Showing 90001 words to 93000 words out of 215266 words
hnkli ta mike tana rufe bakinta da mayafi kar ta saki ihun da taji na shirin fitowa, sauke idonsa yyi daga kallonta ta kama hannunta ya shiga tafiya tana binsa har suka isa inda jirgin British Airline (B.A) yake tsaye, yana rike da hannunta suka shiga jirgin, a first class ya samar masu empty seats, a hnkli ta xauna ta jinginar da kanta jikin kujerar tare da lumshe ido, ya saka trolleyn hannunsa daga sama inda ake ajiye luggages, snn shi ma ya xauna, announcement aka shiga yi na cewa "Passengers on board shud pls fasten their seat belts, British Airline flight is about taking off" Abuturrab yyi fasten din seat belt dinsa yana kallonta, gani yyi ko motsi bata yi ba, ranan da suka yi boarding same plane daga Maiduguri xuwa Abuja ya tuna, yyi shiru yana kallonta, a hnkli ya kai hannunsa ya mata fasten din belt din da kansa, ta bude rinannun idonta tana kallonsa, lkci daya ya hade rai, da sauri ta sunkuyar da kanta, wayarsa ya fiddo ya maida shi flight mode ya jona earpiece ya sa a kunne ya lumshe ido, jirginsu na tashi ta fashe da wani kukan tausayin rayuwarta, bude ido yyi yana kallonta sae dae bae ce komae ba, tayi mai isarta bayan wani lkci tayi shiru ta kwantar da kai jikin kujeranta lkci daya bacci ya dauketa, sae a snn ya cire earpiece din kunnensa ya rike kansa dake sara masa xuciyarsa a dagule, from Where is he going to start this long explanation to his Ajiddeh, just ta ina xae fara ce mata iyayensa ne suka makala masa Batuul, ya xata dauki xancen, will shi even believe him, tunanin hkn ya sa ciwon kansa ya tsananta, jinginar da Batuul tayi jikinsa tana bacci ya dawo da shi duniyar tunanin da ya tafi, juyawa yyi yana kallonta ya ga bacci ssae take, ya fuzar da iska tare da lumshe ido ya jawota jikinsa don gyara mata kwanciya, muryar wata hostess din jirgin ya sa shi bude idonsa, tana tsaye dai dai kujeran da suke plate holder din seats dinsu ta jawo ta dora ruwa a kai a karamin disposable cup, murmushi dauke fuskarta tace "Sir what would yhu like to have?" Yace "Just coffee" kallon Batuul tayi xata yi magana yace "She's OK" juyawa tayi ba a dau lkci ba ta dawo da cup din coffee ya karba yace "Thank you" d'an bow din masa tayi tana murmushi tace "Yhu are welcome Sir" daga hka ta juya ta bar wajen. Karfe sha biyu saura na dare Batuul ta bude idonta ganinta jikinsa yasa ta kallesa, idonsa lumshe yake alamar ya fara bacci, a hnkli ta xame jikinta ta xauna da kyau, ta shiga rera kuka tunawa da tayi shknn fa ta rabu da Anty, bude ido yyi yana kallonta, ya gyara xamansa a fusace yace "God! What again? Ke wae baki gajiya da kuka ne, am tired of this pls, aiki kawae su Ammah suka hada ni da I knw" jin ta kara sautin kukan yasa ba tare da yyi wani tunani ba ya jawo ta jikinsa murya can kasa yace "are yhu hungry" kin cewa komae tayi, ya watsa mata wani kallo yace "Kina jina dae koh?" Girgixa masa kai tayi, ya hade rai yace "Gud! Go back to sleep ynxun nn" rufe idonta tayi, tayi lamo jikinsa sae dae yana jin ynda xuciyarta ke bugawa. Har asuba daga ita har shi basu rintsa ba, da ta bude ido xae tambayeta ko tana jin yunwa ta girgixa kai ta kuma rufe idon, Karfe bakwae na safiyar washegari jirgin British Airline ya