Showing 195001 words to 198000 words out of 215266 words
mata baifi 2% ba cikin 100% d'in da take mishi, tsoron kada wani abu ya sa ta rasashi ta shiga neman maganin mallaka, duk inda tasan za a bata abinda zaisa Aliyu ya sota ita kad'ai har abada saida suka zagaya itada su Mum da Aunty Jainaba, wani hawaye mai d'umi ta share daga fuskarta tana ci gaba da tunani, tunda ta zauna Kulthum ke kallonta, a hankali taji muryarta tace "Komai yayi zafi maganinshi Allah, ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki shi zai miki jagora", wani iri taji maganar kamar ma ba da ita akayi maganan ba amma sanin su biyu ne kad'ai d'akin yasa ta gane da ita take, bata kulata ba har lokacin, da dare ma haka Ajiddeh bacci kad'an tayi, washe gari ne ganin yanayin Ajiddeh duk ya canja tace "Hauwa tunane tunanen nan da kuka duk da kikeyi matsala zasu k'ara miki, ki samu ki sassautawa kanki, bance ni ba ko inason sanin matsalarki ba, a ah, ki samu wani amintacce da kika yarda dashi kika san zai baki shawara mai kyau ki fad'a mishi matsalarki zaki samu sauk'i a ranki, ko da mahaifiyarki ce ko mahaifinki, zasu fahimceki ko da wacce iriyar matsala kikazo musu, kallonta kawai Ajiddeh keyi ta kasa ce mata komai, batasan komai game da matar ba amma daga yanayinta tasan bazata cutar da ita ba, tashi tayi ta fice daga d'akin tayi side d'in Mummy, masu aiki ne sukace mata Mummy tun da asussuba ta fita amma tace kada a bari ki fita ko inane, wani kallo ta jefeshi dasu kamar in tayi niyyan fitan zasu iya hanata, juyawa tayi ta koma side d'in can, a hankali ta fara magana ta shiga zayyanowa matar abinda ke damunta, matsalarta da kuskuren da duk ta aikata, batace dai asirin kisa sukayiwa Batuul ba, tace kawai na zubda ciki ne da kuma barin gidan sukayi mata
Da asuba shi ya fara tashi, bai tada Batuul ba dan yasan bacci bai wani isheta ba, kwanciyarta ya gyara mata snn yayi wanka ya zira jallabiya ya fesa turarukanshi masu sanyin k'anshi ya fita zuwa masallaci, a masallaci ya had'u da Abui da Sadiq, Bayan an idar da Sallah snn suka gaisa, Abui yana tambayanshi ya jikin Batuul ya amsa mishi da "Alhamdulillah taji sauk'i", Sadiq ma ya gaisheshi yayi mata ya jiki daga haka suka shigo gida kowa yayi side d'inshi, a hankali ya turo k'ofar d'akin, da mamaki ya kalleta ta kunna bedside lamp tana zaune kan abin Sallah riqe da Qur'an tana karanta Suratul Qasas cikin muryarta mai dad'i, Ido ya lumshe ya bud'e snn ya shigo d'akin tareda mai da k'ofar ya rufe, tunda yake da Ajiddeh bai tab'a ganin ta tashi Sallah batareda ya fad'a mata ba, ko ya fad'a sai lokacin da ta ga dama take tashi tayi, da sauri ya kawar da tunanin Ajiddeh yayi da sauri, daga gefenta yazo ya zauna, godiya ya dinga yiwa Allah cikin ranshi da ya bashi Batuul, a zuci yana bin duk ayoyin da take karantawa, kamar yau ya fara jin Qissoshin Annabawa dake cikin surar jin yadda take karanto shi, har saida tayi kusan rabi snn ta rufe ta shafa addu'o'inta ta maida Qur'anin kan bedside drawer, a hankali ta juyo ta kalleshi tace "Ina kwana", wani farin ciki yakeji a ranshi da ganinta, ji yakeyi kamar ya d'auketa ya kaita wajen da babu kowa, inda babu abinda zai sameta sai farin ciki, ido ta d'an wara ganin yana kallonta bai amsa mata gaisuwarta ba tace "Yaa Abu ina kwana", sai lokacin