Showing 114001 words to 117000 words out of 215266 words

Chapter 39 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1735

dan batason tayi anything
stupid, murmushin yak'e tayi tace
"Baby naga har na fara bacci baka
shigo ba shine nace bari in fito in
dubaka, ashe kana d'akin Sis dinmu",
ta fad'i da wani irin expression
shimfid'e fuskarta ta sake kallon
d'akin, hannunta ya kamo yace "Yeah
ita na shiga dubawa, kinsan batajin
dad'i", tace "hakane, nima saida na
shiga na dubata before in shiga ciki",
yace "kin kyauta", ya rungumota
jikinshi suka shiga ciki. Batuul kam
yana fita ta tabe baki ta fad'a gado, ko
yunk'urin rufe k'ofarta batayi ba tayi
kwanciyarta dan ko ta rufe in ya tashi
bud'ewa yakeyi, addu'ar bacci tayi ta
tofe jikinta da d'akin taja duvet ta
kwanta, bata fi minti goma a kwance
ba bacci ya d'auketa, k'arfe biyar
daidai ta tashi da addu'a bakinta, tana
zaune kan gadon har biyar da rabi, sai
da taji an idar da sallah ta mik'e ta
shige toilet, wanke toilet d'in ta farayi
tukunna tayi wanka, mayukanta ta
shafa ta gyara gashinta ta tufke da
ribbon sannan ta isa closet d'in
kayanta, tsayawa tunani tayi na kayan
da zata saka, wani gown d'in atampa
ta ciro ta saka, ta fesa turarruka
sannan ta d'au vacuum cleaner ta
tsaftace d'akin tsaf, ta gyara gadonta
ta kunna electric burner ta saka
turaren wutan, lokaci d'aya d'akin ya
d'au k'anshi, sakkowa tayi k'asa ta
shiga kitchen, wutan ta kunna taga
kitchen d'in na nan yanda ta barshi,
shiga tayi ta gama examining komai
taga mey zata dafa, fridge ta bud'e ,
nama ta ciro ta shiga had'a lasagne,
tayi peanut butter smoothie, Garlic egg
Muffins, sannan tayi offals pepper
soup, Abuturrab na dawowa masallaci
yaga wutan kitchen a kunne sai dae
bai bi ta kan kitchen din ba ya wuce
sama dan a tunaninshi Ajiddeh ta
sauk'o tayi wani abin, 7:30 Batuul ta
gama duk abubuwan da zatayi ta jera
komai kan dinning, gyara gidan tayi,
takwas dai dai ta gama ta saka
turaren wuta gidan ya bade da kamshi
me ddi, tea ta hada jin cikinta ya fara
ciwo don ta samu ta sha magani, tana
gama sha ta haura sama ta dauki
magungunan ta sha snn tayi
kwanciyarta don sae goma take da
lectures, abinda zatayi ne ta rasa
kawai ta janyo macbook d'inta ta
shiga kallon Boss Baby.
8:30 Abuturrab ya fito sanye da
pyjamas d'inshi, tun daga bakin kofa
yake jin k'anshin masu dad'i sun
had'e gidan, kanshin turaren wuta da
na abincin da ta dafa, sauk'owa kan
stairs d'in yayi, yadda gidan ke
shining ya bi da ido har ya k'araso
dining, da mamaki yake kallon kan
dinning d'in ganin anyi arranging
abinci Kai, k'arasowa yayi ya
bubbud'esu, aroma din abincin ya bugi
hancinshi, maidawa yayi ya rufe, for
the first yaji Batuul ta birgeshi, yasan
training d'in Aunty ce ita din,
murmushi yayi ya haura sama,
d'akinta ya nufa ya tura kofar ya shiga,
kwance ya ganta kan gado a kife,
bayanta kawai yake gani sai screen
din computer, ya karasa cikin d'akin
don ganin abinda take kallo, har yazo
bakin gadon bata sani ba sai tuntsirar
dariyar da take ta faman yi, jin mutum
ya zauna kan gadon yasa ta saurin
