Showing 81001 words to 84000 words out of 215266 words
da su halin da ake ciki, kan kace me sae ga Ammah da Anty Amnah sun taho asibitin, sae bayan kusan minti talatin likita da nurse uku suka fito daga emergency ward, likitan ya bukaci Anty ta bi sa office sanin da yyi ita ce Mahaifiyar Batuul, jiki a sanyaye Anty ta shiga office din likitan, likitan ya dauki farin gilashinsa ya sa yana kallonta yace "Gskya Madam 'yar ki na cikin wani yanayi, a daina daga mata hankali don Allah, dab take da kamuwa da hawan jini" hawaye cike idon Anty tace "Ya jikin nata Dr?" Yace "Da sauki, ta samu bacci ynxu, sae dae meyasa baxa ku tuhumeta ku ji damuwar ta ba Hajiya?" Anty ta share hawayen idonta tace "Xa muyi hkn Dr, mun gode," yace "Gud!" Tace "xan iya shiga in ganta Dr?" Yace "Xa ki iya, amma kada a tada ta" mikewa tayi ta kuma yi masa gdya ta fita, bacci me nauyi ta tarar Batuul na yi an sa mata drip, su Ammah ma duk suka shiga suka dubata, ganin bacci take duk hankalinsu ya kwanta, sae a snn suka iya barin asibitin, Farida ta maida Yayya ma gida don sae gyangyadi take a asibitin, Anty bata kira baba ta sanar da shi halin da ake ciki ba sanin suna Maiduguri har lkcn, Karfe sha biyu kiransa ya shigo wayarta ta daga, nn yake gaya mata sun sauka Abuja lfya, sae a snn ta sanar da shi halin da Batuul ke ciki, hankalinsa ya tashi ssae, ya sanar ma Abui daga airport suka nufo asibitin. Karfe daya saura Abuturrab ya shigo gida duk a gajiye ga damuwa da yyi masa yawa bae san ynda xae yi da Ajiddeh ba idan ta ji xancen auren nn, sa'arsa daya bbu wanda ya sani cikin 'yan uwanta, tun da aka daura auren gabansa ke faduwa ya ji kmr an daura masa abu me nauyi ne a kai, part din Abui ya nufa direct don Avoidin mutane dake cike gidan, ko minti biyar bae yi da kwanciya ba Ammah ta shigo, ya mike xaune ya gaisheta yace "Mun dawo Ammah" murmushi tayi ta xauna gefensa tace "Toh Allah ya taya ka riko babana, sae dae fa Batuul din na asibiti ya kamata ka je dubata ynxu duk da nasan yhu are tired" yace "Asibiti kuma Ammah, me ya sameta?" Ammah tace "Kai dae ka je ka dubata, Allah dae ya bata lfya" a hnkli yace "Toh," Ammah ta mike, yace "Ammah ki ce Sadeeq ya kawo min makullin mota" fridge ta nufa ta bude ta dauko chill yoghurt ta mika masa tace "Gashi ka sha Abuu, nasan baka ci komae ba yau" karba yyi yace "Nagode Ammah" ta juya ta fita tana cewa bari in dauko maka makullin, ajiye yoghurt din yyi don bae jin xae iya sha. Driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa baya jikinsa, a hka ya iso asibitin, Ahmad ya hadu da a haraban asibitin, Ahmad ya gaishesa da ladabi snn ya kai sa har ward din da Batuul take, Wata Sistern Anty ce xaune ward din, don Anty ita ta koma gida sbda baki, har lkcn Batuul bacci take, Abuturrab ya gaida Anty Hafsat, ta amsa masa da fara'a tana tsokanansa don sun saba, murmushi kawae yake kansa a kasa, har dae ta tashi ta tace masa tana xuwa ta fita, Ahmad ta bi bayanta. Ya dde tsaye yana kallonta snn ya ja kujera ya xauna, ya kusa minti talatin xaune ya ga tana juye juye, ya kafa mata ido ko kiftawa bae yi, a raxane ta mike xaune ta bude ido tana kwala wa Anty kira tana kkrin sauka daga kan gadon, ya Mike da sauri ya riketa, hkn bae hanata ci gaba da kiran antyn da take ba tana kuka xata sauko, ko kadan bata lura da wanda ke rike da ita ba don idonta rufe yake, rungumeta yyi jikinsa, lkci daya ta daina fixge fixgen da take tayi lamo jikinsa tana sauke ajiyar xuciya, lumshe ido yyi yaki budewa.
