Showing 186001 words to 189000 words out of 215266 words
phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Ba Zuciyarta kad'ai ba , har jikinta rawa yakeyi jin kalaman da suka fito bakin Abu, tasha jin ana fad'in wadannan words d'in a films da kuma novels amma bata tab'a tunanin haka mutum keji ba in aka furta mishi su, bata tab'a jin irin wannan abinda take experiencing ba yanzu, wani irin fad'uwa gabanta ya shiga yi lokaci d'aya zuciyarta na mata nauyi, hawaye ne taji yana gangarowa kan fuskarta, ta d'auka baza ta tab'a jin wad'annan kalaman daga wajen wani ba bayan y'an uwanta, shak'ik'anta, tasha jin Farida na ce mata "I love you" duk randa wani abin farin ciki ya giftasu a lokacin, batasan mesa wannan ya fita daban ba, wannan har cikin ranta take jinshi gabanta na tsananta faduwa, she wasnt expecting it, not from him, tunani takeyi itama kamar yadda taji ana fad'a a movies "I love you too zatace?, ta dad'e da sama ranta salama akan jin wadannan kalmomi sabida tasan har sai in ana sonka za a nuna maka, batasan ko tana son nashi ba but tasan yayi casting effect ba kad'an ba cikin rayuwarta, jin tayi shiru snn jikinta na kyarma yasa Abuuturab dafata, kamar jira take taji hannunshi jikinta ta fashe da wani irin kuka, da hanzari ya miqe ya zauna tareda kunna bedside lamp d'in snn ya d'agota, ganin hawaye shimfid'e fuskarta yasashi furta "Subhanallah, Batuul kuka kuma, kinsan I hate jin kukanki, Dan Allah kiyi shiru, am sorry kinji, you don't have to love me back, its okay, ni d'in I will love you with all my myth kinji, just keep yourself safe for me, Be happy", kamar wacce aka daka sai ci gaba da kukan nata takeyi, hannayenta duka biyu ya kamo cikin nashi ya d'an murzasu a hankali yace "Its okay I won't say it to you again tunda bakiso, I promise, kwanta ki huta kinji, its getting late", har lokacin batace komai ba sai jinta take kamar akan iska take zaune, rungumeta yayi ganin kukan nata yaqi tsayawa, jin ya rungumeta yasa feeling d'in da take experiencing yafi Nada,bakin shi ya d'aura daidai kunnenta ya d'an hura mata iska yana patting bayanta snn cikin rad'a yace "Shhhhh, I won't say it again kinji, its a prom....", kasa k'arasa maganar yayi jin fragile tiny hannayenta da tasa ta zagayeshi ta baya dukda ba k'arasawa sukayi ba, nutsuwa da baisan yana da ita ba a yau yaji na ratsa shi jin hannayenta zagaye jikinshi, wani irin ajiyan zuciya ya sauk'e tareda sake k'ank'ameta a jikinshi ya lumshe ido yana shak'ar k'anshinta, dukda yadda yakejin heartbeat d'inta is at a faster pace amma bayason wannan yanayin ya wuce shi ko kad'an, sunfi minti biyar a haka snn ya d'an sassauta rik'on ya d'ago hab'arta, har lokacin idonta lumshe suke, kallon kyakkyawan cute face d'inta yayi da yadda lips d'inta suka koma pink sbd kuka tana d'an twitching d'insu,murmushi ya saki yanajin wani kasala na sauk'o mishi tareda sunkuyowa ya had'e goshinsu waje d'aya sunajin sauk'ar numfashi su na fanning juna, a hankali ta bud'e idonta jin yayi shiru ko motsi bayayi, suna had'a ido tayi maza ta mayar ta rufesu, hannunshi ya d'aura bayan kanta d'ayan kuma kan waist d'inta ya matso da kan nata ya cikata gap d'in dake tsakaninsu, lips d'inshi yayi crashing kan nata har wani sauk'e ajiyar zuciya yayi ya shiga kissing d'inta with passion, batasan