Showing 30001 words to 33000 words out of 215266 words
ta dubi Batuul taga tana kallonta tana murmushi, ce mata tayi murmushin mey kike min haka, "ashe Ammah bata sani ba kika fito, da tayi miki faďa sosai ai", murguďa mata baki tayi tace "yanxu ma aikena tayi, ni a gama wannan auren mu huta, ki shirya muje mu karb'o sak'on", Batuul ce ta dube ta tace mata "in shirya muje ina?, ke ni babu inda zan fita yau, kije ki dawo", marairaicewa Farida tayi tace "haba mana, you know i love you, you love me too, muje tare kinji, i will get you pack of twix da Raffaello pls", dariya ma ta bawa Batuul tace "Noooo, dagaske babu inda zan fita, beside Aunty ma bata gida bare in tambayeta", Farida bata cewa Batuul komai ba ta shiga dialing number Aunty da wayan dake hannunta, Aunty na ďaukan wayan tace "Hello Farida ya akayi", cewa Aunty tayi, "Aunty muna tare da Batuul ne Ammah ta k'irani ta aikeni, nace ta rakani wai tace baza taje ba saboda bakya gida, Aunty kiyi hak'uri muje, gidan Yaa Mera ne, bana so in tafi ni kaďai", dariya Farida ta bawa Aunty tace mata "kice nace ta rakaki, wani ihu Farida tasa tace "Nagode Aunty, yanxu zamuje mu dawo, ta katse wayan, tsayawa Batuul tayi tana dubanta, ya zatayi da Farida ne a rayuwa, k'in kulata tayi ta tashi ta hau sama ta ďau wayanta ta bugawa Aunty, tana ďauka tace "Aunty kunyi waya da Farida yanxu ko", Aunty ce tace mata "ehh yanxu ta k'irani, ki rakata Batuul kuje ku dawo", toh kawai Batuul tace ta katse wayan, Farida ce ta biyo ta ďakin tace "zamuje ko Batuul", hararan wasan tabita dashi, tana dariya tazo ta zauna a gefenta tace "ai nasan you cant do without me", suna zaune har Baa Alai yazo yace mata ya iso su fito su tafi, mik'ewa sukayi, k'aramin bak'in gyale kawai Batuul ta ďauka ta yafa akan hulan dake kanta da wayanta, suka fita, Batuul ce ta shiga gba Farida ta zauna daga baya, har cikin gidan ya shigar dasu yayi parking suka fito su biyun, suna fita Batuul ta rik'ewa Farida hannu tace "Farida ya fara", kallonta Farida tayi tace "mene ďin ya fara?", "heart beat ďina mana, its increasing, am telling you ppl, its becoming serious", ce mata Farida tayi "sorry anjima sai mu faďawa Aunty", bata amsa mata ba dan ita kaďai tasan abunda take ji, tafiya sukayi mai ďan nisa tukunna suka isa cikin gidan, har ďakin Yaa mera suka isa, tana ganinsu tayi murmushi tace har kunzo, "wannan ba Batuul ba", da mamaki Batuul tace "ehh nice" dan batasan matar ba, matar ce tace mata "Masha Allah kin girma, tun kina 2yrs rabona dake, mamanki na gidan biki ko", da ehh Batuul ta amsa mata sannan Farida tace "Yaa Ammah ce ta aikomu wai muz...." bata k'arasa ba tace mata "ehh kuje da Ya bawa ta nuna miki inda ake aikin kiga ko sun gama" ta haďa ta da Baiwa ďaya suka tafi, Batuul na zaune tare da Yaa mera tana tambayanta abubuwa har makaranta, tace mata sunyi graduating yanxu university zasu shiga, wayanta take ta dannawa tana sawa a kunne sai ta cire, Batuul ta duba tace mata "Batuul", a hankali ta ďago daga wasan da take da zoben hannunta ta dubi yaa mera tace "na'am", "chamber ďin Massa zakije ki duba min shi inata k'iranshi baya ďauka, intercom ďinshi ma baya