ya lumshe ido ya bud'e yace "Waye malamin da ya koya miki Qur'an?", cike da farincikin tuna mata malamin da baza ta tab'a mantawa dashi ba tace "Malan Ahmad shine malami na, mey yayi?", ta fad'a tana d'an yatsina fuska yace "Har Tajweed duk shi ya koya miki?", ta kad'a kai tace "Har komai ma shi ya koya mana dukkanmu dasu Ahmad da Sa'eed", yace "Ya complete sunanshi yake and yana ina yanzu?", tunanin mesa yake son sani a hankali tace "Sunanshi Ahmad Abu Hamira Daiba, su Ahmad sun san inda yake, nasan har yanzu yana koyar dasu", a hankali ya janyota jikinshi yayi wrapping duka hannayenshi jikinta yace "In na bashi kujerar Hajj da Umara this year yayi?", da sauri ta shiga k'ok'arin juyowa taga dagaske yake nufin abinda yake fad'i amma bai saketa ba saima k'ara gyara mata zama da yayi ya d'aura fuskanshi kan wuyanta, duk da hijab a jikinta bai hanata jin d'umin numfashinshi dake sata jin wani a iri a jikinta ba, da k'yar ta iya bud'e baki tace "Dagaske?", yace "Kuma a bud'e mishi Tahfeez, inaso in princess ta girma ya koya mata", ya fad'a tareda sauk'e hannunshi kan cikinta, "Inaso in ta girma itama tana min irin k'ira'arki", wani irin juyawa tayi ta rungumeshi sosai, yana jin yanayin bugun zuciyarta, shima d'in sake rik'ota yayi, kamar mai jin tsoron abinda zata fad'a tace "I love you", ido ya lumshe ya bud'e yana jin kamar kullum ta zama magana da zata fito daga bakinshi, ta d'ago da sauri tana kallon fuskarshi tace "Yaaa Abu tun yanzu ka fara sani farinciki, am scared yayi min yawa and mayb you might change nan gaba", kallonta kawai yakeyi for seconds ya kasa ce mata komai, da k'yar ya iya samu yace "Baki yadda da son da nake miki ba ko?, baki yadda I can forsake duk wani farin ciki nawa for you to be happy ba ko?", kunya ce taji ta kamata, lafewa tayi jikinshi hannunta kan k'irjinshi tana jin yadda yake heaving a hankali tace "Na yadda, bana so ne yayi min yawa", bakinshi ya d'aura kan nata ya rufe mata baki, saida ya d'ago yace "You deserve all happiness, ki kwantar da hankalinki kinji, you have got me for yourself", shiru tayi lafe a jikinshi, d'agata yai cak ya kwantar kan gado yace "You need sleep, kwanta kiyi bacci", ya shiga k'ok'arin cire mata Hijab d'in dake jikinta zai gyara mata kwanciya, kai ta girgiza mishi tace "Yaaa Abu da sanyi, I don't want to remove the hijab", bai ce mata komai ba har saida ya cireshi sannan ya rungumota jikinshi ya ja musu duvet yace "I will keep you warm", murmushi kawai tayi tana tuna ranan da sukaje gidanshi a London yanda yayi keeping d'inta warm har ta gama duk abinda zatayi, a hankali ta matsa jikinshi ta gyara kwanciyarta, cikin kunnenta ya rad'a mata "are you still cold?", juyowa tayi tana fuskantarshi da kyau tace "Will you always keep me warm all the time?", ya saka hannayenshi duka biyun yana zagayeta yace "Always and forever", daidai lokacin ta tuna da Ajiddeh, tana son ta tambayeshi ina take tana tsoron kada ya sake mata fad'a kamar na ranan, a hankali taji yace "Yaushe zamu koma gida?", idonta a lumshe batareda ta bud'esu ba tace "Nanfa?", yace "This is Ammah's house", ta zumb'uro baki tace "Ni I want to stay here", yace "No gidanki kuma fa, wa zai zauna ciki?", tace "Inada gida ne ni?, d'ayan ai gidanta ne, d'ayan Kumar kace na love of your life ne", dariya