Showing 198001 words to 201000 words out of 215266 words

Chapter 67 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1696

kiyi kuka plss", muje kisa kaya yau sai Farida ta fad'amin yadda akayi kikayi gaining weight" ya  fad'a tareda kamo mata hannu, d'ayan hannunta ta saka kan nashi, juyowa yayi ya dubi fuskanta yaga duk sai glittering d'in hawaye suke, rungumota yayi, bai tab'a ganin mutumin da hawaye bai mishi wuyar zuba kamar Batuul ba, jawota yayi suka koma bakin gadon, a hankali tace "Nasan ban k'ara jiki ba but nan gaba in nayi fa?, you will stop loving me ko?", yanzu ya sake tabbatar da harda yarinta cikin lamarin Batuul, dan kawai tayi jiki sai ya dena sonta?, he love her for whatever she is and whatever she will become of, wani light peck yayi mata a goshi ya rik'o hannuta cikin nashi yace "Hey look at me", kasa d'agowa tayi ta kalleshi saida taji yace "Glitter look at me", d'azu ma taji word d'innan daga bakinshi sai yanzu ta san da ita yake, sunaye biyu kenan ya saka mata yanzu, Haya da Glitter, har cikin ranta takejin sunan, a hankali ta d'ago ta dubeshi, Hannu yasa ya share hawayen dake shirin zubo mata yace "what will make you change the way you feel about me?", shiru tayi ta kasa cewa komai saida yace "Uhmm ina jinki", jiki a sanyaye ta girgixa mishi kai, yace "Ki bud'e baki kiyi min magana a hankali tace "Babu", yace "mesa kike tunanin gaining weight zaisa in dena sonki, wa yace miki jikinki nakeso Haya, wa yace miki structure d'inki nakeso?, Ina sonki for who you are da kuma what you are yet to be, banason sake jin kin sake fad'an haka, zamuyi fad'a kinji ko?", kai ta gyada mishi yace "Good" yana sa hannu cikin gashinta da bai bushe ba yace "zakiyi mura fa kina barin gashinki da ruwa", tace "yanzu fa zansa kaya inyi drying d'inshi", ta fad'a tana k'ok'arin tashi ya rik'ota yace "No ki bari in mun sake jik'ashi sai kiji dad'in drying da kyau", sarai tasan abinda yake nufi da hanzari ta mik'e tana dariya tace "A ah nikam, I can dry it haka nanma", dariyan yayi shima ya kamata ya zaunar kan stool ya shiga drying mata dogon gashin kanta mai santsi da shek'i, sai da ya gama snn ya taimaka mata ta shirya cikin navy blue lace mara nauyi mai k'ananan jan patterns yace su sauk'a ya fara jin yunwa, ya rik'o hannunta suka sauk'o dinning area, suna k'arasowa tayi maza ta janye hannunta cikin nashi, kallonta kawai yayi baice komai ba har ta zauna snn ya zauna, daga kitchen Ammah da Sadiq suka fito, da alama daga exercise yake saboda kayan jikinshi, yana riqe da apple yana taunawa biye da Ammah yana mata magiya, juyawa tayi ta dubi Sadiq tace "Kana jina fa Sadiq nace bansan zancen ba, ka samu Abui kuyi maganan dashi", ta k'arasa dinning d'in, Da sauri Batuul ta tashi ta karb'i pan d'in dake hannun Ammah tace " *Ammah Nda wattu* Ina kwana Ammah", "Ammah da murmushi fuskanta tana goge hannunta tace " *Bitti k3lewa selai, k3lewan fanema? Lafiya Kalau Bitti, kin tashi Lafiya?", ta tambaya tana