Showing 174001 words to 177000 words out of 215266 words

Chapter 59 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1694

ji sauki Alhamdulillah Anty", Aunty Amna tace "Zaki warke kinji, Allah ya rabaki da sharrin masharranta", daidai nan Ajiddeh ta fito d'akin Abu zata sauk'o down stairs itama, jin maganan da Aunty Amna keyi yasa ta kasa d'aga k'afarta kuma, ta tsaya tana kallonsu, Aunty Amna ta dubi Abutturab da ya had'e rai tace "kai kuma yarinya batada lafiya kaje ka ajiyeta baka fadawa mutane ba", hannun Batuul ya janye ya dawo da ita gabanshi yace "Bata fa jin dad'i, she is weak", wara ido Aunty Amna tayi tace "Iyye, kaji mara kunya, da kasan she is weak ka barta tana shan wuya a can, kai a dole mai mata ko, ai sai ka kinkimeta tunda she is weak" sunkuyar da kai Batuul tayi dan kunya, kamar jira yakeyi ko sai gani sukayi yasa hannayenshi duka biyu zai d'auketa, wara ido Batuul tayi tareda matsawa baya tana girgiza mishi kai alamun kar ya mata haka, kamar bai gane mey take nufi ba ya sa hannu ya kamota zai d'agata taji kamar ana kulle mata ciki ta fasa wani razanannen k'ara da yafi na ko yaushe had'e ta rike cikin tana kiran Anty da kyar, lkci daya ta sulale yayi maza ya bita ya kamata a rikice yace "Ya salam, Not again baby, you will get well soon", Aunty Amna da ta tsaya kallon tsiyar Abutturab a tsorace da jin karan ta tsuguna itama ta kamo Batuul duk ta rud'e tace "Abu ciwon nata ne", kasa bata amsa yayi sai d'aukarta da yayi cak yayi k'asa da ita yana k'iran sunan Ammah, Ajiddeh da ke tsaye har lokacin tana kallonsu idonta ciccike da hawaye ta kasa d'aga k'afarta, ta rasa me ke mata dadi a duniylar, ganin yayi k'asa da Batuul ta fashe da kuka ta koma d'akin da take da sauri, a rikice Ammah ta fito tana tambayan mey ya faru, Farida da Sadiq dake side d'in Abui tare suka fito suna tambayan mey ya faru, Aunty Amna ma na tambayarshi ko ciwon nata amma ya kasa ce mata komai sai sunan Ammah da yake k'ira yana girgiza Batuul d'in ta tashi, Gaba daya duk sun rud'e kowa ya rasa abinda zaiyi ganin jikin Batuul d'in duk ya saki, Farida na kuka tace "Ammah ni kam nace ku kaita wajen Dr Zakaa zai dubata ya fad'a mana abinda ke damunta," hawayen dake idonta ta goge tace "Sadiq Abui na Guest room tareda bak'onshi, kace ciwon nata ya dawo", a rud'e Sadiq d'in ya amsa ya fita amsa aiken da Ammah ta mishi, da k'yar Ammah tayi k'arfin hali ta kamo Abun dake riqe da Batuul ya kasa cewa komai tace "Babana kawota ka kwantar da ita, zataji sauk'i In sha Allah, yanzu za ayi mata magani", ta fad'a tana k'ok'arin karb'an Batuul daga hannunshi, girgiza kanshi yakeyi hawaye na gangarowa idonshi, zama yayi kan kujerar Batuul na rungume jikinshi, gefenshi Ammah ta dawo ta zauna zatayi magana kenan Abui yayi sallama shida Ashiekh da Sadiq, Abui yace "Subhanallahi, jikin nata ne kenan", Abu bai iya cewa komai va don shi kadai yasan mey yakeji cikin ranshi, bayason kowa ya tab'ata sbd fargaban abinda za a ce mishi ya biyo baya, bayajin ko d'aya daga cikin nerves da pulses d'in jikinta na aiki, Ammah ce ta kawo hannunta ta rik'o na Batuul d'in, gabanta ne ya rik'a fad'i ganin hannun Batuul d'in ya saki, d'agowa tayi tana kallom Abu da idanunshi suka kad'a, lumshe ido yayi snn ya bud'e yace "Ammah babu abinda ya sameta ko?, I know she will be alright, nasani Fatima zakiji sauk'i i know you won't leave me just like that isn't it Batuul, you have to get up", Aunty Amna Abui ya kalla yayi mata alamun taja Farida da Ammah da ta matsa baya tana girgiza Kai, hakan ko tayi ta kama hannun Ammah tace "Ammah zataji sauk'i fa, ba dama haka yakeyi mata ba, yanzun nan zata farfad'o, muje muyi mata addu'an samun sauk'i", Itama Aunty Amna k'arfin hali kawai takeyi gaba d'aya jikinta yayi sanyi sai hawaye da takeyi, Farida ce ta karb'e hannunta daga rik'on da Aunty Amna tayi mata ta dawo gaban Abu ta tsuguna dab fuskar Batuul d'in tana kallonsa hawaye na sakko mata tace "Yaaa Abu saida nace maka a kaita asibiti fa, don Allah mu tafi", ta kalli Abui dake tsaye ta mike ta isa kusa da shi cikin kuka tace "Abui don Allah nace mu kaita asibiti da yanzu ta warke, ka ganta yanxu kwance ko motsi batayi, Dan Allah muje a kaita", Hannu Abui ya d'aura kanta ya shafa snn yace "Babu abinda ya sameta kinji, zataji sauki" yacewa Sadiq " *Sadiq tai sha samiro Leno*, Sadiq kamata ka kaita sama", tana girgiza kai tana kuka haka Sadiq ya jata yayi sama da ita ya rage daga Abui sai Abu dake riqe da Batuul snn Asheikh, Asheik ya dubi Abui yace "Alanguro akwai Zamzam a kusa?" Abui yace "Ehh bari a d'auko",
[11/15, 11:15 AM] ‪+234 810 957 2036‬: 💖💝BATUUL💖💝

