Showing 102001 words to 105000 words out of 215266 words

Chapter 35 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1731

daga bakin gadon hannunta zagaye a k'irjinta duk kunya ya isheta, tafi minti biyu a haka daga baya ta mik'e ta faďa toilet, ta daďe cikin bath tub ďin kamin ta fito, a hankali ta lek'o kanta dan tsoro takeji kamar zataga wani a ďakin, ganin babu kowa yasa ta k'arasowa cikin ďakin, akwatinta na kayan shafa dake gefe ta cicciro waďanda take buk'ata ta shafa ta maidasu cikin akwatin, gown ďin atamfa holland bak'a mai manyan patterns ďin ja da purple ta saka, bata ďaura ďankwalin ba , comb ta ciro daga cikin kayanta ta dawo gaban mirror ta shiga taje gashinta, sai da ta gama ta haďeshi in a bun, tunanin shirya kayanta dake cikin akwati a closet ďin ďakin tayi, bbu b'ata lokaci ta tashi ta buďe closet ďin, tana buďewa taga electric burner a ciki, sai da ta karkaďe k'uran wajen tukunna ta shiga jera kayayyakinta a ciki, sosai ta shiga gyaran ďakin, har bedsheet ta canja wanda ta gani a cikin closet ďin ďakin, cikin lokaci kaďan ta gama gyaran ďakin ta kunna burner ta saka sandal woods, babu abinda ďakin keyi sai k'anshi, sai da taga ďakin ya koma yadda takeso sannan tayi ajiyar zuciya , faďawa tayi kan gadon tana maida numfashi, idonta ne ya faďa kan wayarshi da ya bata dake ajiye kan bed side drawer, hannu tasa ta dauko wayar, ta d'an tabe baki ta shiga gallery duk hotunan Ajiddeh ne wayar wasu da shigar mutunci wasu kuma bbu kyan gani, k'an wani hotonsa da yyi shi kadae yana xaune office ta tsaya tana kare ma kallo, yyi mugun kyau sanye da suit blue da fadin shirt daga ciki, murmushin sa me rikita Ajiddeh yyi a hoton Lol, Batuul tayi tsaki hade da tabe baki ta wuce hoton, wani hoton ta kuma gani yana sanye da farin 3qtr da farar polo, ainahin kyansa ne ya fito a hoton, ita kanta ta san yyi kyau amma hkn bae hanata kyabe baki ba, ajiye wayar tayi ta juya abun ta ta rufe ido kmr me shirin bacci.






