Showing 66001 words to 69000 words out of 215266 words

Chapter 23 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1757

ba haka bane, yanxu faďa mana muji inda matsala mu san yadda zamu b'ullowa matsalar mu magance ta" , tunda suke surutun su bata ce komai ba sai danna waya da take tayi , sai da ta gama ta ďago tana kaďa hannu tace "Mummy ai Aliyu sai abinda nace, tun farkon aurenmu da ya fara min masifa kullum ni k'azama ce, na faye son jiki, bbu abinda na iya, gashi da bak'in halin jaraba sam ba a zama ayi hira dashi , amma tun bayan nayi muku complain ďinnnan da kukace in turo kuďi , everything have been fine since then, kuma sam baya tambayan mutum mey zakayi da kuďi komi yawansu bayarwa yakeyi shiyasa bamu samu matsala ba, maganan da nakeyi muku yanxu haka Mummy tunda mukayi aure sau ďaya yaje gida, waya kam dama babu magana, ai na gaya muku wannan watan sun turo k'anwarshi tazo, itama ďin dai bata daďe ba Nasa ya maidata , wannan zuwan ma da zamuyi ban yadda mun zauna a gidanmu ba saboda Kar ma susan da zuwanmu " "Jainaba ce tace "ai hakan ma yayi daidai da kikayi, toh ya akayi da wancan abinda nace miki na abincin shi ne, wannan na naman, tunda cewa kikayi ba kya girki, ko kinyi bayaci" , dariya tasa tace "Jainaba kenan, ai in yasan wata baisan wata ba, shi yake dafawa kanshi abinci ko kuma ya siyo, toh watarana yakan ajiye na dare da safe yayi warming yaci, ni dama bana bi ta kanshi, kuma dama ba iya dafawa nayi ba, sai dai kullum in rik'a ordering don of recent ya sallami cook din gidan" , Mik'e wa tayi tana dariya tace "Mummy ,Jainaba, ku bari mu dawo daga dinner in mun nutsu zan faďa muku duk yadda ake ciki, ni sam ban maje naga Amarya ba, tunda aka saka ranan nan ya ďaga mun hankali wai sai nayiwa Ufa magana ayi bikin aurenta a gidannan saboda bata sn y'an uwan mijinta su rainata " , Mummy ce tace "ai da gaskiyarta, Ina zata yadda da raini, gara da ta bar gidansu tazo nan ďin ayi komai a gama, ko ba komai itama tana da y'an uwanta masu akwai " Da haka suka fita daga ďakin, Mummy da Jainaba suka tsaya daga falo Ajiddeh taje side ďin da Amarya da k'awayenta suke.

