Showing 54001 words to 57000 words out of 215266 words
kwantar da ita asibiti", Ahmad da ranshi ya fara b'aci jin tana aibata Aunty yace "Keh Yayya nifa bake na tambaya ba", "ehh ai nima ďin nasan ba ni ka tambaya ba, amsa ce na baka don nasan ba baka xa suyi ba", Aunty dae ko kallon inda suke bata yi ba dan ita tunaninta daban takeyi, Ahmad yyi tsaki yace "kinga zo mu koma, dama Baba cewa yayi in kawoki ki ganta mu koma, toh tunda ba ma dubatan zakiyi ba kizo mu wuce, dan ni in na tafi sai dai ki nemi mai dawo dake", masifa ta shiga yi ganin yayi hanyan k'ofa yana cewa Aunty zai tafi, Allah ya bawa Batuul lafiya, binshi tayi a baya tana ta zazzaga mishi ruwan bala'i har tana cewa sai tasa an karb'e motar ya dena tuk'awa tunda wulak'anci ne abun, suna fita Aunty ta tashi ta gyara windown da Yayya ta buďe, wayan Batuul da ta taho mata dashi ďazu ne ya fara ringing, mik'ewa tayi ta ďauki wayan, ganin mai k'iran yasa ta maida ta ajiye.
Sai dare Batuul ta tashi lokacin har an idar da sallah magrib, da taimakon Aunty taje tayi alwala tayi Sallah, Ce mata Aunty tayi bari in shiga office ďin doctor, tun ďazu yake nemana kina bacci shiyasa ban fita ba, Aunty na fita wayanta dake ajiye gefenta yayi ringing, da kamar baza ta ďaga ba ganin mai k'iran yasa ta ďauka lokacin har ya kusa katsewa, a hankali murya can k'asa tace "Hello", wani irin ajiyar zuciya ya saki jin muryanta, shima murya kaman ta mai damuwa yace "Habibty dont do this to me again kinji, i was so worried abt you, tun jiya nake k'ira you werent picking, do you know how this affected me", shiru tayi tana saurarenshi idonta ya cicciko da hawaye tana tuna abinda Yayya ta faďa mata jiya, jin tayi shiru ta kasa magana yasa yace mata "you there", kasa mishi magana tayi sai kukan da ta fashe mishi da, har cikin ranshi yake jin kukan nata, kiďimewa yayi ya shiga tambayanta "Fatima mey ke damunki, ki daina kuka and tell me whats wrong with you, you are making me distressed, kina inane i will come right away...", da k'yar ta samu ta saita kukan nata tace mishi "Na'am", cikin shesheka, with so much concern yace mata "Its okay stop crying and tell me whats wrong with you kinji", har muryanshi na rawa, murya can k'asa tace mishi "I was sick", mik'ewa yayi tsaye daga zaunen da yake yayi hanyan ďakin Mummynshi, tambayanta ya shiga yi "mey ke damunki Fatima, kuma kina inane", a hankali tace mishi " Nima ban san mey ke damuna ba, I was admitted a asibiti tun jiya", ce mata yayi "Its okay, you will get better soon kinji, i will b on my way right away, take care of yourself", har ya katse wayan sai ya tuna ashe baima tambayeta wane asibiti bane, sake kira yayi ta faďa mishi asibitin da aka kwantar da ita, da haka ya katse k'iran ya karasa ďakin Mummy, zaune ya tarar da ita akan abin Sallah, zama yayi daga bakin gadonta yana jira ta gama azkar ďinta tukunna ta juyo ta dubeshi tace "Babana dama kana gida baka fita ba, ya akayi naga duk ka zama wani iri, what is it", ce mata yayi "Mummy Batuul, i mean Fatima ba lafiya, yanxu haka tana asibiti a kwance, Mum ki shirya muje mu duba ta kinji Mum", kallonshi take yadda ya rikice yana mata magana, bata tab'a ganinshi ya damu akan wata mace kamar haka ba, kanshi ta shafa tace "jeka canja kaya ka ďauko key kazo mu tafi", da hanzari ya mik'e ya fita, girgiza kai tayi tana addu'an Allah yasa son Batuul ya zame mishi alheri ta cire Rigar sallah dake jikinta ta shirya tafiya asibitin da ďanta.
