Showing 207001 words to 210000 words out of 215266 words

Chapter 70 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1695

zata gudu ganinshi jingine bakin k'ofa yayi tucking hannunshi d'aya cikin aljihun wandonshi yana kallonta, da hanzari ya k'araso wajenta ya janyota jikinshi ya rungume, sosai ya matseta jikinshi sabida yanda ta tsorata, shi da kanshi saida ya tsorata ganin irin gudun da ta saka kamar wani abin zai sameta ita da cikin da ya bayyana a jikinta, a hankali ya dinga patting bayanta yana karanta mata ayatul kursiyu cikin kunne, a hankali ta dinga sauk'e ajiyar zuciya, muryarta na rawa kamar mai kuka tace "Amore you scared me", saida yaji ta nutsu snn ya rad'a mata a kunne "am sorry Glitter, I didn't mean, I just wanted surprising you", sake shigewa jikinshi tayi tace "You just did ai", dariya yayi tareda d'agota daga jikinshi "I just remembered, aikin mey kikeyi glitter?", ya tsareta da ido, sunkuyar da kai tayi tareda turo d'an bakinta, cikeda sanyin murya tace "Kagani ko wainar fulawa nake ta son inci kuma bansan ya zanyi ba, kai kuma baka nan shinefa na shiga kitchen ina dafawa, bama dayawa bane muje in nuna maka", tasan babu abinda zatayi ya b'ata mishi rai, koda zai b'aci kallonta na sashi manta komai, bare yanda take mishi magana yanzu, d'an k'aramin bakin nata ya kama yace "wayo zaki min ko, shine harda pouting min lips d'inki?" Da sauri ta girgiza mishi kai tana mirmushi tace "dagaske nake", ya mik'ar da ita shima ya mik'e yace "ba nace ki dinga bari zanyi miki ba, sai kin bawa babyna wahala?", juyowa tayi ta fuskanceshi ta tallabo fuskanshi da duka hannayenta biyu tayi pecking duka tace "ai kam bana so ka wahala, kuma fa ", ya sakar mata hararan  wasa yace "meye shi wainar fulawan da ya saki kin jin maganata?, muje in gani", raurau tayi da ido tace "Amore banqi jin maganan ka bafa?", ta fad'a tana tsaye inda take, juyawa yayi ya kamo hannunta yace "its been long I see these tears, bana son ganinsu yanzu ma", baki ta zumb'uro mishi tace "toh ka yadda ban qi jin maganan ka ba?" Ya had'e rai yace "Muje dai in gani", ya riqo hannunta suka k'arasa gaban stove d'in, yatsina fuska yayi yace "wannan Ne?", a hankali ta gyad'a mishi kai, stool ya janyo mata ta zauna akai snn ya ciri apron d'in dake rataye ya d'aura, cikin watanni ya koyi abubuwa da bai tab'a tunanin yinsu ba, sauran paste d'in da ya rage ya shiga soyawa a pan d'in, tana daga zaune tana kallonshi, tasan ko zata kwana tana cewa ya barta tayi da kanta ba yadda zai ba, a hankali ta bud'e baki tace "Amore", volume d'in stove d'in ya rage yana kallonta yana jiran jin mey zatace, kamar mai jin tsoro tace "Amore fushi kakeyi har yanxu ko?", gabanta ya dawo yana janyo d'aya stool d'in stool d'in ya zauan yana lakuce mata hanci yace "cute face d'innan naki zai bari inyi fushi dake ne?, ko nayi fushi idona na fad'awa d'an lips d'innan nake hucewa", kai ta girgiza mishi dan ita ba abinda take nufi ba kenan, amma tunda bai gane ba sai tace "koh nayi laifi baza ka min fad'a ba?", yace "zan miki fad'a but ban iya fushi dake, you are too cute da son da nake miki bazai barni in iya fushi dake ba, nasan in nayi fushi dake nima zan ji jiki,", tace "Yaa Abu itama kayi mata fad'a mana kaji, fushin nan da kake yi da ita ba tareda tasan makomarta ba yana wahalar da ita, Kayi hak'uri ka yafe mata, kayi mata fad'an