ďauka kuma ya shigo ďazu, ki ce mishi ina k'iranshi", bata sa komai a ranta ba ta mik'e tace "ta ina ďakin yake", kwatance tayi mata "tace in kin fita ki mik'e sai kin wuce dorms uku, chamber yana by the left", ta amsa da toh ta fita, a hankali take tafiya har ta isa ďakin, knocking tayi taji ba a buďe ba, a hankali ta tura k'ofan ďakin taga babu haske, sai ďan dim light daga ciki, kai ta sa ta shiga cikin ďakin, k'anshin da taji ne ya sata jin kamar zuciyanta zai faďo dan bugawa, tsayawa tayi a spot ďin da take ta kasa gaba ta kasa baya
💖💝BATUUL💖💝
18
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tsayawa tayi tana juye juye in zata bi, kawai deciding tayi da ta fara sallama ko zai jiyota inma a ciki yake, sallama tayi ta yi taji ba ba a amsa ba, lalube ta fara ko zata switch ďin ďakin har ta gama lalubenta bata ga komai ba, deciding tayi toh ta k'ira sunanshi ko zai amsa, "Massa" ,shiru tayi tana jira taji ko za a amsa amma taji shiru, sau uku tana k'iran sunan taji ba a amsa ba kawai ta juya zata fita ta ga kamar mutum na kwance a kan seater, k'arasawa tayi wajen seater ta tsaya ta tabbatar mutum ne kwance a kai, broad figure ďinshi na kwance peacefully amma bata ganin fuskanahi dan ya juya mata baya, sake k'iran sunan tayi taji bai amsa ba, deciding tayi ta tab'a shi tunda baccin nashi ya kai har haka nauyi, hannu ta sa a goshinshi taji wani ďumi da laushi, maza tayi zata ďauke hannunta taji wani hannu mai laushi da faďi a kan nata, wani abu ne taji gaba ďaya yabi jikinta ga heartbeat ďin ya fara aikin nashi kamar mai shirin fitowa, idonta ya cika da hawaye tab saura k'iris ya zubo, tsayawa tayi still a wajen ta kasa ko da k'wak'waren numfashi, juyowa yayi ya jawota ta kusa faďawa kanshi tayi hanzari ta dafa kujerar, wayanshi ya ďauko daga gefenshi, flash light ya kunna ya haska yaga ko wacece, idonta ta rintse da ya haska flash light ďin a fuskanta, hawayen da ya taru a idon ne ya silalo ta ido ďaya, tsayawa yayi yana kallon cute face ďinta , k'aramin lips ďinta idonshi ya sauk'a akai, yadda hawayen ya gangaro har kan cute lips ďin yabi da ido, ita dai tana tsaye ta kasa motsi, idon ma bata buďe shi ba dan bata san ma ko waye bane, tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna har lokacin bai sake mata hannu ba, sai da ya zauna ya fara mamakin, ya akayi tazo gidannan, kuma mey ma ya kawota har ďakin nan, k'ara janyo hannunta yayi , a lokacin ta buďe idonta, wara idon tayi ganin wanda ke rik'e da hannunta a gabanta, ihu ta buďe baki zata kurma yayi maza ya toshe bakinta, ce mata yayi "shut up, and tell me y you are here" tare da fixgo ta ta k'arasa gabanshi, sai da yaga kyarman da jikinta keyi ya ragu sannan ya sake mata baki da hannu, mik'ewa yayi ya isa wani waje ya kunna wutan ďakin, gaba ďayanta ya duba tun daga kai har k'asa sannan ya koma ya zauna a kujerar da ya tashi, tambayanta ya sakeyi, "mey kike yi a ďakin nan har kika zo kina tab'a ni", kasa magana tayi dan gaba ďaya ta tsorata da ganinshi, tsawa ya daka mata "yace ba magana nake miki ba kinyi shiru kina kallo na, sai da ta tuna da sunan wacce ta aikotan sannan jiki a sanyaye tace mishi "Yaa mera ce tace in zo nan chamber in k'ira mata Massa, i didnt know inace kaine Massa, kuma ďakin ne da duhu shine nace bari in tashe shi, kayi hak'uri", gaba ďaya ta gama tsorata da ganinshi, juyawa tayi zata tafi yayi maza ypa fixgota, ce mata yayi "tab'a min fuskan kuma na meye", "innalillahi wa inna illaihi rajiun ta ambata a zuciyanta, ba ta faďa mishi tashin Massan zatayi bane kuma da duhu ita bata san ma fuska bane, cikin dakewa tace "ďakin ne da duhu, ban san fuskan ka bane" ta warce hannunta daga ruk'on da yayi mata tayi ta fita daga ďakin a guje, sunanta ya k'ira amma ko sauraronshi bata yi ba tayi tafiyarta, ranshi ne yayi mugun b'acin k'in amsawa da tayi, tashi yayi ya shiga toilet dake bedroom zaiyi wanka
Sai da ta iso k'ofar ďakin sannan ta tsaya ta daidaita numfashinta, ganin ta samu nutsuwa ya sata tura k'ofan ďakin a hankali, da sallama ta shiga ta zauna sannan tace "Yaa Mera , Massan baya nan" kamar kar ta faďa mata taga Abu sai kuma tace "amma naga Yaa Abu a ďakin yana bacci", jin ance Abutturab na ďakin yasa ta cewa "ohh shi yana gida, toh dama ai dan shi nake neman Massan, yau zasuyi wushe wushen ko?", ta tambayi Batuul, ďago kai Batuul tayi tana dubawa ko wani ake tambaya, da ta ga babu kowa a ďakin sai ita ya tabbatar mata da ita Yaa Mera ke magana, " No, ni ban sani ba fa Yaa, bansan mey zasuyi yau ba, sai dai in Farida ta shigo mu tambayeta" inji Batuul, Yaa Mera ce ta sake cewa "ai tunda ma yana gidan bari in k'irashi yazo in ganshi muyi magana dashi", mamakin matar takeyi kamar ba sarauniya ba, babu ruwanta, ita ko bayi ma bata ajiyewa kusa da ita gata da fara'a, ga kyau, kammansu ďaya da Ammah, Abutturab ďinma dasu yayi kama, hasken sune kawai bai ďauko ba sai yayi duhun Abui, su Farida da Sadiq ne sukayi kama da Abui amma suka ďauko hasken Ammah, tana zaune tana ta zancen zuci Farida ta shigo da plate ďin kisre da miyar kuka da yaji kaji, gefen Batuul taje ta zauna ta cewa Yaa Mera "Yaa sun iya kisren sosai, kamar fa da engine sukeyi , ya burgeni yadda sukeyi shiyasa ma na ďebo kaďan, Batuul ci kiji", Yaa Mera ce tace "shiyasa mamanku tace sai anan za ayi, yanxu ma daga nan za a kwasa akai gidansu matar Abun", ido Farida ta wara tace "Yaa drums dayawa fa akayi, kuma duka za a kai musu, wannan matar ta Yaa Abu suna yi bada wasa ba", dariya ta bawa Yaa Mera tace mata "al'adanmu kenan Farida, haka mukeyi in zamu aurar da yara", cewa Farida tayi "lallai, su suka sani", taci gaba da cin abincinta, lura tayi da Batuul bata ci tace "meye kika sani gaba, kici mana", harara Batuul tabita dashi tayi magana a hankali yadda Yaa Mera baza taji ba "ce miki nayi inajin yunwa, ki gama mu tafi ni", Yaa Mera ce ta ďagi taga Batuul ďin bata cin kisren, ce mata tayi "Batuul bitti, beri bei" (Batuul y'ata, kici abinci), a hankali ta amsa da "toh", sannan ma matso tasa hannu a cikin plate ďin