mik'ewa zaune, matsawa tayi daga
kusa dashi ta koma can k'arshen
gadon, kallonta kawai yake, haka
kawae ya samu kansa da murmushi, a
hankali ta d'ago idonta taga ita yake
kallo, maza tayi ta d'auke nata idon
cikin sanyi tace mishi "ina kwana" ya
bude ido yace "Morning! Ashe kin iya
tashi da wuri?" Kauda kai tayi tace
"Eh!" Yyi shiru yana kallonta, satan
kallonsa tayi jin shiru suna hada ido ta
dauke nata da sauri, ya d'aga kafada
yace "Ya dysmenorrhea, ko dama na
kwana daya yake maki?" D'an turo
baki tayi ta juya masa baya, yyi
murmushin da bae san dalilinsa ba,
bae kuma ce mata komae ba ita ma
bata juyo ba sae dae addu'a kawae
take ya tashi ya tafi, wayarta ne dake
gaban mirror ya shiga ring, ta mike a
hankali ya bita da kallo har ta isa
gaban madubin ta dauki wayar, wara
ido tayi tana murmushi ta d'aga, sae
kuma ta hade rai tace "Kin ban
mamaki farida friendship din kenan
dama sae yau kika san za ki kira ni
koh?" D'aga daya bangaren farida tace
"Wayyo Afuwan Besty, kusan kullum
sae nayi xancen ki gun Ammah I just
don't want to call ki fara min kuka ne
wllh, waow hope you are enjoying ur
new home, tell me how it is over
there, have you made friends? Ina
jarababbiyar matar ya Abu, how are
you coping with her, hope she isn't
giving u tough time...." Batuul ta xaro
ido tace "Kai farida spare me those
questions, hakuri ya kamata ki fara
bani da yawa" Farida ta fashe da
dariya tace "Ohhh yhu need to see
how happy I am besty, ur voice is so
lively, from all indication I guess u are
enjoying it over there...." Batuul tayi
murmushi a xuciyarta tace uhm lallai
kam, ko ba enjoy ba, a fili tace "Ni dae
ina Ammah fa?" Farida tace "Tana daki
wllh let me put her on the line" Batuul
tayi murmushi tace "Alryt!" Juyawa
tayi tana kallon Abuturrab da ya kafa
mata ido tayi maza ta dauke kanta,
muryan Ammah ta ji da fara'a tace
"Bitti?" Batuul tayi murmushi ta sulale
nan k'asa ta xauna a hankali tace
"Na'am Ammah ina kwana?" Ammah
tace "Lfya lau Bitti ya gida? In ji ba
matsala dae koh? Kar fa ki boye min
don Allah" Batuul tace "Babu Ammah
ya su Abui?" Ammah tace "Lfya lau
suke, ya karatu kina xuwa dae koh?"
Batuul tace "Ehh ina xuwa Ammah"
Ammah tace "Ma'sha Allah! Ina
Abuturrab din" kallonsa tayi taga ita
yake kallo, a hankali tace "Ga shi nan,
in bashi?" Ammah tace "Bashi!" Hade
rae yyi yana kallonta, ta sunkuyar da
kanta ta mike a hankali ta isa gabansa
ta mika masa wayar, karba yyi ya
fixgota lkci daya ta fado jikinsa tun
kan tayi k'aran da take shirin yi ya
rufe fuskarta a kirjinsa, tayi lamo tana
shakan kamshin jikinsa me dadi,
wayar ya kai kunne yayi ma Ammah
sallama sannan ya gaisheta, da fara'a
ta amsa masa don ba karamin dadi
taji ba jin suna ma tare, tambayarsa
Ajiddeh tayi yace tana dakinta, nan
dae ta dinga masa nasiha kamar
yanda ta saba a kan yaji tsoron Allah
ya xama me adalci tsakanin matansa,
dama irin abinda yake gudu kenan shi,
don jikinsa sanyi yake, lumshe ido yyi
yana sauraranta, ta kusa minti goma
tana nasihan nata har lkcn kuma
Batuul na jikinsa yaki saketa gabanta
