Showing 204001 words to 207000 words out of 215266 words
tace "da spicy French fries plss", murmushi yayi mata kawai ya tafi, baifi five minutes da tafiya ba ya dawo, baisan lokacin da murmushi ya k'wace mishi ba ganinta zaune k'ark'ashin wasu manan rose Petals a wani perfume stall, sosai tayi kyau sbd kayan dake jikinta suma pink ne, abubuwan dake hannunshi ya ajiye ya ciro wayarshi daga aljihu yayi snapping d'inta pictures batareda ta lura ba, har ya isa wajenta yana murmushi, gabanta ya tsuguna tareda mik'a mata floss d'in, da wide smile ta karb'a tayi mishi mouthing "Thank you", kai ya girgiza mata yana nuna mata cheeks d'inshi, wara ido tayi tana blushing tana girgiza mishi kai, baza ta iya ba, kunyan shi duk ya gama cikata, ganin taqi yi ya zumb'uro mishi bakinshi ya miqe zai bar wajen, hannu tasa ta riqoshi, saida yayi murmushi snn ya juyo yana kallonta, a hankali tace "da mutane anan, in munje gida pls", hannunshi zai sake karb'a tace "toh close your eyes", lumshe ido yayi a hankali ta dawo gabanshi, d'age tayi sbd tsawonshi, ji tayi ya d'aura hannu waist d'inta ya d'agata sama, pecking kumatunshi duka biyu snn ta maida kanta ta sinnewa jikinshi, tafi taji duka wajen ya d'auka, tsabar kunya kasa d'agowa tayi, tana jikinshi ya mayar dasu wajensu sukayi zamansu, 11 daidai sukayi boarding jirgi, in banda bacci babu abinda takeyi, lokaci lokaci take tashi, murmushi kawai zai mata ko kuma ya tambayeta in tana da buk'atar wani abin, har suka isa UK
[12/16, 12:14 AM] +234 808 135 1434: 💖💝BATUUL💖💝
96
By Phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Hawayen da kanshi nema take ya zubo ko zataji dad'i ta rasashi, ido ta k'urawa Mummy dake kwance duk jikinta anyi bandaging gwanin tausayi, tunda taga yaqi d'aga k'iranta tasan babu yadda za ayi yazo, tunanin Abutturab yasa ta jin silalowar hawayen da take ta neman zubowarsu ko zata samu y'ar nutsuwa, amma Sam abun ba haka yake ba, saima rad'ad'i da ya k'arama zuciyarta, tun da Dad ya fita bai sake shigowa ba har yau, a hankali taga Mum na k'ok'arin bud'e ido, da kyar ta bud'esu tana k'arewa d'akin kallo, kan Jainaba dake kwance ta d'aya b'arin idonta ya fad'a, hawayene kawai ya dinga silalo mata, a hankali ta maida dubanta ga Ajiddeh dake zaune, rintse ido Ajiddeh tayi ta bud'e snn tace "Mum wani irin fitina ne wannan nake gani a rayuwa?, duk wata masifa ta rayuwa na gama ganinta, Mum kece silar duk wani tashin hankali da nake ciki yanxu, tun ina k'arama tun Dad baiyi arzik'i ba, tun kamin inyi hankali na fahimci duk abinda kike so sai kin sameshi ko da ya kaucewa shari'a, tun bamuda arziki kike cewa mucewa k'awayenmu mufa y'ay'an wane da wanene, tun ban fahimta ba har na gano ma'anar inda kika dosa muka fara biye miki, babu yanda Dad bai nuna k'ok'arisnhi kanmu ba dan mu gyara amma kan ya faskara saboda kullum tare dake muke, zamanmu dake yafi yawa dole mu d'au ak'idarki, Mum kece uwa ta farko da na fara ganin bata tab'a yiwa y'ay'anta fad'a kan abinda babu kyau ba, baki tab'a tsawatar mana akan laifinmu ba, Dad ne kad'ai ke mana fad'a, ana haka Dad yazo ya samu arziki, d'an time d'inshi da muke samu yazo ya zama bama samu, duk wani jin dad'in rayuwa mun samu saboda irin son da yakeyi mana, amma ko shi Dad naga ba time d'inshi kikeda ba sai abinda yake dashi, kin koya mana son abin duniya da muka d'auka muka