Showing 21001 words to 24000 words out of 215266 words

Chapter 8 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1697

amsa da zai bata, sai da ya ďebi wajen 30 seconds tukunna yace mata "Yeah , inaso ne in turo gidanku batun aurenmu, i dont want to take long so ki faďawa su Mum", har ya gama magana ita dai ji take kamar a mafarki take, shirun da yaji yayi yawa yasa ya dubeta ya ga kallonshi take yace mata "you there", da sauri ta girgiza kanta tayi hugging ďinshi a cikin motar, sai da ta sake shi tace, "Aliyu i cant believe my ears, you just said zaka tura gidanmu though bamuyi grand proposal ďinmu ba but its okay, am super excited, I love you soo much baby, ai yau ma zan faďawa Mum, sai ta faďawa Dad" peck ta k'ara mishi sannan ta zauna da kyau tana ta jero mishi abubuwan da zasuyi na bikin





Batuul kam tana can gida tana shirin grads ďinsu, da kuma murnan yau Farida zata dawo, dukkansu biyun kaya iri ďaya tayi musu ďinki ne kawai ya bambantasu, har takalma iri ďaya sukayi, taso taga Farida yau amma babu time, kawai driver ta tura ya kaiwa Farida nata kayan, a washegarin graduation ďin taje saloon aka wanke mata gashinta, sai da ta gama ta k'ira driver yazo ya ďauketa, tana shigowa gida taga kowa a palo, k'arasa tayi ciki ta cire gyalen abayar jikinta ta zauna a kan kujera, su Ahmad ne suka fara cemata" inyeh su graduate, shikenan daga gobe kin tashi daga pupil", dariya tayi musu tace "as in, yanxu sai university, ku ku tsaya ma tukunna, ticket tara aka bani a school that means mutanen gidan nan tara ne zasu" ihun kowa shi zaije suka farayi, dariya tayi musu tace "ai sai dai kawai wasu su hak'ura dan bazai ishe mu ba, we are eleven and nine tickets ake badawa, so excluding Aabid still mutum ďaya bashida ticket, and i want you all there", da taga babu wani da is willing to hak'urane ta ciro wayarta tayi dialling Farida, tana ďauka tace " Riri kinsan meye, i have only 9 tickets mu kuma we are ten, kuma i didnt invite kowa ma, so if akwai extra inaso for one of us", cewa Farida tayi "dama ni am not inviting kowa, zan bawa Yaa Abu 3, sai Abui, Ammah da Sadiq, kinga inama da extra 2, "Yawwa babe, na aika Baa liman da kayanki sunyi daidai ko" inji Batuul, "sosai ma wlhy , thank you soo much", katse ta Batuul tayi tace " I hear you, who are you thanking", dariya Farida tayi tace sorry i gat to go Ammah na k'irana we will talk later, bye" da haka suka katse wayan, cewa y'an gidan Batuul tayi ai ta samu ticket ďin mutum ďaya duk daďi sukaji suka ci gaba da hiransu, k'arfe tara ta tashi ta hau sama





Da murmushi a fuskanta ta buďe ido, k'iran asuban fari ne ya sata tunawa da yau wace rana ce, a hankali ta tashi daga kan gadonta ta shiga toilet, wanka tayi da brush sannan tayi alwala ra fito, nafilfili tayi, ta godewa Allah da ya nuna mata ranar gama makarantan ta lafiya, Addu'a sosai tayiwa iyayenta da al'ummar musulmai, da ta gama tayi karatun k'urani, tana gamawa aka tada sallah ta tashi tayi, koma tayi kan gado bayan ta idar da sallah amma ba bacci take ba, itama bata san tak'amaimai abunda zatayi ba dan murna, wayanta ta jawo ta k'ira Affan, yana ďauka tace "cousin of life" a hankali ya amsa mata kamar mai jin bacci, "Hello best friend what is it kika tadani da sassafe