Showing 111001 words to 114000 words out of 215266 words

Chapter 38 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1726

kar ta kwace min miji ya ji yana sha'awar aurenta don wallahi sae kin ga yanda ta iya girki yarinya" cikin matsanancin kuka ta kare maganar, Mumy tace "Ke dae shashasha ce wllh Ajiddeh, ina ruwan ki da wata yar iska can ke da xa ki turo kudi mu koma gun bawan Allahn can a san abun yi, da yyi niyyar aurenta ae ba ke xae aura ba ita xae aura tunda sun fi kusa can munafukae, kawae dae an hado shi da ita ne don take maki lekan asiri ke kuma wawuya baki gane ba, har xaki wani d'aga hankali ke da xaki saita ma shegiyar xama ta ji xaman gidan ma ya isheta, yarinyar da ba ma wani kyau gareta ba in ban manta ba sae wani dogon hanci kmr tsiya, meye kuma xaki damu kan ki, yana da kamar ki fara doguwa siririya kyakkyawa ga diri, g'ashi har gadon baya, yanxu dae ko kudinsa ya kama ki dauka kawae ki dauke ki turo mu san abun yi, ita kuma shegiyar ki daina d'aga hankali kanta baxa ta dade maki a gida ba nasan abinda xan yi" Ajiddeh na share hawayen idonta tace "Toh shknn Mumy xan turo ko xuwa gobe" nan Momy ta dinga mata hudubar tsiya tana digesting har taji tsayawar motar Abuturrab, ko kan ta fito har Batuul ta shige daki dama, hakan yasa ta nufi stairs, suka kusa cin karo da shi, kallo daya yyi mata ya ga ynda idonta ya kumbura saboda kuka, ya bi gefenta xae wuce ta sha gabansa tana masa kallon raini tace "Wllh yau sae dae ka xaba ko ni ko wancan karuwar a gidan nn, idan ba karuwanci ba don tana jini har sae ta so ka sani tana wani murkushe murkushe kana daukar ta? Ta ina ta xama muharramar ka, to Allah baxa ta kwanan min a gida ba yau, ka je ka biya mata hostel" banda tafasa bbu abinda xuciyarsa ke yi, acting gently yace "Bani hanya in wuce" tana masa matsiyacin kallo tace "Naki sae ka xabi ko ni ko karuwan can" cikin kakkausar murya yace "Xa ki sa na maki abinda ban taba maki ba Ajiddeh" wani shewa ta saki tace "Ka Dade baka yi ba Aliyu, uwar meye baka min ba daga cikin walakancin ka har...." Bata rufe baki ba taji saukan lafiyayyun mari har biyu ya shaketa ya ja tun daga sama har suka sauko k'asa ya jefar da ita yyi wani irin ball da ita, ae daina gani tayi na 'yan dakiku, bin ta yyi yana huci ya kuma fixgota yace "Don kaza kazan ki ke kika koya mata karuwancin?" Cikin tsawa yace "Answer me kar in sumar da ke a nn, kin san matsayin ta a gidan nn kike kiranta da karuwa?" Jefar da ita ya kuma yi ya nufi sama yana huci.
