Showing 3001 words to 6000 words out of 215266 words
mamansu tace Ammi Yaa Abu ba ya tafi Umara ba ? Sadiq ya juyo yana dariya yace bai tafi kuma da shi zaki tafi masallaci tace amma lokacin da mukayi waya da ina school ai kace ya tafi, Sadiq ya sake murmushi yace toh ya fasa tace toh ta sake duban Ammanta tace Amma *ndaso yikêkin* ? (wanne zan saka ?) Ammah tace mata ki saka blue din tace toh ta juyo ta dubi Yaa Abu tace da Abui zaku tafi masallaci ? Kanshi à duke yana danna waya ba tare da ya dago ba yace mata ehhh Ammah da Sadiq basuce komai ba sai tsayawa da sukayi suna kallonta dan suji dalinlinta na tambaya amma bata ce musu komai ba ta koma jikinta a sanye tana fara tafiya taji yace Farida tace naam Yaa Abu yace mata saura ki tsaya kwalliya ki bata min lokaci ba tare da cewa komai ba ta juya taci gaba da tafiya har taje daki sannaan ta zauna akan makeken gadon dake dakinta ta fara yiwa kanta magana tana cewa Yaa Abun nan kullum wai sai da Abui zai tafi dan yasan kullum Abui nake bi shine kuma yace shima dashi zaije kuma ya dinga hana mutane magana wai shi bayason surutu, Ni nan gaba zan dena bin Abui ina bin Ammah
Ammah ce ta kira daya daga cikin masu aikin gidan tace Fanne ba a kawo shayin Abu ba da sauri mai aikin taje dauko flask din ta ajiye ta juya ita kuma Ammah ta tafi bawa mijinta abincinshi , ya dauki flask din tare da zubawa a cup yana kurba kadan kadan kanshin shayin ne ya sani matsawa baya saboda in naci gaba da shaqa toh sai nace musu su zubamin, kanshi ne da ya hada na lemon grass, na'na',citta, kanumfari da cardamom seeds da mint leaves.
Bayan ya gama shan shayin ne ya dauki saucer ya Saka kisre guda daya da miyar kubewa danya da yaji naman kaji à ciki. Ahankali ya dinga ci har ya gama sannan ya miqe ya yaje wajen hand wash basin din dake dinning area din, ya wanke hannunshi ya tsane da towel sannan ya bude fridge ya dauki robar ruwan faro, ya juyo ya tambayi sadiq bayan ya kurbi ruwan Sadiq wane masallaci zakuje da Ammah ? Yace filin polo zamuje kasan bata cika Son zuwa Ramat square dinnan ba yace Toh ni zan wuce bari inje inga ko Abui ya gama sai mu tafi Allah ya kaiku lafiya sai kun dawo ya sake cewa Sadiq kayi tuqi à hankali dont play rough with my life on road Sadiq yayi dariya yace she is mine too y'a karasa falon ya tarar Abui ya gama cin abinci har ya miqe yana saka babbar rigarshi Ammah kuma na fesa mishi turare sannan ta gyara mishi hula Abu yayi murmushi yana son yanda suke kula da junansu dukda Sun tsufa. Abui ne ya juyo ya kalleshi yawwa Abutturab muje lokaci ya kusa kurewa sai kuma ya tuna ashe sarkin rigimar tasa ba ta fito ba ya bude baki kenan zaiyi magana sai gata ta fito da murmushinta mai kyau ta saka riga da skirt din super yellow mai shudin flower ta saka hijab shima blue hannunta riqe da jakar cardio baqa ta karaso taje ta rungume babanta sannan ta tambayeshi Abui *shawangêna*(nayi kyau)? Yace mata sosai mamana kinyi kyau muje ko ? Tace okay su ukun suka fita su kaje inda motar take pake Abu ya budewa baban nasu mazaunin dake gefen driver farida kuma ta shiga baya. kamin su fita Ammah ma suka fito ita da Sadiq tana sanye da laffaya green and red suka nufi GLK din dake pake à wajen parking mota, sai da suka shiga suka tada suka fita tukunna Abu ma yabi bayansu, su sukayi hagu ta su Sadiq kuma tayi dama.
