Showing 123001 words to 126000 words out of 215266 words
lafiya kuma kinason ganina, nasan in yaji haka zai bari, sai kiyi all things possible yadda bazai gane ba", da haka sukayi sallama akan zata k'irata duk yadda akayi, tashi tayi tana matsar k'walla yadda zatayi pretending wa Abu.
Batuul ta d'auko flask d'in fresh milk d'in kenan zata fito daga kitchen taga Ajiddeh na sauk'owa hankali tashe, duk gashin nan an baje shi, ae fa nan gabanta ya shiga faduwa ta k'asa karasawa dinning,
a tsorace take kallonta ganin yanayin da take, wani irin mugun kallo tabi Batuul dashi ganin irin kayan dake jikinta, har sai da tazo zata wuce ta dinning d'in a hankali Batuul tace "INA kwana", wani kallo ta watso mata tareda hararanta, tab'e baki Batuul tayi ta d'auke kanta, dama ita kirkin da Ajiddeh ke mata ba yadda tayi dashi ba, gara tana masifan da ta Saba kawae, tana dire flask d'in hannunta ta haura sama abinta da sauri.
Da wani irin kuka ta fad'a jikin Abutturab dake kwance kan sofa da remote hannunshi yana kallon TV, don yi yayi kamar bae san ta sakko falon ba da farko, a rikice ya d'agota ya shiga tambayanta lafiya, tana kuka kamar zata had'iyi rai tace "Mummy", tashi yayi yana kallonta yace "What happened to her", cikin sheshek'a kamar dagaske ta kasa ce mishi komai, a d'an tsawace ya d'ago fuskarta yace "talk to me Ajiddeh, what happened to Mum", a sanyaye tace mishi "Yanzu Yaa Zee ta k'irani, wai Mummy ba lafiya kuma tana son ganina", ajiyar zuciya ya sauk'e ya jawota jikinshi ya rungume yace "shhhhh, its okay , she will be alright, okay?, gobe zamuje gida", da hanzari ta d'ago tana kallonshi tace "baby bazan iya ba, inason inje inganta yau, bazan Iya ba", ta k'arashe maganar da kuka sosai, tashi yayi ya kamata suka haura sama, sai da ya shiga d'akin ya zaunar da ita kan gado yace mata tashi ki shirya kayan da zakiyi amfani dashi, yanzu zamuje muyi booking flight ko na evening ne sai mu bi", rinannun idanuwanta ta d'ago tana tana kallonshi tace "Baby ai kana da aiki, ba komai ba sai kaje ba, you should stay back ka kula da abubuwan da kakeyi, In sha Allah she will b fine", haka tayi ta insisting har sai da ta samu tayi convincing d'inshi ya fasa bin ta, bakwai da arba'in da biyar daidai suka sauk'o shida Ajiddeh tana riqe da trolley d'inta a hannu, Batuul na palo suka sauk'o tare, mik'ewa tayi tsaye har suka k'araso inda take, Ajiddeh sai hararta takeyi ta gefen ido, sai lokacin ma ya tuna da ita, kud'i ya ciro daga aljihunshi ya mik'a mata sannan yace "David ya kaiki school", da haka suka fita suka barta nan tsaye ko wayanma bai samu ya bata ba yau. Haka kawae taji ranta ya baci ta bi bayan Ajiddeh da harara, suna fita ta ja tsaki ta haura sama don xuwa dauko jakarta ta bar gidan ita ma.