gyara tray d'in fruits, a kunyace Batuul ta ajiye pan d'in dake hannunta tace "Alhamdulillah", ta dubi Abu tace "Ya jikin nata?", Saida ya gaisheta snn ya amsa da Alhamdulillah, ya dubi Sadiq da duk ya shagwab'e fuska yana tauna Apple d'inshi yace "Shi kuma wannan mey ke damunshi?", ya fad'a yana tambayan Ammah, Ammah ta zauna ba tareda ta dubi Sadiq ba tace "Ka tambayeshi gaka gashi, kunfi kusa inajin", kallon Sadiq yayi yace "Whats wrong?", a hankali Sadiq yayi wata magana da babu wanda yaji, Abu da ya had'e fuska yace "In ka shirya fad'an matsalarka ka biyoni ka fad'amin", Ammah tace "Shima da kanshi yasan hauka yake shirin yi shiyasa bazai iya fad'a makan ba, ni bara in fad'a mishi yaji yasan rashin hankalin da yake min", Ammah taci gaba tace "Wai aure yakeson a mishi", daidai lokacin Abui ya k'araso dinning d'in yana cewa "wakeson ayi mishi auren?", Sadiq da sam baiso Abui ya Karaso at this time ba yayi maza ya sadda kai k'asa, Abutturab tsabar mamaki kasa cewa komai yayi sai baki da ya bud'e yana kallon Sadiq d'in, Ammah tace "Wai Sadiq keson a mishi aure", murmushi Abui yayi yace "Har ka shirya kenan, ka shirya kula da y'ar mutane", d'agowa yayi suka had'a ido da Abutturab, Abutturab yayi mishi kallon you are not okay yace "wace yarinyar ce zata aureka bakada aikin yi?, Serving d'inma ba gamashi kayi ba bare ka fara maganan settling ", D'an kafad'a ya d'aga alamun am due fa snn yace "But ai inada gida, what else?" Sosai Sadiq ya bawa Abui dariya, Ammah da Abutturab kam ko kad'an abun wasn't funny to them, Farida ce ta sauk'o sanye da kayan bacci da hula kanta tana danna waya, jin maganan da akeyi ya sata k'arasowa da sauri tana maida wayar cikin aljihu tace "Laaah Ammah ku baku San ma yarinyar bafa, wai fa Layla k'anwar Uncle d'in Aunty Amna yakeso, ina jinshi yana waya da ita kullum, ko wallpaper d'inshi picture d'inta ne, bara ma ku gani" taja kujerar gefen Abui ta zauna tana mik'a hannu zata d'auki wayarsa dake ajiye gefe, Hannu Sadiq yasa y make nata hannun, b'ata rai tayi ta zumb'uro baki ta kalli Abui tace "Abui kana ganinshi ko", tunda Abu ya harareta tayi shiru ta d'auki plate ta d'ebi pomegranate tana sha, Sadiq ma harara ya sakar mata, Abui yace "Sadiq ba gida bane aure, it takes a lot fiyeda wannan, you are just 22, kana buk'atar time da kuma nutsuwa kamin kace zakayi settling, ka bari in ka gama Service ka samu aiki then you talk of settling amma banda yanzu, parents d'in yarinyar da kanta ma ba yadda zasuyi da zancen ba in ba aiki ka fara ba", Ammah da tayi serving Abui soup tana mik'o mishi tace "Sadiq in baka rabani da shirman nan ba ranka zai b'aci, itama Laylan da ta biye maka", Wani kallo ya jefi Farida dashi da ta tona mishi asiri, d'auke kanta tayi tana jin haushin make mata hannu da yayi, Sai da kowa ya nutsu yana cikin cin abinci Abu ya kamo hannun Batuul ta k'asa yana kashe mata ido, kallonshi tayi na ya sakar mata hannu, bai sake ba saima sunan Abui da Ammah da ya k'ira, a