Showing 78001 words to 81000 words out of 215266 words

Chapter 27 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1730

"Alhamdulillah Baa, yayi sauk'i, na warke yanxu", yace "Masha Allah, har yanzu kinason zuwa Uk kiyi karatun?, ya tambayeta yana kallonta, ďagowa tayi ta dubeshi dan ta tabbatar da abinda taji yana faďa mata, ganin dagaske yake da sauri ta shiga gyaďa kai ta daďa rungume shi, tasan dama babu wani aure da za ayi mata kawai Yayyace ta faďa, ce mishi tayi "ehh Baa inaso" murmushi ďauke fuskanta, murmushin yayi shima yana shafa kanta yace "toh zan samo miki admission sai kije kiyi karatunki kinji ko, ai zakiyi karatu sosai ko?", kanta ta gyaďa har lkcn murmushi shimfiďe fuskanta har yafi nada, cewa tayi "Baba toh yaushe ne za ayi, ko sai na gama semester ďinnan sai inyi transfer", ta tambayeshi tana jiran jin mey zaice, Aunty dake aikinta tana jinsu ta saki dariyan takaici dan tasan so kawai Baba yake ya shawo kan Batuul dan yasan tana son karatu sosai, zata iya hak'ura da komai dan tayi achieving dream ďinta, Babane yace "very soon Mamata, amma kinsan mey nakeso dake", kai ta girgiza mishi yace "yawwa, kinga dama bana son zaman hostel, ko", nanma kai ta gyaďa, yace "toh kinga sai kiyi zamanki tareda Yayanki, nasan sosai zai kula dake", kanta ne yaďaure ta fara tunanin wane Yayan kuma, ce mata yayi "nasan tunanin wane yayen kike, Abutturab nake nufi", wara ido tayi ta kalli Baba tana girgiza kai tace "Baa toh zan zauna inyi a gida na fasa wllh, bana son zuwa," hawaye cike idonta ta kare maganar "k'ara janyo ta yayi jikinshi ya goge mata hawayen dake zuba a idonta yace "ki kwantar da hankalinki kinji Batuul, nasan anytime you will be proud of whatever decision i made, nasan Aliyu tun yana k'arami, nasan abunda zai iya da wanda bazai iya ba, ki kwantar da hankalinki kinji, kuma auren da Yayya ta faďa miki gaskiya ne", sosai ta shiga kuka harda sheshshek'a" muryarta na rawa tace "Baba nifa yarinya ce, just last month na cika 18, kayi hak'uri in na girma sai kayi min ko da waye ma kaji Baa", dariya maganan nata ya bashi yace "Batuul akwai Babba ne da k'arami a bautar ubangiji, babu, toh kinga ina laifin tun kina k'arama ki fara bautawa ubangijinki, kinga ladanki nema zai k'aru, ga kuma ladan da zaki samu na yi mana biyayya, ko ba kya so", ya tambayeta yana kallon fuskanta dake ta ambaliyan hawaye, kasa cewa komai tayi, ci gaba yayi da mata magana yace "toh mamata y dont you start it early and be rewarded abundantly, tunda at any point zakiyishi its better you do it now, and am assuring you Abu will b d best husband we will ever recommend for you, Nida Babanshi have been good friends for over 30yrs, har gida yazo ya sameni ya nemawa Aliyu aurenki, duk mutumin da yaso jininka har yaso haďa zuriya dakai yafi k'arfin wulak'anci, kinga ba daďi ince musu a'a, sosai yake ganina da mutunci, friendship ďinmu da muka gina based on trust yafi k'arfin ya nemi abu a wajena in hanashi", jikinta ne yayi sanyi sosai, ďagota yayi yana kallon fuskanta yace "Ko in koma ince musu kince bakya so", a hankali ta girgiza kanta alamar a'a, yace "yawwa Mamana Allah ya miki albarka, yanxu ki share hawayenki ki rok'i Allah ya tabbatar miki da duk alherin dake cikin bikin nan", haka ya dinga bata baki yana kwantar mata da hankali har yasa Batuul ta hak'ura, sai da aka k'ira magrib tukunna ya fita daga ďakin ya tafi yin Sallah.