sae faduwa yake don she's not use to
that, daga karshe ce masa tayi ya ba
Batuul wayar, mika mata wayar yyi ta
karba ta shiga kkrin kwace jikinta
amma ya ki saketa, k'ara wayar a
kunne tayi, Ammah tace "Kina jina
Batuul" a hankali tace "Eh Ammah"
Ammah tace "Kiyi ta hakuri kin ji Bitti,
bbu ruwan ki da Abokiyar xaman ki
tsakanin ki da ita sae girmamawa, ki
kula da ibadun ki, ki xama me tsafta
duk da nasan kina da amma ki kara
kan na da, ko da yaushe dakin ki da
jikin ki ya kasance cikin kamshi kin ji,
Farida na nn xuwa idan sun yi hutu"
Batuul ta wara ido cike da murna tace
"Toh Ammah nagode, Allah kara
girma" Ammah tace "Ameen Bitti sae
mun kuma waya" nan suka yi sallama
Batuul ta d'aga kai tana kallonsa ta ga
idonsa lumshe, kokarin xame jikinta ta
shiga yi ya bude ido yana kallonta, ta
hade rae tace "Makaranta xan tafi ni"
saketa yyi ya mike sanin lkcn tashin
Ajiddeh yyi, ya fice daga dakin, bin sa
da kallo tayi kafin ta lumshe ido ta
kwanta kan gado.
Karfe Tara da wani abu ta sakko da
shirin tafiya makaranta, xaune ta same
su shi da matar tasa kan dinning suna
breakfast, Ajiddeh na ganinta ta sunnar
da kai don bata so ta sakko ta sameta
tana cin girkin ta ba, idon Abuturrab na
kanta har ta karaso falon kanta a
k'asa ta ce "Ina kwana Anty" Ajiddeh
ta kirkiri murmushi tace "Lfya lau
sister, ashe kin tashi, nace Aliyu ya
shigo ya dubo ki muyi breakfast yace
wae ba kya tashi da wuri" Batuul dae
bata ce komae ba sae kofa da take
kallo, Ajiddeh tace "Toh ki karaso ki
karya mana" girgixa kai Batuul tayi
tace "A'a na sha tea tun daxu" Ajiddeh
tace "Ohk," kofa Batuul ta nufa jin
Abuturrab bae ce komae ba, yana
ganin hka yace "Ki jira ni gun mota, na
aiki driver" toh kawae tace ta fita,
Ajiddeh da mood dinta ya canxa lkci
daya ta sunkuyar da kai kar ya lura, da
sauri ta D'ago tace "Honey ko kuma in
kai ta kawae tunda motar biyu ne kar
ka makara" ba tare da ya kalleta ba
yace "Ae ita ma ta iya driving din,
Akwae kudin da xan bata ne shi yasa
nace ta jira" Ajiddeh taji kmr ta kwala
ihu, wato har kudi xae bata, murmushi
ta kirkira tace "C'mon babe nima ae
kanwata ce, nawa xaka bata in bata
kawae?" Ajiye cup din coffeen
hannunsa yyi yace "Don't bother suna
da yawa kudin" mikewa yayi yana
goge bakin sa da tissue yace "Na tafi
babe, sae na dawo take care of ur self
for me" yana kai wa nan ya nufi kofa,
bin sa da kallo tayi xuciyarta na
tafarfasa, tana ganin fitansa ta mike
da sauri har tana neman faduwa ta nufi
kitchen don lekawa ta window ta ga
inda Batuul xata xauna a motar, ae ko
dai dai lkcn da Batuul ta bude front
seat ta shiga, shi ma ya xaga ya shiga
maxaunin driver, ta fashe da kuka da
karfi wani mugun tsanar Batuul na
k'aruwa a xuciyarta, anya xata iya ci
gaba da yin abinda momy tace tayi
kan Batuul kuwa, ynxu idan Abuturrab
ya ji tana burgesa d'an girkin nan da ta
iya ya xata yi da rayuwarta ita da ko
indomie ba lallai ta dafa shi ruwa bae
yi masa yawa ba, tunanin hakan yasa
ta rushe da kuka ta fito kitchen din
tana rerawa.
[8/22, 14:49] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’