Batuul na gama waya zata ajiye taga an turo k'ofar ďakin, a zatonta Aunty ce ta shigo, Farida ta gani bakin kofar rik'e da Basket a hannunta, Murmushi ta saki tana kallonta, ba shiri murmushin dake fuskanta ya bace ganin wanda ke tsaye bayan Farida, sunkuyar da kai tayi da sauri, farida ta karaso ta xauna gefenta murmushi dauke fuskarta har lkcn tace "Waow Besty, I can see yhu are getting much beta ynxu, ga abinci na kawo maki, ur favourite!" Batuul tayi murmushi sae dae bata ce komae ba don ita ko kadan bata ji ddin dawowan Abuturrab ba, karasowa cikin ward din yyi ya ja kujera ya xauna fuskarsa a daure, farida ta sauka daga gadon ta nufi basket din abincin don dibar mata farfesun da tayi mata, Batuul ta kalleta tace "Don't wrry dear, am okay ynxu, bn dde da cin abinci ba, ltr sae in ci, hope yhu are spending d nyt here?" Farida ta wara ido tace "Y not love, ae da shirin kwana dama na xo" wani harara Abuturrab ya watsa mata yace "Ki gama abinda xa kiyi mu tafi, dnt waste my tym" Bata fuska farida tayi tace "but Ya Abuu Ammah fa ce tace in kwana wllh" mikewa yyi kmr xae maketa yace "Tafi mota ki jira ni" kuka ta saki, ganin ya yo kanta ta fice da sauri daga dakin, juyawa yyi yana kallon Batuul ya galla mata harara yace "C'mon sense din ki bae baki cewar hakurin filthy abinda kika min a jiki daxu ya kamata ki ban ba" ganin taki kallon inda yake bare ya sa ran amsa yasa ya karasa inda take yana mata wani irin kallo, bude kofar dakin aka yi Anty ta shigo, da sauri ya koma baya, Anty ta karaso cikin dakin ya juya kai a kasa ya gaisheta, amsawa tayi d'aga hka ta nufi inda wayarta yake ajiye ta dauka ta fita, Batuul ta dauki wayar ta da ya soma ring a gefenta ta dauka ganin me kiranta, "Hello love gani a hospital din ban san ward din da ku ke ba" satan kallon Abuturrab tayi ta ga idonsa kyar a kanta, ta sunkuyar da kai tare da dauke kai, a hnkli ta gaya masa ward nmbrn da take, snn ta katse wayar ta ajiye, shi kam har lkcn bae bar kallonta ba xuciyarsa na tafasa ganin ynda ta ki ko da kallon inda yake, Anty ce ta kuma dawowa dakin da mamaki take kallonsa tace "ga kujera Abuturrab, ya da tsayuwa" murmushi ya kirkira yace "Tafiya xan yi Anty" Batuul ta kalli Anty a hnkli tace "Anty Abubakar ya xo wae yana waje, na gaya masa ward nmbr" kallonta Anty tayi xata yi magana aka tura kofar dakin, kansa a k'asa ya shigo da sallama mum dinsa na biye da shi a baya, da fara'a Anty tace "A'ah sannun ku da xuwa" Kallon Abubakar kawae Abuturrab ke yi ko kiftawa bae yi, Anty ta ajiye ma mum dinsa kujera ta xauna tana kallon Batuul tace "Sannu Fateema, ashe baki ji ddi ba" Batuul da kanta ke k'asa ta dan yi murmushi cike da jin kunya tace "Ina yini Mama" Matar ta fa'da'da murmushin fuskarta tace "Lfya lau Batuul ya jikin?" A hnkli tace "Da sauki" tace "Allah ya sauwake" har k'asa Abubakar ya kai ya gaida Anty ta amsa murmushi dauke fuskarta tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh Mumy" mikewa yyi yana kallon Abuturrab dake kallonsa har lkcn ya mika masa hannu, Abuturrab ya sunkuyar da kai suka yi musabaha, snn Abubakar ya juya yana kallon Batuul sae dae taki kallon inda yake, sae a snn Abuturrab ya ga daman gaida Mahaifiyar Abubakar ta amsa da fara'a, Mikewa Mumy tayi daga karshe ta nufi gun Batuul ta ajiye mata ledan hannunta tace "Toh fateema Allah ya kara lfya kin ji" Batuul tace "Ameen ngd Mumy" Mumyn ta kalli Anty tace " Hajiya ni xan koma Allah ya sauwake" Anty tayi mata gdya ssae, Abubakar yace "Momy ki jira ni gani fitowa ynxu" dariya Mahaifiyar tasa tayi tace "Dama ae xan jira ka" d'aga hka Anty ta rakata suka fita ward din, Batuul ta sace kallon Abuturrab ta ga kallonta yake, ga Abubakar da duk ya kagu ya fita ya basu waje da Habibtyn sa.
