Showing 36001 words to 39000 words out of 215266 words
yin shi kamar masu yiwa junansu hiran soyayya
Batuul na isa gida ta hau sama, wipes ta ďauka ta goge abinda ke fuskanta sannan ta shiga tayi wanka tayo alwalar isha ta hau abin sallah, tana idarwa ta cire hijabin jikinta ta ninke shi ta ajiye a gefe, ko hula bata ďaura akanta ba ta sauk'o k'asa dinning dan yunwa takeji, kwanukan wajen ta shiga buďewa, plate ta jawo ta ďebi white rice da stew sai potato salad, ďakinta ta tafi da abincin sannan ta zauna taci a a nutse, tana gamawa ta buďe fridge ďinta ta ďauki ruwa tasha, sai da ta gama abubuwan da zatayi tahau gado ta yi addua ta kwanta, bacci nebmai nauyiya ďauketa, can cikin bacci wajen k'arfe goma sha ďaya ta jiyo murya kaman na Farida, a hankali ta buďe idonta taga Farida tsaue kanta da wannan wide smile ďin nata tana kallonta, ta kunna hasken wutan, Aunty ce ta shigo ďaki tana tambayan Farida "tayi bacci ko, watak'ila kan ne ya ďan saketa", ganin Batuul ta farka ne ya sata cewa "ya kan Batuul, yayi sauk'i", a hankali tana goge ido tace "ehh Aunty yayi sauk'i nasha analgesic ", da Masha Allah ta ta amsa sannan tace mata "Allah ya k'ara lafiya" tayi musu sai da safe ta fita, kallon Farida Batuul ta tsaya yi, "You didnt tell me you were coming over", baki Farida ta buďe da mamaki tace "toh ko in koma ne, wannan tambaya haka da ake jeho min", bata cewa mata komai ba taja bargonta ta rufe kanta ta kashe wutan daga gefen gadonta, Dariya Farida tayi bata ce mata komai ba sai da taje tayi wanka tayi sallah ta canja kayan bacci, wutan ďakin ta sake kunnuwa tayi tsalle ta hau gadon, Mik'ewa Batuul tayi ta dubi Farida tace mata "meye matsalanki wai", tashi Farida tayi daga kwance da take tace "my problem is i love you so much", tsaki Batuul taja zata koma ta kwanta ta farida ta janyota "kinsan na faďa miki dama gida ya isheni, wait ma, keh da na barki kina yiwa ango lik'i sai nemanki nayi na rasa, Allah kinga yadda kika yi kyau a wajen kamar kece amaryar sai lik'i ake miki , ko amarya ma ba ayi mata ba, Yaa Massa ne ya fara miki ai ko sunace kece amarya har Pounds an zuba miki, mehn i enjoyed that part", "Allah Farida ke ko, yanxu dan wannan kika tada ni, Allah ya shiryaki", wayanta ta jawo ta k'ira Affan, yana ďagawa kamin yace komai tace "Bestfriend com and carry your girl, tun ďazu take damuna ta hanani bacci", ce mata yayi "bata wayan, mik'awa Farida yayi, zama tayi tana jira ta gama wayan, amma har bayan minti talatin basu gama ba, da taga basu da ranan gamawa ne ta jawo bargonta ta kwanta
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)
WHATSAPP NO:
+2349030159301
💖💝BATUUL💖💝
20
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Bayan Aunty ta duba Batuul, ďakinta ta koma ta tabbatar su Yusra sunyi bacci, addua tayi musu ta tofesu dashi gaba ďaya jikinsu sannan ta tofa a duka angles ďin gidan, toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito tayi sallah, sai da ta idar ta gama addu'o'inta sannan ta mik'e ta cire doguwar rigar dake jikinta, ninkesu tayi sannan ta ďauko kayan baccinta doguwar riga har k'asa, yellow silk mai flaps biyu ta