[8/22, 14:48] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






53






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





D'akinshi ya shiga bayan ya kwashe ledojin da ya zubar corridor tun lokacin da Ajiddeh ta fara mishi shirmenta, babu abinda yake buk'ata irin ya watsa ruwa a lokacin, toilet ya wuce ya sakarwa kanshi hot shower, har saida yaji ya fara komawa daidai sannan ya fito daga cikin cubicle d'in wankan, alwala yayi a sink sannan ya fito cikin toilet d'in, gaban vanity table ya tsaya ya shafa mai sannan ya fesa turarukanshi masu k'anshi, closet d'inshi ya bud'e ya ciro farar jallabiya cikin jerin jallabiyoyin dake a ciki, xirawa yayi har xai fita idonshi ya fad'a kan ledojin dake ajiye a k'asan d'akin, d'an tsaki yaja ya kwashi wasu daga ciki ya fice waje, d'akin Batuul ya wuce kai tsaye ya tura k'ofan ya shiga, tana kwance kan gado ta kifa cikinta, rabin k'afanta duk ya sauk'o daga kan gadon, d'an tsaki yaja ganin bacci takeyi ya ajiye ledojin dake hannunshi ya fita, makulli ya sa ma kofar dakin ya rufe, snn ya sauk'o kasa don tafiya masallaci, bai tarar da Ajiddeh a palon ba ya fice masallaci, sai da akayi isha sannan ya shigo gidan, wutan palon ya kashe ya haura sama, har lokacin Batuul na bacci, a hankali ya d'an tab'a ta alamun ta tashi, a hankali ta bud'e idonta daga nannauyan baccin da take yi, ganinshi a tsaye yasa tayi maza ta mike zaune, had'e rai yayi yace "tashi kici abinci kisha maganinki", baki ta bud'e zatace mishi ita bata jin yunwa, wani kallo da ya bita dashine ya sata zumb'uro baki ta miqe a hankali, yana tsaye ta shiga toilet tayi brush ta fito, kamar zatayi kuka lokacin da ta fito daga toilet d'in dan har ta fara bleeding kuma bata san inda xata samu pad ba, har lokacin da hijab a jikinta, kan gadon ta koma ta zauna a d'arare, tana tsoron b'ata bedspread d'in, "Ni zan tashi in kawo miki abincin", ya tambayeta yana jifanta da wani irin kallo, jiki a sanyaye ta mik'e zata sauk'o daga kan gadon ta take dogon hijabin dake jikinta, fad'uwa tayi k'asa ji kake tim, y'ar k'ara ta saki da yasa Abu saurin k'arasowa wajenta, d'agota yayi yana kallon idonta da ya cicciko yace " c'mon kin cire hijabin nan ko sai na b'ata miki rai yanxun nan, yhu are bothering me fa a gidan nan", raurau tayi da idonta tana tsoron ta cire hijabin dake jikinta ko tayi staining kayanta, ganin ta tsaya taqi yin abunda ya sata ya sa ya d'age hijab d'in da take qin cirewan, y'ar k'ara ta saki ta d'urk'ushe a wajen, binta yayi ya kamota yace "ina miki wasa ko", kai ta shiga girgiza mishi tana hawaye, yace "Au kuka ma kika sami daman yi?", sulalewa ta shiga yi daga rik'on da yayi mata zatayi k'asa, ya wani fixgota yana mata mugun kallo yace, "I will slap you right now, meke damunki?", shiru tayi ta kasa mishi magana, tsaki yayi ya turata "tashi ki d'auki abincin nan" ya fad'a mata a tsawace, jiki a sanyaye ta tashi ta isa inda ledojin suke tana hawaye, a hankali ta shiga bud'e ledan, pad ta fara cin karo da, ajiyar zuciya ta sauk'e ganin pad d'in a ciki, a hankali ta d'ago idonta taga ita yake kallo a tsayen, harara ya sakar mata da yasa tayi saurin d'auke kanta, maza tayi ta ciro pad d'in daga cikin Leda ta miked da sauri ta shige toilet ta banko k'ofar, bin inda tabi yayi da kallo, tsaki yayi tareda girgiza kai, sae kuma yyi murmushi ya fita daga d'akin.