Washegari misalin goma na safe Abuturrab na kwance falo kan 3sitter abun duniya ya taru yyi masa yawa ganin ynda Ammah ta dage sae Shirye shiryen aurensa take ba ji ba gani, Ammah ce ta shigo falon ya mike xaune ganinta, da fada ta fara magana tace "anya kuwa Abuturrab kana son gamawa da mu lfya, tun jiya ina bin ka ka je gida ka duba yarinya an sallamesu ka ki xuwa?" Sakkowa k'asa yyi da sauri yace "Don Allah kiyi hkuri Ammah, ynxu nake son shiryawa in tafi wllh" bae jira cewarta ba ya mike ya nufi stairs, cikin mintunan da basu wuce goma ba ya sakko sanye da kananun kaya yana rike da makullin mota, cikin falon ya karasa yana kallon Ammah yace "Xan tafi Ammah" ta d'an sake fuska tace "Toh Allah ya tsare, kuma saura ka je masu empty handed, don nasan ba kai ya isheka ba" murmushin karfin hali yyi ya fita daga falon, parkin space ya nufa ya dauki motar da xae dauka ya bar gidan rae ba ddi. A waje ya bar motarsa ya fito ya shiga gidan, har xae danna bell ya fasa ya murda kofar a hnkli ya ji sa a bude, turawa yyi ya shiga falon da sallama, bbu kowa falon sae kamshi me ddi dake tashi da sanyin Ac, da alama duk yaran gidan sun tafi makaranta, ya karasa cikin falon ya xauna kan kujera, motsin da yake ji a kitchen ya sa shi sanin da mutum, ba a dau lkci ba ta fito rike da bowl din fruit salad da alamar lkcn ta hada ganin ynda taje jujjuya shi, sanye take da d'an mini skirt da top, ta bar gashinta in a messy bun s, cak ta tsaya tana kallonsa gabanta yyi mugun faduwa, shima kallonta yake daga sama xuwa k'asa, mikewa ta ga yyi, bata tsaya wani tunani ba ta nufi sama da gudu, yyi kwafa ya koma ya xauna, ya kusa awa daya xaune falon masu aikin gidan sae kai komansu sake bae ce su kira masa kowa ba, Anty ce ta sakko don shiga kitchen ta daura girkin rana da masu aiki ganin sha biyu ya kusa, da mamaki take kallonsa tace "A'a Abuturrab, yaushe ka xo" ya sunkuyar da kai yace "Ban jima ba Anty, ina yini" tace "Lfya lau, maimakon ka aika su fa'ixa su kira mu" murmushi kawae yyi bae ce komae ba, Anty ta nufi kitchen fa'ixa na biye da ita a baya, sae da suka shiga kitchen din snn tace "Tafi ki kira Batuul" juyawa tayi ta fita daga kitchen din. Batuul na kwance dakin Anty sae dae ban da faduwa bbu abinda xuciyarta ke yi, da ta tuna maganganun baba sae ta ji hawaye ya sakko mata, ynxu shknn hka tana ji tana gani xa a aura mata Ya Abuu, fa'ixa ce tayi knocking, ta share hawayen fuskarta tayi mata ixinin shigowa, fa'ixa ta ba ta sakon Anty snn ta fita, mikewa xaune tayi jiki a sanyaye.
💖💝BATUUL💖💝