💖💝BATUUL💖💝
25
By Phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tsayawa yayi ya zubawa fuskanta lumshashen idonshi, babu komai fuskanta daga dogon hanci sai lashes ďinta da suka kwanto a fuskan da ďan k'aramin baki, ya kai minti biyu yana kallon fuskanta ya ma rasa me yake kallo a fuskar, daga k'arshe ya dan ja tsaki ya tada motar sukayi gida, Batuul kam tunda ta kwantar da kanta bata ďago ba, parking yayi da suka isa gida ya kashe motar, jin an tsaida motan ya sata buďe idonta a hankali ta dubi side ďin da yake, maza tayi ta ďauke idonta don kallonta yake, buďe k'ofa tayi zata fita yace mata "wa zai ďaukar miki maganin", bata kulashi ba ta dawo ta ďauki ledan magani tayi gaba abinta, ďakin Ammah ta nufa, a hankali ta tura k'ofan ďakin tasa kai, babu kowa a ďakin sai k'anshi dake tasowa ta kowane angle, shiga tayi ta zauna kan gado tare da jinginar da kanta a jikin gado ta lumshe idonta, numfashi take sauk'ewa kamar wacce tayi wani babban aikin, buďe k'ofan ďakin yayi shima ya shigo, babu kowa sai Batuul jingine a gado, k'irjinta na heaving, a zuciyanshi yace "she is lazy, kamar wacce ta ďauko gari" tabe baki yyi yaja k'ofan ya rufe, falon sama ya tsaya zai k'ira Sadiq ya tambaye shi inda Ammah take, yana ciro wayan ya hango Ammah ita da ďaya daga cikin masu aikin gidan ďauke da babban tray suna hawowa sama, sai da suka hawo tukunna ya k'arasa wajen ta yace "Ammah mun dawo", ba tare da kalleshi ba tace "mey suka duba sukace ya sameta", ta faďa tare da tura k'ofar ďakin, sam shi baya jin daďin yadda Ammah ke yi mishi akan yarinyar nn, binta yayi shima jiki a sanyaye ya shiga ďakin, trayn hannunta yarinyar ta ajiye ta juya ta fita, sai da ta fita tukunna ya zauna ďan nesa da Ammah yace "pneumonia ne sukace yana son kamata, sunce ta guji anything cold sai ta rage yawan wasa da ruwa da shan abun sanyu", katseshi tayi da "wane irin ta rage wasa da ruwa, ai dama ba yi takeyi ba, kuma da k'yar aka samu ta rabu da wannan pneumonia tun tana k'arama yake wahalar da ita, sai da aka samu yarinya ta huta zaka sa ya dawo mata, ai da baka sata shiga ruwa ba da babu abinda zai sameta", a hankali yace "Ammah nace kiyi hak'uri fa, bazai sake faruwa in sha Allah, kiyi hak'uri", tana kwance bata buďe ido ba tana jiyo duk abinda yake faďa, wani ďan k'aramin murmushi tayi dan taji daďin yadda yake yiwa Ammah, ashe akwai waďanda yake jin maganarsu, "ai dama aikin kenan , da kayi abu ka fara bani hak'uri, k'arfe nawa zakuje gaisuwan iyayen?", sakin murmushi yayi dan ya gano cewa ta hak'ura tunda ta fara wani zancen, ce mata yayi "bayan azahar zamu je, sai dare kuma aje a ďaukota", "Allah ya kaimu , Su Aunty Amna sai suje su ďaukota, ba sai kun shiga gidan naka ba ai tunda kwana huďu kawai zakuyi ku wuce, tayi zamanta kawai a nan a side ďinka, kar a bata mata gida, duk ranan da kuka tashi dawowa