84

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



Wani nannauyan ajiyan Zuciya Aunty ta sauke lokacin da Yusra ta mik'o mata wayanta tace "Mama ga wayan inji Yayya wai ta gama", karb'an wayan Aunty tayi tace "Kuje ku shirya, its getting late, kice wa Fa'eezah a gama sa muku kaya ku tafi", kai Yusra ta kad'a tace "Toh Mama", daga haka ta fice tana tsalle, wayar ta sake janyowa ta dialling number Baba, ringing biyu ya d'aga, jin muryan Aunty a sanyaye ya sashi saurin cewa "mey ya samu muryanki haka, its so weakening", kamar jira takeyi taji muryan Baba hawayen dake cike idonta ya gangaro, ido ta bud'e ta lumshe snn tace "Uncle ashe Batuul ce bataji dadi ba saida aka dawo da ita d'azu Ammah tamin waya tana fad'amin wai sun dawo da ita tana can gidansu, shine nakeso in ganta koma mu taho gidan tare, we should treat her here a gida hankalina sam yaqi kwanciya, inason ganinta Uncle", "Maryam", Baba ya kirata daga d'aya b'angaren, kasa amsawa tayi har saida ya sake cewa "Maryam", kuka ta fasheda ta kasa amsa kiran da yakeyi mata, Baba dake zaune office yace "Subhanallahi Maryam kuka kuma, mey kikeso?", cikin sheshekar kuka tace "Uncle gida nakeso ta dawo, hankalina zaifi kwanciya in ina ganinta, kaga fa cewa Ammah tayi batasan mey ke damun Batuul d'in ba, toh haka zatayi ta zama da ciwo ba'a nema mata magani ba Uncle", D'an Murmusawa Baba yayi yace "Haba Maryam, kada son y'arki ya rufe miki ido ki manta da cewa tanada aure, kinfi kowa sanin yanzu duk wani nauyi da responsiblity d'inta na kan mijinta, in kikace zaki dawo da ita gabanki bakya tunanin kin musu shishigi har ma suyi tunanin gazawar su muka gani, am very sure kin san su masu kula da Batuul ne dama duk sauran yaran nan ko bama nan", tana share hawayen dake zubo mata tace "Uncle nifa bawai gani nayi sun kasa ba, rashin sanin takamaimai abinda ke damunta da ba ayi bane yafi d'aga min hankali", Abui yace "Duk naji wannan, ki kwantar da hankalinki da izinin Allah zata samu sauk'i, tunda shi Aliyun ya sanar dani rashin lafiyarta, yanzu haka sun d'auko masu magani ana dubata, kiyi mata add'ua sosai kinji, sai kiga ta samu lafiya kamar da, amma in taga kina tada hankalinki itama nata hankalin kinsa tashi zaiyi", kamar Baban na gabanta ta shiga gyad'a kai tana share hawayen fuskarta, da haka ya samu ya rarrasheta ya kwantar mata da hankali