saka, turare ta shafe jikinta dasu sannan ta nemi hula ta saka a kanta, k'asa ta sauk'o ta k'arasa kicin ta tsiyayo fresh orange juice a cup ta ďaura a kan k'aramin serving tray ta haura sama, da sallama ta shiga ďakin Baba, yana zaune a kan gado da farar jallabiya idonshi da glasses yana rik'e da ipad, da alama aiki yake, ďagowa yayi ya kalleta cike da Kulawa sannan ya amsa sallamarta,har ta k'araso ciki, a bakin gadon ta zauna sannan ta ajiye juice ďin a kan bed side drawer, dubanshi tayi itama da kulawa tace "uncle sannu da hutawa, ya dare", bai ďago daga kallon da yakewa ipad ďin ba ya ansa da "Alhamdulillah", sai da ya amsa sannan ya ajiye ipad ďin a gefe ya juyo ya dubeta yace "Ya gidan biki", cike da natsuwa Aunty ta amsa da Alhamdulillah, amaryar tashi ma mai kyau, Allah ya basu zaman lafiya", Amin Baba ya amsa da sannan yace "nima ďin sai jibi zan tafi , ďaurin auren 11 ne, by nine zanbi flight sai mu dawo a ranan", "Allah ya kaiku lafiya, ya dawo daku lafiya, su kuma Allah ya basu zaman lafiya", a tare suka amsa da "Amin", a hankali ta sake cewa "uncle", bayan ta mik'a mishi cup ďin juice, kurb'a yayi kaďan sannan ya juyo bayan ya ajiye cup ďin yace "Maryam, ya akayi ne", a hankali ta ďago ta dubeshi kamar bata son magana tace, "uncle dama karatun Batuul ne, kwanaki da sukayi graduation tace min inyi magana da kai akan karatunta, wai in baka hak'uri ka barta ta fita waje, dama kunyi magana ne da ita kace baka son zuwan nata waje?", cewa yayi "Allasarki mamana, eh munyi maganan da ita na ce mata tayi hak'uri da wajen nan , ta zab'i duk inda takeso a nan Nigeria zan kaita, "toh uncle mey zai hana a kaitane tunda munsan Batuul mun san hankalinta, am sure zata kula da kanta da mutuncinta, baza mu samu matsala ba in sha Allah", glass ďin dake idonshi ya cire ya dubi Aunty sannan yace "Maryam, nafi kowa son ganin na bawa Batuul abinda takeso a duniyan nan, amma bazai yiwu ba, wannan zuwan da mukayi Maiduguri sallah Yayya ce min tayi indai Batuul zata fita waje karatu toh sai da miji, ni kuma ban shirya yiwa Batuul aure ba, tayi k'arama da yin aure shiyasa nace gara in nemo mata makarantanta a nan gida tunda ita Yayyan cewa ma tayi ko a gidan ne sai an mata aure, toh yanxu bakinta nake son rufewa in bar Batuul a gida tayi karatunta dan ta dage sai anyi mata aure", kallo kawai Aunty ke binshi dashi, cewa tayi "aure kuma uncle, nawa Batuul ďin take da za a fara mata zancen aure, ko 17 fa bata cika ba uncle, yaushe za a fara sata a lissafin aure, tayi zamanta a gida tayi karatunta, zan bata hak'uri tayi a gida, in yaso sai taje ko da msc ďinta ne a waje, by then zan yadda da aurenta", sai da tagama Baba yace "Allah ya tabbatar mana da alheri , ya zab'a mata abinda yafi alheri", ta amsa da "Amin", mik'ewa tayi ta ďauke cup ďin da Baba yasha juice ďinshi da ta kai k'asa ta dawo sama ta kashe musu wuta suka kwanta, tunanin maganan da suka gama yi da Baba ta rik'a yi, addu'a tayi daga k'arshe ta shafa ta kwanta ta barwa Allah komai