Abuturrab na fita daga ďakin dama dakinsa ya wuce, direct toilet ya shiga yayi wanka, tsakin da baisan dalili ba ya riqayi har ya fito daga toilet ďin, sweatpant grey da farar shirt ya saka, zama yayi gaban system ďinshi yana dudduba abubuwan da zaiyi, bayan wajen thirty minutes ya mik'e tare da jan ďan siririn tsaki ya fita daga ďakin dan ya fara jin yunwa, ko coffee ne zuwa zaiyi ya haďa kamin ya samarwa kanshi abinda zaici, tunda ya fito daga ďakinshi yakejin wani k'anshi mai daďi, lumshe ido yayi yana shak'ar k'anshin, sauk'a yayi k'asa yayi hanyan kitchen, Ajiddeh na kwance nan inda ya barta ta tasa bowl ďin Tacos a gaba tanaci, ďauke kanshi yayi cike da haushinta ya wuce cikin kitchen, coffee maker ya nufa ya haďa sannan ya fito, sama ya koma yayi hanyan ďakin Batuul don ce mata ta fito ta samawa kanta abinda zataci, tun kamin ya kai ga shiga ďakin yakejin k'anshin nan na daďa k'aruwa, a aljihunshi ya fiddo makulli ya buďe ďakin ya shiga, a figice ta mike daga kwancen da take dan tasan saida ta rufe k'ofarta kamin ta kwanta, lumshe ido yayi ya bude ya shiga bin ďakin da kallo ganin yadda ta gyara shi yayi kyau, abinda dakinsa bae samu daga Ajiddeh ba, tashi tayi daga kwancen da take ta zauna tana kallonshi, kyab'e baki yayi ya k'arasa shigowa cikin ďakin, gashin kanta da yasha gyara yabi da kallo, ita kam wasa ta shigayi da zoben hannunta zuciyanta na bugawa taqi ďagowa ta kalleshi, kyab'e bakinshi ya kuma yi ya ďauke idonshi daga kallonta yana daďa bin ďakin da kallo yace "abincin da zakici sai ance ki fito ki nemawa kanki?, ko dan ki samu na fađa wa Ammah cewa bana baki abinci", bata ce mishi komai ba kuma bata ďago ta kalleshi ba, sipping coffee ďin dake hannunshi yayi yace mata "in kin gama zaman sai ki sauk'o ki nemawa kanki abinci don baki taho da Cook daga Nigeria ba", daga nan ya juya har xae fita ya dawo ganin wayarsa gefensa ya dauka, gabanta ne ya fadi tunawa da tayi a gallery take, kunna wayar yyi ya ga hotonsa, kallonta yyi yace "Ohh hotona ma kike kallo knn," dariya yyi yace "Lallai kina da wahala yarinya, xa ki iya kishi da matata?" Ji tayi kmr ta rusa ihu don takaici sae dae bata iya ta ce masa komae ba, yyi murmushi yace "Ae kam da kin gamu da aiki" daga hka ya fita daga ďakin, bayanshi ta bi da kallo tareda da fadawa kan gado tana kukan takaici.