Yana fitowa daga toilet ďin bayan yayi wanka da alwalar la'asar, wayanshi ya ďaga ya k'ira Massa, yana ďagawa yace mishi " Kana inane", Massa ne ya amsa da "muna tare dasu Imran a Protea, ya kan naka, yayi sauk'i", ce mishi yayi "Yeah sosai, ina jiranka kazo ka ďaukeni", sannan ya katse k'iran, kaya ya saka cikin sabbin kayanshi da suke gidan da ya ďinka na biki, bayan ya gama ne yayi sallah la'asar, yana idarwa wayarshi tayi k'ara, ďauka yayi yasa a kunne, "salamu alaikum, Yaa Mera nda dubdo", ehh ina gida, toh bari in sauk'o sannan ya katse wayan", sosai yayi kyau da kaftan ďin da ya saka, ya ďaura hula akanshi sannan ya fita, side ďin Yaa Mera yayi, da shiga ya samu waje ya zauna ya sake gaisheta, Farida ma gaisheshi tayi , bayan ya amsa ne Yaa Mera ta dubeshi tace "yau ne wushe wushen naku ko", kai ya gyaďa tare da amsa mata da "ehh", ce mishi tayi "wane time za ayi?", "k'arfe bakwai ne zuwa sha ďaya", "toh yanxu kace musu su shiryata k'arfe biyar, anan za ayi mata kéla tul kamin ku wuce wajen wushe wushen, zamu tura musu mota, daga nan zamu kaita wajen, har kaya zamu bata ta saka, mun gama magana da mamanka", cewa yayi "okay Yaa, In sha Allah zan faďa mata, sai ta faďa a gidan nasu" , sallama yayi da ita ya mik'e kenan zai yi hanyan waje yaga an buďe wani k'ofa, k'ofan yabi da kallo, Batuul ce ta fito daga ciki hannunta rik'e da hand napkin tana gogewa, ta cire gyalen dake yafe akanta ďazu sai hular kawai, idonta dake kan abinda ke hannunta ta ďago suka yi ido huďu, wani irin abu taji gaba ďayanta, shima tsayawa yayi kallonta, idonta ta ďauke daga kanshi shima yayi k'wafa ya fita daga ďakin
k'iran Massa ne ya shigo wayanshi, recieving yayi yace mishi "ka iso ne?, toh gani nan fitowa", motar da Massa ke ciki yaje ya buďe ya zauna , Massa ne ya tambayeshi "ya jikin dai Man, wannan rashin lafiyan ai sai ya bari a kwanakin nan ba, kai da kake shirin zama ango da dai ya isa wani wajen, yayi wrong timing gashi da yake ka fishi k'wari kayi fighting ďinshi", kallon Massa yayi da ďan murmushi a fuskanshi ya girgiza kai yaci gaba da danna wayarsa, "Hello", yace bayan ya an ďauki wayar da ya buga ďin, amsa akayi da "Hello baby, am missing you over here, ya gajiya dan ni gaba ďaya na gaji so nake kawai a ďaura auren nan mu tafi mu huta dan ba k'aramar gajiya nakeji ba a jikina, yanxu ma a ďaki nake ni kaďai wai za a min gyara....", yasan idan ya barta taci gaba da magana sai ya manta dalilin da yasa ya k'irata, katseta yayi yace "gajiya Alhamdulillah, ki faďawa su Mum za ayi miki kéla tul before a tafi wushe wushen a gidan Aunty ďina, kuma kayan wushe wushen ma daga can zaki sa, zan aiko mota by 5, you should be ready", ce mishi tayi "Aliyu gaskiya waďannan abubuwan naku na al'ada na gaji dasu, tunfa last week ake ta yi, kuma kayan ma mum ta riga da tasa an siyomin a turkey, ni gaskiya a bar wannan ďin kawai, ai anyi sauran, kuma ma its too late yaushe zan faďa musu su shirya", ranshi ne ya fara b'aci, cikin dakewa yace "wani shiri zakuyi, ce miki nayi zan aiko mota ki taho ke kaďai, kuma in kin faďawa mum ďin nasan ba hanaki zatayi ba", tsaki yaja dan ranshi daďa baci yayi yace "in na aiko da motar kar kizo" ya kashe wayan , Massa ne ya dubeshi yaga ranshi ya b'aci yace "lafiya naga kana tsaki", tsakin ya kuma ja yace mishi "yarinyar nan , tun last few days nayi observing that duk abinda na faďa sai ta canja, ce mata fa nayi yanxu zan turo driver a kaita gidab Yaa, take cemin ita baza taje ba", bai ci gaba ba Massa ya dafa kafadmďanshi yace mishi "Man its okay, zata dena in sha Allah", da haka suka canja hira, hotel ďin sukaje yaga abokananshi dayawa sun sake k'aruwa, sai da ya ďan huta yake tambayan Massa, "gobe what time za a tafi ďaurin auren Maiduguri", "sunce flight ďin goben k'arfe huďu ne , so muna da time da in mutane suka k'aru za a yi musu booking tunda da yamma ne", "okay" kawai yace mishi suka shiga cikin abokanan
Ganin ya katse wayan ne ta tsaya ta k'urawa wayan ido kamar wanda sukayi wayan dashi ďin zai fito, Mesa Aliyu yake min hakane take tambayar kanta, jibi nefa ďaurin aurensu amma kawai dan ta faďi magana ya katse mata waya harda cewa in ya turo motar kar tazo, ai gaskiya ta faďa tun kwananki suke ta yi musu abubuwa wai al'ada, shi kuma kawai sai ya ďau fushi, a ranta take cewa "dan yaga inasonshi ne yake wasu abubuwan", k'wafa tayi ta cewa mai yi mata gyaran jikin zata je ta dawo, matar tace mata babu komai sai kin dawo, fita tayi daga ďakin, tun daga bakin k'ofa gidan cike yake da y'an uwa d abokan arziki, matane kyawawa, farare da gashi kowa taci kwalliya an zuba gwalagwalai, ďaďďaya zaka bak'i a gidan nan, tana tafiya mutane na ta gaisheta wasu ta gaishesu cikin yarensu shuwa, wani ďaki ta buďe ta shiga, ďakin babba ne mai kyan gaske, babu mutane a ciki sosai, daga Mum , sai wata mata da zatayi sa'ar Mum sai Yaa zee, k'arasawa tayi ta zauana daga gefen mom, matar kawai tace wa "Jainaba inta afe", matar ce tace mata "afe selai Ajiddeh, ya shirye shirye, da gajiya", tace gashinan fa na gaji sosai, ina su Attutu, Abba Mahammad da Adum", ce mata tayi "suna gida bamuzo tare ba anjima za a kawosu", juyawa tayi ta dubi mum da ke jiranta ta gama ta faďa mata dalilinta na fitiwa ana mata gyaran jiki, ce mata tayi "Mum yanxu Aliyu ya k'irani wai zai turo a ďaukeni k'arfe biyar a kaini gidan k'anwar mamanshi, wai akwai wani abu da zasu yi min daga can zamu wuce wajen wushe wushen, kuma ma wai kayan da zan saka ma su zasu bani", cikin ďaga murya Mum ta fara magana "nifa Abun nan nasu Hajiya Bilqees ya isheni, wace al'adarsu ce bamu gani ba fara bikin nan, ni sanin da nayiwa Hajiya Bilqees ma ba kanuriya bace amma gaba ďaya dan tana auren kanuri ta canja gaba ďaya, a ina ake wani kéla tul a Ndjamena, kuma da suke cewa su zasu baki kayan kisa ai ganin kasawarsu ne yasa muka ce zamuyi miki , ko ďari mukace muna so ai yaci a kawo miki, kinfi k'arfin akwatuna arba'in, ba dan Babanku yace a bari ba kuma zai sab'awa duk wanda ya tada maganan wlhy da sai an maida musu tunda dama cewa tayi a dawo dashi in muka k'i karb'a", Yaa zee ce tace "Mum ai ita tabi ta liqewa yaron kamar babu wani namiji a duniya sai shi, ni gaba ďayanshi bai min, sai girman kai da uake dashi kamar mutumin da", matar da aka k'ira da Jainaba ce tace "toh ku yanxu menene na tada jijiyoyin wuya, ai damu suke zancen , ku bari kawai a gama bikin zasu shigo hannu, tayi yadda yace ďin, anjima in ya turo driver kije, tashi kije a gama miki gyaran kamin lokacin yayi", da haka ta mik'e ta koma ďakin, tana zama ta k'irashi, ansawa yayi shiru yana