Showing 51001 words to 54000 words out of 215266 words
abin shi, Batuul kam kin ďagowa tayi ta kalleshi bare tasan abinda yake, cikin nutsuwa ya shiga maimaita mata maganan ďazu ya kara da cewa "yhu beta pretend yhu are nt recovering, ki kuma gaya ma likita auren dole xa a maki, I bet he will find a solution" ko kadan Batuul bata san mey yake cewa ba dan ji tayi abincin da taci yana son dawo mata tsabar tashin xuciya, ranshi ne yayi mugun b'aci ganin ynda tayi banxa da shi tak'i cewa komai, a fusace ya tashi ranshi a haďe, cikin tsawa yace mata "keh kurma ce ina miki magana kin wani min shiru kina jina, are yhu stupid", ko ďagowa batayi ba bare ta nuna mishi tasan abinda yake faďi, ranshi ne ya daďa b'aci yace "Kehh!" k'ala bata ce mishi ba, jin amae na shirin taho mata yasa ta tuge drip ďin hannun ta ta yunk'ura xata sauka daga gadon yyi saurin rik'eta yana mata mugun kallo yace "ina zaki?", hawaye ne ya shiga zuba daga idonta tana girgiza mishi kai alaman ya saketa amma yaqi, sai ma daďa rik'eta da yayi da k'arfi don mamaki reaction din nata ya bashi to ko dae ba ita kadae take ba, bai ankara ba kawai yaji ta kwararo mishi amai a jiki.
Aunty na komawa gida tasa aka kawo mata Aabid dake wajen Fa'izah ta bashi abinci, dan rabonta dashi tun jiya da Batuul ta zama unconscious, tana gama bashi ta mik'ashi ta shiga yin wanka, fitowanta kenan daga toilet taga Baba zaune akan gado, har ta ďan tsorata, ganin shine ta k'arasa fitowa daga toilet ďin, dubanshi tayi taga ita yake bi da ido, ce mishi kawai tayi "Uncle sannu da zuwa", snn tayi gaban mirror, kwaso mayukan da zata shafa tayi ta dawo bakin gadon itama ta zauna, Kallonta yayi yadda takeyin abu kamar bata san yana ďakin ba, hannunta ya rik'o tare da cewa "Maryam", bata ďago ta kalleshi ba tace "Na'am", yace "ya jikin Batuul ďin, waye a wajenta", k'ok'arin maida hawayen dake shirin zubo mata tayi a hankali tace "Abu na wajenta, wanka nazo inyi in kai mata kayan da zata canja itama", matsowa yayi kusa da Aunty ya jawota jikinshi, hawayen da take ta k'ok'arin maidawa ne ya shiga zubowa, kuka sosai ta shiga yi mishi, patting bayanta ya shiga yi , bai hanata ba har sai da ta ďan tsagaita dan kanta tukunna ya ďago tareda da k'iran sunanta, ajiyar zuciya tayi tace "ina jinka", yace "Maryam yanxu akan nace zanyi wa Batuul aure shine kika bi kika ďagawa kanki hankali?" yayi tambayar yana kallonta, ganin tak'i magana sai hawayen dake zuba daga idanunta yasa yace "auren nan da zatayi kamata yayi kifi kowa murna, wannan yaron ďanki ne, kinfi kowa sanin waye shi, ke da kanki kinsan babu wanda Batuul zata aura hankalinmu ya kwanta da yafi Aliyu, da bakin ki kin yabi nutsuwarshi, toh sai yanxu dan zai auri y'arki shine kike qi, wani hali garesa da har baki son ba shi 'yar ki? Naga dae auren nan ko ba yanxu ba dole ta yishi, toh meye amfanin a barshi nan gaban bayan yin hakan shine gatan da zamu iya yi mata, kuma shine rufin asirinta da namu baki ďaya, inma karatunta kikeji, da kaina zan sa a nemo mata admission a can inda zatayi auren, babu abinda zai