Babu abinda ke tashi a wajen nan sai sautin kiďa, Hall ne mai girma da aka yiwa ado sosai na gani na faďa dan da gani kasan yaci Naira, Tun daga mota Abutturab yake k'iran number Ajiddeh amma bata receiving, fitowa yayi daga cikin motan yayi heading cikin hall, mata ne tare da maza kowa yana displaying talent ďinshi na rawa, Ajiddeh ya hango daga cikin y'an rawa sai kaďa waist takeyi, ranshi ba K'aramin b'aci yayi ba ganinta cikin maza tana rawa ga wasu shegun kaya da ta saka duk bayan ta a buďe, ji yakeyi kamar yaje ya fincikota amma babu hali, waje yaje ya samu ya zauna daga gefe yana jiran lokacin da zata gama, sai da suka gama tik'a rawansu tukunna bayan Dj ya k'are suka bar filin rawar, tana juyowa idonta ya sauk'a kan Abutturab, haďe rai tayi kamar ba ita ke dariya ba yanxu, k'arasowa tayi inda yake zaune ta tsaya mishi a ka k'erere tana ďan karkaďa k'afa, ďagowa yayi ya dubeta tare da cewa mata "Babe har kun gama rawan ne? " wani Harara ta sakar mishi tace "Kai fa ka cika wulak'anci, tun ďazu muyi da kai zaka zo shine sai yanxu ka wani ďebo k'afa kazo, y'an uwana sai tambaya sukeyi ina kake, kowa yazo da mijin shi sai ni kaďai ce babu mijina, ni tun farkon nasan wulakantani kaso yi dama bada son ranka muka zo ba....." katse mata maganan yayi tareda kamo hannunta ya zauna da ita kan kujeran dake kallon nashi, magana ya fara yace "Babe c'mon, tun ďazu fa nake wajen nan ina k'iran wayanki baki ďauka, da na shigo kuma na ganki you guys were busy dancing" , a ranshi yana son yi mata maganan cewa ita matar aurece, bai kamata tana irin wannan shigar ba har tana Cuďanya da maza, amma bazai iya ba, kawar da zancen yayi yaci gaba da cewa "so bana so in dameki shiyasa na bari sai kin gama tukunna sai ki ......" bai k'arasa ba yaga ta warce hannunta daga rik'on da yayi mata ta bishi da harara ta juya daga wajen ta nufi tsakiyar hall ďin Jin an ambaci cewa y'an uwan Amarya suzo ayi hoto da ita, wani irin bak'in ciki yaji a ranshi wai shi Ajiddeh ke yiwa abubuwan nan da takeyi haka "toh meye ke damuna ne? " ya tambayi kanshi, inda tabi shima yabi da ido ya ganta ita da sauran y'an uwanta maza sun sata a tsakiya cameras nata haskasu sai washe baki takeyi yana cikin tunani yaji an da dafashi daga baya, a ďan firgice ya juya yaga ko waye, kanshi ne yaji yayi dammm tare da zaro ido ganin mutumin da yake expecting gani least a wajen, zagayowa yayi ya zauna daga ďayan kujeran murmushi ďauke a fuskanshi yace "Ashe kana gari, Well i can see you are surprised to see me here ko bro? , bai bashi ansan tambayan da yayi mishi ba sai ma jifanshi da yayi da nashi tambayan shima "What brought you here Sadiq? Mey kazo yi?" Shima bai bashi amsa ba sai ce mishi da yayi "Answer me first bro, ni na fara tambayanka kuma your question is irrelevant, yaushe ka shigo Nigeria, ko da shike dama ance mana kana shigowa mune dai bama ganin ka " ďagowa yayi da sauri ya dubi Sadiq Jin abinda Sadiq ďin yake faďi , cikin rashin Jin daďin abinda Sadiq ya faďa mishi yace "ance muku ina zuwa Nigeria? Su waye ke faďa muku cewar ina zuwa" murmushin takaici Sadiq ya saki yace "Allah sarki these doesn't matter now, Ni auren Abokina Muhsin nazo, shine angon, so banma jima da shigowa ba, but tunda na shigo na ganka wani xuciyar ke cemin ba kai bane, I thought ma gizo kake yimin ba kai bane cus I wasn't expecting you " , sai da yayi shiru tukunna Abutturab yace mishi "Ai Amaryar k'anwar Ajiddeh ce, so shine muka zo Dan kusan Ajiddeh ce tayi sponsoring biki saboda mamar yarinyar ai ta rasu" kai Sadiq ya kaďa yace "Ohhh , that's nice then, toh yau ďin zakaje gidane ko kuwa zaka koma ba tare da kaje ka gaida Ammah ba " jikinshi ne yaji ya daďa sanyi Jin an ambaci sunan Ammah, ba tare da ya yadda sun haďa ido da Sadiq ba yace "toh shikenan bari in faďawa Ajiddeh zamuje yanxu, k'ar inje kuma bata sani ba hankalinta ya tashi " , da tausayin ďan uwan shi a ranshi yace "gaskiya hakan ma yayi kyau, kaga kar tazo tana ta nema ai babu daďi" , yace "Ehhh shine yanxu zan k'irata, naga ma she is so busy yau ďinnan" , yaci gaba da dialling ďin number ta, da k'yar aka samu ta ďauki wayan bayan ya k'ira kamar sau bakwai , tana ďauka tace mishi "baby wai meye haka, baka ganin am busy ne ? Kasan fa ni nayi komai na auren nan kuma na daďe ban haďu da y'an uwana ba ai sai ka barni in huta, da ka k'ira kaji ban ďauka ba ae sai ka hak'ura, amma ka ta wani k'irana sai kace ladan a masallachi" , sai da ta gama ya kwantar da murya yace "sorry Babe, something came , zanje wajen su Ammah ne in duba su, ya daďe da na gansu, I will go briefly and come back " , batasan lokacin da ta mik'e daga zaunen da take ba, gumi ne taji gaba ďaya ya fara tsatsaffo mata, Ce mishi "Aliyu ba muyi haka dakai ba, mu da zamu koma gobe mey zakaje yi, toh ni dai bana son zuwanka, kuma baxa kaje ba " , samun kanshi yayi da katse wayarta, har sai da yayi mamakin kanshi shima, mik'e wa yayi ya cewa Sadiq "muje ko? " kallon mamaki yabi Abutturab dashi wai wannan shine yayanshi da yake takawa maza ma birki amma yau shine da kanshi mace ke mishi tsawa har yana ji a waya, ji yayi hawaye na son zubo mishi yayi maza ya maidasu yace "Yaa Abu muje" , ya shige gaba Abutturab na binshi daga baya,