girma da, nima nasa a raina zanso mutum amma saboda kud'inshi", tayi shiru tana shesheka ta kalli Mummy da ta rintse ido tana kuka, taci gaba, "Allah mai yi yadda yaso da bayinshi ya had'ani da Aliyu da kallo na d'aya naji duk duniyar nan babu wanda nakeso kamar shi, babu possible ways d'in da ban bi dan yasoni amma ko zamana baisan da ba, a haka na tareki da zancen, tashin farko Mum cewa kikayi zamuyi maganinshi, haka mukayi ta bin bokaye, duk basuyi tasiri akanshi ba har saida na samu nayi plan d'in da ya bigeni da mota, ni nasan Aliyu bai tab'a sona ba, amma saboda son da nake mishi yasa bazan iya barinshi ba, ya aureni bawai dan yana so ba, nasan ya rasa abin yine saboda matsa mishi da akayi a gida, na samu fatana ya cika, my dream came true na zama matar Aliyu amma son zuciya da tsoron rasashi suka rinjayeni, babu abinda na tashi saka mishi da sai rabashi da nayi da iyayenshi da danginshi har tsawon shekara, Allah da yake shi ba azzalumin bawanshi bane ya saka mishi, iyayenshi sanin da sukayi ba haka kawai zaiyi haka ba, ba zasu zauna suna gani d'ansu ya halaka ba suka nema mishi aure", dariyan takaici ta saki tana girgiza kai taci gaba tace "Dole ma Allah ma yayi mishi sakayya ta alheri, mey na tab'a yi mishi na zamantakewar aure?, ko tsinke ban tab'a dagawa gidana ba bare inje ga zancen girki, a haka ya dawomin da yarinyar gida, tun had'uwata ta farko hankalina bai kwanta da ita ba, dukda kullum ina admiring duk wani abu nata, nutsuwa, kunya, k'awaici amma hakan baisani ganin gaskiya ba sabida son zuciya, Baiwar Allah jikina dama yana bani da wani abu a tattare da ita mai girma, amma son zuciyata yasa na cutar da ita, da na tab'a sanin akwai ranan da zan bud'i ido inji Aliyu na korata kan yarinyar nan da ko kallon banza ban jifarta dashi bare mugun kaba'iri, gashi a dalilin cutarta da nayi yasa yace ko kallona bai sakeyi, am not putting all the blame on you Mum, I have a commision a ciki, in kinyi abu mara ai nima nasan daidai zan iya gyarawa, shiyasa Allah ya bani hankali amma naqi aiki dashi, gashi we are accounting for all our deeds, we are reaping what we sow, Mum ni bansan mey kikaje yi har illorin ba amma nasan ba alheri bane ya kaiki, gashi nan Allah yana nuna mana ishararsa, Na kirashi yazo mu nemi yafiyarsu Mum yaqi d'agawa, ko yafiyarshi ne yazo in roqa", Sai lokacin Mum ta bud'e idonta da suka kad'a da k'yar tace "Hauwa duk wani abu da nayi dan Ku nayishi, babu wanda nakeso da k'auna duk duniyan nan sai ku da Allah ya mallakamin, banida kowa sai y'ar uwata Jainaba, mun taso cikin k'unci nida Jainaba da nayiwa kaina alk'awarin y'ay'ana bazasu fuskanta ba, ba haka naso rayuwa ta juya mana ba, kuyi hakuri Ajiddeh, nafiku jin ciwon duk abin nan da yake faruwa, tafiyan nan da nayi duk dan nema muku farin ciki na fita yinshi, farin cikinku shine nawa, ku yafemin, ta fashe da wani sabon kukan
