Showing 45001 words to 48000 words out of 215266 words

Chapter 16 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1719

kika ji ciwo", hawayen da ta ke ta k'ok'arin dannewa ne ya zubo , takowa Aunty tayi tazo gabanta ta rik'e ta tareda tambayanta "Batuul lafiya kike kuka, meye ya sameki, kinyi shiru ki faďa min, ciwon da kikaji ne?", kai ta girgiza, "toh meye" Aunty ta sake tambayanta, a hankali ta amsa da "babu", "Ban yadda babu ba, babu ne ya saki zuwa da cemin zaki gida ko kuma babu ne ya saki yin kuka", ita dai Batuul ta kasa cewa komai dan batasan ma mey ke sata kukan ba, cewa tayi "kawai inason komawa gida ne dan gidan da hayaniya ba zan iya bacci ba", ta k'arashe maganan tana share hawayen fuskanta, ba dan Aunty ta yadda da maganan ta ba tace mata "toh yanxu idan na koma da ke mey zaki cewa Ammah ya maida ki gida, ki bari tunda bikin ma ya k'are gobe sai ki dawo gida kinji" ta faďa mata tare da ďan dafa kanta, kai kawai ta gyaďa a sanyaye , "keh da wa kika zo ne ma", ajiyar zuciya tayi tace tare da Yaa Abu mukazo", Aunty batace komai ba tace mata "toh yanxu ki koma ciki, su Ammah ma yanxu zasu tafi, kiyi maza ku tafi, gobe sai Ki dawo gida ki huta abun ki", toh kawai tace, Baa Liman ne yazo inda motar ke pake yace "Hajiya zamu jira wani ne", tace mishi "a ah Baa Liman, yanxu zamu tafi", sai da safe Batuul tayiwa Aunty a sanyaye ta yi hanyan hall ďin, sai da ta jira taga Batuul ta shiga snn ta shiga mota suka tafi