amma kayi hak'uri ka janye fushin nan da kakeyi mata plsss", take far'ar dake fuskanshi ya b'ace, hannunta dake cikin nashi ya janye tareda mik'ewa zai bar wajen, da sauri ta riqo mishi hannu tana girgiza mishi kai idonta tab da hawaye, d'an siririn tsaki yaja yana girgiza mata kai dan bayason hawayen nan su zubi yace "Glitter I thought we were done with that, ba nace bana son zancen nan ba", tace "Allah ni har raina na yafe mata, wlhy son da take maka ya sata aikata abinda duk tayi, Amore tayi hak'uri sosai, batareda da ka sani ba kayi auren nan, mey kake so tayi?, she was angry, she was feeling betrayed, tunaninta duka kaci amanarta ne", wani irin rik'o da yayiwa hannunta saida ya tsorata ta, with stern masculine voice d'inshi yace "shine take so ta kashe min, akwai wani abu da yakeda hujjan kisa a duniya?, in kin mutu me zatacewa Allah?, because she was feeling betrayed sai ta nemi yin kisa?", kai kawai Batuul ke girgiza mishi tana hawaye, tana son ya fahimci kishi babu abinda baya sawa indai kana son maishi, ba kishi saida so, hab'arta ya d'ago yace "Look at me", a hankali ta d'ago idonta ta kalleshi, yace "goge hawayen", babu musu tasa hannu tana goge hawayen, hannu yasa yana goge mata sauran hawayen yace "This should be the last time we will talk about this kinaji?", a hankali ta kad'a mishi kai, yace "Look at me and talk", a hankali tace "toh, am sorry kaji?", ido ya lumshe ya bud'e yace "tashi muje kici wainar taki", ya d'agata ya sauk'ar kan kujera snn yayi mata plating wainar, Fridge ta bud'e ta ciro jug d'in zob'on da ta had'a, kallon jug d'in yayi snn ya kalleta yana langab'ar mata da kai, tayi murmushi tace "inasone fa insha, tun safe nake kwad'ayinshi", baice komai ba ya sa hannu ya karb'i Jug d'in daga hannunta, flask d'in dake ajiye kan island d'in yaga ta d'auka, ido ya wara yace "again?", this time ita ta langab'ar da kan, da sanyin murya tace "kunun kane nayi maka", kai kawai ya jinjina ya d'au flask d'inma, palo yaje ya baje mata komai snn ya koma ya d'auko cups d'in, ganin yanda ta baje tana cin wainar fulawan har dariya ta bashi, d'agowa tayi tana kallonshi da tsukakken bakinta da yaji ya dama, ruwa ya mik'o mata yana dariya yace "dole ne cin yajin?", bakinta ta sake tsukewa tace "yafi dad'i da yaji", zama yayi yana janye plate d'in gabanta yace "nidai kar a koyawa babyna cin haji", raurau tayi da ido tace "toh buh lemme have my plate back", kai ya girgiza mata yana juye yajin a d'aya plate d'in da babu komi, marairaicewa tayi tace "Da yajin fa yafi dad'i", kai ya girgiza mata yace "am not taking the risk, ga wannan na rage miki", ya mik'a mata plate d'in da d'an kad'an ciki, karb'a tayi ta zumb'uro mishi baki tana cin abinta, zama yayi yana shan kununshi bayan ya gama yace ta rakashi pool d'in dake bayan gidan, tare sukaje tana zaune ya shiga ya gama wankanshi dan ya hanata koda k'arasawa wajen bare ta shiga pool d'in, bayan sunyi sallahn magrib suka fita tare tafiya asibiti dan EDD d'inta ya kusa, snn akayi reffering d'insu asibitinsu na Nigeria dan Ammah tace Lallai Lallai su dawo tunda ta kusa haihuwa, a waje suka ci abincin dare snn ya biya dasu Trotters, waje ya samar mata ta zauna, da kanshi ya dinga zagayawa yana kwaso kayan baby da maternity clothes tunda ga kan coats, jumpers, leggings, shauls, towels, Baby bathing sets, craddles, ds duk saida