Showing 138001 words to 141000 words out of 215266 words

Chapter 47 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1747

Ajiddeh ce ta samo ta dirqo, chain d'in aka rufe k'ofan da ta warware ta bud'e musu suka fito, ba a jin motsin kowa sai kukan tsuntsaye, a haka suka fito suka kama hanya, saida sukayi tafiya mai nisa duk sun galabaita har sun fara canza kamanni tukunna suka ga wata mota da aka kwaso bunsurai a ciki, tsaida mai motan sukayi sukace mishi ya kaisu cikin gari, cikin bunsuran nan suka kutsa suka zazauna duk wari, Ajiddeh dae kasa kuka ma tayi don takaici, sai da ya kaisu cikin gari sannan Mummy ta ciro kud'in can ta bashi dan bai wuce d'ari biyar ba, sai da suka nemi abinci sukaci daga nan suka fara tunanin yadda zasu koma gida, Ajiddeh ce tace "Mum nifa ban kuma kwana garin nan, kusan yadda zanyi In koma dan in Aliyu ya gano k'arya nayi mishi to kowa sai ranshi ya b'aci", Aunty Jainaba da tayi tagumi tace "yanzu abinda za ayi, ni akwai kudi guna tunda shi d'an iskan can bai shigo ya tsiyata mu ba, amma kud'in ba masu yawa bane, ba zaiyi sponsoring mu duka ba, sai dai in zaki fara tafiya ke sai ki turomana mu koma muma, kamin nan zamu zauna wajen Ayyi har ki turo sai a San abin yi, da haka suka yanke shawara suka rakata airport suka yankar mata ticket, Mummy ta share xufa tace "Toh ae ynxu sai mu koma gun mai mana aiki da, don dama ba wai bae iya aikin bane, aikinsa daukan lkci gare shi kafin ya ci," ko kallonta Ajiddeh bata yi ba, don abun duniya sun taru sun mata yawa, ga uban asaran kudin da tayi.






Kuka Batuul ta dinga yi tana sauk'e ajiyar zuciya jikinsa, ya kasa cewa komae don har cikin ranshi yake jin kukan nata, dad'a rungumeta yayi sosae ya daura kanta a kirjinsa, a haka har ya samu tayi baccin amma har lokacin tana sauk'e ajiyar zuciya, shi kam sam ya kasa rintsawa gashi yana son yayi wanka amma ya kasa dauketa daga jikinsa, sai wajen k'arfe biyu ya samu bacci ya dauke sa shi ma, da asuba ya dad'e da tashi har lkcn tana jikinsa ya kasa kwantar da ita jin yanda jikinta ya dau xafi, kallonta yake yana kwantar mata da dogon gashinta da ya barbaje a hankali, kamar ya maidata ciki haka ya dinga ji, wani irin feeling yake ji a tattare dashi da ya kasa gane ko wane iri ne, a hankali ya lumshe ido yayi kissing lips d'inta ya kwantar da ita ya shiga toilet, da k'yar ta iya bud'e idanuwanta da suka kumbura sukayi ja jin ya shige toilet don tuni ita ma ta tashi sai dai bata nuna masa idonta biyu ba, tayi yunk'urin tashi taji wani azababben ciwo, bakinta ta toshe dan kar tayi k'ara ya jiyota, da k'yar ta samu ta miqe daga gadon tana d'ingishi ta fice daga d'akin, babu abinda takeyi sai hawaye, tana shiga d'akinta xani kawae ta iya daurawa ta fad'a kan gado ta fashe da kuka abin tausayi, sunan Aunty da Baba ta dinga k'ira, ita kadai tasan abinda take ji a lokacin, wani baccin wahala ne yayi gaba da ita, Abuturrab na fitowa daga toilet yaga bata dakin, murmushi yayi, yayi hanyan kofa zai fita yaji wayarshi na ringing, komawa yayi ya d'au wayan, da mamaki yake kallon screen d'in ganin mai kiranshi, yana d'auka yaji tace "Hello bae na dawo fah, yanxu na baro airport ina hanya, na ma kusa" girarshi d'aya ya d'age kamar tana wajen a daburce yace "ke hankalin ki d'aya