yayi yace "So baki manta ba?", tureshi tayi daga jikinta tace "Ni kam ka dena min dariya, a nan zan zauna", yace "Toh bud'e idonki in fad'a miki wacece love of my life d'in?", kamar yana ganinta ta murgud'a mishi baki, juyo da ita yayi yace "Plsss mana, ki bud'e idonki in fad'a mki gidan waye?", a hankali ta bud'e idonta suna had'a ido tayi maza ta rintse su, dariya yayi ya d'agota yace "Fatima get up and listen, gidan nanfa nakine, I built it for the woman I will love, I designed everything for her, banida ra'ayin k'ara aure, I want to live with just a single wife and then Allah yayi Hauwa baza ta zauna gidan ba, then it was you, tun lokacin da akace zan aureki a raina nasa gidan zai zama naki, I then programmed everything ya koma naki, censor and all but God so kind you turned out to be the love I wanted, the love I wanted to give and take and there the house is yours, kinga sai mu koma ko tunda kinada gida, only I and you have access to wannan gidan", jin shirun yayi yawa a hankali ya k'ira sunanta bata amsa ba, da wayarshi ya haska yaga bacci take, murmushi yayi tareda pecking goshinta ya gyara mata kwanciya suka kwanta bacci
Tunda Ajiddeh ta fara Magana Kulthum ke karanto Innalillahi wa inna illaihi raji'un, sosai ta tsorata da jin lbrn snn ta tausayawa Ajiddeh, tasan duk so ne ya sata aikata abinda take nadama a yanzu, ta jima kamin ta bud'e baki da k'yar "Kuskure kikayi Babba, shirka ba k'aramin laifi bane, da lokacin kin mik'awa Allah lamuranki da ko baki had'a da kowa ba yaron nan zai zama mijinki tunda Allah ya kaddara da aure tsakaninku, amma da yake komai rubuttace ne babu yadda za ayi ki tsallake hakan, gashi nan yanxu koda ya hak'ura bazai dena kallonki da abinda kika aikata ba, kada ki gaji da bashi hak'uri koda yana korarki ne, itama yarinyar da ki nemi ta yafe miki dan ita akafi zalinta, batada haqqin kowa sai dai nata da kuka d'iba, ni bansan Mummy d'inki ya take ba da zai yiwu sai kije ki sameta kuyi magana da ita, yanda na fuskanci mijinki yana sonki har yanzu, ki sameshi ki sake bashi hak'uri", d'agowa Ajiddeh tayi da idanunta da suka rine tace "Baya sona, ya dena sona, cemin yayi in fita kada in sake nuna mishi fuskata", ta fad'a tana share hawaye, Kulthum da har ranta ta tausaya mata tace "Fushi yayi, in ya huce zai saurareki, ki bashi lokaci ya sauk'o, snn ki fad'awa Babanki cewa bazai yiwu ki koma gidanshi ba, sbd yace baya son ganinki", a tsorace Ajiddeh ke kallonta, batasan da ya Dad zai d'au zancen ba,haka tayi ta rarrashinta tareda kwantar mata da hankali, da yamma Dad da ya dawo duba ya jikin Kulthum da mamaki yake kallon Ajiddeh yace "baki tafi ba Hauwa?", hawaye ne ya fara zirya idonta, da kyar ta samu ta iya cewa "Dad ya koreni, yace I should not show my face to him ever", kallonta kawai yakeyi har ta gama magana, bayason raising family issue gaban Kulthum duk da hankali ya kwanta da ita amma baijin yin magana gabanta, Kulthum ya duba yace "ya jikin yayi sauk'i ko?", wani awkward haka take jinta, ce mishi tayi "Alhamdulillah tana jin sauk'i", yayi mata sannu da jiki snn yace in tana buk'atar abu ta fad'awa masu aikin a sama mata, ya juya kamar Ajiddeh bata d'akin ya fice, da gudu Ajiddeh tabi bayanshi, wani kallo da ya bita dashi yasa ta tsaya with pleading eyes tana so ya