sauka airport a UK, nn fa Abuturrab ya ji duniyar gaba daya tayi masa xafi, da ya tuna Ajiddeh sae gabansa ya fadi ba kadan ba, da kyar ya mike yana kallon Batuul da idanuwanta suka rine ssae, hade rae yyi lkci daya ta mike kanta a kasa, ya fiddo trolley dinsa ya shiga tafiya, bin bayansa tayi hawaye cike idonta har suka sauko daga jirgin, duk da ta sha xuwa kasashen turawa da Baba har ma da Anty Hafsat yau komawa tayi kmr bakauyiya a haraban airport din, don sae shishshige masa take, ba komae kuma ya janyo hkn ba sae don duk a tsorace take, ba kuma wae turawan suka bata tsoro ba sae don tunawa da tayi da Ajiddeh
[8/22, 14:41] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝
43
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Amma na ganin tafiyarsu ta koma cikin gida itama tana jimamin rashin Batuul da zatayi, ďakin Abui ta wuce ta sameshi zaune yana kallo da glass idonshi, daga gefenshi ta zauna tace "Barka da zama Abui", yace "Yawwa Ammah, naga har kin fara missing yaran naki", murmushi tayi mishi tace "Ai ni tausayin yarinyar nan ke cikani, sosai nake tausayinta danma dai tana da nutsuwa", juyawa tayi ta kalli Abui with full attention tace "Abui amma hankalina gaba ďaya yaqi kwanciya, matar Abu nake jiyewa Batuul dashi kanshi Abun, ko wancan karan ni nasan Abu ba yin kanshi bane zaman da yayi ba tareda dawowa gida ba har na shekara ďaya", with full concentration Abui yake kallonta har saida tayi shiru yace "Ehhh shiyasa this time da mukaje Maiduguri kamin a ďaura aurenshi sosai nasa aka mishi addu'a, sauk'an Alqur'ani kuma kullum sai anyi har yau ďinnan Allah ya rabasu da sharrin masharranta", wani ajiyar zuciya Ammah ta sauk'e tace "Alhamdulillah", ta gyara zamanta tana fuskanta Abui tace "Nima tun lokacin da Ashiekh yace a dage da addu'a ban daina ba, yanxu naga komai ya fara daidaita, dan banga alamun abinda akayi mishin har yanxu yana jikinshi ba, sai dai mu sake dagewa Allah ya sake rufa asiri, wannan karan har Batuul ďin sai da na sa ana yiwa sauk'an Qur'ani da addu'a, daga baya ma zan sake tura mata maganin kariya dan yanxu lokaci ya k'ure shiyasa ban basu ba" Abui yace "Allah ya sake karewa, tare suka amsa da "Amin", mik'ewa tayi tana kallon Abui tace "Abui abincin fa baka ci ba gashi har takwas ya wuce", murmushi ďauke fuskanshi yayi mata alama da tazo ta zauna gefenshi, ba musu ta dawo ta zauna gefenshi tana kallonshi yace "naga kina ta hidiman yaranki bakizo bani abinci ba shiyasa nima banci ba", murmushi tayi dan tasan tsokanarta yake ta ďan kalleshi tace "Toh su ba yara bane, kai ai kullum inayi maka kuma daga yau su tafiya zasuyi", k'ok'arin tashi take daga wajen tana cewa "Abui bari in kawo maka tea toh tunda baza kaci abincin ba", jawota yayi jikinshi yace "No am okay, kiyi zamanki nima bana jin yunwa, i ate late in d evening shiyasa banci abincin ba, kuma tea ďinma i dont feel like taking it", batace komai ba ta sake shigewa jikinshi daga nan sukaci gaba da hiransu,