38






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Jiki a sanyaye ta mik'e ta fito daga ďakin ta sakko downstairs, ganinshi zaune a palo yasa ta jin daďin kimonon da ta ďaura kan kayan dake jikinta, ďauke kanta tayi kamar bata ganshi ba tayi hanyan kitchen, da ido ya bita har ta shige tukunna ya ďauke idonshi daga wajen, tana shiga tace "Na'am Aunty, gani", tray da aka cika da snacks iri iri sai drinks da ruwa Aunty ta nuna mata tace mata "ďauki ki kaiwa Abuu", da sauri ta ďago zuciyanta sai faďuwa yake tana kallon Aunty dake ta aikinta tace "Aunty ni kuma", ba tareda da ta juyo ta kalleta ba tace "ehhh ďauki ki kai mishi tun ďazu yake zaune ban sani ba kuma babu wanda ya faďa min", zuciyanta duk babu daďi har idonta ya fara hawaye ta matsa gaban Island ďin ta kinkimi trayn tayi waje, tunda ta fito yake kallonta har ta iso palon, ďan nesa dashi ta ajiye mishi trayn fuskarta daure ta juya tayi tafiyarta, murmushi yyi ya ci gaba da kallon tv da yake, kitchen ďin ta koma ta tsaya bata cewa kowa komai ba ta hau kan deep freezer ta zauna, juyowa Aunty tayi zata cewa Janet ta mik'o mata abu a Fridge taga Batuul zaune kan Fridge, kallonta Aunty ta tsaya yi da mamaki tace "Batuul meye hakan, mey kika dawo yi kika barshi shi kaďai a palon", kanta ta girgiza tana kallon Aunty tace "Aunty toh ai abinci zai ci kuma ma nifa.....", bata k'arasa ba ganin kallon da Aunty keyi mata ta sauko tace "kiyi hak'uri zanje", ta juya jiki a sanyaye ta fita daga kitchen din, da k'yar take ďaga k'afanta har ta isa palon, yana nan inda ta barshi yana kallonn Discovery channel, sau ďaya ya ďaga kai ya kalleta ta sadda kai k'asa tana ta fidgeting yatsunta, ya ďauke kai yaci gaba da kallonshi har ta k'araso ta zauna can nesa dashi, lokaci lokaci yake satan kallonta ita ma hka, sai da programm ďin ya k'are tukunna ya dubeta, ta sadda kai k'asa tana wasa da yatsunta, sauk'a yayi daga kujeran ya janyo trayn yana kallonta murya can kasa yace "Baki faďa musu sak'ona ba knn har ynxu koh?" Kin cewa komae tayi kuma bata d'ago kanta ba, kallonta ya tsaya yi, ta dan sata kallonsa jin shirun yyi yawa, suka hada ido ta dauke kai da sauri, kallon hanyar kitchen yyi kafin yyi kwafa ya dauki glass cup ya bude lemon kwalin dake kan trayn da ta ajiye masa ya tsiyaya ya mayar ya rufe, ba tare da ya kalleta ba yana girgixa kai cikin sanyayyan muryarsa yace "Ni tausayin rayuwar ki da nake yasa ki ka ga ina maki kashedin kar ki yrda su makala min ke, yhu are too young to start facing challenges or rather I shud put it as problem, ni ina da matata kuma muna son junan mu like! har kika kuskura aka yi auren nn u will only end up shattering ur life, it's still not late for yhu...." Bata Bari ya kai karshe ba ta xamo kasa da sauri hawaye na bin kuncinta xuciyarta na tafasa tace "Kai wae me xae hanaka yin magana sae ni? Naga kai ma xaka iya gaya masu baka son auren ae koh?" Yyi wani murmushin da ta kasa fassara nufin shi yace "Ni baxan iya yi ma iyayena musu ba, ina ganin darajan su shi yasa kika ga har ynxu ban musa masu ba" wani mugun kallo ta shiga yi masa har lkcn tana hawaye ssae tace "Kai ne kasan darajar iyaye ni ban sani ba koh, toh kmr ynda baxa ka iya masu musu ba nima baxan iya ba, sae dae idan an makala maka ni ku kashe ni kai da matarka" tana kai wa nn ta mike tana kuka ssae ta haura sama da gudu, bin ta da kallo yyi yana murmushi, kafin ya fara shan drink din hannunsa, cake kawae ya dan ci ya mike yace ma Janet da ta fito daga kitchen ta ce ma Anty xae koma, fitowa Anty tayi bayan Janet ta bata sakon shi, tayi Mamakin rashin ganin Batuul a falon sae dae bata nuna ba tace "Har xaka tafi Abuturrab" Yace "Eh Anty, it's almost time for sallat ne" tace "Toh shknn, Allah ya tsare" fita yyi daga falon, ita kuma ta nufi sama don xuwa jin dalilin kin jin maganarta da Batuul tayi rai a bace, dakinta ta sameta kwance tana kuka har da sheshsheka, Anty ta tsaya daga bakin kofa tana kallonta tace "Meye hkn Batuul?" Mikewa xaune tayi da sauri ta kuma fashewa da kuka tace "Don Allah Anty ku rufa min asiri a fasa auren nn wllh bana son ya Abuu shi ma baya sona ..." Harara Anty ta galla mata tace "Wnn kuma sae ki jira idan babanku ya dawo ki sanar da shi" tana kai wa nn ga juya ta fice daga dakin.





