Showing 213001 words to 215266 words out of 215266 words
us to realise each others worth, how much we mean to each other, Yaa Abu plssssss", ta k'arasa maganan tana lumshe ido , shi kad'ai yasan irin impact d'in da Batuul ta yiwa rayuwanshi, mesa baza ta fad'i wani abin ba sai wannan, har ga Allah ko jiya da Abui ya sake mishi zancen Ajiddeh ce mishi yayi zai rabu da ita, zai sallameta, duk da ya yafe mata shima amma ya kasa samun wajen da zai ajiye abinda ta aikata ya manta dashi, baya tunanin zai iya d'aukan wani abin da zai sami family d'inshi ya qyale maishi nan gaba, amma its about Batuul yanzu, she is worth more than that, He can sacrifice that atom of happiness da ya rage mishi for her to be happy, tana son ya maida Ajiddeh d'akinta, kuma alk'awari yayi mata akan ta fad'i abinda takeso, how can he just deny her , a hankali ya sauk'ar da idonshi kan fuskan Batuul ya shafi gefen fuskarta da d'aya hannun nashi yace "will that make you happy?", kai ta kad'a mishi, murmushi yayi mata yace "Anything for you Fatima, just know I will always love you", murmushin ta mishi amma jin yanayin da yake sab'ule hannunshi cikin nata yasa murmushin dake fuskarta bajewa, duk da rashin k'arfin da takeji hakan bai hanata damqe hannunshi ba, kallonta yayi, ganin hawaye idonta yasashi zama da wuri yana girgiza mata kai, cikin siririyar muryarta tace "Are you sad, angry about what I requested for?, ka bari na fasa if you are not okay with .....", bai bari ta k'arasa ba ya d'aura dogayen yatsunshi kan lips d'inta yace "Shhhh, am happy with whatever that makes you happy, okay?", kai ta kad'a mishi yayi murmushi yace "Good girl, get some rest", ya fad'a yana d'aga mata girarshi d'aya, murmushin tayi mishi itama tareda lumshe ido, ido ya tsura musu itada y'ar Babyn dake gabanshi yana kallonsu yana dad'a yiwa Allah godiya da ya bashi wad'annan precious kyautan a rayuwanshi, yana nan zaune yana kallonsu aka turo k'ofar d'akin, Abui ne sai Ammah, Farida sai Sadiq, lokacin doctors suka sanar dasu da Batuul ta sauk'a lafiya zasu iya shiga su kanta, tsabar murna Farida har rawa jikinta keyi sbd d'okin zuwa taga niece d'inta, y'ar yayanta y'ar Bestyn ta that turn out to be a sister, Abui ne ya fara d'aukan Babyn da murmushi a fuskanshi yana tuna lokacin da ya fara riqe Abu for the first, yace "This is how I held Aliyu , kamar jiya fa gashi yanzu Allah ya bani tsawon rai nayi witnessing haihuwar y'arshi, Allah yayi muku albarka baki d'ayanku", ya fad'a tareda kissing goshin yarinyar, duk suka amsa da "Amin", Ammah ce ta karb'eta daga hannun hannun Abui murmushi d'auke fuskanta snn ta kalli Batuul dake kwance tana bacci tace "Allasarki Bitti, yadda kukaga wannan jaririyar haka Fatima take lokacin da aka haifota, tun ranan Allah ya dasa min sonta a raina kamar ni na haifeta, ashe itace zata fara samar min jika, Allah ya k'ara miki lafiya ya d'ayyiba miki zuri'a", duk suka amsa da Amin, Abu ya dubi Ammah yace "Ammah an fad'awa su Aunty? Tun d'azu take nemanta", ya fad'a yana kallon Batuul, Ammah tayi murmushi jin Batuul nata Neman Aunty tasan zafin haihuwar yasa ta neman Aunty, tace "Dama ana shiga da ita na fad'a musu toh bayan doctor ya fad'a mana sauk'arta lafiya nayi maza na sanar dasu, da yake ma can d'in za a kaita basai sunzo nan d'in ba ai", ya d'an tsuke baki yace "Ammah har yanzu wai zancen kaitan na nan?, wlhy