barta ta mishi bayani tukunna kamjn ya yanke kowane hukunci kanta, jiki a sanyaye ta durk'ushe wajen ta fasheda kuka, Daddy kam a ranshi yake tunanin irin tashi kaddarar, ko jiya da daddare saida Mum ta gama mishi tijara harda cewa mey ya tab'a mata duk zamansu, da yake ba mai son hayaniya bane bai biyeta sunyi surutu, masifa ta dinga yi akan zaman kulthum gidan, ganin yaqi kulata ta fice ta banko mishi tana cewa zai gani, duk sai tayi maganinsu, kanshi ne yaji yana sara mishi Dan abin yayi mishi yawa, Ajiddeh da yake ganin gara ita itama gashi tana fad'a mishi wani zancen daban, nan inda Ajiddeh ta durk'ushe ta jiyo k'arar wayarta, addu'a take a ranta Allah yasa Abutturab ne, da k'yar ta mik'e taje ta d'auki wayan, ganin Mum ce yasa ta maida wayar ta ajiye dan batasan mey zatayi mata ba in banda k'arin b'acin rai, har ya katse bata d'aga ba aka sake k'ira, d'auka tayi tasa a kunnen tana jiran jin mey zata fad'a mata, kamar a mafarki ta dinga jiyo abinda ake fad'a Mata, ta kasa yadda da Mum d'inta ce ake cewa tana Illorin, yaushe ta bar Abuja har ta tafi Illorin, wayar ce ta kubce mata daga hannu itama ta sulale tayi k'asa.
💖💝BATUUL💖💝
93
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Gabanta ne ke fad'wa, batason son tabbatar da abinda kunnuwanta ke jiyo mata, yaushe Mum ta bar gida har ta tafi Illorin, so take ta k'aryata zancen amma tunanin da wayar Mum aka k'irata ya sata saurin mik'ewa, a guje kamar wata mara lafiya tabi bayan Daddy, ba tareda tasan ta inda zata fara ba ta isa gabanshi tace "Daddy Mummy", Kallonta yayi yanason jin mey ya samu Mummy, a ranshi yace mey ma zai sameta, a daburce cikin kuka tace "Daddy wai Mummy ce wai sunyi accident", duk da maganar tazo mishi a ba zata bai nuna ba, dakewa yayi yace "Hauwa mey kuma kikeson sake aikatawa bayan wanda kikayi, burinku ne a kullum ku kunyata ku tozartani ku sani magana, dake da y'ar uwar taki duk kunyi nasarar cikar burinku, kun biyewa son zuciya, ki koma kiyi zamanki tunda shi d'in ya fiye miki shi kika zab'a", wani sabon kukan ta fasheda hawaye d'aya na bin wani tace "Dan girma Allah Dad kayi hak'uri ka saurareni, wlhy ba k'arya nake ba, yanzun nan aka min waya da wayar Mum akace tayi accident hanyar Illorin, Dad dagaske ne dan ko da naje side d'inta bata nan, kayi hak'uri kasa a bincika muji ko itance dagaske", kallon Ajiddeh kawai yake a ranshi yana tunanin abinda zai kai Zuwairah Illorin, wa ta ajiye wa take dashi can garin da har zata tafi bada sanin shi bs", juyawa yayi ya tafi Side d'inshi a Ajiddeh na biye dashi a baya tana hawaye, yana k'arasawa d'aki ya d'auki waya yasa a bincika mishi ko dagaske ne abinda Ajiddeh ta fad'a mishi, ba a jima ba aka k'irashi aka tabbatar mishi da "Ehhh gaskiyane, matane uku da Driver d'insu sukayi accident d'in", ajiyar zuciya ya sauk'e dan ya rasa tak'amaimai abin fad'a, tashi yayi zai fita Ajiddeh dake zaune tana hawaye gefenshi ta taso tace "Kaji ko Daddy, an tabbatar maka da Mummy ce ko?, Na shiga uku Dan Allah Dad muje mu dubata, wayyo Mummy na",wani irin kallo da ya watsa mata ne ya sata saurin had'iye maganar dake bakinta, tun da take harara Dad bai tab'a yi mata shi ba sai yau, jiki a sanyaye ta koma ta zauna, fita yayi shida driver yana neman yanda za ayi a dawo dasu gida dan sai an had'a da police, baisha wahala sosai ba kasancewarshi d'an siyasa ko ina sunada mutane,