Aunty na shigowa daki taji wayanta na ringing, kamin tayi picking taga har ya katse, ďauka tayi ta duba taga wa ya k'ira, missed calls biyu ta gani duk Ammah ce ta k'ira, zama tayi daga bakin gado zata k'ira kenan wayan ya fara ringing, Ammah ďince ke k'ira, ďagawa tayi tare da yi mata sallama, bayan sun gaisa Ammah ke tambayan Aunty "Maryam ya shirye shirye", murmushi Aunty tace "Alhamdulillah Ammah", ita har yanxu mamaki take na zata aurar da Batuul nan da y'an kwanaki, Ammah ce ta katse mata tunani da cewa "dama kayan Batuul ne nakeso a tambayar min ita inda akwai abunda take buk'ata dan Aliyu ya tambayeta tace ita bata son komai, toh ni ba yarda nayi dashi ba shine nakeso a bincika min sannan gyaran jiki zan turo a kawota gida sai ayi mata duk abinda ya kamata", shiru Aunty tayi har sai da Ammah ta kai aya tukunna tayi ajiyan zuciya tace "Toh Ammah zan tambaya miki ita, sai dai gyaran kamar zai fi tayi a gida nake gani ba sai taje can ďinba ai hidima zaiyi yawa, har nayi magana mai gyara gobe zata zo daga Ndjamena", cewa Amma tayi "toh shikenan hakanma yayi", da haka suka gama wayan, zaman tunani Aunty ta yi dan ita bata da wani shiri ma da zatayi na bikin, ko y'an uwanta ma bata faďa musu, waya ta sake ďauka tana k'iransu ďaya bayan ďaya duk ta sanar dasu auren Batuul, sai mamaki sukeyi ganin abun yazo da wuri.