💖💝BATUUL💖💝
39
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Sunfi minti biyar a haka, har lokacin idonshi lumshe, hannu ya sa yana kwantar da dogon gashin kanta da aka kitse rabi aka bar rabi, k'amshin turaren da ya cikata ne yasa ta tunanin inda tasan turaren, a hankali ta buďe ido tana k'ok'arin janyewa daga jikinshi, saketa yayi ya ďan matsa da baya, idonta cike da hawaye ta juya tana k'arewa ďakin da take kallo, ganin shi kaďai ne ďakin yasa ta matsa can k'arshen gadon ta fashe da wani matsanancin kuka, sosai take kuka tana k'iran Aunty, tsayawa yayi yana kallonta, can ya k'arasa inda take ya haďe rai yace "Wai kukan mey kike yi ma mutane hka, baki ga inda kike bane or did yhu want to worsen yhu condition, tunda na dawo nake sintirin asibiti, am even wondering anya ke ba sicker bace, da ko tawa ta sameni" ko kallonsa bata yi ba ta shiga kkrin sauk'a daga saman gadon zata fita daga ďakin tana kuka, yayi maza ya fixgota, baya tayi zata faďi yasa hannu ya taro ta ya maido ta k'irjinshi, ďago kanta yayi har lkcn tana kuka yace "Allah zan mareki in baki nutsu ba, mey ke damunki da zaki rik'a abu kamar yarinya, are yhu okay!" kai ta girgiza mishi ta ďago rinannun idanunta ta sauk'e kan kyakyawan fuskanshi cikin sheshek'an kuka tace "Yaa Abuu wai an ďaura ko, tunda baka sona bana son ka dan Allah ka taimakamin kacewa su Baba su barni a nan inyi zamana, in kayimin haka nima Zan yadda da duk wani condition ďinka ko na meye ne, ko kuma zanyi zamana ba tareda da kowa ya sani ba sai ka saken......", bai bari ta k'arasa maganan ba ya k'ara k'arfin rik'on da yayi mata ya daka mata tsawa yana mata mugun kallo yace "Da alama baki da hankali, sae ynxu kika san da hka, C'mon wuce kije ki kwanta", ssae ta tsorata ganin yanayinshi, tana hawaye ta juya tayi kan gadon, sai da ta koma ta kwanta tukunna ya juya ya danna bell ďin k'iran doctor.
A gida can Ammah ta haďa kayan lefen Batuul Babban mota guda, su Aunty Amna da sauran Aunties ďinsu matane suka kai, su bakwai suka haďu sukaje, da mutunci aka karb'esu can gidansu Batuul ďin, abinci kala kala aka shiga serving ďinsu, kowa ya ya6a ganin yawa da kyan kayan da Batuul ta samu, Basuci abubuwan da aka kawo musun ba sai juye musu Aunty tasa akayi, tukuicin 1million ta bawa Sisters ďin Baba su basu, k'in karb'a sukayi har sai da Yayya ta saka baki tukunna suka karb'a sukayi godiya suka koma.