Wani ihu ta saka tare da fashewa da kuka, hankalin su Mummy yayi kanta a tashe, tambayanta suka shiga yi lafiya take ta ihu haka amma tak'i magana, Yaa Zee ce tace mata " a k'ira miki mijin nakine ko wani abin ne ya sami mijinki", wani irin kallo ta Watso mata tace "Da wani abun ne ya same shi ai duk mai sauk'ine akan abinda yake shirin faruwa" taci gaba da kurma ihunta, su Mummy ganin tana Janyo hankalin mutane kansu tayi maza tasa su tafi da ita gida, har suka isa gida tana kuka suko sun sata gaba suna kallonta suna jiran Jin meye ke damunta, sai da tayi shiru tukunna tace " Mummy Aliyu ya tafi gidansu, duk k'ok'arina na kar yaje sai da yaje kuma gashi malamin nan sai da yace indai nayi mishi toh ko kar in yadda ya haďu da ďan gidansu ko ďaya in ba haka ba Babban Al'amarine zai biyo baya, Mummy ni ban san meye Al'amarin ba amma duk yadda akayi ba mai kyau bane, gashi kuma ya tafi, Mummy ya tafi na shiga uku, bige mata baki Mummy tayi tace "akan wannan abin kika ďagawa kanki hankali, mu inane bamu shiga, ai in yasan wata baisan wata ba, ki kwantar da hankalin ki ba gobe zaku koma ba, toh babu abunda zai sameku daga ke har shi ďin " a haka dai suka ci gaba da bata hak'uri da baki har suka samu tayi shiru amma ba Dan hankalinta ya kwanta ba, Dan gaba ďayansu basu san waye Aliyu ba, ita tasan yadda ta wahala a hannunshi farkon aurensu , tasan idan asirin nan ya karye toh nata ya k'are

Tafiya sukeyi babu wanda yace da wani komai, Abutturab ne ya ďago ya dubi Sadiq yace "Farida ma last month taje wajena ai, amma kai ko sau ďaya baka nemana ko? " wani siririn dariya Sadiq yayi, yasan yayanshi is feeling guilty of himself shiyasa baisanma mey zaice ba, Sadiq yace "No Yaa Abu, abubuwa ne sukayi min yawa, ga hidiman Ammah, Abui da kuma na wasu shiyasa, amma in kuka koma har can zanzo , In shaa Allah" , jikin Abu ne ya kuma yin sanyi yace "Allah ya yadda " a ranshi yana tunanin mey zai fara cewa su Ammah, sai yanxu yake sake ganin rashin kyautuwar abinda yayi, a haka suka isa gida suna hira jefi jefi, a k'ofar gida Sadiq ya tsai da motar tare da yiwa masu gadin horn, da sauri saurinsu suka taso suka buďe, ba K'aramin mamaki sukayi ba ganin Abutturab, da sauri suka faďaďa fara'arsu suna "Alhaji K'arami sannu da zuwa , an sha hanya to ya iyali , fitowa yayi daga motan ya mik'a musu hannu suka gaisa , sai murnan dawowanshi suke dan yana da kyauta sosai duk rashin dariyarsa, wucewa Sadiq yayi tukunna Abutturab yabi bayanshi, a hankali yasa kai cikin falon har wani faďuwa gabanshi yakeyi, Farida ce ta fito daga kitchen da tray a hannun ta, to abin ka da jini batasan lokacin data ajiye trayn ba tazo da gudu ta rungume shi ba, har da hawaye a idonta bayan ta sassauta rik'on da tayi mishi ta kalleshi tace "Yaa Abu ashe za kazo, Dan Allah kana zuwa gun mu kaji" Janyota ya sakeyi jikinshi yace zan rik'a zuwa kullum kinji Autan Abui" Dariya tasa ta goge guntun hawayen dake idonta tace "yawwa Yaa Abu, gidanmu babu daďi da baka nan, gaba ďaya abinda yayi mata da taje wajenshi last month ya rik'a tunawa, sae yaji bai kyauta ba, duk rashin shirin su da Farida amma cikin k'annenshi yafi sonta, haka itama tafi sonshi, masifanshi ne kawai bataso, juyawa tayi tace "bari in kira Ammah ya Abuu tana daki" k'asa cewa komae yyi sae bin ta da kallo da yyi, dai dai nn Ammah ta shiga sakkowa daga stairs.
💖💝BATUUL 💖💝






