Showing 63001 words to 66000 words out of 215266 words
hak'ura, murna fal cikin ransa ya fita tareda yiwa Abui alk'awarin hakan bazai sake faruwa ba, Ammah kam har yanxu tak'i hakuri tana nan kan bakanta
A ranan da ya cika kwana huďu a gida, da yamma ya fito falo ganin babu kowa kuma he is bored of zama a ďakinshi shi daya, ďaya daga cikin dogayen kujerun falon yaje ya kwanta a kai tareda lumshe ido kamar mai Jin bacci, Batuul ce ta shigo gidan ďauke da royal Food flask mai shegen kyau sai kuma leda a ďaya hannun Aunty ta aikota, mutum ta gani kwance kan kujera duk tunaninta Sadiq ne, da yake suna dan ďasawa dashi cikin sanďa ta tako tazo inda kujerar take , daidai fuskanshi ta tsuguna tare da yin k'ara, mik'ewa yayi xaune da sauri don har ya fara bacci rike da remote a hannu, ya juya don ganin wane isasshen ne hka , sai da hanjin cikinta suka kaďa ta xaro ido a tsorace don she wasn't expecting him ko kaďan, da sauri ta koma baya Dan gaba ďaya ta gama tsorata da ganinsa, kallonta yayi tsaya yi ko kyaftawa baya yi, juyawa tayi zata bar wajen da sauri ya daka mata tsawa yace "Dawo nan " , tsorata ta sakeyi ba kaďan ba ta sake ledan dake hannunta dama tun farko ta ajiye food flask ďin ta haura sama a guje ta shige ďakin Ammah, Ammah na ganinta ta shigo a guje ta mik'e tace "Subhanallah bitti, ke da waye haka? Wa ke binki " , ba shiri ta k'irk'iri murmushi tace "Ammah ba komai" tare da k'ara faďaďa murmushinta, komawa Ammah tayi ta zauna tace "Bitti sak'on fa" , tace "yana falo Ammah, bari in taje in ďauko , bata k'arasa rufe bakinta ba ya shigo da Sallama rik'e da ledan a hannunshi, sai da ya ajiye tukunna ya sami waje ya zauna, shi da kanshi ya rasa mey ya hanashi komawa Dan yasan ba magana Ammah zata yi mishi ba, itama Ammah duk da ta fara tausaya mishi ta kuma ajiye fushinta kansa gaba daya ganin yanda ya rame har ya ďan k'ara duhu kuma tasan ba yin kanshi bane amma sam bata nunawa, Ammah tace "Bitti bakiga Yayanki ba" , pretending tayi tareda murmushi tace "ai mun gaisa a falo" , Mik'e wa tayi tace "Ammah zan tafi, Aunty tace kar in zauna muna da aiki, Dan taxi ma nazo da, motana ya samu problem kuma su Ahmad basa gida, Baa Alai da Baba kuma sun tafi Kaduna" , ta gyara gyalen kanta bayan ta gama maganan, Ammah ce tace "Taxi kuma, No baza ki koma a taxi ba, bari ďaya daga cikin drivers ďinnan yazo ya kaiki " ta Janyo intercom zatayi waya ďaya ya maida Batuul gida, Abutturab ne cikin sanyin murya kamar mara gaskiya yace "Ammah drivers ďinfa ďaya yana office tareda Baba, ďayan kuma na aikeshi, bata kalleshi ba tace "bari in k'ira miki Sadiq ya kaiki kinji , nasan baiyi nisa ba" ta ďauki wayanta zata k'ira Sadiq Abutturab ya mike yace "Ammah zan kai tace tunda ina nan " , a firgice Batuul ta kalleshi ta gefen ido, ďaure fuska Ammah tayi tace "Allah ya kiyaye, kuma daga nan ka tabbata ka shiga ka gaida Aunty "toh" yace ya juya yana yiwa Batuul wani irin kallo ya fita zuwa ďakinsa ďauko makulli, Batuul na ganin haka ta mik'e tareda k'irk'iro murmushi tayiwa Ammah sallama tace zata jira shi a k'asa ta fice a ďakin cikin sauri, da gudu ta sauk'o daga sama ta fita gidan gaba ďaya, waige waige takeyi tana sauri har ta iso bakin titi, tana zuwa ta samu taxi ta shige ta faďa mishi inda zai kaita, Ammah kam tun bayan fitan Batuul tayi tagumi tayi shiru zuciyarta na raya mata dama tun farko Batuul suka aurawa Abu da yanxu basu shiga bak'in cikin nan da suke ciki ba, wata zuciyar ce tace mata ai yanxu ma ba b'aci yayi ba, still zasu iya hadasu, a haka ma sai su k'ara k'arfin bond ďin dake tsakanin family, ji tayi zuciyarta tayi Na'am da zancen, take wani murmushi ya shimfiďu fuskarta, ta samu kanta cikin farin cikin da ta daďe bata ji irinshi ba, zama tayi kawai tana jiran Abui ta faďa masa wannan [truncated by WhatsApp]
💖💝BATUUL💖💝
30
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR**
Yana fitowa daga ďakinshi bayan ya ďauko makullin ya dawo ďakin Amma, dubanshi tayi tace mishi "baku tafi ba wai, mey kake jira", cewa yayi "Eh ita nazo k'ira ta fito mu tafi", ďauke Idonta tayi daga kallonshi tace mishi "tana palo k'asa ae tana jiranka", juyawa yayi ya fita daga ďakin jin abinda Ammah ta faďa mishi, sakkowa falon yyi, yyi murmushi ganin bata nn ya fita compound, nan ma sai da ya dudduba bai ganta ba, masu gadi yaje ya samu ya tambayesu suka ce mishi ai ta wuce, bai sake ce musu komai ba ya koma wajen motarsa ya hau ya bar gidan, hanyan gidansu ya ďauka , dai dai tana isa ta sauk'a zata bawa driver taxi kuďi shima yayi parking motarsa gaban gate ďin gidansu saboda yayi beating traffic ďin cikin gari, su ko sai da suka bi ta ciki, gaba ďaya hankalinta ya gama tashi ganin motarsa, kasa tsayawa tayi ta karb'i canjinta tayi maza ta nufi cikin gida, yana ganin haka shima ya buďe motanshi ya fito cikin sauri yabi bayanta, dai dai k'ofan palo ya cimmata tareda da fizgota, gaba ďaya ta gama tsorata dashi har kyarma jikinta yakeyi, kuka ta fashe mishi da, rintse idonshi yayi ganin ta fara mishi kuka a ranshi yana cewa "she will neva change",lkci daya ya buďe ido ya hade rae tare da k'ara janyota har jikinsu na tab'a juna, yana mata mugun kallo ya fara mata magana "wato rainin nan naki yana nan har ynxu ko?, yaushe na zama sa'an wasanki, I mean yaushe na fara miki wasa da zaki min kara a kai ki gudu, kuma kukan da kikeyi sai ki faďa min na meye, wato ke har yanxu baza ki canja ba ko?", shiru tayi tana saurarenshi har tana jiyo heartbeat ďinshi, sai da taji yayi shiru tukunna ba tareda da ta ďago kanta ba ta fixge jikinta daga rik'on da yayi mata ta shige palo da sauri, inda tayi yabi da ido, da kamar zai koma sai kuma ya fasa ya tura k'ofan palon, dai dai nan Aunty ta fito daga kitchen, da mamaki a fuskanta ta buďe baki tace "Lalala, wa