sanda ta fara maida masa martanin kiss d'in da yakeyi mata ba a hanKali, saida ya gaji dan kanshi ya k'yaleta yana maida numfashi, jawota yayi ta fad'a kanshi shima ya fad'a ya kwanta, hannu yasa kan lips d'inta yana making circles,yana shaping lip d'in nata a hankali, yana sata jin kamar ana royal rumble a cikinta, rintse ido tayi da k'arfi dan baza ta iya d'aukan feeling d'in da takeji ba yanzu, cikin maganarshi da ke dad'a sata jin wani iri yace "I missed you, your kiss though.....", sake shigewa jikinshi tayi batace komi ba ta k'ank'ameshi dan tasan mey yake shirin cewa, dukda bata ma ganin fuskanshi tasan murmushi yayi jin chuckles d'inshi datayi, turo baki tayi ta kai mishi dukan wasa tace "But I did well today ai", caraf ya rik'e hannun ya d'an matse, d'an k'ara ta saki tace "oucchh, it hurts mana Yaaa Abu, let me be I want to sleep", "That's exactly what I want you to feel, its okay you not loving me, but then missing me, shima bakiyi?", shiru tayi kamar bazata yi magana ba, batasan much about love ba ita, batasan ya yakeba, dukda taji wani al'amari na daban d'azu da ya furta mata yana sonta amma har yanzu ta kasa gane yaya wanan feeling d'in yake, she doesn't know if she loves him but missing d'inshi, ko bata fad'a mishi yasan she did, yasan tayi kewarsa, she is used to him now, kamar zatayi kuka a shagwab'e tace "Toh do I have say it, ai kasan nayi, much more than you do, I missed you more", ko da wannan ta barshi zaiyi baccin farin ciki ba sai ta furta son da take masa ba, yasan with time kamar yadda ya samu kanshi da sonta, yadda ya shigeshi farat d'aya ba tareda ya tab'a kawo hakan a ranshi ba, itama zata soshi da yardar Allah, murmushin dake fuskarshi ya fad'ad'a ya gyara mata kwanciya, bayanta na a jikinshi yayi cuddling tiny figure d'inta da duka hannayenshi biyu, Addu'a ya kuma yi, saida ya gama ya tofa ya shafeta dashi , ya sauk'o da hannunshi saman cikinta cikin rad'a yace and "Lil princess too, sleep safe Daddy loves you" snn ya shafawa kanshi ya dad'a matso da ita jikinshi yaja duvet ya kashe musu bedside lamp d'in, Batuul duk rufe ido da zatayi kalmar "I love you" d'innan ke ringing cikin kanta, ta kasa dena jiyoshi, batasan lokacin da bacci ya d'auketa ba a haka, saida ya tabbata tayi bacci snn ya fara tunanin abinda ya faru yau, mesa Ajiddeh zata mishi haka, does he really deserve this?, laifin nashi ne, meyasa suka zab'i Batuul ba shi ba, how could she be so heartless and cruel, duk irin wannan azaba da Batuul tasha was because of her, wani d'aci yakeji daga mak'oshinshi, ya tabbata da wani ne ba Ajiddeh ba to da saidai yayi kwanan prison, ido ya rintse yana son kawar da tunanin, daga haka bacci ya d'aukeshi
Tana fita Allah yasa taci karo da cab, lokacin da Mum ta fito bata ganta ba drivern ta dake zaune yana jiran ta tambaya ko yaga Ajiddeh yace yaga fitanta a guje, komawa tayi ciki tayiwa Ammah gargad'in wani abin in ya samu Ajiddeh she wont take it lightly, snn ta fito suka tafi da driver, sai kalle kalle takeyi ko zataga Ajiddeh, saida sukaje gida taga cab d'in parke k'ofar gida, ta tambayeshi ko shi ya kawo Ajiddeh by description yace ehhh amma bata bashi kud'i ba kuma ta fita ba tareda bayani ba, Mum ta ciro kud'i cikin jakarta ta mik'a mishi ta koma mota driver ya k'arasa da ita cikin