Suna sauk'a cab ya tara suka wuce d'ayan gidanshi, ko da sukaje Bacci Batuul keyi, ita kawai ya d'auka a hannu cak ya shiga cikin gida ya kwantar snn ya dawo ya kwashi Luggages d'insu ya shigar, saida ya fara wanka ya rama sallolin da ake binshi kanshi kamin ya dawo gefenta ya zauna, hannu yasa ya shafi gefen fuskarta tareda matsar da kitsonta dake kwance kan fuskartata, baccinta har dariya yake bashi, slight opportunity take jira ta rufe ido, a hankali ya furta "Glitter", kamar ma bataji ba sai juyawa da tayi tana gyara kwanciyarta, hannu yasa d'agota yace "Sleepy head tashi kiyi Sallah kici abinci", zumb'uro mishi baki tayi tana sulalewa saga jikinshi tace "um um, bacci nakeyi nikam", ya d'agata ta zauna snn ya hura mata iska a fuska yace "Its getting late Glitter, kinga kuma bakiyi Sallah ba, and my Baby needs to eat", a hankali ta bud'e ido tana mik'a, tashi yayi ya tsayar da ita taje toilet, saida tayi wanka snn tayi alwala ta fito d'aure da towel, yana zaune gaban Desktop yana danne danne, ido ya kafa mata ko k'iftawa bayayi yana roaming dukan jikinta, duk kallon da yake mata bata lura saida ta zauna zata shafa mai ta ga idonshi a kanta, zumb'uro baki tayi tace "ashe kai ke kallona shine naji towel d'ina yana so ya fad'i?", murmushi yayi yace "ai inma bai fad'i ba ni da kaina zan cireshi", dariya kawai tayi ta janyo hijabi ta saka dan tasan zai iya cirewan shiyasa batace komai ba, saida ta idar tukunna ta tayi shafe shafenta ta saka kaya, y'ar sweat doguwar riga ta d'auka ta saka navy blue, tashi yayi ya dawo kusa da ita yana girgiza mata kai yana isa wardrobe d'inta yace "we are going out to eat, sai mu wuce hospital, kinada appointment, kayan nan basu min ba, change into something light, waje akwai sanyi", kaya ya ciro mata ya mik'a mata, karb'a tayi ta saka kayan, straight gown mara hannu da beach kimono peach mai brown patterns snn ta d'auki brown veil ta yafa, tare suka fita ya bud'e mata front seat ta zauna ya zagaya d'aya side d'in ya shiga, asibitin ya fara zuwa suka ga doctor, bayan ya gama dubata yace itada Babyn are all fine, shawarwari ya basu sosai akan abinda ya kamata tanayi da wanda zatayi avoiding, snn yace ta fara Exercises ko da kad'an na 30 minutes ta na kuma wasu sporting activities ko indoors ne, tun suna zaune office d'in take yatsina fuska tana jin yunwa ta k'osa subar wajen taje taci abinci, suna fitowa ta marairaice mishi fuska tace "Yaa Abu", shi da kanshi yasan yunwar takeji amma, a hankali ya rik'o hannayenta cikin nashi yace "Yunwa ko?", kai ta gyad'a mishi yace "sorry yanzu zamuje kici abinci, okay?", a hankali tace "Ehen", saida ya zaunar da ita a mota snn ya zagaya ya shiga side d'inshi, driving yakeyi yana ta mata hira duk dan ya d'ebe mata damuwar yunwar da takeji, duk inda taga restaurant sai ta kalleshi taga ko zai tsaya amma sai taga ya wuce har taga sun d'auko hanyan gida, a gaban Orwell's restaurant taga ya tsaya da motar, ajiyar zuciya ta sauk'e amma ganin kamar babu kowa wajen ta dubeshi tace "kaga bafa su bud'e ba", baice komai ba sai hannunta da ya kamo sukayi bakin restaurant d'in, gaba d'aya wutan a kashe yake kamar ba a aiki a restaurant d'in, bakin k'ofan taja ta tsaya, raurau tayi da ido tace "mey zamuyi a nan?, nikam tsoro nakeji, mu tafi", hab'arta ya d'ago yana kallon idonta dake glittering yace "The trust?", idonta ta sauk'e k'asa tace "toh fa cikin duka duhu, basu bud'e bama yau naga", hannunta ya kama suka kutsa ciki, dukda duhun da wajen keda wani irin k'anshi mai dad'i ke tashi a wajen, a hankali taji ya sake mata hannu, sai nemanshi tayi ta rasa a wajen, gabantane ya shiga fad'i ta shiga lalubenshi, har idonta ya fara tara hawaye jikinta ya soma rawa, a hankali kamar wacce bataso a ji abinda take cewa tace "Yaa Abu", sau biyu tana maimaitawa taji shiru bai amsa ba, da