hankalina zaifi kwanciya in ina kusa dasu, zan kula dasu Sosai In sha Allah, Plssss Ammah", ya k'arashe maganan kamar mai shirin yin kuka, dariya ma yaso ya bawa Ammah amma ta dake tace "Kai nifa ban cike da shirme kana jina, ba al'ada bace da zaka wani ce kafison a bar maka su?, toh ba kanka za a dena ba, gidansu ne sai ta tafi yin wanka", badan yaso ba ya hak'ura ya miqe tareda yin sallama dasu, Farida da batasan me ke faruwa ba duk hankalinta na kan jaririyar kamar zata maidata ciki ya duba yace "Farida let her be plssss, bacci takeyi", kallonshi tayi da murmushi a fuskanta tace "nifa nasan da ni take Kama, bari ta tashi zaku gane abinda nake fad'a muku", kai kawai ya kad'a yace "Naji ai ke zakiyi rainaonta but for now barta ta huta, bata ma saba da iskan duniyar ba bare wahalar cikinta", cikeda murna Farida jin yace ita zata yi raino ta matsa da baya da sauri tace "Ai na ma matsan, Allah ya raya mana Babyn mu, Sunan waye za a saka mata?", har ya fara tafiya kamar ya fad'a mata ko sunan wa yarinyar zataci ya fasa, Abui ne kad'ai yasan meye sunan jaririyar, yayi murna sosai ya sa musu albarka su dukkansu, tareda fatan Allah ya k'ara had'a Kansu, Sallama yayi da Ammah da Farida ya fice daga d'akin, Kai tsaye gidan Aunty ya, yasa akayi mata magana dan bata parlour ko kince, kamar kullum cikin shigarta ta alfarma da gayu ta sauk'o, ganin Abu ne yasa ta d'an fad'ad'a murmushin dake fuskarta, yana hangota ya sauk'o daga kan kujeran tareda d'an duk'awa ya gaidata, wani kunyan Aunty yakeji yau na daban, ta amsa mishi snn ta mishi barkan k'aruwan da ya samu tareda addu'o'i, murmushi kawai yakeyi yanajin dad'in addu'ar da take musu, tasa aka kawo mishi refreshments, ruwan kawai ya bud'e bai kai ga sha ba ya fad'a mata abinda ke tafe dashi, might murmishi Aunty tayi, ita da kanta taji tausayin Batuul, tasan wahalan haihuwan da ta sha ya sa take son ganinta, da murmushinta tace "Kaima Aliyu sai ka biyewa shirmenta Batuul kaima, me zuwan nawa ma zai mata in banda shirme irin na Batuul, addu'a kawai zamuyi mata da fatan sauk'a lafiya kuma Alhamdulillah Allah ya amsa mana addu'a, sai kuma yanzu muce Allah ya k'ara musu lafiya ita da abinda ta haifa", kanshi a k'asa yace "Aunty ayi hak'urin dai muje in ta farkan ta ganki dan tun d'azu take ambatonki, she will be to wake up to you by her side", Murmushi kawai Aunty tayi tace "Tohh shikenan bara insa a shirya mata abubuwan da na sa akayi mata sai insa Baa Liman ya kaini in tq gannin hankalinta ya kwanta na dawo", Sam Abu yaqi yadda saidai Aunty ta bishi, badan taso ba ta haqura suka tafi, a asibiti da kanshi ya bud'e mata k'ofa tareda samo ma'aikata su shiga da kayayyakin dake baya, har lokacin Batuul bacci takeyi, har mamakin yawan mutanen dake d'akin yayi, sai barka suke mishi da Allah ya raya, gaisawa yayi dasu snn yayi musu sallama ya fita, yana fita ya qira Massa akan zaizo ya sameshi zai rakashi, kai tsaye gidan ya wuce, Abu ke tuk'a motar Massa na daga gefe yana taya Abun murnar k'aruwa, sai shak'iyanci yake mishi, ganin yaqi kulashi yace "Wai kai inama zamune haka?", Abu ya shafe fuska yace "Gidansu Hauwa zani, I promised Batuul to take her back", Massa ya wara ido yace "Amma kai duniyanci duk ka iyashi, are you telling me all these while tana gidansu da aurenka kuma kanta?", Tsaki yaja yace "Kaga ni karka dameni, she caused everything, and