tauye mata karatun ta, kiyi hak'uri kiyi mata addu'a Allah ya bata zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk inda zata tsinci kanta", jikinta ne yayi sanyi har yanxu hawayen na ci gaba da zubowa ta shiga gogewa cikin sheshek'a tace "Uncle Batuul k'arama ce fa, batasan meye aure ba bare abinda ke cikinshi, kuma fa mai mata zaku aura mata, abin ai zai yi mata yawa, kai da kanka kasan yadda Batuul ke da rauni, haka zataje a cutar da ita tunda ita ba wani wayo gareta ba", murmushi yayi tareda ďagota yace "yanxu naji dalilinki na k'in auren, bakiso y'arki ta auri mai mata saboda kema ke kaďaice gidanki ko, nima ďin ai zan k'ara", da sauri ta ďago tana kallonshi ya sake jawota jikinshi yana murmushi yace " Be optimistic Maryam, in kika nuna tsoron kishiya y'ar taki kuma tayi yaya, addu'a zakiyi musu Allah ya haďa kansu ya basu zaman lafiya, shi kuma Allah ya bashi ikon rik'esu da amana, sannan Batuul fa University take, tana second year ďinta, kinga ba yarinya bace, she is matured enough, she can decide what is wrong and right, tasan abinda zai cutar da ita da wanda zai amfaneta, mubita da Addu'a Allah yasa hakan ne mafi alkhairi", ya faďa yana goge mata hawayenta, da haka Baba ya rarrashi Aunty har ta hak'ura da zancen auren, tace Allah sa hkn shine mafi alkhairi.
Su Ammah na isa gida tayi summoning chefs guda biyu, mace ďaya dattijuwa sai ďayar budurwa, order ta shiga basu na abinda takeso a dafawa Batuul kuma kar su ďau lokaci, waya ta ďauka ta k'ira Farida data haura sama, ba jimawa ta sauk'o, Ammah tace mata "je ki ďauko min computer yanxu kizo kimin ordering wasu abubuwa, babu b'ata lokaci Farida ta haura sama bata jima ta sauk'o rik'e da Macbook ďinta ta ďaurashi kan table ďin dake gaban Ammah sannan ta samu waje daga k'asa wajen k'afan Ammah ta zauna ta buďe system ďin tana k'ok'arin jonawa da internet, sai da ta gama taga yayi connecting to internet ta ďago tace "Ammah mey zakiyi ordering, Jumia za a shiga ko konga ko kuma universal shopping zakiyi? ta dubi Ammah tana dariya, zama Ammah ta gyara tace mata kayan lefen Abu nakeson haďawa, lokaci ya k'ure bazan samu aje a haďo kayan ba, shiyasa zanyi ordering komai", da sauri farida ta kalleta tace "Ammah wai auren nan dagaske kukeyi sai anyi, rashin lafiyan nan mafa da take nasan lbrn da taji ne ya sata" harara Ammah ta maka mata tace "sannun gyatuma, ai fimu son Batuul ďin kikayi, in baza kiyi abinda na saki ba tashi ki bani waje in Sadiq yazo anjima in sashi yayi min, xancen banxa kai", jiki a sanyaye tace "zanyi Ammah,mey za a duba miki yanxu, tace "customised designer akwatuna nakeso kimin order, wanda babu wani da za a sake yiwa irinshi sai ita", murmushi Farida tayi ta shiga surfing sai gashi ba b'ata lokaci tace "Ammah gasu nan da hotunansu, wai akwai na Macs n spencer, sai D&G, LV, Mandarina Duck, Versace, paclane, cartier, ralph Lauren da BOSS, Ammah suna da yawa mafa", sai da Ammah ta karb'i Laptop ďin ta ga pictures ďin tace "ki zab'i ten best kiyimin ordern su, kije credit card ďina yana kan shelf a ďakina ki dawo