Ji tayi wayanta na ringing, ta duba taga Aunty ke k'iranta, da sauri ta goge hawayenta cike da murna ta ďaga ta gaida Aunty tace "Aunty har na fara zuwa school yau, Aunty sai kinga makaranta, i couldnt believe it sai da na ganni a lecture hall, da i thought i will never get d chance to study there, but God has other plans, am just happy tun ďazu", Aunty tayi murmushi daga ďaya b'angaren tace "Ai dama every disappointment is a blessing in disguise, kinga you were sad abt getting married, but God knows best, sai kinyi aure zaki samu kiyi fulfilling dream ďinki", ajiyar zuciya Batuul ta sauk'e tunawa da tayi auren da tayi ne yayi silar zuwanta makaranta, jiki a sanyaye tace "Aunty its so nice, Nagode", Aunty tayi dariya tace "godiya kuma, Allah zaki godewa ai", tace "Ai nagode mishi sosai shima, saura Baba shima zance mishi nagode", Aunty tayi dariya tace "toh shikenan, kayanki sun iso?", da mamaki tace "Aunty wane kaya?", Aunty tace "kayayyakinki mana da kuma su turaren wuta", tace "A'ah Aunty, ni kawai wanda nazo dashine, sai turaren wutanma ďan kaďan ne", Aunty tace mata "toh shikenan, in sun iso Abu zai kawo miki, sai ki gayamin", tace "toh", hira sukayi da Aunty daga nan sukayi sallama, tana ajiye wayar aka bude kofa, mikewa tayi da sauri sanin shi ne ya dawo, wani mugun kallo yake mata daga bakin kofar ta sunkuyar da kai a hankali tace "Anty ce ta kira ni" juyawa yyi ya bar kofar ta bi bayansa da sauri, downstairs ya sakko tana biye da shi a baya, xama yyi gefen Ajiddeh yana kallonta yace "Kin yi sllh babe?" Xata basa amsa idonta ya kai kan Batuul dan zaro ido tayi kafin ta mike cikin fada ta fara magana "Aliyu meye hka xata wani sakko mani falo da kwalliya hka kmr gidan mijinta? Ohh dama ita ce ta cika min gida da turare hka?" Kallon Batuul da ta k'asa ci gaba da tafiya Abuturrab yyi don shi bae ga wani kwalliya da tayi ba banda kaya da ta sa, xae yi magana Ajiddeh ta ci gaba da masifarta "Toh gskya baxan yi tolerating haka ba, cin arxiki ta xo yi gida na don hka ta bi ni a hankali, daga yau ni kar ta sake sa min turare a gida kuma kar ta kuma sakko min falon miji bbu hijab, idan ba hka ba gskya xa a ga bala'i" murmushi Abuturrab yyi ya ajiye cup din coffesn hannunsa ya kalli Batuul dake tsaye har lkcn a tsawace yace "Baxa ki bar wajen nn ba" juyawa tayi a d'an tsorace xata koma sama, yace "C'mon kin wuce kin yi abinda xa ki yi ko sae na xo kan ki" kitchen din ta nufa hawaye cike idonta, rasa abinda xata girka tayi gashi tana tsoron kar ya shigo ya ganta tsaye, bude deep freezer tayi ta ga kayan miya kala kala da nama, deciding kawae tayi ta soya Irish, tayi sauce kadan, cikin mintunan da basu wuce ashirin ba ta hada abincin ta kashe gas, kan kace me tuni kamshin d'an sauce din da tayi da hanta ya bade gidan, Ajiddeh sae wani yatsine fuska take tana kyabe baki, Abuturrab ya juya ya kalleta yace "What's that?" Tsaki tayi bata ce komae ba, ya mike ya nufi kitchen din, goge goge ya sameta tana yi ga abincin ta ajiye gefe, juyawa tayi tana kallonsa, kmr baxae ce komae ba sae kuma yace "Iyakar girkin knn?" A hnkli tace "Um!" Tabe baki yyi har xae fita sae kuma ya karaso cikin kitchen din, plate ya dauka ba tare da ya kalleta ba ya nufi inda ta ajiye abincin ta bi sa da kallo, kadan ya dibi Irish din da sauce a gefe, ya daga kai suka hada ido, sauke idonta kasa tayi tace "ya ishe ka hka?" Juyawa yyi yace "Yea!" Snn ya fice, hade rae Ajiddeh tayi tana kallonsa har ya xauna gefenta tace "Haba babe, wnn ae xub da girma ne, maimakon ka fita ka siya ko ka aiki driver" yace "koh? In xa ki ci ki sa hannu mu ci" tsaki tayi ta dauki remote, fork ya dauka ya fara cin abincin, he was so surprise at the taste of the food, bae taba tunanin Batuul ta iya girki hka ba, lumshe ido yyi yana cin abincin, amma sbda bae son ta rainasa bae cinye potatoe din ba duk da bae ishe shi ba ya ajiye, dai dai nn Batuul ta fito bayan ta gama tsaftace kitchen din rike da plate din abincin ta, bata yi gigin kallon inda suke ba ta haura sama. Abuturrab na gama kallon program din da yake kallo ya mike ya haura sama ya bar Ajiddeh nn falon, har xae shiga dakinsa sae kuma ya nufi na Batuul, ya kusa minti biyar tsaye don bae ma san me xae kai sa dakin ba, bude kofar dakin aka yi ya koma baya da sauri duk ya daburce, kallonsa take da mamaki, ba tare da yyi wani tunani ba ya samu kansa da cewa "Tnx!" Sae kuma ya juya da sauri ya nufi dakinsa, bin sa da kallo tayi sae kuma ta kyabe baki ta sauka downstairs, dai dai lkcn da Ajiddeh ta duka ta dauki plate din potatoe'n da Abuturrab ya rage xata d'an d'ana taji taste din girkin da ya cika ma mutane gida, sae a idon Batuul, sake plate din tayi duk da har ta kai daya baki, duk ta daburce.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝

49

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Sunkuyar da kai Batuul tayi ta karasa sakkowa, Ajiddeh ta ji kmr ta nutse wajen don kunya, mikewa tayi tana yatsine yatsinen borin kunya ta nufi kitchen da sauri, hannu ta wanke da bakinta a sink ta shiga kakarin amai, Batuul bata san lkcn da dariya ya subuce mata ba, ta juya da sauri ta koma sama ta dinga tuntsirar dariya a corridor, bude kofa Abuturrab yyi yana kallonta da mamaki, xae yi magana sae ga Ajiddeh kmr xata tashi sama, ganin dariya Batuul take ya sa ta tsaya daga stairs tana huci, Abuturrab ya kalleta ya kalli Batuul da ta k'asa daina dariya ganin ynda Ajiddeh ke huci, a fusace Ajiddeh tayi kanta ae bata san lkcn da dariyar ta koma ciki ba tayi bayan Abuturrab a tsorace tana kiran Anty, ya hade rae yace "meye hka wae?" Lamo Batuul tayi bayansa, a fusace Ajiddeh tace "Honey ni fa take ma dariya hka kmr sa'arta fa?" Juyawa yyi yana kallon Batuul yace "kina da hankali kuwa? Dariyar me kike mata?" Batuul ta turo baki tace "Ni ba da ita nake ba fa" wani kallo ya shiga mata ya fixgo ta daga bayansa yace "ki fadi Dariyar me kike idan ba hka ba I wil slap yhu" sunkuyar da kai tayi don wani dariyar taji na taho mata, ya daka mata tsawa yace "Baxa ki yi magana ba" a hnkli tace "Kaga abincin da ka rage fa naga tana ci a falo kuma tana gani na sae ta shige kitchen ta fara amae...." Bata karasa ba ta shige bayansa ta dinga dariya har da kyakyatawa, dariyar shi ma ya fara yi yana kallon Ajiddeh da ke kikkifta ido, ganin irin dariyar da suke ya fusatar da Ajiddeh tayi bayansa da gudu xata fixgo Batuul, tura Batuul yyi bedroom dinsa da sauri shi ma ya shiga ya rufe, ae tsit kke jin Batuul don ta tsorata ssae, shi kam bae fasa dariyar da yake ba, Ajiddeh kam dakinta tayi hawayen takaici na bin kuncinta tana da ta sanin kallon potatoe'n, kallon Batuul Abuturrab yyi bayan ya gama dariyarsa ya hade rae yace "Xaki yi spelling Doom yau, ba dae dariya kike mata ba" kmr xata yi kuka tace "Wllh ni ban sani ba... Sharrin shaidan ne" sae ga hawaye na bin kuncinta, wani sabon dariyar Abuturrab ya shiga yi, Batuul ta durkushe wajen a sanyaye tana kallonsa don ita har ga Allah tsoron Ajiddeh take, ya shafa kansa yace "Ki tashi mu je ki bata hkuri idan ba hka ba ta kora ki daga gidanta yau" mikewa tayi tace "Toh" ya mike shi ma ya nufi kofa tana biye da shi a baya, yana bude kofan ya juya da sauri yace "Gata nan" a guje Batuul ta juya xata bar wajen cikin rashin sani ta take dogon gown din jikinta, ji kake tim a k'asa ta fadi, wani kara ta saki ta fashe da kuka tana kiran Anty, ya durkusa da sauri ya d'ago ta yana kallon kafarta yace "Ohh sorry!" Kuka take tana yarfe hannu don ji tayi duk jikinta na mata ciwo, ae fa nn ya rikice yana dube duben ko ta ji ciwo, gefen gado ya xaunar da ita yace "Yhu c, me ya kai ki sa kayan da ya fi ki tsayi" kukan ta kawae take bata ce komae ba idonta a runtse, ya galla mata harara yace "Ina ke maki ciwo?" Kneel dinta ta nuna masa, ya daga gown din jikinta idonsa ya sauka kan smooth fresh long leg dinta, k'asa dauke idonsa daga cinyarta yyi don har cinya ya kai rigan, ita kam jin ya daga mata riga kuma bae ce komae ba yasa ta bude ido, da sauri ta janye kafarta daga gabansa ta sauke riganta, ji yyi kmr ya nutse don kunya amma da yake gogagge ne, wayancewa yyi ya mata mugun kallo yace "Don kin samu ina tofa maki addu'a" sae kuma ya mike yace "Idan kin ga dama ki tashi mu je ki bata hkuri" a hnkli ta mike ganin ya fara tafiya ta bi bayansa, suna isa kofa ya juya yaga dingishi take, yace "Meye hka?" Kmr xata yi kuka tace "Ciwo yake min" fixgo hannunta yyi suka koma dakin ya xaunar da ita gefen gado snn ya nufi gaban mirror ya dauko man xafi ya dawo, ya wani hade rae shi a dole Lol, nan dae ya daga mata rigar kuma ya bude man ya diba, ya fara shafa mata a gwiwan, runtse ido tayi jin xafi ta dafa kafadarsa tana kiransa, kallonta kawae yake har ya gama snn ya mike ta bude idonta, ganin ya nufi kofa ta mike ita ma ta bi bayansa da sauri, a hnkli ya murda kofar Ajiddeh Batuul na boye bayansa, xaune ya sameta ta cika tayi fam tana girgixa kafa, yace "Babe!" Wani wawan kallo ta jefa masa, ya gintse dariyarsa ya juya yana kallon Batuul don yasan bata san tare suke ba, a hnkli yace "Baxa ki bata hakurin ba" Batuul kmr xata yi kuka tace "Don Allah Anty kiyi hkuri ni ba da ke nake dariya ba fa" mikewa Ajiddeh tayi da sauri tace "Ohh biyo ni daki kika yi don kin isa?" Batuul tace "A'a kiyi hkuri ni ban san xa ki ji haushin dariyar ba" Ajiddeh tace "Ae sae kin gaya min me kike ma dariya xa ki kwana gidan nn yau" shiru Batuul tayi, hkn yasa Abuturrab ya fara dariyar da yake gintsewa yace "Ta fa baki hakuri Anty" Ajiddeh ta fashe da kuka tace "Aliyu ni na gaji da wnn walakancin naka, na gaji" dariya kawae yake yace "Babe ita fa ba potatoe'n da kika ci ya bata dariya ba, aman da kika tafi kitchen kike yi shi ya sa ta dariya, ko ba hka ba Batuul" a hnkli Batuul tace "Ehh!" Ajiddeh ta kuma rushewa da kuka kmr an aiko mata da sakon mutuwa, me Abuturrab zae yi bn da dariya, dariyar da bae taba yi ba a rayuwarsa, ita kanta Batuul hadiye dariyan take tana lekan Ajiddeh.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝

50

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Had'iye dariyarshi yayi ganin kukan da Ajiddeh keyi kamar wacce aka daka ya juyo yana kallon Batuul da tayi saurin gintse dariyarta ta sunkuyar da kai, hannunta ya kamo ya dawo da ita gaban gadon Ajiddeh ya hade rai yace "sake bata hakurin", a hankali Batuul tace "kiyi hak'uri" jajayen Idonta da suka rine ta dago tana mata wani mugun kallo, kallon Batuul yayi yace mata "Get out", kamar munafika ta fice daga d'akin, tana fita ya dawo bakin gadon ya zauna tareda janyo Ajiddeh jikinshi, kukan ta sake fashewa da, bayanta ya shiga bubbugawa yace "Hey babe, tace fa ba dake take ba, beside meye Na zuwa da yin amai bayan har ta ganki kinci, ai cemata zakiyi ta zubo miki ma tunda gidanki ne" ya k'arashe maganan yana murmushi, d'ago kanta tayi tana hararansa da rinannun idanuwanta a fusace tace "toh kai dariyar da kake yi ta me? Memakon kayi mata fad'an abinda tayi shine ka biye mata kuna min dariya don walakanci koh", har lokacin yana murmushi yace "its okay yanxu ai na sata baki hakuri, i will deal with her next time she tries anything stupid thing" d'ago kanta tayi ta sake kallonshi , kai ya kad'a mata yace "i mean it wife, kin ma yi sllhn kuwa" shirun da yaji tayi yasashi gane batayi ba, yace Mata "tashi kije kiyi sllh, I will b back right away" daga haka ya mik'e ya fita

Batuul na fita ta wuce d'akinta, kan gado ta fad'a taci

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login