A can asibiti kuwa nurse ce ta shigo da saurinta jin bell ďin yayi ringing, ganinshi tayi tsaye daga gefen gadon ya nuna mata gadon yace "call her doctor immediately" da sauri ta fita suka shigo tareda da doctor da stethoscope rataye wuyanshi da wani ďan board haka a hannunshi, nurse ďin kuma rik'e da wani k'aramin silver tray da allura akai, yana zuwa ya saka stethoscope ďinnan a kunnenshi yana ďan gwada gudun pulse ďinta, alama yayiwa nurse ďin ta mik'o mishi alluran zai yi mata , ba shiri ta mik'e tana kuka, sosai ta bawa likitan wahala da Aunty Hafsat dake k'ok'arin rik'eta itama, yana tsaye jikin bango yana ganin shure shuren da take tayi, ganin taqi tsayawa ne yasa shi matsowa gaban gadon ba tare da yyi wani tunani ba ya kwanto da ita jikinshi, cikin raďa yace mata "I will slap you idan baki tsaya kin dena bawa mutane wahala ba", lamo tayi jikinshi gabanta na faduwa, har sai sai da aka tsikara mata alluran ta daďa k'ank'ameshi ssae tana hawaye, bai ďagata daga jikinshi ba bayan likitan yayi mata allura itama dae kasa tashi tayi don duk bata da karfi, a nan jikin nashi bacci ya ďauketa ya shimfiďar da ita ya dubi Aunty Hafsat dake ta kallonsu da sha'awa don sae ka rantse masoya ne, yace zaije gida ya dawo.
Sai yamma Aunty tazo tare da Baba, a kan gado suka tarar da ita tana bacci, daga bakin gadon Baba ya tsaya yana kallonta, sosai ya tausaya mata ganin yadda ta rame ta k'ara haske, hannu ya ďaura kan goshinta ya tottofa mata addu'a, snn ya ja kujera ya zauna bayan ya gama ya kalli Aunty yace "Yaushe sukace zasu tafi da ita?", Aunty tace "D'azu dai da suka zo basu ce komai ba toh inaga sai gobe", Aunty Hafsat ce tace "Uncle a barta mana in ta warke sai su tafi da ita, amma yanxu ai bata jin daďi", sai da ya gama jin abinda Aunty Hafsat tace yace "A'ah Hafsat, in kuma yana da abin yi a can fa?, in dae xa a sallameta ko xuwa gobe kawae su tafi ta warke a can din", tashi yayi ya fita yacewa Aunty zai je wajen doctor ya tambayeshi yaushe za a sallametan, ita Aunty bata cewa komai sai ido da ta bishi da, tausayin Batuul sosai takeji a cikin ranta, Babane ya dawo yace musu gobe doctor yace za a sallameta, a nan ya tafi ya bar Aunty da Aunty Hafsat, yana fita Aunty ta dubi Aunty Hafsat tace "Hafsat wlhy tausayin Batuul nake, ban tab'a kawowa zatayi aure so soon ba, sannan kuma ma mai mata, Batuul yarinya ce amma sun k'asa fahimtar abinda nake nufi" Aunty Hafsat ta girgiza kai da damuwa tace "Yaa Maryam ko ni yanxu jimamin abin nakeyi, danma dai naga Aliyun nada hankali da nutsuwa sosai, ko ďazu shi ya taimaka akayi mata allura da k'yar", Aunty tace "dama nifa bata Aliyu nake ba, nafi kowa sanin Aliyu tunda rainona ne, matarshi nake jiyewa Batuul, familyn su basuda daďi akan kishiya, bare Batuul da take yarinya, bata ma san meye kishiyar ba", ajiyar Zuciya Aunty Hafsat tayi tace "Yaa Maryam addu'a kawai zamu tayata yi, itama a sata ta dage da yin addu'a, duk abunda zatayi ta kasance shine a bakinta, kuma ai can zata ci gaba da karatu ko?", kai Aunty ta gyaďa tace "Ehhh haka Babanta yace, har admission ďin wai ya nemata a can, yace gidan nasu ma da makarantar babu nisa, makarantar na Houghton street, gidan kuma na ST GEORGE'S, kinga da kanta ma ta rik'a zuwa", Aunty Hafsat tace "yawwa hakanma yafi kinga zata rage damuwa sosai in tana zuwa school, baza ma tana zaman gidan ba bare su ishi junansu har su samu misunderstanding, Allah dai ya basu zaman lafiya", Aunty tace "Amin ya Allah, sosai zansa ana yiwa Batuul addu'a , duk sati a rik'a mata sauk'an Qur'ani", Aunty Hafsat tace "Allah ya dai ya rufa asiri Yaa Maryam, Allah ya karemu daga sharrin duk mugun abu naji ko na gani", daga nan suka ci gaba da hirarrakinsu.