A k'ofar gidansu Ajiddeh ya tsayar da motan ba tare da ya shiga ba, enveloles guda biyu manya ya mik'o mata, sai da ta karb'a sannan yace mata "Wannan tickets ne na masu zuwa ďaurin aure, mun riga da munyi chattering plane ďin, in bai isa ba gobe before 1 ki sanar dani dan 3 zamu tafi, ki faďawa Su Mum an gama readying komai har na sauk'an baki, kuma a ranan zamu juyo bayan an ďaura aure, daďi taji sosai , burinta na auren Aliyu Ahmad Kyari ya kusa cika, bata tab'a jin tana son mutum kamar shi ba , tsayawa tayi tana kallonshi kamar a mafarki, hure mata fuska yayi ya ďaga mata gira yana tambayanta ya akayi, rungumeshi kawai tayi ta shige jikinshi gabs ďaya, bayanta ya ďan bubbuga sannan ya janyeta, hannunta ya rik'e yana kallon lallen dake hannunta, "yayi kyau yace mata", da murmushi tace mishi "thank you baby, tun ďazu nake jira kace nayi kyau amma baka faďa min ba", kallonta yayi gaba ďayanta tayi kyau dagasken dan baima lura ba ďazu, gefen fuskanta ya shafa sannan yace "ai keh mai kyauce", wani daďi ne ya kamata ta rasa mey ma zata ce mishi, ce mata yayi "ni zan wuce gida yanxu , kuyi mana addua, zamu wuce gobe mu dawo saturday, so sai mun dawo kenan, kamar kar ya tafi ta rik'a ji, har wani ďan hawaye ne ya taru a idonta, buďe k'ofan tayi ta fita, sai da ta shige kamin ya ja motarsa yayi gaba, kamar ba su sukayi faďa ba ďazu, sha biyu saura ya isa gida, hayaniya ne ko ta ina kamar dare bai yi ba , ko ina kunne yake da haske, ďakinshi yaje yabi ta wata hanya da zata sada shi da ďakin Ammah saboda yawan jama'ar dake gidan, tura k'ofan yayi tare da sallama ya shiga, tana zaune da wasu manyan kwalaye a gabanta Sadiq na daga gefenta tana mishi bayanin wani abu, waje ya samu daga kusa da ita ya zauna kamar zai shige mata jiki, juyowa tayi ta dubeshi tace "Abu kaine da daren nan", kai ya gyaďa tare da cewa "nine Ammah , nazo ne muyi sallama tun yanxu dan gobe ba lallai mu samu time ba", Sadiq ne ya sake wane murmushi mai haďe da dariya yace "Yayanmu ango, daga gobe kuma ka zama posession ďin Hauwa", murmushi ya tare da girgiza kai yacewa Sadiq "you will never change" jujjuyawa yayi ya duba ďakin can ya juyo ya dubi Ammah yace mata "Ammah ina Farida ne", ce mishi tayi "Ai Farida tun da rana ta gudu gidansu Batuul, mita take ta yi min wai ana b'ata mata ďaki da toilet ita baza ta zauna ba, shine ta tafi wajen Batuul", sunan Batuul ne da Ammah ta ambata ya sashi tunata, kaďa kanshi yayi yace " Faridan Abui, ai da ta faďa wa Abui cewa zaiyi tazo ďakinshi", Sadiq yace "Riri akwai case", Abutturab ne ya sake matsowa kusa da Ammah, hannunta ya rik'e yace "Ammah gobe zamu tafi Maiduguri ďaurin aure, a yi mana addua Allah ya kaimu ya dawo da mu lafiya", kallonshi tayi na y'an dak'ik'u sannan ta shafa kanshi tace "Allah yayi maka albarka Abu, Allah ya tabbatar muku da alherin rayuwanku, ya baku zaman lafiya, ya azurtaku da zuriya ďayyiba, Babana you are taking a great step a rayuwanka, amana zasu baka ita, ka rik'e ta tsakani da Allah, in tayi laifi ka nuna mata tayi ba daidai ba, in yayi girma ka hukuntata daidai da laifin da tayi, ka zama mai yi mata adalci a koda yaushe, hankalin mace ba irin naku bane, kayi hak'uri da duk abinda zaka fuskanta , Allah yayi muku albarka", ji yayi duniyar tayi mishi wani