ki gama", Farida na fita Ammah ta ďau waya ta k'ira Aunty Amna dake Paris, sai da ya kusa katsewa ta ďauka, Ammah ce tace mata "keh kullum sai waya ya kusa katsewa kike ďauka, watarana har ya katse ma ba a samunki", tace "Ammah wayan ne tana hannunsu Nawwal basa barina dashi, yanxu ma ita ta kawo min a guje", Ammah tace "toh yanxu duk bama wannan ba, turaruka nakeso ki siya ki turomin da English Golds, Diamonds, Inner wears, vanity sets sai English wears, sai perfumes, shoes, da nighties sai bags" da sauri Aunty Amna tace "Ammah ba dai auren Sadiq bane ya tashi ban sani ba, yaushe za ayi, wace ma matar", ta tambaya with so much excitement sounding vry surprised, Ammah tace "A'ah ba shi bane", Aunty Amna tace "toh waye za a siyawa kayan nan haka da naji kaman lefe", ta faďa excitement ďinta na komawa ciki jin ba Sadiq ne zaiyi aure ba, cewa Ammah tayi "Aliyu ne zai k'ara aure", da mamaki Aunty Amna tace "aure kuma Ammah, yaushe yyi aure har yake son kara wani, wace matar da zai aura ďin, kardai Abu ya zama mai son aure aure fa", cewa Ammah tayi "Amna auren Aliyu na farko ba amfani ne dashi ba", tas Ammah ta gama gayawa Aunty Amna yadda auren Abutturab ďin na farko yake da dalilin da yasa take son ya k'ara auren, jiki a sanyaye jin abunda Ammah ta faďa mata tace "Ammah ni inace ma ni kaďai ya share baya nema, ashe har gidan ma hakane, toh Allah ya rufa asiri, wacece matar da xae auran yanxu", Ammah tace "Batuul", da sauri Aunty Amna ta karb'e tace "Batuul dai, Batuul ďaya da na sani?", Ammah tace "k'warai kuwa ita", guďa Aunty Amna ta sa tace "Ammah dama yarinyar nan nada hankali, sosai nakeson yarinyar tana birgeni, Toh Allah ya tabbatar da alheri, yaushe ne bikin, idan yara na hutu sai muzo kawai gaba daya" Ammah tace "ai next week kenan ďaurin auren, biki ko daga baya ne sai ayi", da mamaki Aunty Amna tace "Laah Amma, everything so fast, toh shikenan, zan duba sauran, amma Ammah perfumes ďin bazai yiwu su biyo plane ba, kuma in za ayi shipping zasuyi taking time, so akwai wani abokin Babansu Nawal yana da perfume shop a Aminu Kano crescent, yayi sabon order recently, so kawai zan mishi magana ya kawo har gida, inma container zaki duba, that will be better sai ku zab'a mata, amma sauran yanxu zan shiga in dudduba", Ammah tace "toh shikenan Amnah, zan turo miki kuďin sai kiyi siyayyan, yanxu zansa Farida ta turo miki sizes da details ďinta tunda k'awartace tasan komai", da haka sukayi sallama, suna gamawa ta shiga k'iran mai gold ďinta dake Dubai, yana ďagawa shima ta bashi order ďin Gold har na wajen 50 mil zai turo mata samples in ta zab'i waďanda take so sai a sakosu a jirgi a turo, shima da haka suka rabu, Farida ganin Ammah dagaske take kuma tasan kayan da k'awatar tafi so tace "Ammah a saka mata abaya a ciki, tana sonsu sosai", Ammah tace sai ki dubo mata suma online shima ki mata ordering ko set 30 ne", sai da ta tabbata ta gama order komai har atampopi daga London tasa aka turo mata su sai laces da lappayu daga switzerland, sai da tabbata ta gama tukunna ta tashi taje tayi sallah.