kuwa? bakice min zaki dawo ba kika d'auko hanya kika taho" da mamaki tace "Haba babe, sai nace maka xan dawo, beside kwananmu nawa bamu had'u ba, ko d'okin ganina ma bakayi" ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "ohk then, Fine naji" da haka ya katse k'iran ya jefar da wayar kan gado, hannu yasa ya baje gashin kanshi ya lumshe ido, duk ya rasa abun yi, he is just confused, idonshine ya fad'a kan bedsheet d'in da yayi staining, d'an tsaki yaja ya yaye bedsheet d'in yayi toilet dashi ya jefa cikin washing machine, fitowa yayi ya canja wani, ya juya kenan zai koma toilet Ajiddeh ta turo kofan dakin ta shigo wani iska mai d'umi ya furzar daga bakinshi, a guje ta k'araso ta rungumeshi cike da farin ciki, murmushi ya kirkira yana kallonta kawae, tace "Babe jikin Mummy Alhmdllh, duk ita ce ta takura sae na dawo Wai ta ji sauki, taki bari na inje gidan 'yan uwa mu gaisa, kai babe kaga yanda nayi missing dinka kuwa" kallonta kawae yake sai dai gaba d'aya hankalinshi baya kanta, kallon gadon tayi tace "A'ah Baby kai ka canja bedsheet d'in?" kai kawai ya iya gyad'a mata da sauri, d'agowa tayi tana kallon fuskanshi tace "Baby toh mesa ka canja? Me ya same shi, ae sabo ne na shimfida" murmushi ya k'ak'aro yana kkrin controlling kansa kar ta gano sa yace "Yeah, yea coffee ne ya zube jiki, and I changed it just now" bata bari ya gama ta had'a bakinshi da nata, janye jikinshi yayi daga nata ya zaunar da ita kan gado yana murmushi yace "Am, am coming babe" toilet ya shige, yyi saurin tarawa bedsheet din cikin machine ruwa dan yasan halinta zata iya zuwa ta duba, da kanshi ya dirje sannan ya maida cikin washing machine din, fitowa yayi ya sameta zaune inda ya barta, kissing d'inshi ta shiga yi passionately, amma gaba d'aya hankalinshi na gun Batuul, so yake yaga halin da take ciki, da k'yar ya samu ya lallab'ata har tayi bacci wajen k'arfe takwas, tana fara bacci ya sauk'e ajiyar zuciya ya janye jikinsa daga nata ya dauki makullin mota ya fice daga d'akin, kai tsaye d'akin Batuul ya nufa, tana kwance kan gadon har lkcn bacci take, amma kana gani kasan a wahalce take, wani tausayinta ne yaji ya ratsa shi, dab bakin gadon ya tsaya ya d'auketa cak, kara ta saki a tsorace, yyi saurin rungumota jikinsa, har cikin ranshi ya dinga jinta" k'asa ya sauk'o da ita ya bud'e mota ya sakata ciki snn shima ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar compound din, hade kai tayi da gwiwa tana rera kuka a hankali, duk ya ma rasa me xai ce mata har suka isa daya gidansa, yana gama parking ya bude motar ya fito ya xagaya ta inda take ya bude, daukarta yayi kamar daxu suka shiga cikin gidan, bai direta a ko ina ba sai kan gado, ya xauna kusa da ita ya rungumota cikin sanyin murya yace "I said am sorry, kiyi hakuri plss" kuka take har da shessheka, a hankali yace "Its painful ko? forgive me plss" bata ce komai ba, ya lumshe ido yana shafa bayanta a hankali, kwantar da ita yayi jin tayi shiru sai ajiyar xuciya da take saukewa ya mike ya shiga toilet, very warm water ya hada a bathtub ya fito ya dauketa, sai da suka shiga toilet din ya fara cire mata xanin jikinta, ta rike da sauri hawaye na xubo mata tace "A'a ka bar ni xan yi da kai na" yace "But you are in pain ki bari in taimaka maki" ta fashe da kuka