iri, kamar an ďaura mishi wani abun mai nauyi, ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace "in sha Allah Ammah, Allah ya k'ara muku nisan kwana" shafa kanshi ta sake yi tace "Amin Babana", Sadiq dake zaune a gefe ne ya ciro handkerchief daga aljihunshi yana goge hawayen k'arya yace "wannan emotional moment ďin naku can melt a mountain, har kuka zaku sani", Ammah ce tace "saura kaima, ai kana hanya", dariya yayi tare da nuna kanshi da yatsanshi yace "Ammah ai ni yarone tukunna, mun bar manya sai sun gama tukunna" ya k'arashe maganan yana murmushi, ce musu tayi "in kunje gobe Yaa Mera ta sa a shirya komai da zaku buk'ata a shehuri na abinci, accomodation dama kun gama shiryawa ai ko" kai suka gyaďa mata a tare suka amsa da "ehh", tace "toh shikenan Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, Allah ya taimaka, ku tashi kuje ku kwanta yanxu dare yayi kuma kuna da abun yi", mik'ewa sukayi dukkansu biyu suka rungumeta tare da sumbatar goshinta sannan sukayi mata sallama suka fita
Washegari k'arfe huďu jirginsu ya isa Maiduguri, motocine masu yawa suka zo taransu, samari ne gaba ďaya a airport ďin, sai da Abutturab, Massa, Sadiq da Abba suka tabbatar kowa ya isa masaukinsa sannan suka sukavbar airport ďin suma, gida yaje ya tarar da Abui zaune tare da mutane a palon gidansu, gaishesu yayi ya zo kusa da Abui sukayi magana ya haura sama, wanka yayi ya canja kaya ya fito , sake zuwa yayi suka yi magana da Abui sannan ya fita daga falon, mai gadi ya k'ira yace mishi ya ďan goge mishi mota zai fita dashi yanxu ya mik'a mishi key, zama yayi k'ark'ashin wani bishiya ya danna wayanshi har aka gama wankin aka dawo mishi da key, mik'ewa yayi ya karb'a sannan ya isa inda motar take ya buďe ya shige, rear mirror shi ya seta zai juya kenan idonshi ya hango mishi wani abu, hannu ya mik'a daga baya ya ďauko abun da ya gani, tsayawa yayu ya kafawa ďan kwalin dake hannunshi ido kamar mai karanta wani abu, ranan da ya fara ganin Batuul ya tuna, ya ganta a masallaci, sai kuma da Ammah tace ya maida Batuul gida, ranshi ne ya b'aci kamar ranan akayi abun, k'ofa ya buďe zai yar da ďankwalin ko me ya tuna kuma sai ya fasa ya mayar cikin safe keep ďin motar, tadawa yayi ya fita daga gidan, Muna guest inn yaje , buďe mishi k'ofa akayi ya shiga inda aka sauk'i abokanshi yaje , yana shiga yaga kowannensu har sun canja kaya, wasu na sallah wasu na cin abinci, alwala shima ya shiga yayi ya jagorance waďanda basuyi ba sallah , abinci ya ďebo bayan sun idar da sallah dan baici komai ba tun safe, yana cin abinci suna hira da abokananshi har ya gama suna ta hira
Mik'a Batuul tayi daga kan gadonta, gaba ďaya jikinta baya mata daďi, tashi tayi taje tayi wanka ta dawo, agogo ta duba taga k'arfe ďayan rana, hannu tasa ta tada Farida, "ki tashi Riri, rana tayi", da kyar ta samu ta tada Farida, tashi tayi ta zauna akan gado tacewa Batuul "Nifa ban koma na kwanta ba tun asuba sai eleven shine kika tada ni", Batuul bata ce mata komai ba ta tashi taje saka kayanta, doguwar rigar atamfa ta saka, fita tayi daga ďakin ta tarar da Aunty a palon sama, gaida Aunty tayi sannan ta zauna kusa da