Har ta gama aman bai saketa ba yana nan rik'e da ita duk ta wanke su gaba daya, murya can kasa yace " Srry!" Kkrin sauka ta shiga yi yaki sakinta, a hka wata nurse ta shigo ta samesu, da sauri ta karaso bakin gadon tana cewa "Wat happened?" Sae a snn Abuturrab ya sake ta, nurse din ta shiga yi mata sannu, shi kam unbutton din shirt din jikinsa ya shiga yi ya nufi toilet, nurse din ta shiga cire mata rigar jikinta ganin tana da vest a ciki, da sauri ta rike rigar taki barin ta cire mata, nurse din tace "Haba! you've messed the blouse, ki cire sae in baki wani abun ki lulluba da shi kafin a kawo maki kaya" bbu ynda Batuul ta iya hka nurse din ta taimaka mata ta cire rigar jikinta, ta sakko daga kan gadon, nurse din tace bari ta kawo mata wani abu ta rufe jikinta, Cleaners ta fara kira su je su gyara wajen su canxa bedsheet, Batuul na tsaye duk ta kagu nurse din ta dawo ta rufe jikinta kafin ya fito, ae ko sae gashi ya fito da singlet rike da shirt dinsa da ya wanke, suna hada ido ta juya masa baya da sauri ta ji kmr ta nutse wajen, dai dai nn nurse din ta dawo rike da hijab cleaners biyu na biye da ita, daya rike da xanin gado daya kuma na rike da bucket da mopper sae Freshner, da sauri ta karasa ta karbe hijab din tasa, ficewa yyi daga ward din bayan ya dauki makullin motarsa da wayarsa, ko minti biyar bae yi da fita ba Anty ta shigo rike da kayan Batuul a leda.
Ammah ta bi sa da kallo bayan ta amsa gaisuwarsa ganin ya nufi stairs tace "Meye hkn Abuu?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Amai tayi min" daga hka ya haura sama, farida ta saka dariya sanin ynda Amai ke bala'in irritating yayan nata sae gashi an masa a jiki, Ammah tace "Allah sarki, Allah dae ya bata lfya". Da daddare yana kwance kiran Ajiddeh ya shigo wayarsa, ya dde yana kallon wayar kafin ya d'aga ganin ya kusa katsewa.
💖💝BATUUL💖💝
36
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Yana ďaukan wayan ya hau ta da bala'i, "wai ba nace miki zaki iya tafiyar ki bane, wat are yhu still waiting for, in kuma ke da amaryar za a kai sai inji", kashe murya tayi cikin salo tace mishi "Babe na wuce fa tun ranan da kace min in koma, naga ko sau ďaya baka nemeni ba shiyasa na k'iraka yanxu tunda ni ina sonka ya na iya da halinka", kallon screen din wayar yyi, sae a snn ya lura da international Number ma ta kirasa, jin yayi shiru bai ce mata komai bane yasa taci gaba da cewa "Babe am missing you, wai yaushe zaka dawo ne, am so lonely without you here", d'an ajiyar xuciya ya sauke yace "soon, i gat things to do over hear, i will be back immediately when am done dear", ssae taji ddin abinda yace mata, cikin muryar shagwaba tace "Aii baby, i will be waiting, take care of yourself, i will also do that for you, bari in barka ka huta", da haka ta katse k'iran tayi wani murmushi a ranta tace zaka shigo hannu ne vry soon, baza ma ka samu k'afar zuwa Nigeria bama nan gaba bare har kaje kaqi dawowa har ka mance ni na kwanaki, wani irin dariya ta saki da ta tuna irin tanadin da takeyi a kanshi, shi kam lumshe ido yayi bayan sun gama wayan, aman da Batuul tayi mishi ne ďazu scene ďin ke dawo mishi kamar yanxu abin ke faruwa da yadda yaji jikinta yayi zafi lokacin da ya rik'eta, buďe idanunshi yayi ya mik'e ya nufi toilet yin alwalan sallar Isha don bai ma jin yau zai iya fita masallaci, yana fitowa daga toilet ďin Farida ta