[8/22, 14:50] Umar Dalha: ππBATUULππ
60
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
A bakin mota ta tarar da David tsaye yana jiranta, hannu tasa ta bud'e motan ta fad'a sannan shima ya shiga, sau biyu David na maimaita gaisuwarshi, sai a na ukun ta amsa mishi, zuciyanta ne taji yana mata xafi ta rasa dalili, ta ja tsaki yafi sau biyar zamanta cikin motan, hawaye ne mai d'umi ya shiga sirarowa daga idonta, hannu tasa ta shafo hawayen ta tsaya tana kallo da mamaki, kifa kanta tayi tsakanin cinyoyinta ta fara kukan da batasan dalilinshi ba, daga sama taji David na fad'in "We ve arrived", a hankali ta d'ago kanta ta k'arewa wajen kallo, batace mishi komai ba ta d'auki jakanta ta fita daga motan, department d'insu ta nufa taga Su Samantha da Aisha da wasu students d'in na tsaye hall way d'in, agogonta ta duba taga saura 15mins su fara lecture, tana juyawa zata bar wajen suka had'a ido da Aisha, d'auke kai Batuul tayi kamar bata ganta ba, can bayan faculty d'insu ta nufa ta zauna taci gaba da kukanta, k'anshin turare mai dad'i ne ya bugi hancinta amma bata d'ago taga daga ina k'anshin yake ba, cikin wani irin masculine voice mai dad'i da nutsuwa taji ance "Here, take this", ta d'ago rinannun idanuwanta ta sauk'e kanshi, da sauri ta d'auke idonta ta juyar da kai gefe ta hade rae, har lokacin bai bar wajen da yake tsayen ba, juyowa ta kuma yi ta ga har lokacin hannunshi na mik'a mata farin handkerchief d'inshi, a sanyaye tasa hannu ta karb'a, wani k'anshi mai dad'i ne ya bugi hancinta da takai fuskanta, ido ta lumshe ta shiga goge hawayen dake fuskanta, daga d'an nesa da ita ya zauna, bai ce mata komai ba har sai da ta juyo ta dubeshi sannan yayi mata murmushin shi mai kyau, kau da kai tayi ta fara wasa da biron da ta ciro cikin Jakarta, a hankali ya fara magana "if you don't mind, may I know d reason behind those tears, I might help", sai lokacin ta sake tunowa da yadda taga Abu ya riqe Ajiddeh, wani siririn tsaki ne yayi escaping lips d'inta ta fara k'ok'arin maida hawayen dake shirin dawowa, jin tayi shiru batace komai ba yasa ya sake kallonta, suna had'a ido ya d'aga mata girarshi d'aya yana jiran jin mey zatace, agogon hannunta ta duba taga lokacin lecture yayi, da hanzari ta mik'e ba tareda ta bari sun had'a ido ba ta miqa mishi handki d'inshi, ganin bai amsa ba ta ajiye mishi tace "Thank you, I need to go right away", bata jira jin cewarshi ba ta tafi cikin sauri ta bar wajen", murmushi yayi yabi bayanta da kallo tare da lumshe ido, tana isa taga har an fara shiga class itama taje ta zauna, waje d'aya suka zauna itada Aisha, bayan sun zauna ne Aisha tace "Fatima wai meye problem d'inki, ko yau you look pale, in bakida lafiya dolene sai kinzo school", had'e rai Batuul tayi tace "wa yace miki banida lafiya", dan bata jin yin magana da kowa, murmushi Aisha tayi tace "ai ba sai an fad'i ba, you look sick, red eyes, plump lips, pale face, nasan inda zan tab'a temperature d'inki nasan yayi sama", yak'e Batuul tayi tace "Am totally fine, bacci ne kawai ban samu nayi ba jiya", ta d'auke kanta tana sauraron maganan da lecturer d'insu ya fara, baki Aisha ta tab'e bawai dan ta yadda da abinda Batuul ta fad'a mata ba itama tayi concentrating da jin lecturer d'insu, Batuul dai na zaune ajin ne amma gaba d'aya mind d'inta is off, batasan ma dalilin da yake sata damuwa ba, har suka gama lecture l batayi grabbing komai ba, jiki a sanyaye ta mik'e suka fito daga lecture hall d'in, Samantha ce tace "Let's go and get some food, am hungry just as the glutton I'm, then we go home after then, no any other class, done for d day",ta fad'a tareda d'an tsalle, dariya sauran suka sa amma Batuul was absent minded bata ma san mey suke cewa ba, sai da Samantha ta sa hannu fuskanta ta fara waving sannan tace "Hello, you there", sannan ta dawo daga tunanin da take tace musu, "You carry on, I will b there right away, I need to clear somethings over here", Aisha dai batace komai ba tayi gaba abinta haka ma Samantha tare suka tafi, suna tafiya itama ta juya ba tare da tasan inda zata ba, wani guri ta hango duk bishiyoyi ne, wajen very serene, ba tareda wani tunani ba taje ta zauna abinta ta fiddo littafi kamar me shirin karatu sae dae ita kanta tasan ba karatun xata yi ba.