💖💝BATUUL💖💝
4
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
A gaban gate din wani mansion ta tsai da motar tare da yin horn, masu gadine su biyu suka fito cikin hanzari suka bude musu gate din suna yi musu sannu da zuwa, karasawa tayi cikin gidan har ta isa inda ake parking, kamin ta tsaida motan Yusra tayi sauri ta bude kofan ta fita Hafix ma ya bita a baya, cikin hadin baki Aunty da Batuul suka ambaci "Inna lillahi wa inna illaihi rajiun"Fa'iza ta fito itama a guje ta bi bayansu tana fadin bakuji ciwo bako su kuma suna ta kyalkyala dariya Yusra tana fadin ai na rigaka shima Hafix yana ya rigata, suna karasawa bakin wani sliding door mai girma na glass suka tsaya dan baza su iya danna kararrawar ba yayi musu nisa sai Fa'iza ce da ta karaso ta danna musu kararrrawar suka tsaya jiran à bude musu kofar, à dannawa na biyu ne aka bude musu kofa daidai lokacin Aunty da Batuul suka karaso suka Shiga ciki, parlour ne mara tarkace amma yana da kyau, wallpaper ne baqi mai flowers fari da grey zagaye da dakin , daga tsakiya akwai farin kujera mai L shape da throw pillows akai ,karamin round Table daga gaban kujeran, office chair daga gefe sai Babban TV da ya kusa cinye bango dan girmanshi à manne da bangon.
Kanshine mai dadi na sandal wood ke fitowa daga parlour hade da iskan Ac mai dadi da sanyi ,bayan sun karasa daga ciki sun wuce wani bene mai rails silver suka isa wani dinning area shima créam ne da Brown mai dauke da dogon dining Table da kwanuka na alfarma sai chandelier daga tsakiya
Bayan sun shiga sun zauna ne yarinyar da ta bude musu kofa tace "sannunku da zuwa Aunty " cikin hausar ta da ba dai dai ba " Aunty tace mata sannu Janet, Su Ahmad Sun fita ne naga motan da suka fita dashi à parke "
"Janet tace à ah Aunty sun dawo tun dazu Sun hau dakinsune, su da babane dukkansu Sun dawo shima ya tafi sama" " Batuul ce ta juyo bayan ta ajiye wayar da take dannawa tace Tabawa fa ko har yanxu aiki take ba à samu tayi wanka ba, Janet tace à ah Aunty taje dakine zatayi wanka, tace okay
Tafiya sukeyi suna ta gaisawa da dimbin jama'ar da suka halarci sallah Massa ya dubi Abutturab ''Man yaushe zaku koma Abuja ne ?
Abutturab ya furzar da iska daga bakinshi sannan yace " Yeah i want to leave in the next four days dan inada appointment da Minister amma nasan su Abui sai next week cuz su sai Sun gama sallah anan. I cant wait that long"
"Massa yace okay nima sai next week din zan shigo ", suna tafiya har suka iso inda su Abui suke, Abui ne ya Juyo ya dubesu tare da cewa mutumin da suke tsaye tare, "ai gasu nan ma", mutumin ne ya fadada murmushinshi tare da fadin "Masha Allah" ya miqa musu hannu suka gaisa, yacewa Abui "Its been long i met them , almost 19 yrs nasan bazasu tunani bama, anyway ya kuke ? Ana karatu ko kuma an gama ? Ko kuma aure za Ayine ya fadi maganar tare da dariya ? " , take fuskan Abuturrab ya canza dan baya so ana mishi maganan aure in Abui na kusa , yanxun nan zai tada maganar har sai ya dinga magiya taré da bashi hakuri
Abui ne ya bawa mutumin ansa tare da fadin "ai aure kam sunqi shi, Shi Aliyu(Abutturab) architect ne dan yanxu ma yana da contact da minister Abuja, Mustapha(Massa) kuma Doctor ne tunda yayi karatu à Germany sukayi retaining dinshi, but munaso ya dawo dan baza mu barshi cikin turawa ba", mutumin yace "gaskiya kam, Allah ya taimaka. " *Alai*(Alhaji) Ahmad Kyaree zan wuce yanxu dan nasan su Madam suna jira, tare mukazo dasu kuma ga ruwan da akeyi, zan kawosu before ku koma in sha Allah " , Abui yace okay à gaidamin su, ace musu muma muna nan zuwa.
Tunda mutumin ya fara magana Abutturab bai dago kanshi ba har sai da mutumin ya fara maganan aure, a snn ne ya dago kanshi ya k'arewa mutumin kallo har yaso gano inda ya sanshi amma ya kasa, sai cewa Abui yayi bayan mutumin ya karasa barin wajen, " Abui is he an old friend"?
"Yeah à good one too inji Abui ", tare da basu labarin tare da ce musu su tafi kamin ruwan ya kara yawa "
Ta miqe kenan tana cewa Aunty zata haura dakinta tayi wanka ta canxa kaya dan Sun jike ta hango Babanta na saukowa daga bene, da gudu taje ta rungumeshi, "tace Baa yanxu nakeso inje wajenka, ya d'an janyeta daga jikinshi yana tambayarta
"Batuul ya kayanki à jike" ? "Tace Baa ai anyi ruwa à waje ku tun dazu kuka dawo ko ? Ya sake ce mata "Batuul yanxu sallahn Allah shine kika saka baqin kayan nan kikaje har masallaci dashi ? Batuul ta danyi kasa da ido ta zumburo karamin bakinta kamin tace "Baa sabone fa kuma designer ne na Hauté Èlan kai ka siyomin mafa " , yace mata "toh naji maza Je ki cire su kar kiyi mura, tayi murmushi tace yanxu zan dawo ai, ta haura sama shi kuma ya karasa saukowa kasa .