55











By phartiemarhk








Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*







Har suka isa makarantar, Abuturrab bae ce ma Batuul komae ba ita ma window kawae take kallo abun ta, sae da yyi parking sannan ta dauki jakarta dake kafarta xata fita yace "Ki na da hankali kuwa, wa ya baki izinin fita" komawa tayi ta xauna ta jinginar da kanta jikin kujerar da take xaune, kallonta kawae yake, ita kam bata ma san yana yi ba, ya wani daure fuska yace "Kin yi breakfast ma kuwa" ba tare da ta kallesa ba tace "Na sha tea" a d'an tsawa ce yace "Hey look at me!" Juyawa tayi tana kallonsa yace "Yaushe na fara wasa da ke xaki wani dinga dauke min kai ina magana" tagumi tayi tana kallonsa ko kifta wa bata yi, dariya ta basa ganin yanda ta tsuke baki, yace "Ayt, naga alama don kin ga na fara bi ta kan ki ne ynxu, ina kare ki gun matata shi yasa kike son ki raina ni koh?" Ita dae bata ce komae ba kuma bata fasa kallonsa ba, kayan jikinta ya kalla da d'an karamin bakin gyalen da tayi rolling a kai yace "Wae ma kina matar aure xaki dinga irin wannan shigar kina xuwa makaranta kina da hankali kuwa" kallonsa take har lkcn kuma bata ce komae ba, kafin ya kara cewa komae ta kalli agogon wrist dinta tace "Its almost time for lecture" tana fadin hka ta dauki jakarta ta bude motar ta fice, bin ta yyi da kallo cike da mamakin ta, bae san lkcn da yyi murmushi yana shafa kansa ba, kamar wanda ya tuna abu ya bude motar ya fita ya kulle sannan ya bi bayanta, tafiya take kamar me tausayin kasa tana rataye da jakarta, ko kai ka ganta sae ta burge ka don a nutse take tafiyar, kamar ance ta waiga taga yana biye da ita a baya, ae bata san lkcn da ta tsaya ba gabanta na faduwa sosai, ya karaso ya xaga gabanta yana facing dinta, sunkuyar da kai tayi, yana mata wani irin kallo yace "Are yhu stupid? Yhu walked me out ina maki magana?" K'in cewa komae tayi, ya gyada kai yace "Gud nasan maganin ki?" Kudi ya ciro aljihunsa ya mika mata ba musu ta risina ta karba murya can kasa tace "Thank yhu" wayarsa ya mika mata fuskarsa daure yace "driver xae kira ki" ta karba tace "Toh" tafiya yayi ya bar ta nan tsaye ta bi sa da kallo snn ta ci gaba da tafiyarta ita ma, sae taji for the first Abuturrab ya burgeta, "Upon all, he is kind at heart kmr yanda farida ta gaya mata, he always care and show concern" murmushi tayi ta karasa Dept da sauri ganin few minute ya rage a fara lecture.


Karfe sha biyu saura suka fito daga lecture, Batuul tace "Lets get something to eat frnd am hungry" Aisha tace "It's ok, same with me here" suna tafe ne bbu me cewa komae cikinsu har suka iso wani guri da Shaheed ke xaune da abokansa kusan su biyar, biyu bakake kmr sa uku kuma turawa, hiran su kawae suke shi kuma yana duba wani textbook dake hannunsa" Batuul ta hade rae ganin yanda suke kallonsu tun kan ma su karaso, suna Karasowa wani dake xaune gefen Shaheed yace "Hey Aysha!" Aysha ta tsaya tana murmushi tace "Hei Usman how you, how's lecture?" Usman yace "Alhmdllh, dat gal! Is she ur frnd? So haughty of her!" Sae a sannan Shaheed ya d'aga kai yana kallonsu, Batuul ya bi da kallo don ko tsayawa bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta, ya lumshe ido ya bude ya ci gaba da karatunsa, Aysha tayi dariya tace "No, no, not at all, she's not! just dat ba ku saba bane, Well! We'll chat later Usman, bye for now" yace "Ayt! Take care of ur self bae" dariya tayi ta bi bayan Batuul da sauri. Xaune ta sameta waiter dake aiki a wajen yana tsaye kusa da ita yana tambayar me xae kawo mata, tace "Just caramel bun and frapuccino" mutumin ya juya yana kallon Aysha yace "yhu ma'am?" Tace "Same also!" Juyawa yayi ya tafi kawo masu. Aysha tace "Shine kika tafi kika bar ni koh?" Batuul ta kalleta murmushi dauke fuskarta tace "Yea naga yhu were busy ne" Aysha tace "Ayt, amma ko gaisawa ne ki dinga yi da mutane don ku saba mana" Batuul bata ce komae ba sae juya wayar Abuturrab dake hannunta take, Aysha ta ce "Kawo in sa maki digit dina, it's gud ace mun yi exchanging" mika mata wayar Batuul tayi ta karba ta kunna, "Woaww is this ur sister on the screen, kai she's so beautiful wallahi, ya aka yi ke baki yi hasken ta ba" hade rae Batuul tayi ba tare da tasan ta ma yi hakan ba, don ko lura da hoton screen din ma bata yi ba kawae ta fito da wayar daga jaka ne don ta duba agogo, Aysha bata damu da shirun da Batuul tayi mata ba tayi ta koda kyan Ajiddeh, daga karshe ta sa mata nmbrta tayi mata saving ta mika mata, Batuul na karban wayar ta maida jakarta snn ta maida hankalinta kan abincin da aka dire masu gabansu, ta riga Aysha gamawa snn ta fiddo wayar don hoton ya tsaya mata a rai haka kawae, kare ma hoton kallo kawae take, bata san lkcn da ta ja tsaki ba Aysha ta kalleta tace "Ya dae" yake tayi tace "Naga time ya wuce ne, baxa kiyi sllh ba?" Aysha tace "No bana yi" Batuul bata ce komae ba ta shiga gallery duk tayi mark din hotunan Ajiddeh dake wayar har na screen din ta watsa su a kwandon delete. Tana gama hakan ta ja tsaki ta fiddo kudi jakarta tace "Tambayar mana bill Aysha" ita ta biya kudin duk yanda Aysha ta so biya bata yrda ba, suka mike don komawa Dept.