Abutturab da Ajiddeh kam tunda suka fita airport suke abu d'aya, da k'yar ta samu kujera shima d'in ba first class amma tace taji ta gani zatayi managing, ai Uwa tafi komi, haka dai tayi convincing d'in Abu, wayanshi da ya ciro cikin aljihu don duba karfe nawa ya tuno mishi da Batuul, ba b'ata lokaci ya shiga neman number David ganin zai kai yamma bai dawo ba kuma bai bata wayan ba, David na d'agawa Abutturab yace mishi "Where are you?", David yace Sir av dropped her at school, am at the construction site now to give out d documents", d'an iska ya furzar yace "Did she tell you when she will be done?, i mean for today?", "David yace "No Sir, she didn't", Abu ya gyad'a kai yace "okay, you should leave d site now and b there at her school, make sure you wait for her to finish and take her back home", David ya amsa da "okay Sir", daga nan ya kama hanya ya koma makarantar su Batuul, inda ya sauk'eta nan yaje ya kafa motarsa, tunda yaje yake zuba ido ko zai ganta amma shiru, tun 10:30 yake makarantar gashi har 1 tayi babu Batuul, har lecture halls d'insu sai da ya riqa bi yana yi musu describing d'inta bata nan kuma an tabbatar mishi da sun gama lecture d'insu na yau, ba tare da b'ata lokaci ya ba ya kira Abutturab yace yaje bai ganta ba, calmly yace mishi ya koma yaje ya sake dubota, sau biyu yana komawa amma bata nan har wajen 4, sai lokacin hankalin Abuturrab ya fara tashi, Ajiddeh na lura da shi sae dae bata ce komae ba, Sallama yayi mata daga karshe yace xae tafi sae sun yi waya, ta wani hade rae tace " Ban gane ba Aliyu, a kan wata can xaka tafi ka bar ni jirginmu bae tashi ba, ita din yarinya ce da baxa ta iya kula da kanta ba duk xa ka wani tada hankali haka" ya daga kafada don bai son su rabu da fada yace "Chill babe, wani takardu xae kai min office to suna gida kuma wae ta kulle gidan da makulli shi yasa kika ga na takurasa ya nemota" tsaki Ajiddeh tayi tace "Toh gidanta ne xata wani kulle da makulli kuma wa ma ya bata makullin" peck ya manna mata a lip yace "Yi hakuri mai gida" turo baki tayi, yayi dariya yace "Don't worry babe, i promise to be back soon" bin sa da kallo tayi har ya bace mata kafin ta lumshe ido ta sauke ajiyar xuciya, Allah kadae yasan irin son da take ma Aliyu, kuma In'sha Allah nata ne shi din ita kadae.
Abuturrab kam direct makarantar ya wuce daga airport din, har ya gama zagaye makarantar babu Batuul, a gajiye ya dawo gida lokacin biyar da rabi, ido ya lumshe ganin abincin da ta jera tun safe kan dinning ba a tab'a ba,sai lokacin ya tuna da zancen abinci, yasan dae baxa ta bata ba amma haka kawae ya kasa samun natsuwa.