nake gani kamar Abutturab", murmushi yayi tareda sunkuyar da kai k'asa ya k'arasa shigowa cikin palon,sai da ya zauna tukunna ya gaisheta, ta amsa da fara'a ta shigo falon ta xauna tana tambayarsa yaushe ya shigo gari, hira sosai sukayi da Aunty , Janet Aunty ta k'ira tace ta k'ira mata Batuul, dawowa tayi tace tana zuwa, sai da ta canja kaya ta saka straight skirt baqi da peplum blouse peach, ta sauk'o, kanta da ta taje take tattarewa ta sauk'o ba tare da sanin yana gidan ba, turus ta tsaya ganin mutum zaune yana hira da Aunty a gidansu, ita a zatonta ya wuce tun ďazu, ta hade rae a hankali ta karaso wajen Aunty tace "Na'am Aunty, Janet tace min kina k'irana", cewa Aunty tayi "Ehhh, kitchen nakeso ki shiga kiyi Assisting su Esther ku k'arasa mana abinci, mik'ewa tayi daga hannun kujeran da take tayi hanyan kitchen, ya bi ta da kallo, Aunty ce tace mata "Batuul ya haka, bakya ganin Yayanki ne zaune baki gaidashi ba" juyowa tayi tace "Aunty mun gaisa, shi ya dawo dani gida ma fa", ta faďa ba tareda ta bari sun haďa ido ba ta juya ta ci gaba da tafiyanta, har ta shige kitchen bae daina kallonta ba, a gidan ya zauna har akayi sallahn magriba sukaje suka dawo, suna ta hira shida k'annenta dan yana da son yara, Batuul kam duk aikin da takeyi ranta a b'ace yake , kwata kwata she is not comfortable don da ta fito kitchen sae sun hada ido, dama ga wannan masifan heartbeat ďin nata da ya fara dawowa bayan tsawon lokaci, gaba ďaya ya sata ta sake takura, k'ara b'ata rai tayi ta fito tana jera abincin da suka girka a dinning, suna haďa ido ya sakar mata harara, ďauke kanta tayi bata sake kallon inda yake ba, tana gamawa ta haura sama bata sake sauk'owa ba har ya bar gidan bayan Aunty ta tilasta shi cin abinci har tana ce mishi ko dai sabawa da yayi ne da girkin Ajiddeh yasa baya jin daďin wani abincin sai nata, murumushi yayi a ranshi dan shi baisan ma ya taste đin abincin Ajiddeh yake ba dan ba iyawa tayi ba, haka ya hak'ura ya zauna yaci dan babu yadda ya iya, bazai iya yiwa Aunty musu ba
Bayan anyi sallahn Isha Abui ya shigo gida, dama Ammah duk ta matsu ya dawo ta faďa mishi abinda ke ranta, bayan ya dawo saida ya sauk'o palon k'asa tukunna Ammah ta kawo mishi abincinshi har palon, sai da tayi serving ďinshi yana ci tukunna ta fara magana, shima dama ya lura da magana a bakinta, cewa tayi "Abul Aliyu", ďagowa yayi bayan ya cinye spoon ďin abinci da ya saka a bakinshi yace "Na'am Umm Aliyu", ya tsaya yana kallonta yana jiran yaji mey zatace, sai da tyi ajiyan zuciya tukunna tace "dama wani shawara nayi đazu akan yaran nan namu, kuma ina ganin its beneficial to both families, mey zai hana mu nemawa Abutturab auren yarinyan nan Batuul, yarinyar nutsatsiyace sosai kuma gidan da ta fito nan aka fara yiwa Abutturab tarbiya, a gidan ya fara koyon komai na rayuwanshi, kuma ko babu komai in suna tare a can , toh nasan lallai