Har ta wuce wani daki à sama sai kuma ta dawo daga baya, cikin sand'a ta bude kofar dakin, a hankali take turawa, sai da ya fara karane ta bude shi gaba daya tana fadin Taraan, yara ne maza a dakin su biyar, kowa da game controller a hannunshi suna ta ihu,typical dakine na maza da akayi littering gwangwanaye drinks, kayansu da suka cire daga k'asa, gadajen à hargitse sai plates din abinci da spoons.Yan manyan guda biyu da baza su wuce 13-15 yrs ba sanye suke da wandunan shadda sai fararen vest à jikinsu hannunsu kuma maqale da agogo, sai mai bi musu shi kuma sanye yake da complète kaftan dinshi brown harda hula akanshi ya tsaya akan sofa yana ihun ni zanyi winning, dayan kuma sanye yake da three quarter da T-shirt shima yana riqe da game controller, karamin cikinsu ne snn duk yafisu haske yana daga gefe riqe da Ipad à hannunshi yana ta aikin dannawa, Suna ganinta suka yadda abubuwan dake hannunsu, Manya ukun na ihun Aunty ta dawo kanana biyun kuma suna cewa Mama ta dawo, a guje suka fito kowa na rige rigen ya riga dan uwanshi fita daga dakin, Da sauri Baatul ta matsa daga bakin kofa dan kar su bigeta tana ta dariya ta juya ta bar kofar dakin ta karasa nata dakin ta murda kofan ta shiga.
💖💝BATUUL💖💝
5
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tana shiga daki ta nufi inda towels dinta ke rataye, ta janyo daya sannan ta cire kayan jikinta da suka jiqe, ta daura towel din a kirjinta, ta nufi toilet din dake dakin nata, bayan minti goma ta fito tana kanshin shower gel da sabulun Makari,da towel a jikinta daya kuma a daure a kanta kamar turban, gashin goshinta ya kwanta lub lub, fuskanta ya kara haske da kyau, ta karaso gaban mirror dake cike da turararruka da yan kayan kwalliya da na shafa , ta jawo stool din mirror ta zauna sannan ta dauko man Makari, a hankali ta riqa shafa man kamar baza ta gama ba, bayan ta gama ne ta karasa gaban closet din kayanta, ta bude ta dauko peplum blouse da skirt din atamfa baqi mai pattern din purple ta saka à jikinta, kayan ba karamin kyau yayiwa jikinta ba, komawa gaban madubin tayi ta shafa powder a fuskarta sannan ta saka kwalli a idonta, ta shafa nude lipstick a bakinta , ta bude costume box dinta dake kan madubin daga gefe ta dauko dankunne da sarka silver masu duwatsu a jiki, sai abun hannu da zobe shima silver, sannan ta fesa turare, ta kalli kanta a madubin tare da murmushi sannan ta koma ta zauna a kan gadonta tare da d'aukan wayanta,
bayan ta d'an daddana wayan ne ta kara à kunne tare da fadin "Hello Riri, shine kikace min a Ramat Square zakuyi sallah, kuma bakije ba,
Daga daya bangare aka amsa ana dariya tare da fadin
"Yo babe nan naje mana, i wanted calling you inji inda kike sai sai da na duba wayana naga ban fito dashi ba, You know anytime Yaa Abu na gida toh komai nawa doesnt seems to be ryt"
"Batuul tace babu wani Yaa Abu, anytime kika samu matsala sai kice shine, toh duk ranar da zan ganshi sai na fada mishi
"Riri tayi dariya,tace mata dan baki sanshi bane ai, koh face dinshi idan kika gani zakiga ko smiling bayayi, brows dinshi kullum a hade, bayayiwa mutane ma magana wai surutu na saka mishi ciwon kai, kuma ko bashi zaiyi ba wai baza ayi a kusa dashi ba,
"Batuul tace all these apart, ni zanzo yau dan Baa yace nan da kwana hudu zamu koma dan yana da aiki sosai kuma gobe da jibi zamuje wajen su Yayya da sauran Family
"Riri tace yawwa bae of earth,daman ina ta tunanin yadda zan ganki, I missed you soo much wlhy, kizo yanxu i have have So many things for you alone, Batuul tayi dariya tace
"You are not serious, ai sai na fadawa Baba tukunna, sai yayi approving zuwana