tace "No plss" bai kara bi ta kanta ba ya cire xanin ya saka ta cikin ruwan dumin, ihu ta kwala jin wani sabon axaban, ta dinga kiran Anty tana yarfe hannu idonta rufe don baxata iya kallonsa ba, sosai yaji tausayinta, yasan bai kyauta mata ba, tunda ba haka yayi ma Ajiddeh ba, ko da yake ita wannan bbu gardama ta bashi kanta kamar jira take, sau uku yana canxa ruwan sannan ya taimaka mata tayi wankan tsarki, tayi wanka ta wanke baki, ta dauro alwala ya dauketa suka fito, rufeta da bargo yayi ganin yanda take rawan sanyi, ya sauka downstairs don hado mata tea, da kyar ya lallabata ta sha tea ta koma ta kwanta, makullin mota ya dauka ya fita xuwa phamarcy don siyo mata pain reliever jin yanda jikinta yayi xafi sosai, ko kan ya dawo har tayi bacci, ajiye ledan drugs din yayi ya xauna gefenta yana kallonta, sai lokacin ya tuna ashe fa bai yi sallah ba, mikewa yayi da sauri ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya shimfida darduma yayi sllhn. Yana xaune kan darduma har lkcn wayarsa ya fara ringing, ya mike ya dauka yaga Ajiddeh ce, d'agawa yayi daga daya bangaren tace "Babe ina ka tafi haka har yanxu?" A takaice yace "Aiki, I saw yhu were sleeping shiyasa ban tashe ki ba kawae na wuce" a d'an shagwabe tace "Toh come back early plss," yace "Ayt!" Tace "Babe ban ga yarinyar nan ba fa tun da na dawo" ya lumshe ido yace "Yea bata nan, tana gidansu wata kawarta wai, tun da kika tafi" Ajiddeh ta tabe baki a xuciyarta tace Allah sa ma tai ta tsayawa gidan kawar tata, a fili kuwa ca tayi "Eyya, ashe tasan mutane a nan" kallon Batuul dake motsi yayi, da sauri yace "look babe, We'll tok later, am busy yanxu" daga haka ya katse wayar ya nufi Batuul da sauri.


πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’





68






By phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*











Lumshe ido yayi bayan ta fita daga d'akin, tunani kawai yakeyi na yadda zai sanar da Ajiddeh Batuul matarsa ce, sai yanzu yake ganin rashin kyautuwar fad'a mata da bai yi ba tun farko, yasan da ya fad'a tun lokacin da duk wani rikici ya kau by now, amma gaba d'aya kanshi a k'ulle yake as of then, yana ce komai zaizo da sauk'i amma yadda yake jin Batuul a ranshi, bazai iya yin nisa da ita ba, not for a second, d'an siririn tsaki yaja ya mik'e ya koma gaban desktop d'inshi yana duba ayyukan da baiyi ba yau a office, kamar wanda aka tsikara ya mik'e ya fita daga d'akin ya shiga d'akin Batuul, har ta canja doguwar rigar dake jikinta ta saka wani d'an bingel d'in gown pink ta baje gashinta kan pillow dan yasha iska, tana kwance ta d'aura Laptop d'inta saman cikinta tana danne danne, wani irin ajiyar zuciya ya sauk'e ganin she is fine, a hankali ta juyo da kanta ganin shine ta maida kallonta ga abinda takeyi, tura k'ofan d'akin yayi ya shigo ya maida ya rufe, daga bakin gadon ya zauna yana kallonta, ya kai wajen 3mins amma ko sau d'aya bata juyo ta kalleshi ba, hannu yasa ya d'auke laptop d'in, sai a lokacin ta d'aga ido ta kalleshi, idanunsu na locking cikin na juna tayi maza ta sadda kanta k'asa ta juya mishi baya, hannu yasa cak ya d'agota yana kallonta yace "are you okay?", kai ta gyad'a mishi ta sulale zata koma ta kwanta ya rik'ota yace "then why are you like this, aman ne har yanzu?", har