Har suka fito daga terminal ďin bata dena kuka ba, shidai bai ce mata komai ba dan kukanta ya ishesa, tafiya yake tana biye dashi sai shishige mishi take har lkcn abun har yaso bashi dariya, Taxi ya tarar bayan sun fito yace mishi "GEORGE'S street", driver da kanshi ya fito zai buďe musu k'ofa yace "No its okay you can sit back", gidan baya ya buďe mata ta shiga sannan ya zagaya ya buďe ya shiga shima, babu abinda zuciyan Batuul yake sai faďuwa, hawayen da take ta k'ok'arin mayarwa yaqi tsayawa sai ma daďa zubowa yake, sau ďaya ya kalleta ya ďauke kanshi, har sukayi nisa bata dena kukan ba, ranshi ya gama b'aci sosai, juyowa yayi yana kallon yadda take ta sheshek'a kuka, hannu yasa ya kama kafaďunta yace "Behave! Kinaji na ko, tun farko i gave you option, da kin buďi baki kince bakyaso am sure babu mai miki dole, but kikayi kunnen k'ashi shine yanxu zaki dameni da kuka", jajayen idanunta da suka rine ta ďago ta kalleshi taga shima idonshi akanta yake, hannunshi dake kafaďunta ta ture taja da baya tana goge hawayen fuskarta, kallonta ya tsaya yi da mamaki daga baya yayi k'wafa ya juya jin wayarshi na k'ara, iska ya ďan furzar daga bakinshi ganin mai k'iranshi, recieving yayi tare da sawa a kunnenshi a hnkli yace "Babe am back", wani irin k'ara tasa da har ya sashi cirewa daga kunnenshi tukunna ya mayar yace "Hae chill ba sai kinzo ba ina hanyan dawowa ko David ban faďawa muna hanya ba", da mamaki a ranta tace suna hanya kuma, shi da waye? oho ko ma dai waye shi ya sani, abunda ta shirya mishin in yaso duk munafikin da ya biyoshi shi ya sani ya faďa musu, da sauri ta kawar da tunanin tace "Baby ai da ka faďamin da ko breakfast nayi maka, but ban tashi ba ina bacci har yanxu, babe kazo min da Domino's pepperoni Pizza da Cold stone Ice cream tunda akwai a hanya dashi nakeson yin breakfast", kai ya girgiza yana mamakin halin Ajiddeh, ko yaushe ma ta iya girkin da har zata ce wai da ya faďa mata tayi mishi breakfast, ya sauke ajiyar xuciya yace "Fine naji, mun kusa isowa gida you should get up from your slumber and get ready", yana iya jiyo murnar da takeyi tace "Right away baby", da haka ya katse k'iran, suna gama wayan ta dirk'o daga kan gadon, straight away garden ta wuce da ďan bingel ďin rigar bacci dake jikinta taje duba kuttun data ajiye, ganin yana nan very safe ta dawo bakin palo dan tun ranan da ta dawo zuba abin ba ayi shara a gidan ba sai bayan ta aiwatar da abinda tayi niyya, sai da tabbata komai daidai ta koma cikin gida tayi wanka ta sako wata y'ar crop top da bum short, sosai ta gyara dogon gashinta ta baďe jikinta da turare ta koma ta kwanta, Batuul kam banda bugu babu abinda zuciyarta keyi, haďuwarta da Ajiddeh ba wani mai yawa bane tasan babu abin arzikin da ya taba haďata da ita in banda hararta da takeyi kullum in sun hadu, maganganun da Ammah tayi mata ne suka dinga dawo mata kai, Ammah tace mata kar ta yadda su rainata, yes hakane baza ta yadda su rainata ba, toh ita inama ruwanta da ita ne, ba sai ta kulata bane bama zata rainata, ďan tsaki taja ba tare da ta san tayi hkn ba, juyowa yayi yana kallonta jin tsakin da tayi, ganin za a wuce Domino's yasa shi cewa driver ya tsaya, parking driver yayi ya fita ya shiga Domino's bayan 10 mins ya fito rik'e da kwalaye a hannunshi na pizza da ledan Ice cream, kanta na daga jikin window tana ta kalle kallenta ta ďago tana kallonshi, wani irin relief yaji ganin idonta ba hawaye, shiga yayi ya zauna driver ya tada motar suka tafi, tafiyar 8mins suka isa anguwansu, gini ne uniformly