gidanku ya zamana sabo", yace "hakan ma yayi Ammah, inaso inci abinci" ya faďa mata kamar wani k'aramin yaro, tray ďin ta nuna mishi tace "dama Batuul na sa akawowa, amma yana da yawa zaka iya ci a ciki, Ammah ce ta mik'e ta isa inda Batuul take ta tasheta taci abinci, har kan gadon ta bita da abincin, ta ansa, kasa cin abincin tayi da hankalinta sam yaki kwanciya, shiko ko kallon inda take ma bai yi ba sai abincin shi yake ci suna ta hira da Ammah, a hankali ta ďan tsatsakuri abincin ta tace ta k'oshi, mik'ewa yayi ya yiwa Ammah sallama akan zaije ya shirya suje gidansu Ajiddeh.
Wayan hannunta ta k'urawa ido xuciyarta na bugawa da karfi ga wani mugun bacin rw da ya baibayeta, gumi yana ta tsatsafo mata, mesa takejin faďuwan gaba ne duk lokacin da taji sunan Batuul ko ta ganta, yanxu akan yarinyar nan Aliyu ya katse min waya harda yi min tsawa, danshi taji a fuskanta tana kai hannun taga hawaye a fuskanta, rai a b'ace ta mik'e ba tare da tasan mey zatayi ba, ďakin Mum ta nufa hawayen wani na bin wani, mata ne sun kai takwas a ďakin wasu kwance wasu kuma na cin abinci suna hira, ba sallama ta shiga ďakin tafaďa jikin Mum, kuka ta saka kamar wacce aka daka, a firgice Mum ta ďagota tana kallon jikinta taga ko da akwai abinda ya sameta, da taga jikinta lafiya ta tambayeta "meye ya faru haka, mey ya sameki, ko Aliyun ne wani abu ya sameshi", kasa magana tayi sai ci gaba da kukanta takeyi, Yaa zee sake gefe taja tsaki tace "waye kuwa in bashi ba, ai ďan wulakancin nan nema ko baku tambaya ba", tambayanta kowa ya shiga yi amma ta kasa basu amsa, sai da ta gaji dan kanta Mum na rik'e da ita ta ďago tace "Mum kefa kikace idan mukayi aure zai soni fiyeda koma..." bata k'arasa ba Mum ta tareta da cewa "toh meye ya faru yanxu", cikin sheshek'a tace "Mum katse min waya yayi harda min tsawa wai ya kai k'anwar shi asibiti, kuma ba k'anwarshi bace, ni bana son yarinyar nan, duk randa na ganta sai zuciyana ya rik'a faďi, har gumi nakeyi, ko a wajen dinner kuna ganin yanda ya rikice wai dan ta ji ciwo, mum na tsaneta wllh", sai da ta gama tukunna Mum ta mik'ar da ita tace mata "mey na yin kuka toh, ba wannan bak'ar yarinyar bace dai y'ar Maryam, mey zaiyi da ita yana da farar mata kamar ki, ko kuma kin tab'a ganin wanda aka yiwa kishiya duk zuri'armu, ai mun fi k'arfin kishiya, duk jarabar mutum sai dai ya rabu damu rabuwar kuma sai ya ďanďani kuďarsa amma ba dai yace zai shigo da wata matar muna ciki ba, kuma ke ďinnan da kike gani auren mutu ka raba, bare azo zancen kishiya, ki share hawayenki babu abinda zai faru dake", Yaa zee ce ta turo baki tace "Ammah nifa yaron nan bai kwanta min ba, ya rik'a wani huhhura hanci yana kallon mutane ďai ďaya, ni mugun haushinsa ma nake ji", juyowa Ajiddeh tayi cikin rashin kunya tace "ai ni dama bance mijina ya birgeki ba, kinje kin kaso aurenki kin kasa zama a