Sadiq ne ya d'auko Zamzam d'in da ake buk'ata a side d'in Abui, a cup Asheikh ya d'an tsiyaya snn ya samu waje ya zauna ya fara tofi cikin ruwa, Abu dai har lokacin ya kasa cewa komai sai ido da ya zuba mata idonshi duk ya kad'a, motsin kirki ya kasa yi, he is so freaked, gani yakeyi duk wanda ya tab'ata ce mishi za ai ta bar rayuwa, Asheikh da ya gama tofin shi ya miqe ya dawo gaban kujerar da Abu ke riqe da ita, Abui yace "Aliyu ko zaka samu a gyarata tasha maganin", kamar badashi akayi maganan ba, saida Asheikh ya sake maimatawa snn ya d'ago rinannun idanunshi dake cike taf da hawaye kamar wani yaro, kai Abui ya kad'a mishi alamun he should be strong tare da zuwa kusa dashi ya zauna ya dafa mishi kafad'a yace "Abutturab you have to be strong okay?, zata samu lafiya In sha Allah kaci gaba da yi mata addu'a, ido ya lumshe snn yace "Abui bata mutu bako, baza ta mutu ba In San Allah", sosai Abui ya tausaya mishi yace "ciwo ai ba mutuwa bane Aliyu, zataji sauki da yardar Allah, kayi yadda yace d'in ka kwantar da ita a nema mata lafiya", gani yakeyi kamar in ya sauketa daga jikinshi wani abun zai sameta, kallonta yayi for some seconds snn jiki a sanyaye ya shimfid'eta kan doguwar kujerar amma har lokacin hannunta na cikin nashi, Asheikh ya karaso gaban kujeran ya tsuguna daidai kan Batuul snn ya mik'awa Abu ruwan yace "amshi ka shafa mata a fuskarta", hannu Abu ya mik'o ya tsiyaya mishi ruwan snn ya shafa mata shi a fuska, bayan ya gama ya sa a mik'o k'aramin spoon yace Abu yana sa mata droplet a baki, jiki a sanyaye ya anshi cup d'in ya d'ebi kad'an ya d'iga mata shi a baki, wani irin dogon numfashi taja da ya sa Abu saurin kamota yace "Batuul am glad you are alive, don't leave me again kinji, don't plsss", sai ga hawaye nan idonshi, bata bud'e ido ba haka nan batasan abinda akeyi ba, kamar ba ita tayi wannan numfashin ba ta koma yadda take d'azu, Asheikh yayi gyaran muryan yace "Alhamdulillah, wannan ruwa da ta sha ya dad'a tabbatar mana da lallai asiri akayi mata kuma yana nan cikin jikinta, yawo yakeyi gaba d'aya jikin nata dan a ruwa aka jefa sihirin da akayi mata, yadda yake yawo cikin ruwa haka itama yake yawo cikin jikin nata snn gaba d'aya rayuwar aka so ta bari da ita da abinda ke cikinta amma da yake Allah yayi tana da saurin numfashi bata mutu ba sai dai za a ci gaba da magunguna snn anayi mata sauk'ar Qur'ani da kuma tofi kullum, In sha Allah da yardar Allah zata samu sauk'i", Abui yace "Subhanallahi, La hawla wala quwata illa billahil aliyyil Azim", Sadiq dake tsaye shi ma tun d'azu ya rasa ma abin fad'a, yanzu har Batuul abar ayi ma asirice, duniyan nan is so cruel, Allah ya bata lafiya su kuma Allah ya toni asirinsu koma su waye sukayi mata", kamar wanda aka tsikara haka Abu ya mik'e ya isa gaban Asheikh yace "Asheikh inaso in san su waye sukeson cutar da ita da dalilinsu na cutarta, yanzun nan bama sai anjima ba, Ko su waye su sai nasa sun gane kuaransu na cutar min mata da sukayi", Asheikh yayi murmushi yace "Toh mu dai baza muce ga wadanda sukayi mata ba har sai ta samu sauk'i, in akwai likita sai a samoshi ya riqa dubata da abinda ke jikinta, snn tunda ba abinci zata ci ba, su sai su duba suga yadda za ayi tana samu, mu kuma a namu b'angaren zamuyi kok'arin ganin mun taimaka da addu'a", Jinshi kawai Abu yayi amma ba wai ya aminta da zancen ba, Abui yace "Toh Asheikh mun gode sosai", yace a k'ira mishi Aunty Amna ko Ammah yayi musu bayanin sauran magungunan nata da yadda za ayi amfani dasu, Aunty Amna ce tazo amma Abu sam ya kasa ya tsare sai shi aka bawa magungunan yace "Zaitun d'in za a riqa shafa mata shi a dukkan jikinta, Ma'ul ward d'in kuma ana d'iga mata shi a baki, kad'an kuma a saka a wool a kai mata hanci ta shak'a, Habbatus saudanma jikinta za a riqa shafewa dashi kamin ta kwanta, Abu ne ya anshi komai.