lokacin batace mishi komai ba sai gyad'a mishi kai da tayi, hannu yasa ya d'ago hab'arta yace "talk to me and stop nodding, wani abun ke damunki?", ganin idonta ya fara ciccikowa yasa yace "stop that, don't you dare drop a tear, tell me mey ke damunki", kamar cewa yayi ta fara kuka ta fashe mishi da wani matsanancin kuka, har cikin ranshi yakejin kukan nata, rintse ido yayi ya janyota jikinshi ya rungumeta, patting bayanta ya shiga yi har saida ya samu tayi shiru, sai ajiyar zuciya take sauk'ewa, a hankali ya d'agota yasa hannu ya share mata d'an guntun hawayen dake fuskanta ya had'e rai yace "Look at me", bata d'ago ba sai da ya sake maimaitawa jin yayi maganar in a serious tone ya sata d'agowa tana ajiyar zuciya yace "Fatima kinada hankali kuwa, keh abin kuka baya miki kad'an, ko don kinga ina k'yaleki kullum sai kinyi kuka, gari baya wayewa ya wuce bakiyi kuka ba, tell me what your exact problem is", ajiyar zuciya ta sauk'e ta zumb'uro mishi baki tace "ni ai ba kullum nakeyi ba sai in kaine ka.....", tsareta yayi da ido yace "ehhn, sai in nine nayi mey?", sadda kanta tayi k'asa tace "You always talk abt your wife, kullum sai kace min your wife your wife, I know she is your wife, but ai ba sai ka dinga tunamin ba", baisan lokacin da dariya ya k'wace mishi ba, dariya ya dinga har sai da abin ya bata haushi, haushin kanta ma taji da ta fad'a mishi hakan, takaicin dariyan da yake yasa taja bargo tayi kwanciyarta, sai da yayi mai isarshi sannan ya d'agota har lokacin yana murmushi, kwace jikinta ta shiga yi zata kwanta amma yaqi saketa, fuskarta ya kamo da duka hannayenshi yana kallon idonta da duk ya cicciko yace "Toh ni yau duk yaushe na ambaci my wife", baki ta zumb'uro mishi tace "ko d'azu ma ba ka....", sai kuma tayi shiru, saketa yayi sannan yace "indai wannan ke saki kuka baza ki sake ji ba, you won't hear that from me okay?, ya hade rai ya ci gaba "but promise me kema baki sake yin kukan, kinga Farida will b coming so banso tazo taga kina wannan koke koken tayi tunanin wani abun ake maki", kamar wata y'ar yarinya ta gyad'a mishi Kai, ajiyar zuciya ya sauk'e ganin yayi convincing d'inta kan kukan nata, yanzu saura Farida, itama sai yayiwa tufkar hanci tun wuri, hannunta ya kamo yace "inason shan kunu, can you make some now?", kai ta gyad'a mishi yayi d'an murmurshi yace "Thank you", tsuke baki tayi zata tashi daga kan gadon yayi saurin janyota yace "Did you just pout?", da sauri ta kad'a mishi kai tace "baka ganiba, ni ba pouting nayi ba", murmushi yayi ya janyota jikinshi sosai ya d'anyi brushing lips d'inshi kan nata yayi mata light kiss, lips d'inta na d'aya daga cikin abinda bazai Iya resisting ba akan Batuul, suke tempting d'inshi yayi abubuwan da ma bai shirya yinsu ba, mik'ewa yayi itama ya mik'ar da ita, kallonta yayi yace "muje?", a hankali tace mishi "Ehh", Hijab d'inta ta d'auka zata saka ya riqe yace "Do you really need to put on this?", kai ta gyad'a mishi kawai taci gaba da saka Hijabinta, ita tayi gaba ya biyota a baya, turus ta tsaya bakin k'ofa ganin mutanen da suka hauro wa sama, kallon mamaki suka tsaya yi mata, wani irin bugawa Ajiddeh taji k'irjinta nayi ganin ya fito daga d'akin Batuul, tun bayan dawowanta bata tab'a tunanin har lokacin yana shiga d'akin ba, baki