ďakin miji shine zaki dameni da mijina bai birgeki ba, toh ni a haka nake sonshi kuma babu ruwanki dashi, a fusace Yaa zee ta mik'e tayo kan Ajiddeh kamar zata daketa tana faďin "da wa kike, maimaita abinda kika faďa yanxu inji in baki da hankali", Mum ce tareta da cewa "Mey kukeyi hakan wai, kuda zaku haďu ku rufawa kanku asiri kunkama kuna faďa, keh zainab babu ruwanki da mijinta, kema Ajiddeh babu ruwanki da ita" taja tsaki, Jainaba dake gefe itace ta taso ta ďago Ajiddeh tace "ke yanxu kukan na meye kikeyi haka, akan dan ya ďauki yarinyar ya kaita asibiti koko dan taji ciwo ne ya taimka mata kike kuka, share hawayenta tayi tace "Jainaba tun randa na fara ganin yarinyar kawai naji bana sonta, gashi mamarshi sai tayi ta haďashi da ita, haka ranan graduation ďinsu tace wani wai su biyu su tsaya ayi musu hoto, wlhy da na gansu tare sai da zuciyana ya kusa harbawa ga wani gumi da nakeyi kamar nayiwa sarki k'arya duk da sanyin da akeyi, ko jiya da zamuje dinner da ita yazo wai babu motoci a gidan sun k'are duk yawan motocin gidansu amma sai da ta haďoshi da ita, haka ma da aka tashi ta tafi yawonta sai da akayi ta nemanta duk sunbi sun ďagawa kansu hankali, ni wlhy bana sonta", sai da tayi shiru Janaba tace "toh meye alak'arshi da ita?", "ni ban sani ba, kullum ce min yakeyi wai cousin ďinshi ce, ban san ta ina ta zama cousin ďin tashi ba, ko a wajen wannan wushe wushen nasu kunga yadda abokanshi suka tsaya yi mata liki kamar itace amaryar, ni in bata dena shiga harkata ba Allah illatata ma zanyi", Mum ce tace "Ai ba wani alak'a na jini bane a tsakaninsu, abotace kawai a tsaksninsu na iyaye tun suna yara", kai Janaba ta girgiza tace "toh ita mamartasa mesa take son haďashi da ita kullum, ko tana son shi ne ya aureta", ďagowa tayi ta dubi Janaiba da idonta suka rine tace "babu wani, mey zaiyi da ita, kawai dai iko take nuna mishi na ita ta haifeshi dole yayi abinda takeso, kuma ni bata tab'a nuna bata sona ba", "toh ki kwantar da hankalinki, babu abinda zai sami aurenki indai muna raye, ku da zaku bar k'asar ma gaba ďaya, ki kwantar da hnklin ki kinji", kai ta gyaďa kawai ba tare da tace komai ba, haka suka ci gaba da hiran babu namijin da ya isa yi musu kishiya ko da ta wasa ce, da yadda za ayi da duk wani wanda yayi gigin cewa zai yi dashi da wacce zai auran.
Convoy ďin motoci sukayi shida abokanshi bayan sallar azahar har gidansu Ajiddeh, daga waje suka tsaya ya k'ira wayanta, shi yama manta da ďazu ya b'ata mata rai, a dak'ile ta amsa wayan har yanxu ranta a b'ace, ce mata yayi "ki faďawa su Mum gamu nan mun iso, zamu shigo yanxu", tsaki taja tace "meye toh sai ka k'irani ne, ko gidan bak'onka ne", cire wayar yayi daga kunnenshi ya duba ya tabbatar da wacce yake magana, mayarwa yayi ya k'ara wayar a kunnenshi yace "Ajiddeh kinsan da wanda kike waya kuwa", "na sani mana , wanda ya daka