tare kowa ya kalleshi suna jiran suji mey zaice musu, Batuul dai gabanta sai fad'uwa yakeyi tana tunanin abinda zaice musu tana k'ok'arin kwace hannunta amma ya dad'a k'arfin rik'on, jin yayi shiru Abui ya maida hankalinshi kan abincin da yakeci, Ammah ce tace "Muna jinka", a nutse yace "Ammah inaso mu koma ne, inada aikin dayawa that are pending", tace "Dama can kai ne kayi zamanka, tunda taji sauk'i ka tafi abinka ka rik'a dawowa kana dubata, ido ya lumshe ya bud'e jin abinda Ammah tace snn yace "Ammah tare fa nakeson tafiya da ita, ba nan zan barta ba", Wani kallo Ammah tayi mishi a taqaice tace "baza ta koma gidan nan ba, ka barta nan in ya so ka riqa dawowa kana dubata", marairaice fuska yayi ya kalli Abui da puppy eyes d'inshi, yace "Ammah ba gidan nan zata zauna ba, tun kamin ta fara ciwo take d'aya gidana, Plss Ammah", Abui yace "Anytime you are ready ka d'auki matarka ku tafi", Kallonshi Ammah tayi zatayi magana yace "Meye amfanin barin nata da zaiyi a nan, ko ya tafi hankalinshi ba kwanciya zaiyi ba, su koma kawai zai ci gaba da kula da ita In sha Allah babu abinda zai sameta", Badan ta yadda ba ta hak'ura, Abu kam dariya yayi yace "Nagode Abui, Allah ya k'ara girma da d'auka, Allah ya k'ara Nisan kwana, Allah ya gafartawa magabata yasa a gama da duniya lafiya", "Amin" dukkansu suka amsa, dariya ma ya bawa Abui Dan kawai yace zai iya tafiya da matarsa shine duka wannan addu'a haka, yace "Kaje ka dubo Hauwa?", gaban Batuul sai da ya fad'i jin sunan Ajiddeh, take expression d'in fuskan Abu ya canja jin sunan Ajiddeh, har idonshi ya fara canja launi yace "Abui am not ready, bana so inyi taking decision out of anger, kar inyi abinda we  all will regret", kai kawai Abui ya gyad'a mishi alamar he understands him, Batuul dai gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa, mey zaiyiwa Ajiddeh da har zaisa suyi regretting, kuma meye sa tunda ta farka bata gidan, tana sak'e sak'enta har suka gama cin abincinsu,





Da yamma aka dawo dasu Mum asibiti aka wuce dasu kai tsaye, ita Jainaba, sai wata mata da Dad d'in bai Santa ba, babu wanda baiji mugun ciwo ba cikinsu, Da ya dawo gida suka taho tareda Ajiddeh, in banda kuka babu abinda Ajiddeh keyi, ta rasa bakin cewa komai, Zainab ma sai da Daddy ya qirata snn ta taho, itama kukan ta saka ganin yanayinsu, Dad baice musu komi ba ya tafi wajen Doctor, Doctor yayiwa Dad bayanin cewa Mum ta sami raunika hannu da k'afa da kuma spine d'inta, babu ita babu tafiya a yanzu, d'ayar matar kuma Brain d'inta ya tab'u amma suna fata in ta farfad'o a samu a sake dubawa, sai Jainba ita kuma hannayenta ne kawai suka ji raunin sai kuma kafar ta da sai an yanke sbd ya lalace, tunda doctor ya fara magana Dad ke danne zuciyarshi yana addu'a sbd wani irin abu da yakeji yana taso mishi, saida likita ya gama bayani yayi mishi godiya ya fita, gida ya wuce kai tsaye dan bayajin zai iya komawa cikin d'akin, har ya isa gida yana tunanin abinda ya kai Zuwaira Illorin.