ya tanada kuma duk designers, daga M&S sai Ck, duk in ya d'auko sai ya kawo mata ta gani tukunna kuma yawanci na mata yake kwasa ko kuma unisex, tun tana ganin yawansu tana cewa ya bari in ta haihu lafiya a siya sauran yana qi har tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido, da tayi mishi maganan yayi mata addu'a kawai, ba lallai ta haihu da rai ba, had'e rai kawai yakeyi yace mata shi tana dena fad'a, shiru kawai zatayi dan batason ranshi yana b'aci, sai wajen sha d'ayan dare ya gama siyayyan nashi yasa akayi packaging wasu aka tura Nigeria saura ya barsu a nan, kamar ba kud'i yake zubawa ba haka suka dawo gida, washegari ma da ddare suka sake fita ya sake kafa wata sabuwar siyayya, ana gobe zasu dawo Nigeria suna zaune parlour tana jikinshi yace "Glitter?", d'agowa tayi ta kalleshi yace "Kina da sunan da kike so a sawa Babyn?", kallonshi ta tsaya snn ta girgiza mishi kai a hankali tace "A ah, duk wanda ka saka ma zaimin", kitson da shi ya kama mata yake warwarewa yace "you sure?", kai ta kad'a mishi, a hankali ya sunkuya yayi pecking goshinta "I love you", murmushinta mai kyau tayi tace "I love you more", tara ya kashe musu wata ya taimaka mata suka haura sama, baccin su sukayi peacefully cikeda shak'uwa, washe gari suka shirya suka tafi Nigeria, babu yadda Abu baiyi Ammah ta barshi su sauka gidansu ba tace sam bata San zancen ba, a gidansu zata zauna, tun a waya yace "Ammah Al'ada nefa duka wannan, ya za a raba miji da matarsa bayan ba fad'in Allah bane, tun lokacin ta balbale shi da masifa, badan yaso ba suka sauk'a a gidan Ammah akan bayan kwana biyu zai kaita, ana gobe zai kaita gidan Aunty tana zaune kan gadon tana shan cream in chicken soup, shi kuma yana gaban desk top yace "Glitter yanxu kema yadda zakiyi a d'aukemin keh har tsawon wata da wani abu?, I can't even imagine a day without you, nasan in keh kika fad'awa Ammah zata yadda", murmushi tayi tace "Amore you know I will miss you more ko, with every passing second?, its a tradition, yanzu zaka ga ya wuce", pouting bakinshi yayi yace "Shikenan", ta bud'e baki kenan zatayi magana taji wani suka ta bayanta, ido ta rintse tana ambaton sunan Allah, plate d'in dake hannunta ta ajiye ta a hankali tana k'ok'arin mik'ar da k'afanta, lip d'inta na k'asa ta cije tana cewa "Yasalam", juyowa yayi ya kalleta, da hanzari ya sauk'o yana d'agata yace "Glitter mene, cikinki ne?", ido ta rintse tana riqe mishi hannu tace "Yaa Abu bayana", duk ya gama rikicewa yama rasa ya zaiyi, d'agota yayi yana yi mata sannu zai fita da ita, kamin su fita Ammah ta shigo d'akin kawowa Batuul kunu, da sauri ta ajiye abinda ke hannuta ta k'araso tana "Subhanallah, Bitti ciown ne?", Batuul da ta kasa magana Ammah ta k'araso ta riqe tace "Aliyu d'auko key, I think its delivery, duk ya gama rikicewa ya d'auko key snn ya ciccib'i Batuul dake ta cije lips sbd azabar zafi, a parking lot suka had'u da Farida ta dawo daga school tana parking mota, da gudu ta k'arasa wajensu tana tambayansu, ganin babu mai bata amsa ta koma motan ta bi bayansu, suna zuwa asibitin aka karb'e cikin gaggawa akayi Labour room da ita
[12/16, 12:15 AM] ‪+234 808 135 1434‬: 💖💝BATUUL💖💝




By Phartiemarhk





98









Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Binsu yayi a baya zuwa d'akin da aka shigar da Batuul d'in, daidai bakin k'ofa wata nurse tace "We are sorry Sir, but you can't get in", wani irin kallo ya jefeta dashi da yake mata nuni da bakida hankali ko, da sauri ta sauk'e idonta k'asa tana cewa "am sorry sir", hannu yasa ya matsar da ita gefe ya tura k'ofar shiga d'akin, kan gado ya tarar da Batuul kwance har an bata maternity wear, sun fito da duk wani abu da ake buk'ata, da sauri ya k'arasa gadon da take kwancen, ido kawai ta rintse tana ambaton sunan Allah dan yau hawayen ma nemanshi take ta rasa, dukda azabar da take sha hakan bai hanata jin d'umin hannunshi cikin nata ba, a wahalce ta bud'e idanunta ta sauk'e cikin nashi, ido ya lumshe ya bud'e, bayason ganin wannan yanayi da take ciki, a hankali tace "Yaa Abu Aunty", kamar wacce ta watsa ruwa haka sweat duk ya jik'ata, hannunta dake cikin nashi ya riqe ya kai bakinshi tareda kissing yace "You will be fine Babyna, we will make it together, am here kinji?", ido ta lumshe tana kad'a kai cikeda azaba tace "inaso inga Aunty, plss call her for me kaji Yaa Abu, inaso in ganta", ta fad'a tana sake cije leb'e, gaba d'aya ta gama rikitashi, shima so yake kawai yaga hawaye ya zubo mishi ko zaiji dad'i da wannan irin ciwon da yake jimata, daidai fuskarta ya sunkuyo yace "Glitter you will b okay, Aunty will be here anytime,Ammah zata fad'awa Aunty, am upright sure, she will b here shortly, sannu kinji?", daidai lokacin da doctor da nurses d'in suka k'araso cikin shirin aikinsu, ganin Abu zaune Doctor yasa yace "Good Afternoon Mr Kyaree, we are sorry but we need you to stay outside to carry out our work efficiently", fiyeda kallon da yayiwa Nurse d'in d'azu yayiwa Doctor dukda sabon dake tsakaninsu amma yau mantawa yayi da hakan, gaba d'aya ranshi ya gama b'aci, matarshi in such a pain maimakon yayi attending to her yake kawo masa shirmen banza wai ya fita, a fusace yace "Get yourself composed Doctor and attend to my wife, She is my wife, we are in this together, I ain't moving an inch from here", ya sake maimatawa sternly snn yace "And if anything happens to her?, am gonna shut d whole hospital down, you will all pay for it", yayi maganan idonshi na kad'awa, "Damn it, Doctorrr", ya fad'a kamar zai make doctor, ganin dagaske yake kuma zai b'ata musu lokaci yasa kawai suka fad'a aikinsu cikeda k'warewa, duk wani kuka na Batuul yau nemanshi tayi ta rasa, Addu'o'in da Abu keyi yana tofa mata duk wanda ta kama shi takeyi, da taji azaba lokacin take tuna Aunty, take zata fara Rabbir Ham huma kama rabbayani Sagira, duk wani motsi da Batuul zatayi har cikin ranshi Abu ke jinshi, sosai ya tausaya mata ganin irin wahalan da take sha, a lokacin ya sake ganin kima da daraja irin ta mata had'e da tausayinsu, in basu ba wazai iya enduring irin wannan ciwon, addu'a yayiwa duk wata mace wacce aka haifa da wacce ta haifa, a hankali ya fara tofa mata "wa tilka hujjatuna atainaha Ibraheema ata qaumihi, narfa'u darajatin man nasha, inna rabbaka hakeemun aleem", a zuci ta dunga maimaita aabinda taji yana fad'i, a hankali taji ciwon na raguwa, ba a cika one hour ba ta sumb'ulo y'ar Babynta k'arama mai kyau itama, Hamdala Abu yayi yana kai hannu zai tab'a Babyn Doctor yace Mishi "No pls, not now", yatsina fuska yayi ya janye hannunshi, tareda shi suka taimaka aka gyara aka kimtsa Batuul da Baby, bayan an fito da Babyn yana zaune bakin gadon da Batuul ke kwance yana mata sannu suka mik'o