zata na watching moves ďinshi dan tana da lura da sanin ya kamata, xa kuma tana nuna masa what's right nd wrong, gata kuma da hankali, kaga inma shi ya tafi yaqi dawowa toh ita ba yadda zatayi tayi ta zama babu ganin gida dole sai ta dawo, toh ,kaga a haka zai biyota su dawo ko dan kunyanmu", tunda ta fara magana ya maida spoon ďin abincin cikin plate ďin, murmushi ďauke a fuskanshi yace "Masha Allah, wannan ai abin farin ciki ne sosai kuma nima zanfi kowa murnan ganin wannan al'amari ya faru, kamar Farida haka nake jin Batuul a raina, gobe in Allah ya kaimu zanje in tuntub'i mahaifinta akan zancen muji in babu matsala ko kuma da akwai wanda takeso ", Ammah tace"Abul Aliyu in sun yadda ma kawai a ďaura auren su tafi in yaso daga baya ayi biki , sai taci gaba da karatunta a can,", yace "okay duk zanyi trying inji, Allah dai ya taimaka" haka dai sukayi ta zancen haďa Abutturab da Batuul aure har Ammah na cewa ai da tun farko ma sunyi tunanin nan da duk yanxu basa cikin matsala
Washe gari ranan juma'a bayan an idar da Sallah a masallaci Abui ya haďu da Baba, bayan sun gaisa Baba yace "Alhaji mu dai bama tab'a haďuwa dan kanmu sai dai ko masallaci ko kuma meeting",dariya Abui yayi yace "rayuwan kenan Alhaji, in mukace zamu zauna gida abin bazai yi kyau ba, da shike ma yanxu girma yazo, mun kusa sauk'a mu huta ai", duk su biyun suka sa dariya, Abui ne yacewa Baba " *Alai wa office lan gèrezain, dai fatoro iske kèla kwamnyen* , Alai ana jirana office yanxu, amma anjima zanzo gida, there is this issue i want to discuss with you", da haka sukayi sallama, da yamma wajen k'arfe biyar Abui na tashi daga office yayi gidansu Batuul ko gida bai je ba, lokacin Baba na gida saboda its a short day duk sun tashi aiki da wuri, fitowan Batuul kenan daga backyard đin gidansu, tayi mamakin ganin Abui a gidansu, har k'asa taje ta tsuguna ta gaisheshi sannan ta tashi da taje tayi serving ďinsu drinks da snacks, bayan ta ajiye zata mik'e Abui yake tamabayanta ya makaranta, tace Alhmdllh, nn yayi ta sa mata albarka har sai da taji kunyanshi sosai , bayan ta tafine Abui ya fara magana , sai da ya gama baynin abinda ya kawoshi tukunna Baba ya fa'da'da murmushin fuskarsa yace "Alai nidai b'angarena babu matsala dan babu abinda zaka nema matsawar inada iko akan abun in hanaka, kuma ma ai Abutturab yaron kirki ne sosai, dama dai akwai wani yaro da naga ya fara zuwa wajenta tun wancan watan amma bansan ko sunyi maganan aure ba, kuma tunda ga na gida da aka san halinshi ai yafi da a bawa na waje da ba'a san halinshi ba, dan ma dai naga yaron nada hankali amma zamu bashi hak'uri, yanzu dai ni zanje inyi shawara da y'an uwana da manya na sai mu san abin yi dan Yayya ma ta matsa tafi kowa son a aurar da Batuul sai gashi Allah ya taimakeni akai", godiya sosai Abui yayiwa Baba daga nan suka shiga hirar politics da matsalolin dake damun Nigeria.
Batuul na kwance kan gado wajen k'arfe 8 na dare bayan tayi sallah isha, kayan bacci ne jikinta dogon wando da y'ar riga, kan gadon duk ta baje takaddu sai Macbook ďinta daga gefe, chocolate bowl ta janyo ta ďau twix ďaya ta b'are ta jefa a bakinta tukunna taci gaba da duba takaddan, tana ci taji wayanta na ringing, tashi tayi ta ciro wayan daga caji, Recieving tayi tareda komawa kan gadon ta kwanta, kamin tayi magana daga ďaya b'angaren akayi sallama tareda da faďin "Ranki ya daďe Habibty, i cant imagine life without you", murmushi tayi har ana jiyo sautin daga ďaya b'angaren tace "tareda naka, you can live normally mana tunda ai da can ma baka sanni ba and you were living", dariya yasa yace "that was then, amma ai yanzu tunda na sanki, life is gonna be hard without you, promise you wont leave me", ji tayi gaba ďaya ya gama bata tausayi, ita tasan ba sonshi takeba but tana respecting ďinshi sosai, avoiding promise ďin da yace tayi mishi tayi tace "Ya jikin Mummy, ta k'ara samun sauk'i ko?", da sauri ya tareta yace "Ba kinqi zuwa in kaiki wajenta ba, kullum sai ta tambayeni yaushe zan kawo mata kene, har banaso tana tambayana dan bansan mey zance mata ya hanaki zuwa ba", kai ta girgiza kamar yana gabanta tace "No fa ba naqi zuwa bane, we have time , kuma i dont think its right muje gidanku tun yanzu , i will come when its time", tambayanta yayi mey takeyi dan yaga mind đinta is not with him, tace mishi assignment takeyi, da haka ya barta tace they will talk ltr
Bayan Abui ya tafi, Aunty ce ta sauk'o k'asa ta sami Baba zaune yana kallon CNN channel, daga gefenshi ta samu waje ta Zauna tayi mishi sannu da gajiya tareda ajiye. abinda ke hannunta, volume ya rage ya juyo ya dubeta ya faďa mata yadda sukayi da Abui, ita gaba ďaya bata expecting haka, ta k'asa daina kallon mai gidan nata, hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba jin xancen Baba kuma tasan babu yadda za ayi yaqi bawa Abutturab Batuul tunda har gida Babanshi yazo nema mishi aurenta, ajiyan zuciya tayi cike da damuwa tace "Uncle Batuul ďin kuma, shi da yayi aure ko shekara bai wuce ba, ai sai ya bari ko matar tasa in ta haihu ne sai ya fara zancen k'arin aure amma ba daga aure ya bijiro da sabo ba", ta faďa tana jiran jin mey Baba zaice, cewa yayi "indai zai kula dasu duka biyu ai bamu da matsala, kuma ai ba sanin matsalarshi mukayi ba na son k'ara aure, kuma ma dai yaron nan ďanki ne, kinfi kowa sanin halinshi, ya kamata kifi kowa murnan kasancewar wannan al'amari, kinsan ko shekaran jiya kina zaune kina ji sai da Yayya ta k'irani akan Batuul, toh yanxu mafitar addu'an da nayi na samu, nasan Aliyu yaron kirki ne zai kula da Batuul in sha Allah", ido kawai Aunty ta zubawa Baba yana magana hankalinta na dađa tashi, Batuul tayi yarinya da auren mai mata, barema irin su Ajiddeh, cutan Batuul kawai za ayi indai ta zauna a gidan nan a matsayin matar Abutturab, dan tasan yadda familyn Ajiddeh suke akan kishiya, mik'ewa kawai tayi ba tareda ta sake cewa komai ba ta haura sama don bata jin xata amince da wnn batun at all, idonta ya kaďa har ya canja kala.
💖💝BATUUL 💖💝
28
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tana fita ta wuce gidansu daga hotel din, cike gidan yake da mutane da suka zo biki, wucewa takeyi tana ta daga kai ita a dole matar mai kuďi, matan dake zaune sai gaidata suke wasu kuma suyi gulmarta, ďakin da tasan zata samu Mum straight ta wuce, ba ko sallama ta saka kai cikin ďakin, Mummy na ganinta ta taso cike da murna ta rungumeta tana faďin "Yar albarka baki min waya kince kun iso ba " ta fadi tana K'arewa Ajiddeh kallo ganin yadda ta canja lokaci kaďan, ga wani kyau da ta k'ara dama can Masha Allah, Hannunta ta jawo bayan ta saketa daga rungumar da tayi mata taja hannunta suka shiga bedroom, Junaiba dake zaune ce ta bisu cikin ďakin, a tsakiya suka sa Ajiddeh, Mummy ce ta fara ce mata "Ajiddeh kinga yadda kika canja , lalalala Masha Allah, kin zama matar manya, duk komai yana tafiya yadda muka shirya ko? , Jainaba ce tayi maza ta karb'e maganan da cewa " Mummy ai ko baki tambaya ba gashi kin gani, yarinya zata cuci kanta, ana so a ayi miki abin kirki a taimakeki kina ke mijinki, kefa kina sonshi, toh da mun barki haka da yanxu duk