Palo ya koma ya kwanta, remote ya d'auka yayi powering TVn, yunwa yakeji amma bazai iya tashi ba, he is too stressed, kitchen ya koma ya had'a coffee, snn ya dawo parlour ya jinginar da kanshi kan sofa yana kurb'an coffee d'inshi a hankali, tasha ya canja daga TLC zuwa NATgeo Gold, don Ajiddeh ke kallon TLC, d'an tsaki yaja tunawa da yayi da ita da shirmen da ta gama yi mishi d'azun, ko kadan bae yi nadamar abinda yyi mata ba don ta kai sa bango, iska ya furzar daga bakinshi yaci gaba da shan coffeensa a hankali, ta baya yaji an rungumeshi, ko ba k'anshin turarenta ba yasan ita ce, ya b'ata rai, a hankali cikin rad'a tace mishi, "baby fushi kayi", k'in kulata yayi kamar baisan tana wajen ba sae dae he was so surprise bae yi tunanin xata sakko da wuri haka ba, kai it's vry unusual of her ma kawae, sae dae if she's up to something, zagayowa tayi ta gabanshi ta zauna kan cinyarshi tareda sak'alo hannayenta duka biyun wuyanshi tace "babe, am am sorry", ci gaba yayi da kallonshi kamar baiji mey take cewa ba, fuskanta ta kawo daidai nashi tace "talk to me mana babe, am truely remorseful wllh, sae daga baya naga ban kyauta ba forgive me plss, in dae akan....." Kasa ambaton sunan tayi, cije leb'enta tayi daga baya ta d'anyi murmushi ta kalleshi tace "indae akan Sister Batuul ne I promise baxa mu sake samun matsala ba", rintse ido tayi jin sunan Batuul ya fito daga bakinta, da mamaki shi kam yake kallota jin ta ambaci Batuul as her sister, anya Ajiddeh bata da brain disorder ma kuwa, k'ara shigewa jikinshi tayi tace "Yes our sister, I mean it, I was so stupid da na dinga yin abubuwan da nayi maka, I don't know what came over me that I reacted that way calling her names, but babe I promise bazan sake ba, kayi hak'uri kaji, I was just being pessimistic about her , thinking zaka sota if she stays here, but yanxu I have realised my mistake, she is like a sister to me also, I will gladly keep her in my house, I promise" a hankali ta kare maganar ta d'ago kanta tana kallon kyakkyawan fuskanshi, lumshe idonshi yayi sannan ya bud'esu, rungume shi ta sake yi murya can kasa tace "Trust me babe" rungume ta shi ma yyi sosae, ya lumshe ido yace "why didn't you realise it since then, but anyway am happy that you finally realised it, kinga yarinyar nan bata da matsala, nasan she will b obedient to you indai har kika kwantar da hankalinki kika jata a jiki, zakiji dad'in zama da ita, am also sorry for everything Honey" kai ta gyad'a mishi tace "nima nasan bata da matsala baby, kasan sharrin shaid'an kuma da irin son da nakeyi maka, I can't risk seeing you with another woman, zan Iya mutuw....", hannu yasa a bakinta yace "shhhh, I will always be yours alone" kallonshi tayi tace "promise", bakinshi ya d'aura kan nata tare da janyota jikinshi, sai da ya gaji dan kanshi ya saketa, k'ank'ameshi tayi jikinta ta saki wani mugun murmushi, hiran da suka gama da Mummy d'azu ta tuna, da kuka dama ta shiga d'aki bayan Abu ya haura sama ya bar ta falo, waya ta d'auka ta shiga neman layin Mum, bugu biyu ta d'aga, wani irin razanannnen k'ara Ajiddeh ta saki da har ya tsorata Mum d'in ya sata janye wayar daga kunnenta tana tabbatarwa ko da Ajjideh take waya, a rikice ta maida wayan kunnenta ta shiga tace "keh daina shirmen nan kiyi min magana, mey ya faru kuma", Cikin sheshek'a ta gama zayyanewa Mum yadda akayi, da mamaki da tsoron jin abinda Ajiddeh ta gama fad'a mata ta sauk'e ajiyar zuciya tace, "wane rashin hankalin ne ya kaiki zagar mishi y'ar uwa harda ce mata karuwa a gabanshi, keh kinsan halinshi mey ya kaiki