ta aje tai d'akin su ganin Salmah zaune tana kwalliya yasa cikin mamaki tace "ke kuma ina zakije kike ca'ba wannan adon kamar zaki gasar kyau"? Dariya Salma tai tana cewa.
"To da fa ina zanje amma tun wancan satin nake fad'a miki saurayi na zaizo ko"? Tabe baki Nafisa tai "au kuma shi kikewa wannan kwalliyar lallai kina da aiki karshen ta mummuna ne me tumbi har kika tsaya bata lokacin ki wajen shafe shafe kamar d'an shugaban kasa ne zaizo gurin ki" had'e rai Salma tai "kuma saikin zagar min shi eh naji koma maye ni ina son kaya na in fitsari banza ne kaza ma tayi inta isa" dariya Nafisa tai tana cewa "ai yarinya ni yanzu na wuce tunanin na auri dan kauyen nan na karfi mahaifi na babu mai kudin sa a halin yanzu a garin nan kinga kuwa ai na tserewa sa'a" mikewa Salma tai tana cewa "haka mukam bamu fi karfin auren d'an garin muba kema zaki sauke domin ba d'an birnin da zai soki" zaro ido Nafisa tai "haka kika ce" daidai Salma tadau hijab zata fita tace "eh haka nace" tana fadin haka tai waje zama Nafisa tai ita kadai sai magana take "hum Salma kenan zaki sha mamaki bari Allah ya kaimu lokacin bikin zakiga irin mijin dazan aura nasan har abada babu wacce zata samu kwatankwacin sa a kauyen nan" karasa maganar tana fad'awa kan katifar su.
Haka nan Amatullahi taji son ziyara a ranta dan haka ganin ba abinda take yasa ta mike tana debar ruwa ta shiga wanka shaf shaf a yan mintuna ta kammala shiri ta fito tana shiga d'akin umma tace "umma ina son zanje ziyara gidan baba Ilyah da Baba Rakiya kuma zan d'an biyo ta gidan su Fatima mun dade bamu hadu ba" d'agowa Binta tai tana kallon fuskar Amatullahi saidai tayi murmushi kawai tana mayar da kanta tace "to ki gaishe dasu saikin dawo" to Amatu tace tana fita a zauren gidan ta hadu da malam Habu zai shigo cikin mamaki yace "Mamana ina zuwa" d'an sauke kaitai tana murmushi tace "zanje gidan baba Ilyah da gidan baba Rakiya saina biyo ta gidan su Fatima" shiru yai kamar zaice mata a'a saidai bazai hanata zumunci ba dan haka yace "to shikenan Mamana Allah ya tsare min ke saikin dawo karki dade" "to baba bazan zauna ba yanzu zanje na dawo" kai ya d'aga mata ta juya ta fita a gidan shi kuma ya shiga ciki iya sallama yai tun bai sauke sallamar ba A'i ta dauko kwaryar garin tuwon da aka niko tana direwa gaban sa tace.
"Malam ga garin tuwon ka nan gaskiya na gaji kullum ace kaine da girki bayan kayi casa ka gyara hatsin kayi surfe ka kai ni'ka da kudin ka kayi hadin abin miya wannan wacce irin rayuwa ce"? Wuce ta malam Habu yai yana zama a bakin kofar dakin sa