musu Babyn, da Bismillah yasa hannu ya karb'eta daga wajen nurse, gaba d'aya komai na jikinta farine, babu komai nata a waje sai d'an k'aramin face d'inta, wani irin k'auna da nutsuwa da baisan daga inda yake sauk'o mishi ba yakeji jin d'umin Babyn jikinshi, murmushi ne ya kufce Mishi ganin komai na fuskan Babyn irin nashi, lips d'inta ne Kad'ai irin na Batuul hatta heart shape d'in bottom lip d'in nata irin na Batuul ne, a hankali ya matso da Babyn kusa da Fuskan Batuul yace "Fatima our child, our Baby, kyautar da Allah yayi mana Fatima, look at her please, she is too cute for me", murmushi kawai Batuul tayi dan bata jin k'arfin jikin nata sosai, daidai kunnen Babyn ya sunkuya tareda k'ira mata Sallah, ya karanto "inni sammaituha (A'eesha) wa inni u'ixuha bika wa xurriyatiha minash shaaid'anir rajim" yayi mata addu'o'i sosai tareda yi mata Hud'uba da Suna A'eesha, Dabinon Ajwan da dama yana cikin kayansu yasa aka mik'o mishi da ruwan Zamzam ya tauna ya d'iga mata tareda ruwan Zamzam d'in, kamar wacce tasan abinda akeyi ta yatsina fuskarta tana lashe baki, dariya yayi ya sunkuya yayi kissing goshinta snn ya matsa jikin Batuul d'in yace "Glitter?", a hankali ta d'ago lumsassun idanunta ta dubeshi, yace "kin bani kyautar da duk duniya babu mai bani irinta, you have given me the best gift I would ever ask off, I will forever be grateful, Allah ya barmin keh Glitter kici gaba da bani wasu Babies d'in, just tell me anything you want, ko meye shi indai akwai shi a nan duniyan, I promise to get it for you, you have given me the best gift of life, I promise you, just ask me duk abinda kikeso zanyi miki shi, just tell me jinni", a hankali ta bud'e idanunta da suke a lumshe, kallonshi takeyi da murmudhi d'auke kan fuskarta tana tunanin abinda takeson cewan, tasan duk murna ne ya cikashi amma da wuya ta samu abinda takeson, a hankali ta bud'e baki tace "You Promise?", kallonta yayi for seconds kamin ya kad'a mata kai, zai yi magana doctors da nurses d'in suka zo za a canja mata d'aki, tana kwanace suka turata zuwa wani d'akin, badan ta saba da ireirensu ba da zatace d'aki ne kawai ba na asibiti sbd girma da kuma kyansu, saida Nurses d'in suka gama duk wani necessary abu da ya kamata suyi mata itada Babyn snn suka kwantar da Babyn gaban Batuul suka fita suna mata sannu, kallonsu yayi with so much adoration yana yiwa Allah godiya da kyautan nan da Allah yayi mishi, Batuul is one part of him da baya tunanin zai iya rayuwa babu ita, hannunshi yasa ya kamo na Batuul d'in yana d'an murzawa a hankali yace "Fatima you are the best thing that ever happened to me kinsan da haka ko?", a hankali ta kad'a mishi kai yaci "I know I love, ban san amfanin kud'ina ba if I can't give you abinda kike nema, komeye shi kike so indai bai sab'awa addini back just mention the anything, zanyi miki shi Glitter", ya fad'a yana sassauta muryarshi tareda sak'ale yatsunsu waje d'aya, a hankali ta bud'e baki tace "Yaa Abu ka dawo Ajiddeh gidanka, zamanta haka ya isa batareda sanin makomarta ba, banasone ka shiga hakkinta, na fad'a maka nikam na yafe mata wlhy, nobody is above mistake, kuma everything happens for a reason, maybe for us to realise each others worth, how much we mean to each other, Yaa Abu plssssss", ta k'arasa maganan tana lumshe ido , shi kad'ai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login