yin abunda har zai dakeki, wama yace kije ki tafka wannan haukan wai", cikin sheshek'a tace "Mum ni bansan ya zanyi bane, I was furious a lokacin, raina duk ya gama b'aci, bazan iya jurewa ba shiyasa nayi mishi wannan haukan, ko ba komai dai ai shima ranshi ya b'aci, sai ita wannan y'ar iskar, da na samu nayi laying hannuna kanta wlhy da sai yadda Allah yayi da ita dan tsanar da nake mata baya misaltuwa", katseta Mummy tayi da cewa, "naji ya isa, d'azun nan su Zainab suka wuce Tchad, kuma duk kan aikin namu na turasu dan ni Daddynku ya hanani zuwa, toh yanzu abinda nakeso dake, siyasa zaki shiga yi masa ki nuna masa kinyi kuskure kuma kin gane laifinki amma hakan bazai sake faruwa, ki nuna mishi kina k'aunar ita yarinyar har sai ya aminta da hakan, itama ki nuna mata k'auna har sai mun samu munyi maganinsu shi da itan dukkansu da ma duk wani munafiki dake gefe, ni yanxu haka ba kud'i hannu na kuma Dad d'inku rabon da ya bani kud'i har na manta dan cewa yayi baisan mey nakeyi dasu ba, wai har sai na nuna mishi abu d'aya da na tsinana mai amfani da nayi da kud'in, yanzu haka nayi niyyan k'iranki in miki bayani akan tafiyansu Zainab d'in sai kika rigani, kud'i kawai xaki turo har Zainab d'inma wani senator da yazo wajen Babanku ya ganta yace yana sonta amma kuma yanada mata sannan Babanku yace ya turo dan ya bashi ita shine mukeso musan yadda za ayi da Matan nashi dan bazan yadda da kishiya ba, kinga kina turo kud'in sai ayi komai a gama, an jefi tsuntsu da dutse d'aya", Hankalin Ajiddeh ne ya fara kwanciya jin bayanin da Mummy ta gama yi mata tace "Mummy wannan kud'i duk ba matsala bane, yau da safen nan ya rubuta min cheque d'in miliyan uku da nace mishi ina buk'ata, banmaje nayi cashing d'insu ba a bank, xan turo sai ayi abinda ya kamata, amma Mummy d'ayan ne ban iyawa, wlhy na tsaneta yadda baki zato, bazan iya nuna ina sonta ba, Kawai in ansamu anyi abinda za ayi ta tattara nata ta barmin gida", tsaki Mummy taja tace "ai kinji ki, toh kije kiyi abinda kika ga dama tunda baza ki d'auki abinda na fad'a miki ba", cewa tayi "Mum ba hakane bane, kawai ni kallonta ma bana son yi ne", Mummy tace "na fahimceki, amma kowane mutum yana son a so d'an uwanshi, da hakan sai ya dad'a kyautata miki, kinga ko ta dalilin ta zaki moreshi bare shi dake son y'an uwanshi, lokaci d'aya zai Iya rabuwa dake ya maida wata gurbinki, amma y'an uwanshi bai tab'a iya canja su, shiyasa nakeso ki nuna mata so", cikin hanzari Ajiddeh tace, "Mummy abar wannan maganan, ni yanzu xan turo komai a gama", ta tsorata da jin da tayi za a iya canja ta, Mummy tace "toh shikenan yanxu ki tashi ki shirya kije ki bashi hak'uri ki nuna kinyi nadaman duk abubuwan da kikayi", wani munafikin murmushi tayi ta sake shigewa jikinshi da ta dawo daga tunaninta, shi kam Abutturab tunani yadda zaiyi da Batuul Kawai yakeyi duk randa Ajiddeh ta gano ita d'in matarsa ce yasan gidan nn sae yayi musu kadan, tunanin Batuul kawai yakeyi zamansu a wajen, Ajiddeh ta kalleshi tace "baby na fara jin bacci muje mu kwanta", kallonta yayi dan shi sam bayajin bacci, Batuul ma kawai yakeson gani yaga halin da take, yace Mata "I will b coming dear, bari in gama program d'innan its interesting, I will meet you up there", peck yayi mata daga haka ta mik'e tayi hanyan stairs, har ta fara tafiya ta juyo ta kalleshi tace "Baby, I will check on my Sister before leaving", da wani munafikin wide smile shimfid'e fuskanta da kana gani kasan yak'e take, kallonta kawai yayi har ta juya ta tafi, ya sauke ajiyar xuciya cikin ransa yace Allah sa har cikin ranki Ajiddeh.