Ammah ta hango ita dasu Aunty Amna sai y'an tsirarun k'awayen amarya da y'an uwanta, inda Ammah take ta k'arasa , Ammah na ganinta ta mik'e tace "Batuul ina kikaje, inace kun tafi da Farida , yanxu na k'irata a waya tace baku tafi tare ba, daga ina kike", cewa tayi "Ammah hayaniya ne yayi yawa a hall ďin shine na ďan fita waje", ajiyar zuciya ta sauk'e tace "toh, da har munji tsoro kowa aka tambaya sai yace bakwa tare, sae Amnah tace kila kin bi mamanku, ga Abun ma can na tsai dashi nace sai ya maidaki ko kuma in an ji kina gida su wuce, mu sai munyi ensuring everyone is safe home zamu tafi", gyaďa kai kawai tayi dan yanxu ta yadda shiga motar Abutturab ďinnan qaddarar tace, Ammah ce tayi mishi alama da yazo, k'arasowa yayi giranshi na sama da k'asa a haďe, harara yabita dashi sannan yace wa Ammah gashi nan, "ku tafi toh tunda tazo, kayi maza kaje ka sauk'e y'ar mutane ta gaji", a tak'aice yace toh ya juya, ko ba a faďa mata ba tasan binshi ya kamata tayi, a baya ta bishi shi da matar tashi dake wani yatsine yatsine har wajen mota, shi ya buďewa Ajiddeh front seat ta zauna, shi kuma ya zagaya ya shiga side ďinshi, itako back seat ta zauna kanta a kasa, a nutse yake tuk'in hannunshi cikin na Ajiddeh yana yi mata magana k'asa k'asa tana ta shan k'anshi, da suka isa gidansu Ajiddeh ma fita sukayi suka barta a motan sai da sukayi wajen minti talatin a waje tukunna ya rungumeta kmr baxa su rabu ba daga k'arshe ya shigo dan da alama aikin lallashi yake ta yi, yana shiga motan sae da ya bari ya fita daga compound din gidan snn ya juya yana kallon Batuul fuskarsa daure yace "waye driver ki, c'mon kin dawo gaba ko sae na sauke ki a titi", ita dai bata ce mishi komai ba ta buďe k'ofa ta dawo gaba, sai da ya kama hanya ssae tukunna ya fara magana ba tare da ya kalleta ba "keh wato ni na zama driver ďinki ynxu ko, duk yadda za ayi sai kin samu yadda kika yi Ammah ta haďani dake koh, kin wuce kin tafi yawon ki kin ďagawa mutane hankali ana ta nemanki, inama kika fita kika tafi in d first place?" kinsa matan aure zama a waje duk da sunan jiranki, tunda ya fara magana bata ko kalli inda yake ba, shiru tayi bata kulashi ba, tsawa ya daka mata tare da cewa "ba tambayanki nayi ba, ina kikaje?" hawayen da tayi ta mayarwa ne ya zubo mata, kuka ta saka da karfi kamar wacce aka daka ta kifa kanta akan gwiwanta tana rerawa, sosai take kukan kamar ran ta zai fita, juyawa yyi yana kallonta, a fusace yace "wato ba a isa yi miki faďa ba shine zaki fashe min da kuka kmr wata yarinya, shut that mouth ynxu", kamar k'ara mata kukan akeyi taci gaba da kukanta kamar bata ji shi ba har da shessheka, tsaida motar yayi xuciyarsa na tafasa yace "fita min a motata", ko kallonsa bata yi ba tana ta aikin kukanta, da tsawa ya sake ce mata "i said get out,", ďago kanta tayi tareda share hawayenta ta dubi cikin idonshi tace "babu inda zanje, ka mayar dani wajen Ammah kace mata baza ka kaini ba mana", mamaki ne ya sashi sakin baki yana kallonta, dama tana magana haka, ranshi ne yaji b'aci, buďe k'ofa yayi ya fita ya zagaya ta inda kofarta take, buďe nata k'ofan yayi ya ce mata "out", tana zaune kamar bata jin abinda yake faďa, fixgota yayi ya fitar da ita daga motan da karfi ya juya ya koma nashi side ďin ya tada motan ya tafi, tana ganin tafiyarshi ta nemi waje ta zauna tana kuka ssae, iska ne ya fara kaďawa mai k'arfi tare sa walk'iya, ďankwalin dake kanta ta warware ta yafa a kanta tana hawaye, tana nn zaune aka fara yayyafi, duk'unk'une wa tayi waje daya dan sanyi yayi mata yawa ga tsoro don bbu alamar mutum wajen, ruwane sosai ya sauk'o kamar da bakin k'warya amma ko niyyan tashi ba tayi ba sae hade kanta da tayi da gwiwa tana kuka a hnkli, ruwan da ya ganine ya sashi parkin, snn juyar da kan motan a hnkli, cikin 'yan mintuna dawo wajen da take sbda gudun da yyi, fitowa yayi daga cikin motar ya isa inda take har lkcn yace "tashi mu tafi", kamr bataji shi ba ta ďauke kanta, sai rawar sanyi take, da taji zai isheta ne ta tashi tayi hanya daban da sauri jin ya biyota yasa ta saka gudu, binta yayi da hanxari ya fixgota, jiri ne taji yana ďibanta dan sanyin ya mata yawa, tangaďi ta fara zata faďi yayi sauri ya tarota jikinshi, mutsu mutsu ta shiga yi xata kwace kanta bugun xuciyanta ya tsananta, kin saketa yyi ruwa na dukansu, cak ya ďauketa daga karshe ya kaita cikin motan yayi mata baya da seat ďin ya kwantar da ita fuskarsa dab da nata har tana iya jiyo numfashinsa cikin kaushin murya yace " Idan kika kuskura kika fito xaki sha mamaki na" kasa motsi tayi daga gurin xuciyarta kmr xae fito don tsoro kamshin turarensa duk yabi ya isheta ga fuskarsa dake dab da nata har lkcn, da kyar take jan numfashi tsabar wani rawan sanyi da take, yafi minti uku yaki daga kallonta duk da ynda yaga jikinta ke rawa ssae, daga karshe ya mike ya rufe motar.






Xagawa yyi maxauninsa ya Shiga, maimakon ya ja motar sae ya kasa, ya fi minti uku daga karshe ya juya yana kallonta yace "Batuul!",ya ji shiru bbu amsa, sau uku yana k'iranta yaga bata ko motsi, kafaďanta ya kama tare da jijjigata yana k'iran sunanta amma ko motsi bata yi, janyota yayi jikinshi da sauri ya kwantar tare da bubbuga mata baya, ko ba a gaya masa ba yasan she is unconscious ne, hnklinsa ya tashi ba kadan ba, all possible ways da yasan xae yi ta farfaďo yyi amma shiru, kawai yayi deciding da ya bata mouth to mouth respiratory aid, ďan kwalin da ta yafa a kanta ya cire, gashinta da ya kwanta lufluf yabi da ido, sunkuyo da kanshi yayi dai dai fuskanta tare da rintse ido yana k'ok'onton yayi ne ko kar yayi, but dats the only alternative, sai da ya kawo bakinshi daidai da nata idonsa na kan lips dinta hannunsa daya na kanta ta jawo wani dogon numfashi amma bata buďe ido ba, wani irin ajiyar zuciya ya sauk'e tare da komawa baya seat ďinshi ya zauna yana kallonta, sai da yaga ta fara motsa hannun tukunna ya lullubeta da dankwalin kanta bayan ya kashe Acn motar ya tayar ya jasu sukayi gida, suna isa gida yyi pakin ya fito ya ďauko ta a hannunshi kamar wata y'ar baby yana kallon fuskarta, mutanen gidan da sukazo biki waďanda basuyi bacci ba duk suka bishi da ido, bai bi ta kallon da suke mishi ba ya haura sama ya shiga da ita ďakin Ammah tare da sallama, Ammah na ganinshi ďauke da Batuul ta mik'e tsaye a rude tace "Aliyu mey hka, mey ya sami y'ar mutane ni Bilkisu, daga ina ku ke", bai ce komai ba sai da yaje ya shimfiďar da ita kan gado , ya kashe AC ďakin tukunna ya juyo wajen Ammah da damuwa a fuskarsa.
💝BATUUL💖💝

33

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Da sallama ta shiga ďakin taga bata nan amma akwatinta da jakanta na daga gefe, sai glasses ďinta dake ajiye kan mirror, zama tayi tana jiranta dan da alama toilet ta shiga, tana nan zaune ta fito tana goge ruwa a hannnunta da ďan k'aramin napkin, da gudu Batuul ta tashi taje ta rungumeta tana faďin, " *Yayya nyi kammo isi min gullèma, biya ngaima amme nya sorin*, Yayya ke kullum baki cewa zaki zo sai dai kawai a ganki kin faďo", Sai da janyeta daga jikinta tukunna tace " *dai fandoro letè chingya nyairo gullukin, kèrma dè fato tadanyi yero kadiko, fanuwa na*?, ku bari ranan da na tashi zuwa gidajenku sai in sanar daku amma yanxu gidan ďana nazo, babu izinin wanda zan jira kuna jina", dariya Batuul tasa tace "duk mey yayi zafi haka Yayya, namun ma in kin tashi zaki iya zuwa kai tsaye ba sai ki nemi izinin kowa ba", ta karashe maganan tana kallon Yayya da ta k'ura mata ido tana ta kallon ta, kai ta ďaga tareda da ďage girarta ďaya tace " *Yaaa kèrma dè ai yo do, wa shimmin rumin dè nyimai nya nèm shawan kongèna ro nonema*, Yanxu kuma menene kika zubamin ido kina kallona haka, kinsan ai ko a yarintarki baki kaini kyau ba, sai ma dai rashin tsayi da kikasa na biyoki da" tsaki taja tace " *ndu nyiro nyiro nyi shawasè gullono, u awo wallimin dè dai rukkin, rui futu ngam nèma dè, biya dai montindo jarawai adè na kwalluwa*, waye yace miki kina da kyan da har zan tsaya kallo, ja'ira ni wannan rama da kuma bak'in da kikeyi nake gani, wannan jaraba ta makaranta da bata k'arewa, gashi duk ya lalataki", rai Batuul ta haďe tace "kin fara ko, ni kinga ma ďakina zan koma", sanin da Batuul tayi sarai akan maganar da zasu shiga nan ne ya sata cewa zata bar mata wajen, cikin ďaga murya tace " *lenèmiya wande waltim yisimi, fuskam yaame yedai a, aima ba kènza gèi ya, nyai sammaso bannazèna, afuno gèi awo gade mananuwin a ba, kamme nyairo kanuri manaja shiro afunon mananuwin, Baan do dè gèrenge yishin ai, shima nyairo sèkèlima fayin ai*, in kin tafi karki dawo, da fuskanki kamar na uwarki, babu komai sai hanci da gashi da kika kwaso, duk ta fama b'ataku, inba Hausa ba babu abunda kuka iya, ana yi muku kanuri kuna maidawa mutumin magana da Hausa, ai ina nan ina jiran dawowan Baban naku, in shi ya koya muku duk zanji", ta gama faďa harda kalmashe k'afa, dariya abun ya bawa Batuul ta girgiza kai ta fita, D'akinta ta koma taje tayi wanka ta saka gown mara nauyi ta fito kitchen taya su Aunty aiki, k'arfe biyar da rabi suka gama aikin da zasuyi suka jera a dinning, K'arfe shida su Ahmad suka dawo daga Islamiyya, lokacin Baba ma ya dawo a tare suka shigo, sai da kowa yayi sallah tukunna suka sauk'o cin abinci, Aunty ce tacewa Batuul taje ta sauk'o da Yayya suyi dinner, ba b'ata lokaci ta haura sama suka sauk'o a tare, cup ďin ruwan da Baba ya ďauka zaisha ya maida ganin Yayya na sauk'owa daga bene, da mamakin ganinta ya mik'e ya isa inda take ya rik'o hannunta suka iso dinning ďin, sai da ta zauna tukunna ya fara gaidata, yace "Yaa baki cemin kina zuwa ba, kuma ko jiya saida mukayi waya dake fa", yaran ta duba sannan tace "toh garin naku wani nisane dashi, ko sae na nemi ixinin ka kafin in xo gidan ka," da sauri yace "A'a wllh ba hka ba yayya nayi mamaki ne kawae" ta dan kyabe baki tace 'a jiyan bayan mun gama magana da ka sanar dani abinda ke faruwa naga gara kawai inzo ayi ta ta kare, nasa Hamza yayi min booking jirgi na taho yau kawae", duk abin nan Aunty bata ďago ta kallesu ba sai da taji Yayya na cewa Baba ya sanar da ita abinda ake ciki tukunna ta ďago ta kalli Baba, cigaba da serving abincin tayi ganin yaqi kallo direction ďinta jikinta a sanyaye.

K'iran Yaa Mera ne ya shigo wayan Ammah, farida dake xaune gefenta ta dauki wayar ta mika mata, Ammah ta daga tare da sallama, gaisawa suka yi snn Yaa Mera tace, "ashe Babana ya shigo gari, ďazun nan kawai na ganshi ya shigo wllh", Ammah tace "ehh ya kai sati yanxu ashe bae je gaida ki ba" Yaa Mera tace "Wllh kuwa sae daxu ya shigo min" Ammah tace "Ikon Allah, amma bae kyauta ba, nima dae ina nn shigowa Yaa akwae wata magana da xamu tattauna, ko xuwa gobe da safe in'sha Allah xan shigo" Yaa Mera tace "Toh sae kin xo" da hka suka yi sallama Ammah ta ajiye wayar tana kallon farida, hawaye taga idonta tana kkrin gogewa kadda Ammahn ta gani, da mamaki Ammah tace "Ya aka yi farida? Ya haka?" Shiru farida tayi tana share idonta, ganin ynda Ammah ta kafe ta da ido yasa a hnkli tace "Ammah why Batuul?" Ammah tace "Ban gane ba" wasu hawayen suka kuma xubo mata tana girgixa kai tace "Ammah Ya Abuu fa ba shiri suke da Batuul ba, ga kuma matarsa masifaffiya muguwa, Batuul baxa ta iya masu ba cutar ta kawae xa su yi tayi gashi ba kowa gare ta can ba, don Allah ku canxa shawara ko cikin family can Maiduguri ki samu dai dai Ajiddehn a aura masa" tsaki Ammah tayi tare da maka mata harara tace "Toh naki yin hkan, da Batuul kadae xuciyata ta Aminta a hada Aliyu, uwar me Jiddahn xata yi mata wanda Allah bae mata ba, shi kuma Abuturrab din idan aka aura masa ita yyi gunduwa gunduwa da ita ya maido mana," mikewa farida tayi har lkcn tana hawaye ta fita daga dakin. Xaune ta ga Abuturrab dakinta ya rike kai da dukkan alama ita yake jira, yana ganinta kuwa ya mike da sauri ya karasa ya kamo hannunta suka xauna gefen gado yace "In tambaye ki farida, wae wnn kawar taki or wat ever ita tace tana son aurena?" Shi kansa jin tambayar yyi wani banbarakwae a baki don yasan Batuul baxa ta taba cewa tana sonsa ba, he is just confuse, farida ta girgixa kai tace "I don't think Batuul tasan da xancen ma, don daxu ta kirani tana ban hkurin xuwan da bata yi yau ba," ya fuzar da iska yace "Do me a favour little sis, don Allah ki xiga ta a kan kar ta amince nasan dae in har tace bata so baxa a mata dole ba" farida tace "Shknn I will try my best, but ni baxan mata magana kai tsaye ba sae in ita ta kawo xancen don ga dukkan alama bata san abinda ke faruwa ba ma" mikewa yyi rai ba ddi ya fice daga dakin.

Batuul na xaune dakin Anty duk hankalinta ya tashi ganin ynda uwar tata ke hawaye gashi ta ki gaya mata abinda ya faru, ae bata san lkcn da ita ma ta saka kukan ba tana durkushe kusa da Anty, da kyar Anty tayi controlling kanta ta shiga lallashinta sae dae ta k'asa gaya mata dalilin kukan nata don bata san ynda 'yar tata xata dauki xancen aurenta da Abuturrab ba, bude kofar dakin aka yi Ahmad ya shigo da sallama sae dae ganin ynda Batuul ke kuka hankalinsa ya tashi ssae don xuwa lkcn Anty ta daina nata kukan, hankali tashe ya shiga tambayar Anty abinda ya faru, Anty tace "kanta ke ciwo wae shine take kuka, ya aka yi Ahmad?" Ahmad ya durkusa kusa da Batuul yana mata sannu, sae da Anty ta kuma tambayarsa ya aka yi snn yace "Yayya ce tace in kira ta, kuma gashi kanta na ciwo bari kawae inje ince she's not okay" har ya mike Anty ta dakatar da shi tace "A'a bari xata je, ae ta sha magani" tayi hkn ne gudun wani maganan don har ynzu xuciyarta bae yi sanyin abinda yayya tayi mata daxu ba daga tace ita Batuul baxa ta auri mai mata ba in ma aurar da ita ake son yi gwara ta fito da saurayinta kawae, nn fa Yayya ta dinga xaxxaga mata ta inda take shiga ba nn take fita ba, mikewa Anty tayi daga karshe ta bar mata falon, shine tun lkcn take kuka a daki har Batuul ta shigo ta sameta. Kallon Batuul tayi tace "Tashi ki je Batuul" ba musu Batuul ta mike tana share hawayenta ta fita. Yayya na kishingide tana cin Apple, Baba na xaune daga gefenta ya tankwashe kafa suna magana da kanuri, k'arasowa cikin dakin Batuul tayi sae dae bata da walwala don tasan Yayya ce ta bata ma Anty rae ko bata fada mata ba, Xama tayi dan nesa da su tace "Ga ni Yayya"

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login