Tuk'i sukeyi hanyar Jere, Driver sai dariya lbr raha yake yi yana kyakyatawa, yana son fita irin wannan da Dad keyi ba tareda entourage d'inshi ba, kamar daga sama sai ganin mata sukayi sanye da Hijab d'inta ta shigo titin a guje, ji kake k'iiii ammma ina saida suka buge ta, daga nan sukayi losing control d'in tasu motar, Babu abinda Daddy yake fad'i sai "Innalillahi wa inna illaihi rajiun", abinda ya dinga nanatawa kenan har motar taje ta bugi wata bishiya snn motar ta tsaya, kan kace meye mutane har sun cika wajen wasu suna wajen matar da aka buge wasu kuma sunyi wajen motar, jin surutun mutane yasa Dad sanin lallai da sauran ransu, a hankali ya d'aga hannunshi da yakeji kamar ba nashi ba ya tura k'ofar motar, Driver dake gaba sai faman kokuwa yakeyi da airbag da ya rufe mishi fuska, mutanen dake wajen ne suka taimaka musu suka fito daga cikin motar, daga can Side d'in sukaji ana ihun "ta mutu", wasu suna "ba mutuwa tayi ba ayi saurin kaita asibiti", da sauri Daddy ya karasa gurinsu, ganin matar taji ciwo sosai yasa cikin hanzari yace "Dan Allah bayin Allah akwai wani wanda ya santa cikinku sai muje dashi asibiti dake cikin gari", duk mutanen dake gurin kowa yace su gaskiya basu tab'a ganinta ba, haka duk suka riqa zuwa suna kallonta suna basu santa ba, ganin ana b'ata lokaci yasa Dad yace musu "Toh koh zaku had'a mu da wani da kuka yarda dashi mu tafi asibitin dashi, sai yaje ya gano inda muke ko daga bayane in Allah yasa an samu y'an uwanta sai mu dawo da ita", duk yawan mutanen dake gurin nan kowa mak'e kafad'a yayi yace shi baxa shi ba, Mutumin birni ba abun yadda bane", d'an k'aramin tsaki Dad yaja yace "Ado zo mu taimaka mu sata mota, mutanen nan ba lafiya ne dasu ba", Ba b'ata lokaci Ado yazo suka kamata suka sata mota, mutanen ganin dagaske suke tafiya zasuyi da ita yasa suka kama surutu, kota Kansu Daddy baibi ba yacewa Ado yaja motar su tafi, Abuja suka karaso direct suka wuce asibiti lokacin ana kiraye kirayen Sallar Magrib, suna zuwa aka karb'eta aka fara bata taimakon gaggawa