Sai dare Abutturab ya dawo tare da Ammah, Ammah ce ta fara shigowa yana biye bayanta, Batuul na cin abinci lokacin Aunty Hafsat na kishingiďe kan sofa dake can angle, tana ganinsu ta mik'e ta zauna suka gaggaisa, Ammah tana tambayanta ya mai jiki, Kan gadon ta zauna ta jawo Batuul jikinta tace "Bitti ya jiki, kina samun sauk'i dai ko", kai Batuul ta gyaďa dan wani kunyan Ammah takeji yau, Abutturab dake tsaye Ammah ta kalla tace "kai baka yi mata ya jikine ka tsaya kana kallonmu", kallon Batuul yayi a takaice yace "ya jiki" hararanshi tayi ta ďauke kanta cike da jin haushin alluran da ya rik'eta yasa akayi mata daxu, mamakin hararanshi da tayi yayi ya girgixa kai ya ďauke idonshi daga kanta, sunfi minti talatin wajen Ammah sai nan nan take da Batuul ta rasa ina zata sa Batuul ďin, shi dai kujera yaja ya zauna lokaci lokaci yake ďaga kai yana kallonsu, suna haďa ido take hararanshi, daga baya dariya ma abun ya fara bashi, mik'ewa Ammah tayi tace "Bitti zamu tafi kinji, Allah ya k'ara lafiya, Aunty Hafsat ta fita rakata shi ya tsaya daga baya, kallonta ya tsaya yi amma taqi ďagowa ta kalleshi, gabanta ya matso yace "kin gama harare hararen mara kunya, irin na fara sake maki fuska a tunanin ki ko, Gud! yhu had beta stop decievin ur self coz am still the Abuturrab yhu knw!," bata ďago ba dan mugun bugawa zuciyanta yake, ya dago kanta yana mata mugun kallo yace "Baki ji na ne?" Kuka ta saki kmr jaririya tana kallonsa, ya koma baya da sauri yana kallonta da mamaki, ya buda manyan idonsa yace "Na maki wani abun ne? Daga magana?" Kin cewa komae tayi sae kukan da take, mamaki ya sa shi k'asa cewa komae, can ya sauke ajiyar xuciya ya runtse ido yana shafa kansa murya can kasa ba tare da ya shirya fadin hkn ba yace "ohkk srry!" Lkci daya ya bude ido jin abinda bakinsa ya furta, D'ago kai tayi tana kallonsa ya maka mata harara ya nufi kofa da sauri, ta bi sa da kallo har ya fita kafin ta tabe baki tana share hawayen fuskarta, lkci daya jikinta yyi sanyi qalau tunawa da tayi ynxu fa ita matar Abuturrab ce, tafiya fa xae yi da ita ya raba ta da iyayenta da 'yan uwanta ya kai ta garin da bata san kowa ba, ta fashe da matsanancin kuka ta fada kan gadon tana tausayin rayuwarta.
Washegari tunda aka sallameta bayan taji ranan za a wuceta da ita take kuka kmr ranta xae fita, duk ta fita hayyacinta, k'arfe takwas aka zo ďaukanta, lokacin Aunty ta bata wani lace blue mai kyau da tsada ta saka, ta bata wani laffaya shi kuma Golden, ta saka mata costumes ďin gwal, Batuul dai babu abinda take sai kuka, duk da ba wani kwalliya tayi ba tayi kyau sosai, wajen Baba aka fara kai ta yayi mata Nasiha sosai, rungumeshi tayi sosai tana rusa kuka, da k'yar ta sakeshi, k'annenta ma kukan sukayi tayi ganinta tana kuka, Ahmad, Sa'eed da Khalil ne kawai basuyi kuka ba amma suma jikinsu yayi sanyi, Aunty kam kasa mata magana tayi dan ji takeyi itama zatayi kukan idan ta bude baki, kanta kawai ta shafa cikin sanyin tace "Allah ya miki albarka, ya kare ki a duk inda kike", daga nan ta juya tayi ďaki, Sistern Baba ce ta kai ta har mota, suka shishshiga convoy ďin motocin dake waje akayi gidan Ammah da ita.