masu kyau duk iri ďaya da red bricks, bambancin wani da wani kawai motocin dake pake ko kuma yadda flowers ďin ke jere, bin ko ina da kallo ta rik'ayi zuciyanta na ci gaba da bugawa, har compound ďin driver yayi parking, tsayawa yayi yana kallonta bayan ya fito daga motan ganin taqi fitowa yace "you can come out, ba motata bace", ďauke kanta tayi a sanyaye ta fito, ta bi bayan shi, murďa k'ofan palon yayi ya shiga da sallama yana kalle kalle, kan vanity table ďin palon ya ajiye boxes ďin hannunshi, Batuul ta kasa Karasowa cikin falon, Ajiddeh ce ta sauk'o a guje daga kan bene tazo rungume shi da murna tare da lumshe ido, shima ya rungume ta ssae, sam bata lura da Batuul dake bakin kofa ba, cikin muryar shagwaba tace "Babe shine ka daďe a Nigeria ina ta jiranka, ka kawomin pizzan?", idonta ne ya faďa kan vanity table ďin ta juya zata ďauko kwalin cike da murna, cak ta tsaya ganin Batuul a bakin kofa, lkci daya komai ya tsaya mata, zuciyanta ne ya shiga bugawa da sauri da sauri tana kallon Batuul da itama ke kallonta duk a mugun tsorace take hkn bae nuna a fuskarta ba, dawowa tayi da baya tana kallon Abu, idonta ya cicciko ruwa tana kallon idonshi ta fara mishi magana da kyar, "Aliyu who is she?", this d time he dreaded dama, runtse ido yyi ya kamo hannunta zai jawota jikinshi ganin yadda jikinta ke b'ari, ta wani warce hannunta da karfi daga rik'on da yayi mata cikin rawan murya tace "wannan wane irin jaraba ne Aliyu, watan ka ďaya can kana tare dasu shine zaka dawo ma baza a bari ka dawo kai kaďai ba sai an haďaka da wata, watanma a rasa da wacce za a haďaka sai wannan mai kama da y'an ethopian ragowar yunwa", sosai ran Batuul ya sosu jin abinda Ajiddeh ke kiranta da, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta sunkuyar da kanta, shima Abu ranshi ya b'aci jin maganganunta amma baison nunawa gaban Batuul dan ya gama cika mata bakin yana son matarsa, kuma bai son ta rainata, iska ya fitar daga bakinshi ya birkita lallausan gashin kansa yace "calm down babe, kinsan she is my cousin, and.. and... Babe karatu fa tazo yi nothin else, babanta ne baison tayi zaman hostel shiyasa yakeso ta zauna gun mu", da mamaki Batuul ta ďago kanta jin abinda yace, shi kansa bai san lkcn da yyi formulatin karyan ba lkci daya kmr da can ya tsara, ajiyar zuciya ta sauk'e ba tare da ta shirya ba, sae dae duk da hka xuciyarta bae bar tafasa ba don ita har ga Allah ta tsani Batuul with passion, ita kanta bata san dalilin k'in ta da take ba, janyewa tayi daga jikinshi tana k'arewa Batuul kallo tana yamutse fuska ganin yadda jikin Batuul ke kyalli saboda gyaran da yasha, tasan hasken Batuul bai kai haka kyau ba, gashi sai wani kyalli takeyi kamar amarya, nn hankalinta ya kuma tashi tace "toh in suna son karatunta waje sai an kawota gidana ne xata yi, nasan duk salon sa ido ne aka haďoka da ita babu wani karatu, sai kace wanda nake yankan namanshi inaci baza a bar mutum ya huta ba, toh wlhy sai dai ko ni ko ita a gidannan dan bazan yadda da harkar munafikai ba", ta fadi hkn tana masa wani matsiyacin kallo tana girgixa kafa, da mamaki ya tsaya yana kallonta, wai shi Ajiddeh ke yiwa shirmen nan a gaban yarinya don ta rainasa, kallon Batuul yayi da itama ta tsaya jin abunda Ajiddeh ke