Wanka tayi ta zauna bakin gadon daga ita sai d'an towel, shima lokacin ya fito daga toilet d'in yace "Bata kawo kayan ba har yanzu?", kallonshi tayi ta zumb'uro mishi d'an k'aramin bakinta tace "Nace fa zanje In d'auko ka hana, nasan bacci takeyi ka tada ta", bai kulata ba ya d'auko wayarshi ya k'ira Farida a waya, yana bugawa ta d'aga yace "Har kin kawo kayan kenan ko?", kamar tana gabanshi ta girgiza kai tace "Yanzu nakeson in k'irata ta fad'amin wanda zata saka fa", yace "Get the whole box here", ido ta wara kaman yana gabanta tace "Kai Yaaa Abu, da nauyi fa", bai jira mey zatace ba ya katse wayan", kayanshi dake ajiye kan gadon ya d'auka ya sanya, kinkiman akwatin ta shiga yi a ranta tana mitar tada da yayi daga bacci, gefen Batuul ya zauna ya shafi gefen fuskarta tareda juyota ta fuskanceshi yace "Fushin meye ne wai har yanzu haka?", ya fad'a yana shagwab'e mata fuska, d'auke kai tayi tace "Ni fa sanyi nakeji ka hana kuma inje in d'auko kayana", kallonta yayi cikin ido da ya sata tayi saurin sadda kai k'asa yace "bana son kina stressing kanki, am there all the time", ya kamo hannunta ya damtse cikin nashi, daidai lokacin Farida tayi knocking tareda turo k'ofan ta shigo da akwatin tana haki,Batuul na jin k'arar tab'a k'ofa dama ta janyo hijab d'inta ta saka, jan akwatin tayi har cikin d'akin ta snn ta dubi Abu tace "Ina kwana", daga gani daga bacci ta tashi yace "Baki iya jiran izini ba kawai you barged into d'akin mutane ko?", zumb'uro mishi baki tayi a ranta tace "Hmmmm ai saidai idan ba Yaa Abu ba", a fili kuwa cewa tayi "yayi nauyi ne shinefa na shigo kuma saida nayi knocking", idonta ne ya fad'a kan Batuul dake zaune daga ita sai d'an towel da hijab, duk ta shagwab'e fuska kamar zatayi kuka, batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba, dariya takeyi harda hawaye snn ta tsagaita dariyar tayi pointing Batuul tace "Ya Allah, you have started gaining weight, Affan have to hear of this, kin ganki kuwa?" Abu da ya tsaya kallonta da mamaki ya daka mata tsawa yace "kina da hankali kuwa?, c'mon get out kamin in tashi in sameki", kallon Batuul da tayi raurau da ido yayi, yasan kuka take shirin mishi, Farida da ke tsaye wayarta ta ciro cikin aljihun rigan baccinta zata k'ira Affan, tsawa ya sake daka mata yace "Na fara wasa dake ko Farida?", kamin tace wani Abu ya tashi ya fizgota ya karb'e wayan ya turata waje, dawowa yayi bakin gadon yana kallon Batuul dake jiran k'iris ta fashe da kuka baki a tab'e, a hankali tace "Dagaskene av gained weight?", in banda iskanci irin na Farida babu ta inda yaga Batuul ta k'ara jiki, dalilin da yasa ma kenan bayason kaita gida sbd yadda duk ta rame, ya d'aura hannu kan wuyanta yana tab'a collar bone d'inta yace "I want you to, kin rame dayawa kuma banaso ni", tasan bazai fad'a mata ba, cire hannushi tayi ta mik'e ta isa gaban human size mirror dake d'akin tana kallon kanta, itama d'in babu ta inda taga ta k'ara k'iba, tasowa yayi ya biyota gaban mirror ya rungumota ta baya tareda tareda sauk'e ajiyar zuciya yana shak'an k'anshinta masu dad'i, ido ya lumshe ya bud'e dai dai nan hawayen da take ta rik'ewa suka gangaro, da sauri ya juyo da ita yana girgiza kai yace "Glitter noo, kar