Karfe hudu da wani abu suka fito daga lecture, Aysha tace "kinga tare da aunt dina xa mu wuce tana jirana, Bus xa ki hau ko taxi?" Batuul tace "No xa a xo daukana ne daga gida" Aysha tace "Ayt sae gobe, don't forget Karfe 8 muke da lecture fa" Batuul tayi murmushi tace "Insha Allah ki gaida aunt din ki" Aysha tace "Xata ji, nima ki gaidar min da pretty aunt din ki, so fyn da ita ga gashi, ina nan xuwa wataran in ganta" dauke kai Batuul tayi kmr bata ji ba har Aysha ta bar wajen, waje Batuul ta samu ta xauna, ko minti goma bata yi a gun ba wayar jakarta ya shiga vibrate ta ciro, d'agawa tayi daga daya bangaren yace "Are yhu done for today?" Mikewa tayi tace "Yea!" Ya katse wayar, ta nufi inda tasan xata gansa. Sauke glass Abuturrab yayi yana kallonta, sae kuma ya fito ya bude mata back door sanin gaba xata taho kuma Ajiddeh na ciki, Ajiddeh ta bi sa da kallon mamaki baki bude taji kamar ta rusa ihu, don da kawae so tayi Batuul ta zagayo ta bude ta ganta a xaune sae ta ga ynda xata yi, meye haka Aliyu ke yi, abinda bae taba yi mata ba wae bude mata mota ta shiga, shine yake bude ma shegiyar nan, what have come over him haka, ita kanta Batuul tayi mugun mamakin abinda Abuturrab yyi sae kallonsa take, infact shi kansa sae da ya ji wani iri a lkcn, don bae taba yi ma wata 'ya mace haka ba apart from Ammahn sa, what's he doing, A hankali Batuul ta raba ta gefensa kanta a kasa ta shiga motar, k'asa komawa seat dinsa yyi ba tare da ya kulle mata motar ba duk da hakan ya so yi don ganin irin kallon da Ajiddeh ke yi masa, samun kansa yyi da rufe motar a hankali, snn ya juya ya koma seat dinsa, banda xufa babu abinda Ajiddeh ke yi cikin motar duk da Ac'n da ke kunne, Batuul tayi mamakin ganinta cikin motar sae a sannan ta gane me yasa yayi hakan sae ta ji ddi da bae bar ta taje gaban ba, does he really care haka dama, d'an murmushi tayi tana kallon Ajiddeh tace "ina yini?" Da kyar Ajiddeh ta Hadiye wani abu da ya tsaya mata a makogwaro tace "Lfya!" Abuturrab ya d'an sata kallonta kafin ya tada motar suka bar wajen, sae da ya fara biyawa domino's, yana isa yyi parking ya fito, Ajiddeh da ke cika har lkcn tana batsewa ta bude motar ta fito ita ma, Batuul dae ta bi su da kallo, kallonta Abuturrab yyi yace "No no ba sae kin fito ba kiyi xaman ki a mota" da sauri Batuul ta dauke kai tana kallon window ta gefenta tana danne dariyar da ke shirin taho mata, bae damu da halin da Ajiddeh ta shiga a lkcn ba na kunya ya bar ta nan yyi gaba abun sa ya shiga domino's din, bayan kusan 10 mins ya fito rike da kwalayen pepperoni pizza da ledoji har biyu me dauke da cold stone ice cream, yayi mamakin ganin Ajiddeh tsaye har lkcn kmr warce ruwa ya ci, ya bude back seat ya ajiye kwalayen hannunsa da ledoji snn yana kallon

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login