27






By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





K'arfe biyar suka sauk'o k'asa ita da Farida zatayi wa Ammah sallama ta wuce , a kitchen suka tarar da Ammah ita da wasu y'an aiki tana masu magana, ganin Batuul da shirin tafiya tace "Bitti ba dai tafiya bako, ko Baa Alai din yazo ne, in baizoba ki bari anjima ko Sadiq ne ya mayarda dake", murmushi Batuul tayi tare tareda da girgiza kai tace "Ammah da kaina nazo, kuma Aunty tace in dena zama a waje har six, shine nakeso in koma gida kamin shida " tace "toh shikenan yayi kyau bitti, yanxu driving din yayi kyau sosai ko" tace "Ehhh Ammah muna trying", tace yayi kyau toh, Allah ya taimaka,muje parlour bari in hau sama in dawo " haks suka koma daga parlour suna jiran Ammah , suna zaune ta sauk'o rike da Babban farin leda a hannun ta, a tare suka mik'e suka isketa, Batuul ta mik'awa ledan tace "gashi bitti, useki kinji, nagode sosai, ga wannan kinji nakine", gaba ďaya sai taji wani irin da yadda Ammah ke mata magana, hawayene ya taru a idonta, kamar tayi laifi haka ta rik'a ji', maza tayi ta maida hawayen dake shirin zubo mata ta karb'i ledan daga hannun Ammah, jiki a sanyaye tace "nagode Ammah" , "Babu komai Bitti, ki rik'a zuwa akai akai kinji, ki gaida Aunty in kin koma da sauran yaran kinji" kasa motsawa tayi daga wajen har sai da taga Ammah ta haura bene tukunna ta juya a sanyaye tayi waje dama Farida ta dade da fita, a cikin mota ta tarar da Farida zaune ta k'ure wak'ar Ed sheeran ta shape of you a motar tana ta rawa, sau uku tana k'iran sunanta bata ji ba, har sai da ta zauna tukunna tace "Dadin abin ke da Affan ďin duk halinku ďaya da ya wahala sosai " juya ido tayi tace "ai inma ba ďaya ba haka zai hak'ura dani, babu yadda ya iya" tana ďaga gira ta k'arashe maganan, Sai da Batuul ta tada mota tukunna tace "Alhamdulillahi ma da halin naku ya zamo ďaya", dariya Farida tasa ta fita a motan tace 'toh ni dai ban shiga school this week , sai next week, Yauwa I forgot to tell you, Guess? Ta tambayi Batuul tareda daga mata gira ďaya, "kinsan I always get it wrong when I guess, so just tell me, time is going" Farida tace "toh naji, Mrs, Yaa Massa is getting married, ďazu Ammah ke faďamin wai da na tafi, y'ar Sultan ďin Sokoto zai aura wai sunanta Rahama" sai da ta gama Batuul tace "Allah sarki Yaa Massa, ashe......" , bata gama faďan abinda zatace ba Farida ta katse ta "wani irin Allah sarki, ke da kika k'ishi kememe kice baki sonshi shine harda wani tausayinshi, shima ďin nei dai ya barki , ai da nice shi Allah straight away Baba zanje in samu, sai dai kawai kiji ance an ďaura miki aure, wai shi tunda baki sonshi zai hak'ura da azo ayi abinda za azo ana magana daga baya , ni haushi ma yake bani , he was very lenient on you ke kuma kikayi ta gwara shi ,muna nan dai muna jiran Jin wanda zaki aura, Kai Allah yasa ma Baba ya badake Sadaka tunda ke kowa bai yi miki ba" Dariya maganan ya bawa Batuul tace " toh muguwa haba dai sadaka, that is not happening , not with me, ni kinga tafiya zanyi before Aunty ta faramin waya" , dariya Farida ma tasa tace "zaki sanine bari mu gaji dake Kiga ikon Allah " Sai da tayi reverse tukunna ta cewa Farida "Dan Allah turomin number shi Yaa Massa inyi congratulating ďinshi dan tun lokacin da yake ta damuna nayi deleting sai kuma number shi ta Germany shi kuma bazai yi Amfani ba", juyawa Farida tayi tana komawa ciki tace "fadi gaskiya dai Dan yanxu yana da matarshi , Dariya sukayi a tare kowannensu na dariya Batuul tayi sallama da Farida ta koma gida.






Daidai ana k'iran magrib ta isa, A cikin gida da taje parking taga kamar motan ďazun nan ne pake, sanin babu yadda za ayi yazo gidansu kawai ta tab'e baki ta shige cikin gida, Aunty na alwala Batuul ta shigo da Sallama tace "Aunty na dawo ", Aunty tayi mata sannu da zuwa, ta juya zata koma ďakinta Aunty ta tsayar da ita ta hanyan cewa "in kin idar da Sallah kinada bako , ji tayi k'irjinta ya bada sauti Dam! Ita?, bako kuma? , toh shi waye ?, ita dai babu wanda yace mata zaizo wajen ta ko a y'an ajinsu , maza maza hankalinta ya tuna da motar dan ta gani pake , toh in shine bakon ni ina na sanshi ta ďan ja siririn tsaki, da sauri tace "Aunty ba wajena yazo ba, ni ban sanshi ba, "matsar min daga k'ofan toilet in wuce ni, waje na yazo tunda nice Batuul " marairaicewa tayi tana girgiza kai tace "Aunty dagaske fa ni ban sanshi ba ", bayan Aunty ta saka hijab zata tada Sallah

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login