💖💝BATUUL💖💝


Da 94






By Phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



Da yamma suna zaune garden itada da Farida da take ta mata iya shege kan ta k'ara k'iba, bata kulata ba dan Yaa Abu ya fad'a mata babu wani k'iba da ta k'ara, gaba d'aya hankalinta yana kan fruit Bump game d'in da take bugawa, Juyo mata da Macbook d'in dake kan cinyarta Farida tayi tace "Kinga nacewa Affan in zaizo ya taho min da wannan cradle d'in, its cute ai ko?", sai a sannan ta d'ago ta kalli cradle mai kyau dashi snn ta kalli Farida with confusion fuskarta tace "Huh?, cradle nefa, kwana zaki koma yi kai?", Farida ta d'ago ta dubeta tayi mata kallon you ain't okay ta girgiza kai snn tace "Babynmu na siyawa, the newest niece/ Nephew, kinga fa unisex nace ma tunda bansan mey zaki haifa ba, Dan Allah kicewa Yaa Abu kuje a duba cuz in san irin kayan da zan riqa keeping", ta fad'a with soo much excitement a muryarta, Sai lokacin Batuul ta fahimci ina ta dosa ta tsuke fuska tace "Ni nace miki zan haihu toh?", Farida ta kyalkyale da wani irin dariya da ya bawa Batuul haushi tace "Wake jiran sai kin fad'a mishi, tun da naje wajenki UK na gano, shiru kawai nayi maki ina kallonki kawai", Jin ambaton sunan UK ta tuna da Ajiddeh, jiki a sanyaye tace "tun yaushe ne bata nan, ni tunda naji sauk'i ban ganta ba", ba tareda ta dubeta ba Farida tace "Wa kenan?", a hankali Batuul ta furta Ajiddeh, kafad'a Farida ta d'aga tace "Oho, da yake she is not my cup of slush", Batuul ta dawo kusa da Farida tana k'ok'arin rufe System d'in tace "Riri mana, dagaske fa nake, she was nice to me da banida lafiya, har Addu'a fa tayimin", wani irin kallo Farida tayi mata, kallon lallai you are not okay, har ta bud'e baki zatayi magana ta fasa, ta sake janyo System d'in zata bud'e, Batuul tayi maza ta riqe tace "dagaske nake I could remember everything har da kukanta, she insisted mu dawo fa ayi min magani a nan, amma tunda na warke ban ganta ba, kuma d'azu naji Abu na cewa bayason ganinta cuz bayason taking decision out of anger, mey ya sameta Dan Allah?", Sai yanzu Farida ta tabbatar da Lallai Batuul batasan mey ke faruwa, kuma baza taji daga bakinta ba, gyara zamanta tayi tana fuskantar Batuul da kyau kamar wacce zatayi wani maganan kirki tace "Kina jina dai koh?", Batuul ma ta gyara zama dan ta fad'a mata, Farida taci gaba "Naga kin fi kusa da Yaaa Abu, just ask him about her, baza kiji daga bakina ba", had'e rai Batuul tayi tareda kaiwa Faridar duka a kafad'a tace "You are a jerk Allah, shine kika b'atamin lokaci kamar wacce zata fad'i abin kirki", mtewww taja tsaki daidai lokacin wayanta ya hau ringing, dubawa taga unknown number ne, har baza ta d'auka sai kuma ta fasa tayi recieving tasa a kune, cikin masculine voice d'inshi taji yace "Are you ready?", lumshe ido tayi ta bud'e tareda cire wayar  ta sake kallon screen d'in da kyau snn ta maida kunne tace "Hello?", yace "Glitter you there?", a hankali cikin siririyar murya tace "Inace fa sai dare zamu tafi kuma", yace "Nah get ready yanzu zanzo mu tafi kinji?", tace "Okay", yace "Yeah sai na k'araso, take care", a hankali ta lumshe ido, this is the first time Yaaa Abu ya k'irata, ko ina ya samu number d'inta, ko dai dama yana dashi ne, kauda tunanin tayi ta d'ago taga Farida ta kafeta da ido tana wani irin smirk tace "And you will later tell me kefa baki iya soyayya ba, dubi yadda kika wani kashe murya kina magana, badan shegen son jin gulmana ba da bazanji ma mey kike cewa ba", Harararta Batuul tayi ta mik'e tace "You have a problem these days kin sani ko, ni matsa min in tafi, kya ji dashi, I pity best friend", ta fad'a tana mik'ewa zata bar wajen, da sauri ta ajiye Macbook d'in hannunta ta biyota tana dariya tace "exactly why he can't do with me", tsaki Batuul taja taci gaba da tafiya abinta Farida na biye da ita tana