Batuul kam Na zaune wannan gurin har 4:15, sosai wajen ya mata dad'i har yasa ta manta damuwar dake ranta, sai kallon tsuntsaye takeyi suna shawaginsu kan bishiyoyi da water fountain d'in dake tsakiyar wajen, agogon dake hannunta ta duba taga 4:15, a razane ta miqe ta tattare kayanta ta fito daga gun, tasan dan bata sallah ne shiyasa time ya qure har haka bata sani ba, rana har ya kusa fad'i lokacin, tafiya kawai ta shiga yi har ta iso dpt dinsu ta tsaya tana kalle kalle, bataga kowa da ta sani ba, haka kawae taji hawaye sun cicciko mata ta nufi hanyan gate a sanyaye zataje ta tari cab ya kaita gida, tafiya takeyi tana ta share hawaye, har wani blur take gani, dab bakin gate taji mota na mata horn, matsawa tayi ta bashi hanya ta koma gefe taci gaba da tafiya, ji tayi horn d'in na dad'a k'aruwa, "Fatima", a tsorace ta juyo tana kallon mai k'iranta, parking yayi ya fito yazo ya sameta inda take tsaye, fuskanta ya gama examining sannan yace mata "do you always cry?", d'ago idonta tayi ta kalle shi tace "Are you stalking me?", dariya tambayarshi ya bata yace , "Mey ya faru baki tafi gida ba tun d'azu and you finished your lecture for d day tun 10", shiru tayi bata ce mishi komai ba, tambayanta ya sakeyi jin tayi shiru yace "ina zaki yanzu?", a hankali tace mishi "gida" ido ya wara yace "by yourself, do you normally go by yourself, mey kika zauna yi a school d'in har kika kai this time?", kai kawae ta girgiza mishi, ya juya zai koma mota yace "let's go, I will drop", ba musu ta shiga gaba yana biye da ita a baya, shi da kanshi ya zaga ya bud'e mata k'ofa, wani kanshi ne mai dad'i yayi mata sallama, ido ta lumshe ta jinginar da kanta jikin kujera, Hamdala ta dinga yi a ranta dan dama tsoron shiga cab d'in takeyi, sai da ya fita gate d'in ya juyo ya dubeta yace "yace where are we heading to?", sai a lokacin ta bud'e idonta tace mishi ST.Georges No 15, daga nan bai sake cewa komai ba ya d'au hanya.
Waya Abuturrab ya bugawa Mr Steven akan ayi enquiring abt Batuul dan har yanzu bata dawo gida ba kuma school d'inma bata can, daga nan ya shiga yayi wanka ya canja kayan dake jikinshi, ko mai bai shafa ba ya sake d'aukan key yayi waje, yana zuwa bakin k'ofa yaga wata bak'ar Rolls Royce ta shigo compound d'in, sai da motan yayi wajen two minutes da parkin tukunna maishi ya bud'e ya fito, ajiyar zuciya ya sauk'e ganin Batuul ta fito cikin motar yayi tucking hannuwanshi cikin aljihu yana kallonta, "Thank you" tace da Shaheed tana kallonsa, Sam bata lura da mutum na tsaye ba sai da ta juyo zata shiga gida, gabanta ne ya bada sautin dam ganin Abu tsaye bakin k'ofa ya zuba mata lumsassun idanunshi ko kifta wa bae yi gashi ya wani hade rai, dakewa tayi ita a dole tana fushi taci gaba da k'arasowa, Sai da tazo dab dashi ta kasa d'aga k'afa ganin yadda idonshi ya canja kala yana kallonta dasu, shi kam Shaheed tuni ya bar compound din ba tare da ya lura da Abuturrab ba ma, a hankali Batuul tace "Ina yini" bae amsa ta ba ya kama hannunta suka nufi cikin gida fuskarsa a daure, gabanta ya dinga faduwa har suka shiga Palo, kulle kofar yayi ya juya yana facing dinta yace "Daga ina kike?" Sunkuyar da kai tayi ganin he's serious, murya can kasa tace "School" wani tsawa ya daka mata yace "I will slap you idan kika ce min school, I repeat my self where are yhu coming from, kuma waye yayi dropping din ki yanxu" hawaye ne ya xubo idonta har lkcn bata d'ago kanta ba.