ita ta jawo remote tana canja channel, Aunty ce ta tambayeta "Faridan fa, ya akayi kika fito kika barta", cewa tayi "wanka takeyi na fito na barta" tunowa tayi da mafarkin da tayi jiya, Juyawa tayi ta dubi Aunty ta cemata "Aunty jiya da safe da ina bacci nayi mafarki, wai ina kwance a wani falo babba akan gado, akwai rami a falon, wata farar mata ni banga face ďinta ba tazo tana tura gadon cikin ramin, wai sai ga wani mutum yazo yana tare gadon, shinefa wai da mutumin ya turani na bar kusa da ramin shi sai ya faďa ciki, amma ya samu ya rik'e wani k'arfe daga ciki yana mik'omin hannunshi in fito dashi, kuma har sunana ya sani, da farko Batuul yake ta cewa, daga baya ne ya fara cewa Fatima, shine na sauk'o daga gadon na rik'e mishi hannu ya fito dani, bayan ya fito ina ta so ya sakeni yak'i, sai kuma ga matar ta sake yowa kanmu, shine lokacin na tashi", saida Aunty ta gama sauraronta sannan tace mata "bakiyi addu' bane kamin ki kwanta" ta tambayeta, "nayi addu'a da zan kwanta, da na tashi ma jikina yana ta b'ari, duk jikina gumi, sai da nayi wanka nayi nafila tukunna na ďanji dama dama kuma da na tashi da safe zan faďa miki naga kun fita", "Allah ya rufa asiri, kina yawaita addua kullum ba sai kin kusa kwanciya ba, kuma next time in kinyi mummunan mafarki kar kina faďa, kinji", "toh" ta amsa da, Farida ce ta k'araso palon , wajen da Aabid ke kwance yana wasa ta k'arasa , zama tayi ta ďaukeshi tare da gaida Aunty, ansa mata da sannan ta tashi ta tafi
Washegari asabar, ranar ďaurin aure, tunda yaje ďakin da ya sauk'a na hotel ďin bai kwanta ba, salloli da addu'a yayi sosai na Allah ya tabbatar musu da duk alheran dake cikin auren nan ya kawar musu da sharran dake ciki kuma sannan yayiwa iyayensu addua , tashi yayi ya shiga toilet bayan ya gama, wanka yayi ya fito yaje ďakin da sauran abokan nashi suke ya tada su suje masallaci suyi sallan asuba, duk ďakunan da ya san abokanshi da mutanen da sukazo ďaurin aure sun sauk'a sai da yabi ya tada su, wasu ya samesu idonsu biyu wasu kuma suna bacci, sai da ya gama ya wuce masallaci, bai shigo ba sai takwas, yana shigowa ya k'ara watsa ruwa, Massa ne ya shigo bayan ya fito daga wanka sanye da bathrobe fari, ko sallama bai yi ba ya fara "ango ango ka sha k'amshi", murmushi Abutturab yayi yace "nasan zanyi aure someday or the other but never thit would be this close, kamar ba ni zanyi auren ba nakeji", gefenshi ya dawo ya zauna ya dafa mishi kafaďa yace "There is time for everything bro, Allah ya sanya muku alheri" sannan ya mik'e ya fice daga ďakin, closet ďin ďakin Abutturab ya bude, kayane a jere iri iri, sai da ya saka under garmenta ďinshi sannan ya ďauko wata farar shadda , ďinkin dogon kaftan ne na zamani yayi kyau, sawa yayi tare da ďauko hula fari da blue da cuff links ďin kayan, agogon Hublot ya mak'ala bayan ya saka hulan, a cikin closet ďin ya ciro turarukanshi masu k'anshi ya fesa su , sai da ya gama tukunna ya ďauko bak'in takalmi daga k'asan closet ďin ya saka, juyowa yayi ya dubi mirror yayi kyau sosai, wayanshi ne ya ringing, sai da ya zauna ya ďauki wayan "salamu alaikum, Abui nda wattu", Abui ne ya amsa da