turo k'ofar ďakin, harara ya watsa mata yace "sallama ne baki iya ba ko knocking da zaki shigo min ďaki kai tsaye", dariyan dake cikinta ta mayar dan tun lokacin da taji Batuul tayi mishi amai da ta tuna take k'yalk'yalar dariya, tasan halinshi na k'in amai, maida dariyar tayi da sauri ganin yana k'ok'arin tada sallah tayi maza tace "Yaa Abu", bai amsa bama bare ya juyo ya dubeta, sake k'iran sunanshi tayi tace "Yaa Abu", tayi shiru ba tare da tace mishi wani abun kuma ba, wani mugun kallo ya jefeta dashi yace mata "fita min a ďaki", da sauri ta juya zata fita, ta tsaya daga wajen k'ofa ta lek'o kanta tace "Ammah ke nemanka fa", tana kaiwa nan ta fice da sauri tana dariya, sai da ya idar da sallah tukunna ya fito, a ďakinta ya tarar da ita Farida na daga gefenta, harara ya sakar mata ganin ta kafa mishi ido, daga gefe ya zauna yace "Ammah gani", dubanshi tayi tace "sae yanxu kayi niyyan zuwa kenan, toh abinci zaka kaiwa Batuul a asibiti, maza kuje tun ďazu aka gama na tura a k'ira ka baka ga daman xuwa ba", ido ya rintse tun da yaji inda zashi har sai da yaji tayi shiru tukunna ya buďe yana kallonta yace "Ammah ba driver na nn ba, wllh kai na sarawa yakeyi, ko Sadiq sai ya kaita in ma drivern bae nn kinji Ammah na", Ammah tace "bakaji inda nace zaka bane, in kaje kace su baka magani a can ďin, tashi kaje kar ku b'ata lokaci", mik'ewa yayi jiki a sanyaye ya koma ďauko key ďin mota, shi baisan mesa Ammah ke yi masa hka kan yarinyar nan ba, k'wafa yayi tunawa da yayi da aman da ta mishi daxu ya ďau key ya fito, a wajen parking ya tarar da Farida da masu aikinsu su biyu rik'e da basket ďin abinci, daga jikin makullin ya buďe musu k'ofa suka saka kayan daga baya shi kuma ya shige gaba hka ma Farida, sai harararta yake, itadai bata ce mishi komai ba har suka fita gidan, k'ira'ar Shuraim kadae ke tashi a motar.
Bayan nurse da cleaners ďin sun fita Aunty ta taimaka mata tayi wanka ta saka kayanta mara nauyi da ta kawo mata, tea Aunty ta haďa mata tasha ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa, gyara mata kwanciyanta Aunty tayi ta gyara mata bargon sannan ta jawo kujera ta zauna gaban gadon ta zubawa y'ar tata ido tana tausayin halin da zata shiga, turo k'ofar ďakin akayi, Yayya ta shigo Ahmad a bayanta, ganin waďanda suka shigo ďakin yasa Aunty ta ďauke dubanta daga kallon k'ofar, k'arasawa cikin ďakin sukayi, daga gefen Batuul Ahmad ya tsaya zuciyarshi fal da tausayin y'ar uwarshi, rashin lafiyan kwana ďaya har ta rame, Aunty ya duba yace "Aunty yaushe sukace zasuyi discharging ďinta?", ya faďa yana ďan tab'a goshinta yaji temperature ta, Aunty tace "Yanxu doctor ya shigo ya duba ta, ta samu tayi amai, amma baice min yaushe zai sallametan ba", da jimami Ahmad ya sake cewa Aunty "Aunty wai mey ke damunta, meye doctor yace muku na damunta all of a sudden", caraf Yayya dake tsaye bakin window tana k'ok'arin ďaga labule kamar an sata ta karb'e maganan da cewa "mey ko zai sameta, daga na ce mata za a haďa aurenta da yaron nan yaron kirki Abutturab shine fa ta tada hankalinta har da rashin lafiya, ko xuga ta uwar tayi oho", jin abunda Yayya ke faďi ya dubi Aunty da mamaki yace "Aunty aure kuma, wai hakane dagaske?", "Au k'arya zanyi maka, toh tambayi uwar taka da bata k'arya sai ta faďa maka gaskiyan zancen, kuma ko nayi rantsuwa baxan yi kaffara va, ita ke daďa ingiza ta har aka