ππBATUULππ
61
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Hade rai Abuturrab yayi yana mata wani mugun kallo yace "if I shud slap yhu! Na maki wani abun ne kike min kuka, waye ya sauke ki a mota nace" share fuskar ta tayi ba tare da ta d'ago ba tace "A frnd!" Yana mata wani irin kallo yace "A frnd? Male or female" a takaice tace "Male" wani xaro ido yayi cikin tsawa yace "What, Male? Da aure nawa kanki kika hau motar wani kato, are yhu insane?" Wani takaici ne ya rufe ta wasu hawayen suka dinga xubo mata, bata san lkcn da ta mayar masa da amsa ba tace "Ohh ashe kasan da auren ka kaina, toh ai ni ban san da haka ba, nayi xaton wanda ka raka airport kadae auren ka ke kanta" tana kai wa nan ta nufi stairs ta bar sa wajen tsaye, bin ta yayi da kallo baki bude, har ta haura sama, sae kuma ya shafa kai yana murmushi ya koma cikin Palo ya xauna, ba dai kishin sa Batuul take ba, No! Ya ma san it's impossible tunda ba son shi take ba. Batuul kam tana shiga daki ta jefar da jakar hannunta tayi xamanta gefen gado, sae dae banda tukuki babu abinda xuciyarta yake, ta fi minti goma xaune kafin ta mike ta rage kayan jikinta ta shiga toilet, warm shower ta sakar ma kanta, ta kusa minti sha biyar a bayin sannan ta fito daure da towel, gaban mirror ta nufa tayi shafe shafenta, xata dauki kaya a closet dinta ta ji wayarta na ring, juyawa tayi ta koma gaban mirrorn ta dauki wayar, ganin me kiran yasa tayi murmushi ta daga tare da sallama "Tace Ammah ina yini?" Maimakon ta ji muryar Ammah sae taji kmr muryar Anty Amnah, daga daya bangaren Anty Amnah tace "Kina ji na Batuul?" A d'an kunyace Batuul tace "Ina ji Anty ina yini" don kunyar matar ita dai take, Anty Amnah tace "Lfya lau Batuul, ya ku ke gaba daya" Batuul tace "Lfya muke Anty" Anty Amnah tace "Toh madalla, cikin kayan da aka kawo maki kinga wani parcel da aka yi wrap kuwa" Batuul ta d'an yi shiru tana tunani, Anty Amnah tace "shi kadae ne karami cikin kayan" Batuul tace "Eh na gan shi Anty" Anty Amnah tace "Yauwa! Kin bude kuwa" girgixa kai Batuul tayi kamar tana ganinta tace "A'a Anty, ina ce turare ne ae" Anty Amnah tace "A'a ba turare bane, maxa dauko yanxu ki bude in maki bayani" xaro ido Batuul tayi tunawa da tayi ae duk kayan na can gidan, tace "Toh Anty bari in dauko" ajiye wayar tayi ta fita da sauri ta sauka Palo, Abuturrab na xaune har lkcn ya jinginar da kai jikin kujera idonsa lumshe, ta wani hade rae ta tsaya gabansa tace "Ya Abu, Anty Amnah ta kira wae xata min bayanin wasu daga kayan da aka kawo kuma basa nan ai" a hankali ya bude ido yana kallonta, gyara xama yayi da sauri yana ci gaba da kallonta, jin yaki cewa komae tace "Kaji, she's still on the line fa, ni ban san me xan ce mata ba" ko kadan bae san ma abinda take cewa