ta zuba, ko da suka shigo a parlour suka tarar da Ammah, Ammah tace "Bitti badai baki shirya ba kam, inace da yamma yace zaku fita", sauk'ar da kai tayi k'asa tace "Shine nazo in shirya yanzu Ammah", Ammah tace "Toh shikenan" Farida tace "Ohhh ashe fita zakiyi shine kike shamin k'anshi dan kada in biki, toh nikam sai naje bara inje in shirya nima", dariya kawai Batuul tayi dan tasan in ta biyewa Farida sai ta hanata shiryawar ma gaba d'aya, tana shiga d'aki ta fad'a toilet tayi wanka snn ta fito, akwatin da Farida ta shigo dashi d'azu ta bud'e ta ciro wani swiss voile purple had'e da underwears suma purple, saida ta shafa mai snn ta saka kayan, turarukanshi dake gaban vanity table d'in ta fesa wad'anda taji sun kwanta mata, Farida na zaune parlour suna hira da Ammah wayarta tayi ringing, da sauri ta d'aga ganin Yaa Abu rubuce jiki takai kunnenta tace "Hello Yaa Abu ina wuni", bai amsa ba sai cewa da yayi "Kina jina?", ta kad'a kai tareda cewa "Ehhh", yace "Har ta gama shiryawan ne?", sarai tasan wacce yake nufi amma ta dake tace "waye kenen?", yace "I mean Fatima, ta shirya ne?", daga yadda yayi maganan tana jiyo how stern muryarshi take, murmushi tayi tace "Yeah ta dai hau sama shiryawa, inaga ta gama by now", yace "ita kad'ai ce saman nan ko?", kamin tayi magana yace "Anyway, kina jina koh?, inaso ne ki taimaka mata ki shiryamin ita yadda duk wannan ramar da tayi zata koma, I mean she should look all presentable, har wannan make up d'in naku na mata if possible kiyi mata", murmushi kawai takeyi tace "Tohh Yaa Abu, lemme check on her rn", ya sauk'e ajiyar zuciya yace "Okay Plss do, Thank you" cikeda da murna yau Yaa Abu yace mata Thank you ta ajiye wayan ta dubi Ammah tace "Wai Yaa Abu ne yace in taimaka wa Batuul ta shirya", batareda ta kalleta ba Ammah tace "Toh shine kike zaune?", mik'ewa tayi ta haura sama ta tura k'ofar d'akin da tasan Batuul na ciki, gaban vanity table ta tarar da ita zaune tana faman taje dogon gashinta da yake gajiya mata da hannu, hannu tasa ta anshi comb d'in tana cewa "Kedai har yanzu baza ki fara retouching ba", bakinta ta tsuke dan in da abinda ta tsana bai wuce a tab'a mata gashi ba ace za ayi mata kitso ko taji amma da yake yanzu yana bata wahala babu yadda ta iya, dariya Farida tayi tace "Hey chill!, bafa ni na kar zomon ba, rataya aka bani, start retouching zaki bar k'uncin nan da kikeyi yanzu", d'an tsaki taja tace "Nikam kiyi shiru ki tajemin", haka ta gama taje mata tayi bun dashi ta baya snn tacewa Batuul "ina zuwa", ta fita daga d'akin bata dad'e ba ta dawo riqe da Makeup kit kan madubin ta fara jera komai, Batuul ta dubeta da kyau tace "You also going", Farida ta kad'a kai tace "Nah, ke zanyi wa d'an touch up", Batuul ta yatsina fuska tace "dayake nace miki inason yi koh", Farida tace "Nifa am trying to help, babu ruwana in kukaje yaga y'anmata masu kyau wajen, kuma kinsan dukkansu y'an matan nan yanzu abinda sukeyi kenan ko", da kyau Batuul ke kallon Farida gabanta na fad'uwa jin abinda take cewa, gyara zama tayi kan stool d'in tace "Toh kiyi min", murmushi kawai Farida tayi tazo ta fara shafe shafe fuskar Batuul, d'an touch up tayi mata da ya k'ara fito da kyan Batuul d'in snn ta fita, bata jima da Fita ba taji an turo k'ofar d'akin, batareda ta damu ta juyo taga waye ba taci gaba da rataya towel d'in da take ratayawa, shikam tun daga corridor yakejin k'anshin turaruka masu dad'i, ido ya lumshe ya bud'e ganinta tsaye tana k'ok'arin rataye towel, a hankali ya shigo d'akin ya rungumeta ta baya tareda sauk'e ajiyar Zuciya, itama abinda tayi kenan jin k'anshin shi da d'umi jikinshi, ajiye towel d'in tayi dan yana neman fad'uwa jin d'umin lips d'inshi a wuyarta tana jin sauk'ar numfashinshi, a hankali ya juyo da ita tana fuskantarshi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login