Bayan Abuturrab ya koma gida da daddare Abui ya k'irashi har siďe ďinshi, daga palo ya tarar dashi kishigiďe yana kallon News, da sallama ya shiga ya zauna k'asa sannan ya gaidashi, gyaran murya yayi sannan ya k'ira sunanshi, "Aliyu", a hankali ya ďago dan gaba daya jinshi yayi wani iri dan Abui baya k'iran shi da sunanshi, yace "Aliyu na nema maka auren Batuul bawai dan na isa inyi maka abinda nakeso ba, bawai kuma dan bana sonka ba sai dan inason ci gabanka, yarinyar nan amana zan baka, ba iyayenta kaďai bane suka baka amanarta, har ni amananta zan baka, ka rik'eta kamar yadda zata zauna a gun iyayenta, in ka cuceta toh ka cuci amanar mu, yarinyace ita sannan mace, she is so naive and weak sai kayi hak'uri da ita, sannan bawai dan an haďaka da ita ka fifita matarka da kakeso kanta ba, kayi k'ok'arin adalci tsakaninsu sai kaga Allah yasa komai yazo maka da sauk'i, Aliyu ban yadda da saki ko yaji a tsarin zaman aurenka inba maishi ya sab'awa shari'a ba da bama fatan faruwanshi, ka kula da ita kamar yadda zaka kula da Farida, bana son ka zama silar rugujewar abotan da yake kulle tun kamin zuwanka duniya, kaji tsoron Allah a duk inda ka tsinci kanka, In sha Allah aurenka da Batuul alheri ne", k'asa ďagowa yayi dan wani nauyi kanshi yayi mishi, ji yayi kamar abu aka ďaura mishi a kan, Abui ne ya sake k'iran sunanshi, da k'yar ya ďago ya iya cewa "Na'am Abui", wani chest box ya ďauko daga gefenshi ya mik'o mishi yace "ga wannan shine Sadakin Fatima, shi za a mik'awa Waliyyin Batuul as Sadaki, sannan a can zataci gaba da karatunta, kayi supporting ďinta in every way to the best of your ability tunda tana karatunta muka nema maka aurenta, Allah yayi muku albarka", wasu makullai guda biyu ya mika masa yace "wannan na motane bayan an ďaura muku aure sai ka bata, wannan kuma gidana na farko dake Mississipi street na bata shi halal", da sauri ya ďago ya kalli Abui da mamaki, shi ya rasa gane wane irin so suke yiwa Batuul dashi da Ammah, ko aurenshi na fari basuyi wannan abin haka ba, da k'yar ya iya buďe baki yace "In sha Allah Abui, zanyi yanda kace,", yace "yawwa, ka gama arranging gidan da zata zauna na nan da can ko kuma haďasu zakayi waje ďaya", kai ya gyaďa tareda cewa "Yeah a can dai tare zasu zauna amma a nan Asokoro nacewa Mum zata zauna", Abui yace hakan ma yayi kyau, Nasa Mustapha da Sadiq suyi duk necessary arrangement ďin ďaurin auren, Allah ya tabbatar muku da alheri ya taya ka riko, Allah yayi muku albarka", jiki a sanyaye ya mik'e yayi wa Abui sallama ya fita.





Har gida Abui yasa sukaje shida Baba da Uncle ďin Abutturab da yaji lbrn Abdallah ke neman sonta suka samu iyayen Abdallah suka bashi hak'uri, Basu nuna komai ba suka ce dama wani ai baya auren matar wani, dama can Allah yayi ba matarsa bace, suka musu add'uan Allah ya bawa Batuul da Abutturab zaman lafiya, kuma sukace zasu bawa Abdallah hak'uri su bashi baki, da haka sukayi musu godiya suka tafi.




Ranar asabar k'arfe goma aka ďaura auren Aliyu Ahmad Kyaree da Fatima Kashim Goni akan sadaki sisin gwal 60, a k'ofar gidan kakanta dake Goni Mukhtar street a Maiduguri, tana kwance ďakin Aunty babu abunda takeyi sai rawar sanyi, Yayya ce ta shigo tana cewa "Keh Batuul fito ai an ďaura, tashi daga kan gadon nan tun jiya kike kai, maza fito a ida miki kitson da kike ta gudu tun jiya", kan gado ta hau ta yaye mata bargon, hawaye ta gani idonta, sai rawar sanyi take, hannu tasa zata ďagota taji jikinta zafi, ba shiri ta janye hannunta, Farida ce ta turo k'ofan ta shigo janye da wani akwati, ganin Yayya kan gadon yasa ta tambayan mey ya faru, da gudu ta k'araso ganin yadda Batuul ďin take yasa ta fita a guje taje ta k'ira Aunty, a rikice Aunty ta shigo, da kanta tayi k'ok'arin ďago Batuul sannan ta nemi key ta mik'awa Farida tace suje dan su Ahmad na Maiduguri ďaurin aure kuma batasan ma ina driver ďinsu yake ba, mutanen dake gidan ne suka tashi ganin yanayin jikin Batuul suna tambayan mey ya faru, babu wanda ya iya basu amsa dan Yayya da kanta ma kuka take tana k'iran sunan Batuul ďin, ikon Allah ne kawai ya kaisu asibitin dan gaba ďayanta Faridan ta rikice, suna isa asibitin aka taso aka karb'i Batuul akayi emergency da ita, Yayya duk ta ishi mutane da kuka wiwi a asibitin, Anty kam xama tayi reception ta jinginar da kanta jikin kujera, da ganinta kasan hankalinta a tashe yake, farida ce tayi karfin halin kiransu Ammah ta sanar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login