gida, sak'e sak'e kawai takeyi a ranta, abubuwan sun mata yawa as of this time, batasan da wanne zata fara bama, komai ya dagule mata lokaci d'aya, masu aikinta ta kwalawa kira sukazo su biyu a tare, ta tambayesu ko sunga shigowar Ajiddeh, "Ehhh ta shigo amma tayi side d'in can na gefen na Sir", Mum ta wara ido duk da tasan nan ne wajen zuwan Ajiddeh duk lokacin da ranta ya b'aci tace "Ba nan aka ajiye matar nan ba da Daddy ya mask?", sukace "Nan ne Hajiya", tace "Kuje, Keh Sadiya ki tabbata kin kai mata abinci da duk abinda zata buk'ata snn ku zauna kuna lura da ita da duk motsinta", suka amsa kai da baki suka fita, suna fita ta janyo waya ta shiga neman layin mutum d'aya da tasan lallai zai samar mata mafita
K'arfe hud'u Abu ya farka, har lokacin yana jin Zuciyarshi bata mishi dad'i, idonshine ya fad'a kan Batuul da yasashi jin wani sanyi cikin ranshi, ya lumshe ido ya bud'e snn ya gyara mata kwanciyarta kamin ya sauk'o da k'afafunshi a hankali dan bayason yayi motsin da zata farka ya mik'e ya shiga toilet, wanka yayi tareda yin alwala ya fito ya zira farar rigarsa ya shimfid'e abin Sallah ya hau, raka'a biyu yayi snn ya d'auko Qur'an kan shelf ya fara karantawa a nutse yadda bazai tasheta ba, saida ya karanta Rabin Suratul Tauba cikin kira'arsa mai dad'i snn ya dakata yayi addu'o'insa, jin ana k'iran Sallah ya tashi ya gabatar da raka'atanil fajr kamin ya koma kan gadon, bayason fita ya barta ita kad'ai a d'akin, shi zai jasu suyi Sallah tare , hannu yasa ya shafi gefen fuskarta a hankali ya shiga k'iran sunanta, "Fatima wake up, lokacin Sallah yayi", a hankali ta bud'e idon da ya cika da bacci snn ta mayar ta lumshesu, murmushi yayi yace "You sleep too much, Sleepy head", tashi kiyi Sallah, its time", sai a lokacin taji mey yake fad'i, zuciyantane ya fara pounding tunawa da jiya da tayi, words d'innan na ringing cikin kanta, sake rintse ido tayi ta kasa bud'ewa, tsoron bud'e ido takeyi kar daren jiya ya zame mata mafarki, She have longed to hear someone say he love her, duk da ba sani tayi tana son nashi ba bataso wannan karon da ta samu taji ya zama mafarki, "Fatima", sulalewa tayi daga jikinshi tace "Toh kayi nima zanyi nawa anjima", mamakinta ne ya cikashi ganin taqi bud'e ido amma tana magana yace " Fatima Open your eyes", kamar baza ta bud'e ba a hankali ta bud'esu ta sauk'esu kanshi, cak ya d'auketa yayi toilet da ita, ya zaunar bakin bathtub d'in, brush d'inshi ya samata toothpaste ya mik'o mata, turo baki tayi ta ansa ta shiga wanke bakinta, tana gamawa ya jawo kan shower ya shiga tsiyaya mata ruwan, saida ta gama alwalan snn ya sake d'aukarta cak ya fito da ita ya saka mata dogon Hijab d'inta dake ninke gefe, saida suka idar yace "Tashi kiyi rak'atainil fajr", mik'ewa rayi ta jero raka'a biyu snn ta bishi suka ci gaba da addu'a, Hannu yasa jikinta yaji temperature d'inta yace "Good morning", kallonshi tayi taga murmushi shimfid'e fuskarshi, bata tab'a ji ya gaidata ba sai yau, kuma from his look its sincere, a hankali cikin jin kunya tace "ina kwana", ya rik'o hannunta yace "Baki amsa min ba", sunkuyar da kai tayi batace komai ba, "How you feeling right now?, kinajin wani ciwo?", kai ta girgiza mishi tace "Am fine", ya sauk'e ajiyar zuciya yace "Mai idon bacci, go back and sleep", mik'ewa tayi ta cire Hijabin