Batuul kam bayan ta saka pad d'in sai da ta leqo kanta taga ya bar d'akin sannan ta sauk'e ajiyar zuciya ta fito dan mugun yunwa takeji, direct wajen ledojin ta nufa ta tsugunna wajen ta shiga bubbud'esu, na farkon drugs d'inta ne ciki, matsar dasu gefe tayi ta bud'e sauran, da murna ta shiga bud'ewa ganin abincin favorite restaurant d'inta Gordon Ramsay, pack d'in ta bud'e taga roast chicken, lavender, apricot, honey, d'ayan bowl d'in ta duba taga starter ne green apples, turnips sai watercress, wani irin farin ciki kawai takeyi, d'ayan pack ta sake dubawa pasta ne with shrimps kebab, babu b'ata lokaci ta tashi ta wanko hannunta, ko using spoon d'inma baza ta iya ba, sai da taci ta k'oshi ta maida ledojin gefe ta tashi ta cire kayan jikinta ta fad'a toilet, ko ta kan Maganin ma bata bi ta shiga tayi wanka abinta, ta fito kenan d'aure da towel taji an turo k'ofan d'akin, a razane ta d'ago kanta warce ta gani tsaye bakin kofa yasa hanjin cikinta mugun k'adawa, Ajiddeh ta karaso tana murmushi tace "Sannu sister ya jikin?" K'asa cewa komae Batuul tayi sae kallonta take, kuma da ganinta kasan a tsorace take, Ajiddeh bata damu da hakan ba sae ma murmushi da take tace "Amma kina da pad kuwa ko in dauko maki a daki" Batuul ta sunkuyar da kanta da kyar tace "Ina da shi" Ajiddeh tace "Toh Allah ya sauwake, kin sha magani kuwa?" Batuul tace "Ynxu xan sha," Ajiddeh tace "Toh sannu, ni na tafi in kwanta sae da safe" Batuul ta kalleta don har lkcn ta k'asa yarda Ajiddeh ce, a hnkli tace "Toh sae da safe na gode" Ajiddeh tace "Yauwa" sannan ta fice, Batuul ta sauke ajiyar xuciya ta isa inda kayanta yake cike da mamakin Ajiddeh, lotion ta shafa, snn ta shafa turarrukanta masu sanyi kamshi ta fiddo wani sabon sleeping gown dinta mara nauyi me d'an karamin hannu ta sa, ta xura gashinta cikin net, ledan maganinta ta bude ta fiddo magungunan ta sha snn ta ajiye su gaban mirror, ta nufi switch din dakin ta kashe wuta kenan don kwanciya xata yi aka bude kofar dakin, kin kunna wutan tayi don bata son ya ganta ba hijab kuma ta k'asa barin wajen, ya shigo dakin ya rufe kofar, da sauri ta nufi inda hijab dinta yake xata dauka yyi saurin fixgota yana mata wani irin kallo cikin duhun yace "Wae me kike boye min da ban sani ba a jikin ki, baki sanin muhimmancin Hijab sae na shigo dakin ki don rainin wayo koh?" Kokarin kwace kanta ta shiga yi a hannunsa yace "Stay still kar in mareki" sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, a hankali yace "Ya cikin?" Kin cewa komae tayi ya D'ago kanta yace "Am talking" ta rufe ido kmr yana ganinta murya can k'asa tace "da sauki" yace "Sure?" Shiru tayi bata ce komae ba, yace "ko kina son a maki massaging Abdomen..." Da sauri tace "No na samu sauki" murmushi yyi yana kallon d'an karamin bakinta dake motsi a hankali, yace "Sure?" Runtse ido tayi ta janye hannunta xata bar wajen, ya fixgota jikinsa, wani irin faduwar gaba taji jinta a jikinsa, suka ji an bude kofa can corridor, saketa yyi da sauri ya juya ya nufi kofa.
[8/22, 14:48] Umar Dalha: BATUUL
54
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Yana fita d'akin Batuul a corridor ya
tarar da Ajiddeh a tsaye, wani irin
kallo ta bishi dashi ganin ya fito
d'akin Batuul, bak'in cikinta ta shiga
dannewa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login