💖💝BATUUL💖💝
40
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Suna isa bayan an shishiga dasu gidan Aunty Hafsat ta d'ago Batuul dake ta faman razga kuka, sauran Aunties ďin Aunty da suka taho tare suma suka fiffito daga motocin, Aunty Amnah ce ta fito ta tarbesu da fara'arta, babu abinda Batuul takeyi sai kuka kmr xata shide tana rungume jikin Aunty Hafsat, k'anshin turaren wutane kala kala ke tashi ta kowane angle ďin babban palon, ga wani sanyi dake bugasu, babu abinda matan palon suke sai guďa, sama akayi da Batuul zuwa ďakin Ammah, Farida na biye bayansu ta rasa farin ciki take taya Bestyn nata ko kuma bakin ciki take da auran Yayanta, A kan lallausan rug ďin dake ďakin Ammah Aunty Hafsat ta zaunar da ita, ďagota Aunty Amnah tayi ta maidata kan gadon tace "A ah baza ta zauna a k'asa ba", Aunty Hafsat dai batace komai ba sai murmushin da tayi, haka akayi ta shigowa gaida amarya amma fir taqi buďe fuskanta sai faman zubda hawayen da take, saida duk suka gama suka fita tukunna Ammah ta shigo ďakin, hannu tasa ta sake janyo gyalen yadda baza a gane ba, Ammah na k'arasowa ta zauna daga gefen Batuul, mayafin dake kan Batuul Ammah ta ďaga tana kallon fuskan Batuul da ke hawaye, "Masha Allah", abinda Ammah ta fara faďi kenan gani yadda Batuul tayi kyau sosai, matso da ita gefenta tayi tace "Bitti kukan har yanxu, toh kiyi hak'uri kinji, ai nanma gidane, karki damu kinji, ki kwantar da hankalinki", ita dai Batuul taki cewa komai sai hawayenta da ya daďu, mik'ewa Ammah tayi tasa Aunty Amna su kawo musu abinci tace tana zuwa itama ta fita.
Yana kwance rigingine ďakin Massa idonshi lumshe kamar mai bacci, Massa ne ya shigo ďakin yana waya ganinshi kwance yasa ya katse wayan ya zauna daga arm ďin kujerar ya ďan tab'ashi, a hankali ya buďe idanunshi dake lumshe ya sauk'esu kan Massa yana jiran jin mey zaice, mik'ewa yayi ya zauna ganin Massa ya ki cewa komae yace "wai meye kake kallona haka ne, is this your first time seeing me", murmushi Massa yayi yace "ango irinka ne ni ban tab'a gani ba, yau za a kai maka amarya shine kazo ka kwanta min a ďaki, da ni nake ango yau ai da tun rana zan tafi, da kanku ma zaku kaini in na isheku", ďan tsaki Abutturab yaja zai koma ya kwanta Massa yasa hannu ya rik'oshi yace "Man what are you doing wai, tun ďazu kazo ka kwanta, kai ko marmarin ďauko amaryar taka ma bakayi, dukda nasan ba kai zaka ďaukota ba ai sai kaje ka dubata koh", wani irin kallo ya sakar mishi yace "ni ba sai ka tsaya yimin surutu ba pls, just tell me you need privacy, i should excuse you", ya koma ya kwanta, baki Massa ya buďe zai yi magana yaji wayanshi na ringing, tashi yayi yaje ya ďauko, ganin Ammah ke k'iran yasashi amsawa a risine, a nutse yace "Ammah Nda dubdo, ya gajiya", ta amsa mishi da "Lafiya Massa, kana tare da Abu ne", juyawa yayi yana kallon Abun da ya mik'e da sauri tun sanda yaji Massa ya ambaci Ammah, ce mata yayi "Ehh Ammah, gashi nan muna tare", tace mik'a mishi wayan", "Toh kawai yace ya isa inda Abutturab yake ya