ta ninke zata koma gadon taji ya rik'o mata hannu, yace "Hey, My princess, I couldn't say Hi to her", juyar da kai tayi tayi murmushi snn ta dake ta kalleshi tace "Its not like I care" ta k'wace hannunta ta koma kan gado, yayi dariya yace "Really?, well her Papa cares, Say Hi to her for me pls and tell her that Papa Loves her so much ", murmushi tayi ta shige cikin bargo tanajin kamar moment d'innan yayi ta zama haka, kada komai ya canja mata, cikin baccinta taji an rungumeta ta baya, gyara kwanciyarta tayi suka koma bacci, k'arfe goma ya farka itama ya tasheta, wanka ta farayi snn ya k'ira Farida a waya ta kawo mata kaya ta saka, bacci ma takeyi kasancewar yau weekend, idonta cikeda bacci ta taso ta kawo mata kayan, sai wani irin kallo take bin Batuul dashi tana dariya k'asa k'asa, Hararta Batuul tayi ta anshi kayanta tace "Kyaji dashi dai", bakin gadon ta zauna tace "Keh ni mey nace miki toh, kawai dan nayi dariya", Abu ya fito daga toilet, ya kalleta yace "kayan fa?", nuni tayi mishi dasu tace "gasu nan", yace "zaman na meye toh?", ta zumb'uro baki ta mik'e zata fita tace "Ammah tace ince muku breakfast is ready" kallonta kawai yayi ta fice Batuul na murmurshi, suna gama shirayawa ya rik'ota hannunta suka fito, tun tana qi har ta hakura, suna sauk'a downstairs ta fakaici idonshi ta warce hannunta tayi gaba abinta, kowa na kan dinning su biyune basa nan, Ammah da Abui da Sadiq ta gaida sukayi mata ya k'arfin jiki, a kunyace ta amsa da Alhamdulillah snn ya ja mata kujera ta zauna sukayi breakfast tare
Da yamma suna zaune itada Farida a main parlour, kamar daga sama ta jiyo muryar su Ahmad, rabonta da jin muryarsu watanni kenan in ba a waya ba, da wani irin murna ta tashi t isa inda take jiyo muryar, da gudu ta isa ta rungumeshi hawaye na k'ok'arin zubowa idonta ganin duka kannenta a gabanta, d'aya bayan y'ata ta dinga rungumarsu snn ta karb'i Aabid dake hannun Sayyid tayi pecking d'inshi, sam ya manta da ita sai kallonta yake kamar yaga sabon mutum, jiki a sanyaye ta kallesu tace "Aunty fa?, batace zata zo bako?", Ahmad ya dubeta yace "ita tace muxo, zasu zo tareda Baba su dubaki wai", kai kawai ta gyad'a tana k'ok'arin maida hawayenta da bataso su gani tace "Ku shiga ku zauna, duk kunyi wani tsayi, Sayyid gashin meye haka ka tara kanka kamr wani black cotton?", dariya kawai ya mata ya sunkuyar da kanshi suka karaso ciki, Farida ta d'auki Hafiz tace "muje ka rakani sweet boy", basu jima ba ta sauk'o tareda Ammah, Ammah tace "Ashe manya bak'i ke tafe bamu sani ba, ya kuka baro gida, Ya Auntyn Ku?", Duk suka gaisheta snn suka amsa mata da tana lafiya, nan tasa aka cika musu gabansu da kayan abinci iri iri, suna nan zaune Abu da Sadiq suka shigo a tare, tausayinta yaji ganin yanda take farin ciki ganin yaran, bama yadda take yiwa Aabid wasa ba, ya k'araso wajenta batareda tasan ya shigo ba ya sunkuya daidai kunnenta yace "Hey am happy to see you happy", a d'an tsorace ta juyo ta dubeshi tayi mirmushi tace "Thank you", ya girgiza mata kai yace "You look cute holding the baby, can't wait to see you babysitting my princess", wara ido tayi tana kallon koda wanda yaji, ganin babu mai kallonsu ta sauk'e ajiyar Zuciya ta d'an bugeshi cikin wasa, dariya yayi ya mik'e ya anshi Aabid hannunta yana cakud'a mishi gashi yace "Hey