k'yar ta iya d'aga k'afa zata juya kenan taga haske ya dallare ko ina, wani irin view take gani ko ina na hall d'in sai glittering sukeyi, komai na wajen peach ne da brown, yunwar da takeji ma gaba d'aya nemanshi tayi ta rasa, sosai wajen yayi mata kyau ba kad'an ba, daga tsakiya ta hango isle dayake da wani irin haske, Abu ta hango daga gefen isle d'in jingine yasa hannunshi cikin wandon riganshi yana mata murmushinshi mai kyau, sai lokacin ta lura da itama murmushin ne a fuskarta, a hankali ya tako inda take tsaye ya mik'o mata hannayenshi duka biyun, har ta mik'ar da nata zata kama nashi ko meye ta tuna ta zumb'uro baki ta fasa, a hankali ya juyo da fuskarta ya rik'e kunnuwanshi duka biyun yace "am sorry Glitter", idonshi kad'ai bazai barta ta iya fushi dashi ba, space d'in dake tsakaninsu ta cike tareda yin d'age ta zagaye hannayenta duka biyu ta bayanshi, shima hannayenshi yasa ya zagayeta, sun kusa minti d'aya a haka snn ta janye jikinta ta kalleshi tace "This is beautiful", hawaye ya gani tare a idonta, kai ya girgiza mata alamun kada ta bari hawayen su zubo, dariyan da tayi yasa su zubowa a tare, shima dariyan yayi yasa hannu ya goge mata duka hawayen snn yace "Anything for you", ya rik'o hannunta suka taka takan flower petals suka k'arasa isle d'in, suna zama wasu mutane da kana gani kasan waiters ne sukazo wajen, da hannu Abu yayi musu alama da su koma, kujerarshi ya matsar kusa da da nata ya warware mata veil d'in dake kanta ya maida matashi turban snn ya d'auki plate yayi serving mata abinci, da kanshi ya d'auki spoon ya d'ebi abincin ya kai mata bakinta, kallonshi kawai takeyi a ranta tana yiwa Allah godiya da ya sa Abu ya zama mijinta, a hankali ta bud'e bakinta ya saka mata, murmushi yayi mata yace "Yayi miki?", ta gyad'a mishi kai tace "sosai", sake d'ebowa yayi zai kai mata baki ta riqe cokalin ta juyar bakinshi , bai musa ba ya bud'e ta zuba mishi abincin, haka sukayi ciyar da junansu cikeda farinciki, sai suka gama cin abinci ya zagaya ta bayanta, a aljihunshi ya ciro wani diamond pendant sark'a, da kanshi ya saka mata snn ya sumkuya daidai wuyanta yayi tareda kwanto ta baya yana kissing wuyarta, ido ta lumshe tana jin d'umi da laushin lips d'inshi a wuyanta, saida ya d'ago yace "For Everything Fatima, I will forever Love you", snn ya dawo ya zauna kan kujerar, hannunta ya kama ya zaunar da ita kan cinyanshi, wani plate ya bud'e, shima zobe diamond ne ciki sai glittering yakeyi, ido ta wara ganin kyan zoben, she wasn't expecting it, ta kalleshi taga murmushi yakeyi tace "This too", girarshi dake cike ya d'aga mata tareda kamo yatsanta, tace "You are not proposing to me right, we are married", yace "You will b the girlfriend I will always want to hear from your melodious Voice, the fiance I will always dream of and the wife that will be be my responsibility to care for, my strength and weakness, a wife that will help me complete my life", bata tab'a voicing wa kowa dreams d'inta ba amma gashi Yaa Abu kamar zuciyarta ya shiga ya gano komai, wani irin murna takeyi da tunda ta dad'e batayi irinshi ba, kai kawai ta gyad'a mishi dan bakinta ya kasa bud'uwa, shima cikeda murna yayi slipping zoben cikin d'an yatsanta na dama, ya sunkuya yayi pecking zoben, batasan mey zatace mishi ba ya nuna cewa itama mai sonshi ce, ta nuna mishi cewa shine completion