cewa, karasawa yyi fuskarsa daure ya kama hannunta yayi hanyan staircase da ita, mutuwan tsaye Ajiddeh tayi ganin abinda yyi, a tsorace take kallon Abutturab ko shi ďinne dan tasan ko da safe sai da ta sake duba magungunan da tayi mishi taga kuma komai daidai yake, toh ya akayi ya iya tsallake maganarta har yaja hannun wannan shegiyar da yake ikirarin k'anwarsa ce su bar ta tsaye, wasu hawayene masu ďumi shiga bin kuncinta ta bisu da kallo, Batuul kam ta kasa cewa komai sai binshi da takeyi a baya gabanta na faduwa, wani ďaki taga ya buďe suka shiga, kallonta yayi yace "Sit right here" ya juya yaja k'ofar ya fita, juyawa tayi tana k'arewa ďakin kallo, ďan madaidaicine mai kyau komai na ciki grey and white, ďaya daga cikin sofan ďakin taje ta zauna dan ita batasan ko ďakin waye nan ya kawota ba, yana fita daga ďakin k'asa ya dawo inda Ajiddeh ke tsaye ta kasa gaskata abinda take gani da idonta, ganinshi yana nufota ya sa zuciyarta yin sanyi dan tasan bokan nan yayi assuring ďinta komai zaiyi daidai, sae dae hkn bae hanata tsuke fuska tana hawaye ba, magana ya fara yi mata yace "Ajiddeh mey ke damunki wai kike abinda kika gama yi yanxu kamar wata yarinya", murmushin takaici ta saki tasan dole ma ai asirin nan ya kamashi, idonta cike da bala'i tace "dole mana kace mey ke damuna, kaje an gama munafirce min kai shine zakazo kana tambayata mey ke damuna", yasan ya fara losing control dan ranshi ya fara b'aci amma bayason biye mata suyi faďa after a long time, matsowa yayi gabanta yana kallon idonta yace "control and hear me out ki dena wannan haukan da kikeyi, its not what you are thinking uhhn?", harzuk'a ta sakeyi dan yanxu ta fara tsorata maganin nan bai kamashi ba knn, rai b'ace tace "Lallai Aliyu, hauka ko" tayi ďan dariya mai sauti tace "ai kuwa yanxu zakaga hauka in baka fita da tsinanniyan nn ba daga gidana wllh", ranshi yaji yayi mugun b'aci cikin tsawa yace mata "Keeeh", idonta na zubar da hawaye tana kallonshi tace "meye zakayi min kuma bayan wanda ka riga da kayi, ni nasan munafikan dake gidane suka haďoka da wannan mai kama da karuw.....", bata samu k'arasa maganan dake bakinta ba ya daka mata wani irin tsawa tareda da damk'ota ya shaketa yana huci, turata yyi lkci daya idonsa ya kada, Batuul dake ďaki tana ta kalle kallenta ta zauna a takure sosai ta tsorata jin k'aran a falo, jiki na b'ari ta buďe k'ofa don ganin ihun mey taji, sauk'owa tayi tana kallonsu, bnda rusa kuka bbu abinda Ajiddeh ke yi, juyawa yyi yana kallon Batuul a tsawace yace "C'mon get back before i get there ynxu", sosai Batuul ta tsorata ganin yanayinshi, sae dae bata nuna ba ta juya a hnkli ta koma sama tana share hawayen dake son xubowa daga idonta ta koma ďakin ta rufoshi.
[8/22, 14:44] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝
44
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Juyawa Abuturrab yyi ya haura sama a fusace ya shige bedroom dinsa, tsaki yyi ganin hw untidy the room is, wae kuma mace ce ke rayuwa ciki, toilet ya nufa ya wanke baki ya dauro alwala ya fito ya tada sllh, ya jima xaune kan darduma yana mamakin hali na Ajiddeh, hw wil she b insulting his family into his face kuma ya dinga tolerating hka, tsaki yyi a xuciyarsa yace na san maganin ki, mikewa yyi ya