Champ", dariya Aabid yayi mishi cute dimples d'inshi na appearing, da maamki ta bishi da kallo, gaba d'aya ba shine Abutturab d'in da ta sani ba months back, murmushi kawai tayi tana jin wani farin ciki a ranta da takeson ya d'ore a haka,d'aya bayan yaran suka gaisheshi yana amsawa, ya kalllesu yace "Maybe we should go out for ice cream ko, Movie or anything? am offering the treat, who wants to join?", Yusra da kamar jira take tace "Ni zanje, muje Blue cabana, they got the best ice cream and Chapman, yafi na ko ina and their Kebab, omg its so yummy, kasan ko Aunty sai ince mata akaini weekends wai saitace saidai a siyomin, am happy you are taking me.....", bata k'arsa ba Khalil ya sakar mata da wani harara, shiru tayi zata koma ta zauna ganin an harareta Abutturab da tunda ta fara magana yake murmushi ya kamo hannunta yace "Then you will get us all in munje ko" kai ta kad'a mishi, Batuul da mamaki take kallonta ganin yanda yarinyar ta k'ara tsayi, Abu yayi dariya yace ku fad'awa Ammah we are going tunda yamma tayi, Farida ta mik'e tareda Batuul zasuje su shirya, Abu yace "Farida ki sauk'o mata da Hijab in kinje sama", kallonshi tayi idonta yayi rau rau har hawaye ya ciko jin yace a kawo mata Hijab ta dawo kusa dashi a hankali tace "Hijab kuma?, dashi zanje?", ya kad'a kai yana wasa da Aabid ba tareda ya kalleta ba yace "Yeah, anything?", matsawa tayi daga kusa dashi ta zumb'uro baki ta zauna kan sofa, Farida ta sauk'o tareda Amamh riqeda Hijab d'in Batuul ita kuma ta d'aura veil kan cape top da skirt d'in dake jikinta, ta mik'awa Batuul hijab din, duk suka mik'e Ammah tayi musu Allah ya kiyaye sai sun dawo, Batuul ce kad'ai bata tashi ba tana fushin da babu wanda ya lura da ita, Ammah ce tace "Bitti tashi ki bisu kema ki warware jikinki kinji, zaman gidan ai babu dad'i, tashi kije", batason yiwa Ammah musu, mike we a tayi ta zura Hijab d'inta ta fita, koda taje k'in shiga motar Abu tayi dukda taga ya bud'e mata front seat, zagayawa tayi ta shiga ta Sadiq tayi zamanta batareda ta kalleshi ba, baima lura da Fishin da takeyi ba, bayan kowa ya shiga yaja mota suka fita tasu Sadiq ta biyosu a baya.
[11/22, 11:21 PM] +234 803 698 6494: 💖💝BATUUL💖💝
90
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Har suka Isa Blue Cabana duk surutun da akeyi a motar batace komai ba, Sadiq ma duk tsokanarshi haka ya gaji ya kyaleta, bayan anyi parking da kamar bazata fito ba ganin kowa ya fito itama ta fito sai b'ata fuska takeyi, Abu na gama parking shima bayan yaran sun sauk'a ya rufe motar yacewa Farida ta karb'i Aabid hannun yaran nan ta rik'eshi snn ya zagaya ta wajen Side d'in da Batuul take, cikin wasa ya harareta ya kamo hannunta yace "Keh wa yace miki ana shiga motar Sadiq, he drives roughly, bare keda kike carrying baby na", ya d'aura hannunshi kan cikinta, da sauri ta wara ido ta kalleshi jin hannunshi a jikinta tayi maza ta ture hannun tana kalle kallen ko wani ya gansu, ko a jikinshi saima tsareta da yayi da ido, kauda kanta tayi ta matsa baya, yaci gaba "Kina ganin irin gudun da ya riqa shararawa kamar mai shirin barin garin, plss kar ki sake shiga driving d'inshi, I will be there for you always, In sha Allah kinji, Let's get going", d'an k'aramin bakinta ta tsuke tareda murgud'ashi tana janye hannunta, daidai kan idonshi, ido