ta bud'e zatayi magana Jainaba tayi saurin rik'o mata hannu, murmushi ta k'irk'iro tace "Aliyu ashe ana ganinku a gari", shima d'in murmushi yayi yace "ai sai in ba a nemi ganinmu ba Aunty, Ya hanya?" Ya tambaya yana k'arasa fitowa daga d'akin, murmushin nan dai taci gaba dayi tace "Alhamdulillah, hanya mun baroshi, mun sameku lafiya?", kai ya gyad'a yace "Alhamdulillah, ya jikin Mummy, kwanaki bata ji dad'i ba, I wanted going with her", ya nuna Ajiddeh da zuciyarta ke tafasa "but abubuwa held me hear", dariya tasa tace "Ai ba komai ma, ai zuwan Ajiddeh ma yayi,taji sauk'i yanzu sai dai Allah ya kiyaye gaba", "Amin" yace sannan ya juya yana kallon Batuul da ta tsaya daga bayanshi kamar wata munafika yace "baki iya gaisuwa bane kika tsaya kallon mutane?", ido ta d'aga ta kalleshi sannan ta kalli Aunty Jainaba da ta bita da wani shu'umin kallo tana jira ta gaida ta, juyawa tayi ta shige d'aki ta banko musu k'ofa, gaba d'ayansu freezing sukayi ganin abinda Batuul d'in tayi, tsabar mamaki kasa magana Abu yayi, Ajiddeh ce a fusace tayi k'ofar d'akin zata bankad'a Jainaba ta rik'ota, "shegiya karamar matsiyaciya har kin isa ki wulak'anta min y'an uwa, toh koma uban wa ya d'aure miki gindi, ko kuma aka zugoki kizo ki min iskanci ko, toh dama hak'uri nakeyi nake k'yaleki, yau sai kin bar min gida y'ar abu kazan uba", Aunty Jainaba ce ta janyota da k'arfi ta d'an kanne mata ido sannan tace "Haba Ajiddeh, bakya ganin yarinya ce, kema ai kinsan hankali ba isanta yayi ba, yarinta ne ke damunta", wani irin kallo ta jefawa Aliyu da ya kasa cewa komai sai kallonsu yakeyi, a masifance tace "ai dama nasan kai ke d'aure mata tana min abinda taga dama, gashi ka janyo min raini da bai tsaya iya kaina ba, har kan y'an uwana ya koma, toh Allah zamanta ya k'are gidan nan ko kuma ni in bar muku gidan sai kuyi xaman auren da ita", Aunty Jainaba ce ta d'anyi magana a tsawace tace "keh wai wace irin yarinyace Jiddah, haka ake yiwa miji magana dama, wuce mu shige tunda bakida hankali wawiya kawae", taja ta sukayi gaba, wani irin iska mai d'umi ya furzar daga bakinshi yasa yatsunshi cikin gashin kanshi ya bajesu, juyawa yayi ya bud'e d'akin Batuul tana tsaye tana waya da alama da Farida suke wayan, a hankali ta juyo ta dubeshi, sai da y'an hanjin cikinta suka kad'a ganin irin kallon da yake tunkarota dashi, dakewa tayi da k'yar ta bud'e baki tace "Hey hold on, I will call you ltr", bata cire wayan a kunnenta ba taji ya fizge ya jefar kan gado tareda fizgota gabanshi, yana mata wani irin kallo yace "What's d meaning of what you just did, kinada hankali ma kuwa?", babu abinda k'irjinta keyi sai heaving kamar zai fito amma ta dake tace "ni kuma mey nayi?", fizgota ya sakeyi jikinshi yana mata wani irin kallo yace "you are asking, i will slap you yanzun nan in baki min magana ba, meye dalilinki na tafiya ba tareda kin gaidata ba, are you stupid?", k'wace kanta daga rik'on da yayi mata tayi zata matsa daga gabanshi ya kuma fizgota a tsawace yace "kehh! na fara wasa da ke koh, I will right away slap you, bakida hankali ne", hannunshi tacire daga rik'on da yayi mata tace "wai ni mey nayi ne na rashin hankali, dan ban gaishesu ba?, dole ne sai na gaishesu? Naga ai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login