Bayan Asheikh ya koma guest side ne Abu ya d'auki Batuul yayi d'akin Ammah da ita ya kwantar da ita kan gado, ya jima yana yi mata addu'a da fatan samun lafiya kamin Ammah tace yaje ya watsa ruwa yayi Sallah dan ko azahar da la'asar d'inma duk a gida yayisu, sam yaqi barin wajenta, abinci kam har lokacin ba a samu ya shiga cikinshi ba, tunda ya dawo sai yanzu ya shiga d'akinshi, gaba d'aya ya manta da zancen wata Ajiddeh a gidan, ajiyar zuciya ya sauke ganinta zaune bakin gadon kamar mai jiran ace cas ta sa gudu, K'araswa yayi cikin d'akin ya zauna kan gadon tareda riqe kan da duka hannayenshi, a hankali ta dawo gefenshi ta zauna ta d'an dafashi tace "Sannu, how is she feeling now?", bai bata amsa ba sai rungumeta da yayi tsam a jikinshi, har saida ta tsorata jin irin force d'in da yasa a hug d'in, kok'arin kwace kanta takeyi amma sam bai saketa ba, maganganun Asheikh kawai yake tunawa da yace da abinda akayiwa Batuul ta fara wannan ciwon, a hankali ya d'aura fuskarshi kan wuyanta ya fara magana a hankali "I can't risk losing her for anyone, they were trying to hurt her, so suke su rabata da rayuwarta, Mey tayi musu zasu maka haka?", kyarma jikin Ajiddeh ya fara bugun zuciyarta ya tsananta har wani danshi takeji yana bin jikinta, saketa yayi ya rik'o kafad'unta yace "Hauwa do you know they wanted killing her?, an encounter with them will have to b their worst nightmare, I will make them pay for each pain they caused her", da sauri Ajiddeh ta d'ago itama idonta duk ya cicciko da kyar tace "Its okay babe, they will surely pay for it, amma kasan su waye?", kai ya girgiza mata alamun No, ta saka hannayenta cikin gashinshi tace "Everything will b fine kaji, kaje kayi wanka, you need rest", mikewa yayi ya shirya ya shige toilet, baki Ajiddeh ta toshe ta saki wani irin kuka, tausayin rayuwarta ta fara, in dai Abu ya gano she is behind komai tasan zamansu ya xo karshe, har ya fito daga wanka tana nan inda ya bar ta, cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya ya dawo kusa da ita ya xauna yace " You also need some rest, ki tafi kiyi wanka, farida will get you something to eat sai ki kwanta" mikewa yayi ya fiddo mata da towel ya mika mata ta karba a sanyaye ta mike ta shiga bathroom din, kwanciya yayi ya lumshe ido ya dafe kansa da yayi masa nauyi, ji yake kamar ciwon Batuul ya dawo jikinsa kawai, da yake a gajiye yake gashi tun jiya rabonsa da bacci, lokaci daya baccin ya daukesa.

Washegari Aunty Jainaba bata koma gida ba sai da ta k'ara kwana har biyu snn ta shirya Mum ta had'ata da kulle kullensu da suka koma gun boka suka amso bayan sun gama planning irin wulakancin da za ayiwa Idrees, shi da kanshi yaje ya d'aukota a airport, tun daga airport d'in taga yadda yanayin shi suka canza, ganin yana wani shan kanshi itama ta watsar da kashinshi a ranta tana ayyana yadda zataci ubanshi har suka isa gida, Babu kowa a gidan tasan duk yaran na makaranta masu aiki na b'angarensu, d'akin ta bud'e ta shiga, turus tayi ta tsaya ganin komai na d'akin an canja shi snn ga jerin sabbin akwatuna an a d'akin har set uku, juyowa tayi zata mishi magana cikeda bala'i, dama kan wannan surprise d'in nashi ne ya sata baro aikin da takeyi can Abuja ta taho amma ganin ba fuska

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login