I can do it bitter and better than what I did, am talking about Fatima, she is my reality, I can't risk anything da zai cutar da ita, and taking back Ajiddeh is a compromise, she told me she dd be happy, so please spare all these naggings", Kafad'arshi Massa ya dafa yace "You are a man, you can take whatever, kawai Addu'a zakayi Allah ya shige maka gaba", a sanyaye ya amsa da "Amin", shi gaba d'ayanshi baisan ta ina zai fara ba, seven months amma bai tab'a waiwayarta ba sai Yanzu, har yazo k'ofar gidansu Ajiddeh yana sak'e sak'e a ranshi, masi gadi da sauran ma'aikatan dake bakinta da murna suka dinga gaidashi dan sun sashi da kyauata da yi musu alheri, saida yayi parking yasa a duba mishi ko Dad na gidan, in yana nan ayi masa iso dashi, hakan kuwa akayi akace musu yana daga garden, can wani yayi musu jagora suka isa, yana zaune kan d'aya daga cikin kujeraun dake k'ark'ashin hut d'in wajen da ruwa gabanshi, da mamaki Dad ke kallon su har suka k'araso wajenshi, a ladabce suka gaida Dad, da fara'a ya amsa musu kamar wani abu bai shiga tsakaninshi da y'arshi ba, har saida Abu yaji kunya ganin yanda Dad ke janshi a jiki, shiru ne ya biyo baya kqmin Abu yayi k'arfin hali a sanyaye yace "Dad munzo mu bada hak'uri kan abinda ya faru, kuskurene da muka aikata bisa son zuciya, nazo in koma da Hauwa d'akinta, Allah ya have mana baki d'ayanmu" Dad da ya k'ura mishi ido ya cire glass d'in dake idonshi yana kad'a kai yace "Aliyu tun lokacin da Hauwa tazo min da zancen kai zata aura nasan tayi sa'an miji, nayi murna sosai dan nasan zaka kula da ita iya gwargwado, tun kana k'arami lokacin Ina aiki k'ark'ashin mahaifinka nasan kai yaro ne mai dattako, Aliyu ta fad'amin duk abinda ya faru tsakaninku da ita saidai kunyar mahaifinka da nakeji bazai barni inje baku hak'uri, nasan sunyi muku kuskuren da bai canci wannan yafiya ba, saidai duba da irin gidan da ka fito yasa bazanyi mamaki ba, ina mai sake baka hak'uri kan abinda suka aikata muku,, maganar kkmawar Hauwa kuma Aliyu tunda ka tako da k'afarka bazan iya hanaka ba, amma tunda hakane inason duk wani kuskure da zata sake maka ka hukuntata fiyeda yanda zanyi dan in har ta yadda ta sake takowa gidan nan da sunan tayi maka laifi toh saidai ta nemi wani uban ba ni ba kuma", daidai Abu zai amsa wata mata ta k'araso da babbar rigan a hannunta, bata lura da mutannen dake wajen ba ta k'arso tana cewa "Daddy nikam baka gama karanta Jaridan ba, you are getting late fa", sai lokacin ta lura da su Abu, dukda face d'in Abu looks familiar but ta kasa tuna inda ta sanshi, Dad yayi musu introducing juna kan itace sabuwar matar da ya aura 4months back sunanta Kulthum, su kuma ya nuna Abu yace "wannan shine mijin Hauwa Aliyu, wannan kuma d'an uwanshi ne Mustapha", sai lokacin ta tuna inda ta sanshi, duk d'akin Ajiddeh hotunan shine hatta gaban wayarta hotunanshine, da murmushi suka gaisa, Dad ya karb'i riganshi yace "Sai su shiga daga ciki, ni inada meeting, yanda kukayi duk ka sanar dani Aliyu", ya Amsa mishi da Insha Allah da yi mishi fatan a dawo lafiya, a d'akinta Aunty Kulthum ta tarar da ita kwance duk ta rame tayi duhu, kamar ba ita bace ba wannan Ajiddeh sarkin gayu da d'osana lipstick ba, gashin nan ma da yake shan gyara duk ya kad'e, wutan d'akin Aunty Kulthum ta kunna tana mai k'iran sunan Ajiddeh
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels