Showing 39001 words to 42000 words out of 215266 words

Chapter 14 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1702

"kelewa Alhadulillah, kuntashi lafiya", "Alhamdulillah Abui", "dama ina so ne in faďa maka ku shirya da wuri kai da abokanka, dan goma saura yanxu, kuyi hanzari kuzo kar a b'ata lokaci", a nutse ya amsa sannan suka katse wayan, Ammah ya k'ira bayan sun gaisa tayi mishi addu'a, Su Massa ne suka shigo su dayawa kowa ya sha gayu, Su Massa har da saka babbar riga kaman shinene ango, tun daga hotel ne photographers suka fara covering , na gida can ma sunayi, fitowa sukayi suka nufi inda motocinsu suke suka shishiga, motocine manyan gaske, su Benz, BMW, Audi, Range Rover...., convoy sukayi har wajen ďaurin aure, tun daga waje yake gaisawa da mutane har suka isa filin dake wajen gidansu Ajiddeh, k'arfe sha ďaya limami yayi announcing an ďaura auren Aliyu da Ajiddeh akan sadaki sisin gwal talatin.💖💝BATUUL💖💝






21





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





K'iran Ajiddeh ne ya fara shigowa wayanshi, kin dagawa yyi da farko don ya rasa gne haushinta yake ji ko akasin hka, ansawa yayi daga karshe tare da yi mata sallama can kasa "salamu alaiki zawjati", wani irin murna takeji kamar ta ganta a gabanshi, ta saki wani murmushi cikin muryarta me ddin sauraro tace "baby an ďaura, am officially yours now", murmushi kawae yayi hade da girgiza kai yana mamakin Ajiddeh ko kaďan bata jin nauyinshi ko kunya, cikin sanyin murya yace"In sha Allah forever" zata sake magana kenan wasu mutane suka zo yi mishi murna, ce mata yayi "hold on wife, zamuyi magana anjima, am busy over here", da murnan sunayen da ya k'irata yau ta katse wayan, daman mum ta faďa mata in ya aureta sai ya sota fiye da komai, gashi nan tun yau ta fara gani, gaisawa yayi da mutanen dake gabanshi, jama'a sai k'aruwa sukeyi suna mishi murna tare da yi mishi fatan alheri a rayuwan aurenshi, walima suka wuce daga wajen ďaurin auren a state hotel, k'arfe ďaya suka gama walimarsu suka wuce airport daga nan, a airport sukayi azahar gaba ďayannsu, 1:45 sukayi boarding plane, k'arfe uku dai dai sukayi landing a Nnamdi azikiwe international airport dake Abuja, basu isa gida ba sai biyar saura, a gajiye ya shiga bayan an gama kai mutane masaukinsu,





Bayan su Batuul sun gama cin abinci, wajen k'arfe uku Aunty ta ce su shirya suje gidan Ammah, ita yau baza ta samu zuwa ba, in sunje gaisheta, sai sun haďu a dinner, dan gudun magana Batuul ko attempting saka abaya ma batayi ba, wani peplum blouse da skirt na atamfa ta saka, ta samu k'aramin pearl pendant ďinta da stud masu kyau suma ta saka, ta ďauki k'aramin mayafi ta yana a kanta, Addua take a gama bikin nan ko zata huta da yawon nn ita kam, Baa Liman suka sa ya kaisu, k'arfe huďu suka isa gidan, gidan a cike yake da mutane kowa nata hidima, gaishesu suka rik'a yu har suka isa ďakin Ammah, basu sameta ba a ďakin ba, ďakin Farida sukaje , da sauri Farida ta janyo k'ofar dan kamar ba ďakinta ba, side ďin Abui ta jawo hannun Batuul sukayi tana cewa Batuul "ni in zanyi aure baza a zauna a gida ba, dubi fa gidan kamar ba shi ba kuma fa masu aiki na ta gyara amma kamar basayi", "dama haka taro yake, sai an kwana biyu zakiga gidan ya koma daidai", suna isa side ďin Abui Farida ta murďa k'ofan ta shiga, Ammah ta tarar ita da Aunty Amna suna zaune a ďakin bak'i na side ďin Abui tana yi mata bayanin wani abu, ga robobi nan manya manya a gabansu cike da kaji da snacks, k'arasawa sukayi daga ciki, Farida ce ta fara gaida Ammah da Aunty Amna, sai Batuul, bayan ta amsa gaisuwan ne tacewa Batuul "Bitti sai yau na ganki tunda aka fara bikin nan, lafiya bakya zuwa", kai ta sunkuyar sannan tace mata "Ammah ina zuwa, shekaran jiya ma naje wushe wushe", " toh yayi , madallah, ďazu tela ma ya kawo kayanku na dinner na sa a ďinka muku, sai kuyi shiri anjima kuje kunji", toh kawai Batuul tace amma ba wai dan ta saka zuwan a ranta ba, suna zaune su Ammah kuma nata bayanin yadda za a kai kayan nan gidan amarya, mik'ewa Farida tayi ta fita, shigowa tayi ita da wata yarinya ďauke da plates a hannayensu na abinci, ajiyewa tayi ta zauna yarinyar kuma ta fita, cewa Batuul tayi ta taso suci abinci, mik'ewa Batuul tayi tazo kusa da ita ta zauna, ďan kwalin dake kanta ta cire ta ajiye daga gefen gadon sannan suka fara cin abinci, sallama akayi a k'ofa, Sadiq ne ya shigo ďakin , sai da ya gaida Ammah da Aunty Amna sannan ya zauna, Ammah ce ta dubeshi tace "kun dawo Sadiq, ya hanya, anyi lafiya babu matsala dai ko", kai ya girgiza tare da cewa "Alhamdulillah Ammah kunyi k'ok'ari mutane kamar turo su akayi a wajen ďaurin auren nan, komai ya tafi lafiya", cewa tayi "Alhamdulillah , dama haka nake son ji, Allah ya sanya Alheri, Allah ya basu zaman lafiya" dukkansu suka amsa da Amin, Farida ce tace "Yaa Sadiq shikenan yanxu Yaa Abu zai bar zama a gidanmu, shikenan daga shi sai kai, gidanmu zai zama daga Abui sai Ammah sai ni, zanyi abinda nakeso", dariya ma ta bashi yace mata "zama gadin gidan zakiyi ashe, ai nima sai kin rigani barin gidan nan, waye ma zai barki ki zauna, next year kema by now munje maiduguri har mun dawo", b'ata rai tayi tare da zumb'uro baki tace "Ammah kin ga Yaa Sadiq ko", kamar ba ita ta fara hiran ba, "Sadiq ka dena damun ta tana cin abinci", dariya yayi ya mike yace "Ammah bari inje in dawo", tace "okay sai ka dawo", Batuul ji tayi sun birgeta, inama tana da yaya itama, amma irin Sadiq ba irin Yaa Abu ba dashi bama a ganin dariyanshi, Sadiq na fita yayi hanyan su ya haďu da ango, tsaidashi yayi yace "Abui ya shigo gidane naganka a side ďinshi, ce mishi yayi "No Ammah na ciki, daga wajenta nake, yace "okay let me get to her", k'ofan falon Abui ya buďe, yana saka k'afa Batuul dake ciki taji gaba ďaya ta zama restless, bugun zuciyan ta ya fara, a hankali ta rik'a tauna abincin dake bakinta, k'ofar ďakin da suke ya tura ya shigo, cak komai ya tsayawa Batuul dan batayi expecting ďinshi ba at this time, k'anshin turarenshi ya cika ko ina na ďakin, da sallama ya k'araso ďakin yana kare ma mutanan ciki kallo snn ya zauna a gefen gado, Gaisheda Ammah dake ta binsa da kallo yayi ta amsa tana masa sannu da xuwa, sannan ya gaida Aunty Amna da ta dage sae tsokananshi take, Farida ce ta gaisheshi ba tare da ta kallesa ba, ba yabo ba fallasa ya amsa mata, sau ďaya ya kalli inda Batuul take ya ďauke kanshi, ita dai bata ce mishi komai ba gashi nan dab da ita ya zauna, xame hannunta tayi daga plate ďin ta cewa Farida ta k'oshi, Abuturrab na kallon Ammah yace "Ammah béri manyin, (Ammah inason abinci) banyi breakfast ba yau throughout bare inci lunch ga yamma tayi", Aunty Amna ce tace "wannan duk ďokin zama angon ne ya hanaka cin abinci" tana dariya tayi maganar, bai ce mata komai ba sae murmushin da yyi dan ya saba da tsokanar Aunty Amna, shi bai tab'a haďuwa da Aunty ďinshi mai tsokana kamar ita ba, Ammah ce ta dubi inda su Farida ke cin abinci ta lura da Batuul bata cin abincin, tambayanta tayi "bitti ya akayine bakya cin abincin", murmushi Batuul ta k'irk'ira tace "Na k'oshi Ammah", ce mata tayi "Bitti ďauko wa Abu abincinshi a palo, yana nan na shirya akan tray xa ki gani", a sanyaye ta mik'e tare da cewa toh, inda ta ajiye ďankwalinta ta duba zata ďauka taga akai ya zauna, bata ce mishi komai ba tayi hanyan palo, binta yayi da kallo har ta b'ace sannan ya ďauke idonshi tare da tabe baki a ranshi yace batason rufe kanta, dan yasha ganin gashinta on several occasion, mik'ewa Ammah da Aunty Amna sukayi suka fita dan sun gama abinda zasuyi, turowa kawai zasuyi a zo a ďauki kayan, inda Farida take zaune ya duba yaga tana ta faman dambe da k'ashi, ďauke kanshi yyi daga kallonta tare da jan tsaki, can ya sake dubanta gnin bata ma san yana yi ba sae fama da k'ashin take bayan ga nama me yawa a plate din yasa ya xabga mata harara yace "ke in baza ki ci abinci nan ba tashi ki fita, kin zauna kina ta kokuwa da k'ashi ko ina zaki kai na cikin plate ďin" zumb'uro baki tayi tareda kinkiman plate ďin abincinta tayi waje a ranta tana faďin "ohh masifaffe, mutum ran aurenshi ma sai yayi masifa ko ina ruwanshi da k'ashin da nake ci oho", ta fice abinta ya bi ta da harara.





Bayan few minutes Batuul ta shigo ďakin kinkime da babban tray, saura kaďan ta sake tray ďin don wani irin faďuwa gabanta yayi ganin shi kaďai ne a ďakin, kanshi ya ďago ya ganta tsaye, ďauke kai yayi yaci gaba da abinda yakeyi a wayarsa, ganin ta fara gajiya da tsayuwan ne ya sata k'arasawa jiki a sanyaye ta shigo, a gabanshi ta sunkuya ta ajiye tray ďin , shi kuma gashin kanta da tayi parking in a messy bun yake kallo, yadda sukayi curls wasu na lilo ya zubawa ido, ďagowa tayi daga tsugunnen ta mik'e tsaye, tsayawa tayi a kanshi tana so tace yana zaune a kan ďankwalinta zata ďauka amma ta kasa bude baki, binta yayi da kallo yace "wa zai zuba min abincin kin wani ajiye kin nemi waje kin tsaya kina kallona, C'mon sense din ki bae baki cewar ba dungure min abincin xaki yi ki mike ba", bata kulashi ba sae wani hade rae da tayi ta tsuguna ta ďauki plate da serving spoon kanta a kasa tace mishi "mey zan zuba maka", ba tare da ya kalleta ba a takaice yace "anything", gima ta zuba mishi a plate ďin, daga gefe ta saka mishi scrambled potato mai cheese sai kémoniye a wani saucer, kallonta kawae yake har ta dago kai tana kallonsa tace " Ya isa?" Bae tanka ta ba sae sunkuyawa da yayi ya ďauki abincin ya fara ci a hnkli, ďagowa yayi da kanshi ya ganta tsaye tana fidgeting yatsunta kamar zatayi magana, kallonta shima ya tsaya yi sae dae fuskarsa a daure, sunkuyar da kanta tayi da sauri, shi kam bae fasa kallonta ba sae a nn ya kuma lura da yarintar ta, k'aramace ssae ya faďa a ranshi, a fili kuma cikin dakewar murya yace mata "get me a bottle of water", ba musu taje ďauko mishi ya bita da kallo har ta bude fridge ta dauko ruwan, kan ta juyo ya maxa ya sunkuyar da kansa, ta karaso ta mik'a mishi, hannu yasa zai karb'a taji hannunshi cikin nata, maza tayi ta sake ruwan ya faďi a k'asa, kallonta yayi tare da jan ďan k'aramin tsaki ya ďauki ruwanshi, ganin ta kasa mishi maganan ďankwalinta ne ya sata kawai ta fita haka, juyawan da tayi zata bar wajen kawai ta bige tumbler dake wajen , a take suka tarwatse a wajen, ba karamin rikicewa tayi ba ta daga k'afa da sauri zata matsa daga wajen ta tak'a ďaya daga cikin broken glass ďin, wani k'ara ta saki ta tsuguna a wajen, wani mugun kallo yake jefa mata kmr xae maketa, ita ko duk ta tsorata ta saka kuka, ganin jini a kafar ne ya sashi ajiye abincin hannunsa a gefe da sauri ya mike, tunawa da yayi lokacin da yake k'arami suna London, Aunty na koya mishi homework ďinshi ya ďauki blade ya yanke hannunshi dashi, rudewa tayi sosai har idonta sai da yacika da hawaye tayi mishi treating hannun, har sai da ya warke tukunna ta fara barinshi yana yin abu da kanshi, karasawa yyi inda take ya tsugunna dab da ita har tana iya jiyo numfashinshi a fuskanta, ga k'anshin turarenshi ita yayi mata yawa, hannunshi yasa zai janyo k'afarta tayi maza ta janye, tsaki yayi tare da janyo k'afan yana dubawa, glass ďin da ya mak'ale a k'afan ya sa hannu ya cire, wani ihu tasa tare da k'ank'ame shi, shiru yayi yaji yadda heartbeat ďinta ke bugawa da k'arfe, idonta ta buďe da taji zafin ya ďanyin sauk'i, da sauri ta sakeshi ta matsa baya ganinta kwance a jikinshi, tashi yayi ya koma gefen gadon ya zauna, yunk'urin tashi tayi itama zata tafi ta kasa, wani k'ara ta sake sawa, tasowa yayi ya dawo gabanta ya mik'a mata hannun alamun ta rik'e ya mik'ar da ita, nok'e hannayenta tayi, haushi ne ya sashi sunkuyowa ya ďauketa cak sae jin ta tayi jikinsa, ta wara ido ganin abinda yayi, k'ok'arin sauk'a ta farayi daga hannunshi, hade rae yyi ssae ya xuba mata idonshi masu kama da na masu jin bacci, hawaye ne makale idonta suna shirin zubowa, ce mata yayi "stay still, ciwo kikaji bazaki iya tafiya ba, am helping, ki tsaya in gama or ki sha mari ynxun nn, ina wasa da ke ne" yana hararanta ya kare mgnr, shiru tayi ta dena k'ok'arin sauk'an da take sae dae ba karamin faduwa gabanta yake ba, toilet ďin ďakin ya shiga da ita ya ajiyeta a bakin bathtub, shower ya janyo ya kunna ruwa yana zubawa a wajen tare da sa hannu yana wanke jinin da ya fara bushewa a wajen, rintse ido tayi ta dafa sa sabida zafin da wajen keyi, sai da ya gama ya sake ďaukanta cak ya fito da ita ďakin, a kan kujera ya kwantar da ita , ďakin Abui ya shiga ya ďauko first aid kit, dab da k'afanta ya zauna ya kamo k'afan ya shiga gogewa da spirit da cotton wool, ido ta rintse tsabar azaba ta rik'e hannunshi da sauri, sae kuma ta sake kuka, hannunta da ta rik'eshi dashi yabi da ido, ďauke hannun yayi daga jikinshi yaci gaba da abinda yakeyi, zafin ne yayi yawa tace mishi "Yaa Abu dan Allah ya isa haka, akwai zafi", dubanta yayi yaga hawaye take ssae ,ce mata yayi "clean your face and close your eyes, it wont hurt, beside raki ne yyi maki yawa", hakan tayi ta rik'e mishi riga har sai da ya gama dressing ciwon , tashi yayi daga wajen ya gyara mata k'afan ta kwanta comfortably, juyawa yayi zai fita tace mishi "Yaa Abu don Allah ka kira min farida", tsayawa yayi cak ba tare da ya juyo ba jin ta k'ira sunanshi sai da yaji abinda take buk'ata, ba tare da ya juyo ba yace "Anki" fita zaiyi daga ďakin kenan Farida ta shigo tana ihun "Batuul mey kika tsaya yi tun ďazu ina jiranki kizo kiga kayan da akayi mana, its f**ki....." bata k'arasa ba tayi maza ta rik'e baki ganin Yaa Abu a tsaye, dariya ne kawae Batuul bata yi ba ganin yadda ta haďiye maganan, a sanyaye ta k'arasa wajen Batuul tace "mey ya sameki, ya akayi kika ji ciwo har haka daga fitana" "Shut ur filthy mouth nd clean up this mess kafin in dawo" yana kai wa nn ya sa kai ya fita, da harara ta bisa snn ta dube Batuul tace "shi ya ji miki ciwon ko, ai nasani, kuma in yaga mutum yaji ciwo yafi kowa damuwa, garin yaya", kai Batuhl ta girgiza tace mata "Ba shine fa ya ji min ciwo ba, nice na fasa tumbler da na ajiye, dama ance everybody will b d first victim of his own corruption, gashi nan ni ya fara ji wa ciwo", tausaya mata Farida tayi tace "sannu", tambayanta Batuul tayi "mey kike faďa ne da kika shigo har da su f**king" ta k'arashe maganan tana mata dariya, "kayanmu ne na dinner, yayi kyau sosai, both d material and d style sunyi kyau sosai, sai ma mun saka tukunna", ce mata tayi "Dinner sai ku, ni yanxu ina naga k'afan zuwa dinner" a ranta kuwa hamdala tayi ta samu rusheshen excuse da xata bada dan dama bata son zuwa, a hnkli Farida tace "toh nima bazanje ba tunda bazaki ba", ido Batuul ta wara ta buďe baki tace "kinsan mey kike faďa , dan bazanje ba kema bazaki ba, ai sai in sa Ammah ta turaki dole, bare da ita ma za a ai dole kije", dariya Farida tasa tace "I wont miss it for the world wasa ma nakeyi, zanje kema kuma zakije yarinya", kamin ta bata amsa Ammah ta shigo ďakin, ganin Batuul a kwance yasata hanzarin k'arasowa inda suke, tambayanta ta shiga yi yadda akayi taji ciwo, faďa mata gaba ďaya, sai da ta gama tace mata "Toh yanxu ina Abutturab ďin, shine dan bak'in hali ya fita ya barki ke kaďai Kuma bai zo ya sanar dani kinji ciwo ba", "yanxun nan ya fita Ammah", Batuul ta faďa mata, taimaka mata sukayi ta tashi, har toilet sukaje da Farida tayi alwala ta fito, kaďan kaďan take ďingisawa, side ďin Ammah suka koma sukayi sallah suka fara shirin zuwa dinner dan Ammah tace babu abinda zai hanata zuwa, har da dan hawayenta don ba hka ta so ba.
💖💝BATUUL💖💝






22





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Shiri suka hau yi bayan sunyi isha da magariba, ďakin Ammah suka zauna suna dudduba kayan, lace ne purple mai ďan ratsi ratsin grey mai kyau, ďinkin ya amshsu soaai, iri ďaya akayi musu, sai da suka gama Ammah ta dubi Batuul "Bitti kunyi kyau, amma babu sark'a da ďan kunnefa, ke Farida ya baki bata ba, sai ki saka keh kaďai", hararan Batuul Farida tayi sannan tacewa Ammah "Ammah kiga jewellery box ďin mafa a gabanta yake, nace ta zab'i wanda zata saka tak'i wai baza ta saka ba", Ammah cewa tayi "A ah Batuul bazai yiwu ba, ina aka tab'a gaye babu ďankunne", mik'ewa tayi ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login