"Riri ce ta marairaice murya hade da cewa nasan Baba zai barki sai dai in kece bakison zuwa, pls kizo, am bored over here, kuma kinsan Yaa Abun in yana nan ba a yawo "
"Batuul ce ta cemata ni ba ruwana and i told you zan fada mishi whenever i meet him"
"Ai bazaki iya ba nasanki, I wish zaki zo yana nan shima yaga wanda ya fishi rashin magana,ai mantawa ma nayi halinku daya nake fada miki
"Ni dai yanxu a bar maganan, yanxu zanje in fadawa su Aunty zanzo wajenki ,
"Aii sai kinxo"
sannan suka katse wayan, tashi tayi ta jona wayan a caji ta juya ta fito daga dakin, har ta karaso kasa, ta sauka daga benen ta jiyo muryoyin yan gidan a dinning suna cin abinci, karasowa tayi wajensu, Mahir na ganinta yace Yaa Batuul kinyi kyau, Hafix ma yabishi yace kinyi kyau, tayi murmushi tace musu nagode, kuyi shiru ku gama cin abinci,
kujera itama taja ta zauna a gefen Baba daga hagu, Baba ne ya ce mata
"kinga kayan nan yayi miki kyau amma ba kiyi ta saka baqin kaya ba a kowane occasion",
Aunty ce tace ai Y'ar kauye ce,"
ta juyo ta dubi Baba tai raurau da ido, yana ganin haka ya yace
"À ah Mamana ba y'ar kauye bace, ai kayan nayi mata kyau" ko ? ya tambayeta ,murmushi tayi sannan ta dauki plate, ta janyo wani babban tray da aka rufe da foil paper ta bude,Danderu ne na kaza yana ta tiriri da kanshin kayan yaji, kadan ta saka à plate din sannan ta sake janyo wani food flask din ta dauki masa daya a ciki tare da miyar masa, a hankali ta riqa ci ba tare da cewa komai ba har suka gama
Sun gama cin abincin ne suka tashi suka koma palo, Fa'iza da Janet ne suka zo suka gyara dinning din tare da kara turaren wuta à duka electric burners din gidan
Sai da kowa ya zauna ya nutsu sannan ta dubi Baba tace
"Baa inason inje wajen Farida tunda gobe da jibi we Will ne busy,
"Okay what time zakije ?
Cewa tayi "ko yanxu tunda naga its already after 12"
" Tunda su Baa Liman(Driver)suna hutu sai Ahmad ya kaiki dan ya fiki iya driving kuma bana Son kina driving ke kadai especially a Maiduguri da ba a bin régulations din driving "
"Okay Baa nagode, " Aunty dai bata ce komai tunda Baba ya yadda shikenan. Tashi tayi ta k'ara haurawa sama ta dauko jakarta ta channel purple shima irin kayan da karamin gyale shima purple amma light, ta kara duba fuskanta a mirror sannan ta sauko
Tana saukowa taga Ahmad riqe da key din mota a hannunshi yana jiranta, karasowa tayi ta ce wa su Baba zasu tafi, "
yayi musu sai sun dawo sannan yace mata idan ta gama sai ta kira a zo a dauketa, tace toh",
Tacewa Aunty sai Sun dawo, Aunty tace mata ki gaishe da Ammah kice mata nima zanzo ko bayan mun koma Abuja ne, Toh tace sannan suka fita suka nufi inda akayi parking motocin gidan suka shiga wata Audi fara sol, Ahmad ne ya tambayeta anguwan da zasu bayan yayiwa mai gadi horn kamin yazo ya bude mishi kofan, ce mishi tayi Old GRA ne in munje zan nuna maka hanya, Ya juyo yace mata
"Yaa Batuul Allah kwatancanki akwai wahala yanxu sai mu kai two hours muna neman wajen da baifi muje a 20 mins ba "
"Tace toh ka bani inyi driving"
baice mata komai ba yaja motan suka bar gidan bayan mai gadin yayi musu a dawo lafiya
Tafiyan minti goma sha biyar suka isa gidansu Farida a old GRA ,Horn yayi aka bude musu gate suka shiga, suna shiga gidan bugun zuciyanta ya karu, ambaton Allah ta riqa yi har sai da taji ya dan ragu sannan ta bude motan ta fito daga ciki tare da yiwa Ahmad sai anjima akan in ta gama zata kirashi
Farida na Jin tsayuwar mota ta fito daga cikin gida a guje tazo ta rungume Batuul ta na ihun i missed you so much babe,
"Batuul ce tace mata sakeni kar ki ballani Baba ya hanani zuwa nan gaba"
Dariya tayi sannan tace nasan Baba bazai hanaki zuwa sai dai in ke