d'in duk wani mafarki nata da takeyi tun tana k'arama, a hankali tayi leaning ta had'e lips d'insu, yau ita tayi dominating, sosai tayi kissing d'inshi saida ta gaji dan kanta ta zama submissive ta bashi entrance, kwanciya tayi lamo a jikinshi ta maida numfashi, a hankali ta furta "I love you more", goshinta yayi pecking snn shima yace "I know and I love you more", haka suka zauna suna savouring each moments tareda nunawa junansu yadda suke son juna, sai yamma suka tashi tafiya, ganin basu shiga motarsu yasa ta tambayeshi yace "Let's walk down tunda babu nisa, I need a walk with you, zasu kawomin motar har gida", murmushi kawai tayi ta sak'ala hannunshi cikin nata suna tafiya cikeda farinciki, a hanya take tambayanshi yaushe duka ya shirya wannan Romantic Lunch d'in, yace ya dad'e yana son yayi but yafi son sai tayi confessing tana sonshi itama, ranan da tayi confessing ranan ya fara shirye shiryen komai, ta kad'a kai tana dad'a jinjina mishi tace "Orwell's fa babban restaurant ne, one of the best in Uk, you paid for it all?", dariya yayi yace "tunda na fara gina wannan gidan naga yadda ake partronising na sayi franchise d'insu, wanda yake Manchester nawa ne, so we are partners, inda kud'i anything is possible" kai ta kad'a sai yanzu ta sake sanin lallai mai kud'i ne shi tunda ya iya siyan franchise d'insu ya bud'e branch a Manchester, suna hira har suka k'arasa gida da k'afa, suna tafiya yana ta d'aukanta hotuna, farinciki fal ransu basuda wata damuwa, itace ma lokaci lokaci take tuna Ajiddeh duk sai taji babu dad'i
Washe gari tunda sukayi Sallah asuba ya sata shiryawa wai doctor yace tana yin exercises, yau zasuyi ball tare, batayi baccin asuba ba ta saka bak'in jeans da jar rigar Adidas, sosai tayi kyau abinta, face cap d'in na NY ta saka, ita ta fara sauk'owa k'asa ta had'a teashi kuma ta had'a mishi coffee, bayan ya gama sha suka fita filin gidan daga baya akwai recreational fields iri iri, football pitch sukayi, dariya ya dinga mata ganin yanda take wasan har suka gama, duk ta gaji, ita ta fara wanka snn ta had'a mishi ruwa ya shiga shima yayi, kamin ya fito har ta shirya ta sauk'o kitchen ta dama mishi kunu ta had'a fish roast a oven tq kunna snn ta ciro bread d'in da zatayi musu musu toasting, snn ta koma sama bayan ta gama kamin ya dahu, zaune ta tarar dashi dagashi sai towel, taimaka mishi tayi ya shafa mai ya shirya snn suka sauk'o sukaci gaba da aikin tare, in ka gansu gwanin sha'awa basuda wata damuwa
*SEVEN MONTHS LEAP.....*
[12/16, 12:14 AM] +234 808 135 1434: 💖💝BATUUL💖💝
By Phartiemarhk
97
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
*.........SEVEN MONTHS LEAP*
Tsaye take a kitchen da yamma tana soya wainar fulawa, wayarta da tayi k'ara ta duba, ganin mai k'iran yasa ta sakin wani k'ayattacen murmushi, da wannan sunyi waya a yau kad'ai yafi sau goma sha biyar, har face time sunyi amma yanzu ma k'iranshi ke sake shigowa, hannunta ta goge da napkin snn ta d'auki wayar tasa a kunnenta, tana d'agawa taji yace "Glitter ki dena bari yayi ta ringing before you pick", murmushi tayi tace " Amore aiki nakeyi before ka bugo", ido ya wara kamar yana gabanta tareda dafa goshinshi yana tafiya yace "Ya Allah, aikin mey kikeyi?, ba nace bana so ba?", ji tayi maganarshi na kusantota, a hankali ta juya inda take jiyo muryan, k'ara ta saki tareda yar da wayan