haka", ido ta wara tace "Affan dont tell me you are still on bed sleeping , its our day fa yau, our graduation day", ce mata ya sakeyi "Batuul saifa 9 o'clock and its still 7, i have two more hours to do everything", ce mishi tayi "ai yanzu zan k'ira Maa ince mata ko tashi sallah bakayi ba, Affan get out of that bed and get ready", katse wayan tayi batajira mey zai ce ba, haka ta k'ira Farida ma, ita ma hira sukayi tayi dan ta kasa bacci itama, sai da takwas yayi suka katse sukaje shiryawa, ďakin su Ahmad taje ta tashesu tace kowa ya shirya kar su b'ata mata lokaci, Janet ce tazo tace mata wata mata tazo nemanta, cewa janet tayi ta hawo da matar ďakinta, ita kuma ta juya ta tafi, tana ďaki sukayi knocking tace su shigo, wata mata ce fara siririya da murmushi a fuskanta suka shigo, wani ďan madaidaicin akwati a hannunta ta ajiye, sai da ta zauna sannan suka gaisa da Batuul, matar ce tacewa Batuul yanxu zamu fara ko dan kince 9 ne event ďin naku ko, da ehh Batuul da amsa mata sannan tace "Light nude make up zakiyi min, ko foundation bana so a sa min, just my brows then liner, i just want everything nude" murmushi matar tayi tace mata "Na gane but brows ďinki are full, ko za a ďanyi carving", a ah Batuul tace sannan suka fara, takwas da ashirin da bakwai suka gama, ba k'aramin kyau Batuul tayi ba, matar ce ta ciro mata kayanta a closet ďinta da takalmi da duk abinda zata buk'ata, matar ce ta taimaka mata ta saka kayan, dogon gown ne bak'i, mai buďaďďan k'asa, wani gold plated pendant da chain ďinshi matar ta saka mata a wuya na montinè da agogonshi sai pin earing da matching bracelet ďin sarkan, cashmere scarf bak'i mai golden crystals ta ďaura mata akai kamar turban, ga front hair ďinta da ya fito ya kwanta lub lub sai ya k'ara mata kyau, wani murmushi ta saka da taga kanta a mirror, ba k'aramin kyau tayi ba , takalmin karen kelly heel bak'i ta saka, a hankali take takawa har ta fito daga ďakin ta sauk'a k'asa, sai da Aunty tace Masha Allah da ta ganta , duk da Batuul bak'a ce bata kai sauran y'an gidan haske ba amma ta fisu kyau, Baba ne yace "Mamana kinyi kyau" da murmushinta mai kyau tace "nagode Baa", break fast sukayi dukkansu sunsa kaya sunyi kyau, matar da tayi mata makeup ďince ta sauk'o ta mik'o mata clutch bag ďinta shima golden shima na karen sannan tayi musu sallama, k'arfe tara da rabi suka isa international conference center inda venue graduation ďin yake, tun daga waje manyan motoci ke a pake, k'arasawa sukayi ciki, decoration ďin wajen yayi kyau kalan graduation gown ďinsu ne purple and blue, sai da suka shiga ta saka graduation gown ďinta da hula, side ďin da aka tanadawa graduants ďin tabi, kujeranta ta nufa seat number twelve, Affan ne daga hagunta sai na Farida daga gefen Affan, tambaynshi tayi Farida bata k'araso ba, bai bata ansa ba ,Affan ne ya dubeta bayan ta zauna, mitsitsika idonshi yayi sannan yace "sorry this is my best friend's seat, can you kindly move to the next seat", dariya tayi ta ďan dugure mishi kai tace "Allah ya shiryaka Affan, in best friend ďin taka tazo sai in tashi", dariya shima ya saka yace "Besty you look gorgeous, i mean i cant say how much beautiful you look, am gonna miss you", ya fara share hawayen k'arya, dariya ma ya bata tace mishi "Farida fa, she isnt here....."bata k'arasa maganan ba ta ciro wayanta kenan zata k'irata taji bugun zuciyanta ya k'aru, a zuciyanta tace "No no, not today, let me be happy its my day" sannan ta fara ambaton Innalillahi wa inna illaihi rajiun, tana cikin addu'a taga Farida tazo kusa da Affan ta zauna, da harara tabi Farida da ido, Affan ne ya kare Farida da hannunshi yacewa Batuul "wannan kallo haka ai sai ta ji tsoro, babe ya akayi kikayi latti, i was waiting for you here all alone", ajiyan zuciya Batuul tayi tace "baza ku gane waye Yaa Abu ba, wai fa girlfriend ďinshi ce mukaje ďauka shine take b'ata mana lokaci tana ta wani abu kamar yarinya,ni shima nake tausayi ansa aurensu nan da three weeks, ya mayi ya bar mana gida mu samu mu huta", dariya Affan yasa yace mata "babe you are too much", lets concentrate on what we are here for, suka maida hankali kan speech ďin da VP ďinsu keyi, ita dai Batuul kawai tayi shiru ne amma bugun zuciyanta k'aruwa yayi dan har hawaye ya fara taruwa a idonta
💖💝BATUUL💖💝






14





By phartiemarhk





Dedicated to
*KHALEESAT HAYDAR*





Shiru hall ďin yayi ana sauraron speech ďin da VP keyi, da ta gama ne sauran members ďin High table ďin suma suka karb'i mic suna yiwa graduating students ďin Nasiha game da rayuwansu da kuma wanda zasu fara a university, sai da aka gama speech ne aka fara presenting su drama, deabate da wasu abubuwan, ana gamawa aka fara k'iran graduating students su karb'i certificates ďinsu,Batuul ce number Twelve, Mc na cewa Fatima Kashim Goni , hall ďin ne ya cika da ihu bayan Batuul ta mik'e, juniors ďinta ne ke ihun dan kirkinta da kuma taimako kowa ya santa a school ďin, hatta malamai sai da sukayi , ihun da aka sane ya sa Abutturab mamakin wacece wannan da ta samu applause haka, a hankali ta sauk'a daga kujeran da take ta k'arasa ta karb'i certificate ďinta daga hannun Vice President, a hankali tace mishi " Thank you Sir" sannan ta amsa bayan y'an hotuna da aka ďaukesu dashi ta koma inda sauran ke tsaye, haka aka ci gaba da k'iran sunayensu har sai da aka k'ira 67 students sannan aka yi musu standing ovation tareda tafa musu, a kan stage ďin kowannensu ya cire graduation cap ďinshi suka sa ihu sannan suka watsa su tare da faďin we made it,kowa kujeranshi ya koma bayan ovation ďin da akayi musu, lokacin ne aka fara presenting prizes, Best in further Physics goes to Affan Abba gana, tafi aka sa mishi, bai dawo ya zauna ba ya sakeji ance shine best in TD, haka ya sake karb'an building and cinstruction sai chemistry, Farida Ahmad Kyari aka k'ira best in Mathematics da Further Maths, sai Hamra Imam Imam best in biology, Maryam Ibrahim Tsoho best in Agric Abdul Azeez Abidemi ne best in Accounting and commerce, Sai da aka gama k'iran sunayensu aka ce best in Economics goes to Fatima Kashim Goni, tashi tayi taje ta karb'a da smile a fuskanta, bata k'arasa wajen zamanta ba aka sake cewa itace best in IRS, Government,Geography, English sai Arabic marketing da Food and Nutrition, tasowa akayi ana tayata dan baza ta iya ďauka ba, haka aka ci gaba da bata prizes har na neatest, punctual da most obedient, Dj ne ya kunna mata wakan stand up for the champion dan tafi k'owa karb'an prizes a wajen, Abutturab na daga zaune tunani ya fara wacece Fatiman nan, koma wacece Masha Allah tayi k'ok'ari, sai da ya sake ambaton sunan ne ya tuna da Kashim Goni ai Minister ne, lokacin ya tuna da ai Batuul ce, kwata kwata bai ganeta ba dan wani kyau tayi da tsawo saboda heel ďin dake k'afanta, Sadiq dake zaune gefenshine ya tab'a shi yace "Yaa Abu yarinyar nan is Genius, ga wani kyau da tayi bari mu fita sai na tambayeta yadda akayi tayi tsawo"ya faďa yana dariya, Abutturab bai kulashi ba illa wayarshi da ya ci gaba da dannawa, haka aka ci gaba da ocasion daga k'arshe aka rufe da addu'a, tun suna ciki suka fara selfie har suka fito waje, Kowa wajen family members ďinshi ya wuce, Baba Batuul ta fara rungumewa shi kuma yace mata "Mamana Allah yasa Albarka, Allah ya taimaka yasa kufi haka", daďi ya sata cewa Amin da sauri, wajen Aunty ta koma, da murmushin murna a fuskanta ta shafa kan Batuul tace "Sannun Batuul Allah yayi miki albarka, Allah yasa afi haka", Hotuna sukayi tayi dama sunxo da photo graphers ďinsu , duk y'an gidan sai da tabisu sukayi hotuna ďaya bayan ďaya sannan sukayi na Family, Affan ma sai da yazo dasu Maa sukayi hotuna, Farida ce tazo a guje tana k'iran sunan Batuul, ganin su Aunty yasa ta gaishesu, sukayi congratulating ďinta, cewa Batuul tayi kixo Ammah nata jiranki tun ďazu muyi pictures, taqi ayi wai sai kinxo, murmushi Batuul tayi tace "toh muje nima yanxu nake tunanin zuwa , tacewa Aunty zataje ta dawo, Aunty ce tace suma gasu nan zuwa wajen su Ammah ďin bari su gama gaisawa da mutane, suna juyawa zasu tafi ta rik'e hannun Farida da k'arfi, kallonta Farida tayi tace lafiya "I dont know y, but these days i use to feel restless kuma heart beat ďina na increasing", Farida da damuwa a fuskanta tace "Dont worry kiyi addu'a, we will talk about it later", k'arasawa wajen su Ammah sukayi, y'an gidansu Farida ne a wajen sai sai wata farar yarinya daga gefen Abu, sai wani da bata sani ba, bata kalli gefen da Abu yake ba ta je wajen Ammah ta rungemta," janyeta Ammah tayi ta dubeta tace "useki Bitti, Masha Allah, Allah bariki", murmushi tayi ta tace "Amin Ammah", juya wajen Abui tayi shima ya shafa kanta yayi mata addu'a, Juyawa tayi ta dubi Sadiq da Massa da suke a tare tace Yaa Sadie "ina wun", smirking yayi yace "Batuul wannan tsayi da kika k'ara ai har nima kin fini, ban ma ganeki ba, ni kai har yanxu banma yadda ke bace", da murmushinta mai kyau tace "Yaa Sadiq u are just too much, kome na saka ai bazan fika tsayi ba", yace mata "gashinan kin kamo hanya", dariya tasa sannan yace mata "congrats Batuul, we are proud of you, keep it up", murmushi tasa sannan tace "Thank you Yaa Sadiq", mutumin dake tsaye da Sadiq tacewa "ina wuni", da murmushi yace "Lafiya kalau, congratulations, kinyi k'ok'ari sosai, Allah ya bada sa'a", duk da bata san ko waye shi ba amma addu'an da yayi mata yasa ya burgeta, da murmushi tace "Nagode In sha Allah", Abutturab na daga gefe shida Ajiddeh sai zuba take mishi, Ammah ce tace bakayi congratulating Batuul ba, Idonshi ya sauk'e k'asa yace "ai mun haďu nayi congratulating ďinta" dan shi har yanxu ya kasa yadda Batuul ce, da mamaki Batuul ta ďago ta dubeshi duk da yadda zuciyanta ke bugawa dan tasan bai yi congratulating ďinta ba amma yacewa Ammah wai yayi, tana ďaga kanta suka haďa ido, sauri tayi ta ďauke nata dan brown hazel eyes ďinshi na sata taji wani iri, matar dake gefenshi fara siririya tacewa "ina wuni", kamar baza ta amsa ba har saida suka haďa ido da Ammah ne tace lafiya a dak'ile, duk da bata san Batuul ba, bata tab'a ganinta ba amma sai da taji bata sonta, Ammah ce tace toh tunda kun gaisa sai ayi pictures, photo grapher ne yazo ya fara arranging yadda zasu tsaya, da Batuul na daga gefen Abui ita da Farida, cewa Batuul yayi ta dawo gefen Abutturab, Ajiddeh kuma ta koma daga gefen su Sadiq, ba dan taso akayi wannan canjin ba haka ta koma daga gefen su Sadiq, itako Batuul kamar bata ji shiba ta tsaya a inda take har sai da ya sake cewa "young madam ki dawo nan, ya nuna mata gefen Abutturab, a hankali take tafiya har tazo inda yake nuna mata ďin , rigarta ta kama daga k'asa tana cikwikuyewa, tsayawa tayi amma gaba ďauanta ji take kamar a kan k'aya take tsaye, tsayawan da tayi gefenshi ne ya sashi jin wani iri, so yake a gama hoton nan gaba ďaya ya bar wajen dan gaba ďayanshi wani iri yakeji, sai da mai hoto yayi clicking wajen talatin sannan ya tsaya, Ammah ce tace Abutturab ya tsaya suyi daga shi sai Batuul, ďago kanta tayi ta dubeshi taga shima ita yake kallo, maza tayi ta ďauke kanta ta k'ara damke riganta da k'arfi har hannunta na gumi, hawaye ne ke shirin fitowa daga idonta dan gaba ďaya a tsorace take, tsayuwa suka dukkansu biyun dan babu yadda suka iya, mai hoton ne yace Abutturab ya ďan matsa kusa da Batuul, matsawa yayi dan so yake aka gama wannan photo session ďin da ta sasu yi, tana ganin ya matso itama ta mata da baya, ysayawa yayi ranshi a b'ace yana kallonta, hannunta ya kama ya jawota har saida ta kusa faďawa jikinshi, ido ta wara ta bishi dashi taga bama ya kallonta, su Ammah ta juya ta gani taga hankalinsu ma baya kansu, wannan farar matar ce kawai taga ta k'ura musu ido tana kallonsu, da Batuul ta kalleta ne ta bita da harara, kanta ta ďauke daga duban matar ta tsaya har pg ya gama snapping ďinsu, yana gamwa su Aunty suka iso, bayan sun gaggaisa aka sake sabon photo session, Ajiddeh kam k'in shiga tayi wai flash ďin na reflecting idonta yana sa mata ciwon kai, suna gamawa Batuul da Farida sukace zasuje suyi pictures da friends ďinsu, Affan suka fara haďuwa da a garden ďin school ďin yana ganinsu ya cewa Batuul "Best friend i will miss, i dont know how i will start over without you, you have been there for me through good and bad times all these six years..." bai k'arasa maganan ba kukan da take ta mak'alewa tun safe ya fito, da gudu taje tayi mishi bear hug tace "Affan i will miss you more, how you always make me laugh, how you make me waffles every week end night, kuma har yanxu ban koya ba, Affan muje Uk tare kaji sai kaci gaba da koyamin,i will miss everything about you", tana buďe idonta dake rufe zata janye daga rik'on da yayi mata taga Abutturab a tsaye daga gefe ya zubo mata hazel like eyes ďinshi yana hararanta, kamar ma waya yakeyi amma ya kasa ci gaba da wayan sai tsayawa da yayi yana kallon inda suke, idonta ta ďauke taci gaba da magananta tace "zan faďawa Maa ma kar a kaika cyprus a bari muje Uk tare" Farida da ta tsaya daga gefe tana share hawaye dan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login