Showing 159001 words to 162000 words out of 215266 words
hawa yana kallon kyakyawar fuskarta, hannu yasa ya gyara mata gashinta da ya bazar tun d'azu snn ya gyara mata duvet, a hankali ta bud'e lumsassun idanunta dake cike da bacci ta sauk'esu kanshi, murmushinta mai kyau tayi mishi ta sake maida idanun ta rufesu, shima har lokacin murmushin ne a fuskanshi, Farida ikon Allah ta tsaya gani, a hankali ya sunkuya yayi kissing goshinta snn ya sauk'o daga kan gadon, Farida ya gani duk ta wara ido tana kallon Abunda yake, harara ya sakar mata yace "kallon na lafiya ne, mara kunya kawai saura ki tada ta, kuma if you try something stupid sai nayi maganinki dan yanzun ma ba k'yaleki nayi ba" daga haka ya fita, itakam yana fita ta murgud'a bakinta tace "masifaffe" tayi windown d'akin tana kallon yadda tsarin gidan mai kyau yake
Mummy zaune gaban boka Namurje bayan ta gama zayyano mishi abinda ke tafe dasu tana haki, saida ya gama jin bayanansu snn ya d'ago kanshi tare da janye abunda ke kife akan nashi mai kamada hood, innalillahi wa inna illaihi rajiun, wani irin mutum ne zaune gabansu da ko kad'an bashida kyan gani, bak'i ne k'irin snn ga wani shafteten maki shimfid'e a fuskanshi, irin mazan nan ne murd'ad'u, Su Mum hankali kwance ko tsoron halittarsa basuji ba, magana ya fara da wata irin razananniyar murya yace "duk naji bayananku kuma zaku sami aiki daidai bud'ewar jakarku, Mummy tayi caraf tace "ai In kud'i ne bakada matsalarsu, ranka shi dad'e munason wannan yarinyar a fara ta kanta, ba abinda ke cikinta kad'ai za a halaka ba har itama in san samune munaso tabishi inyaso daga baya sai musan yadda za ayi da sauran matsiyatan, dan ni har iyayen yarinyar sai naso ganin bayansu tunda suma ganin bayanmu sukeson yi", ya saki wata shegiyar dariya da gama jin maganganunta yace "Aikinki ya gama, a mik'osu tukunna sai kiji kanun bayanin", jiki na rawa Mummy ta janyo jakarta ta shiga zazzage mishi mak'udan kud'in dake cikin jakar masu uban yawa, kai kace ita akayiwa kishiyar sabida yadda jikinta ke b'ari, sai da ta juye tas snn tace "gasu nan ranka shi dad'e, inma da k'ari za a biyoka dasu", baice komai ba ya d'auko wata jaka ya ciro wani abu shi ba nama ba snn ba jini ba k'ulle a leda ya mik'o mata yace "wannan abin da na baki zaki jefa cikin kogi, bazaki bud'i baki ba har sai kin gama aiwatarwa , yadda zai b'ace cikin ruwan nan haka nan cikin jikinta zai b'ace itama tabi sahu", Mummy jiki na rawa tasa hannu biyu ta amsa kamar wacce aka mik'owa abin kirki ta shiga ce mishi "Nagode ranka shi dad'e", Aunty Jainaba tace "muna nan dawowa bada dad'ewa ba", shidai baice musu komai ba har suka gama b'ab'atunsu suka fita, Aunty Jainaba tace "Yaya kinga wannan mutumin da gani bana wasa bane dan har firgitani yayi da farko", Mummy tayi murmushi tace "Ai Bilkisu da zauri'arta wasa suke dani basu san wacece Zuwaira ba har yanzun, sunana kawai sukeji", suka sa shewa gaba dukkansu biyun sukaci gaba da hiran abubuwan sharrin da zasu jefi Zuri'ar Ammah dasu har suka iso inda motar Sadi take, a firgice ya tashi daga baccin da yakeyi jin an bud'e motar ya Shiga
mitsike ido yace "Hajiya ashe har an fito" basuce mishi komai ba tunawa dasukayi da gargad'in da bokansu yayi musu kawai suka fad'a mota, tab'a baki yayi ganin babu wanda ya kulashi yaja k'ofar ya tada mota suka tafi, wajen sha d'ayan dare suka iso garin Abuja, saida suka zo dab Jabi lake snn Mummy ta shiga tab'a Aunty Jainaba ta tsaida Sadi a wajen, hakan kuwa akayi yayi parking suka fito suka gama tsafe tsafensu suka dawo mota sunata murna tareda fatan samun Nasara har suka isa gida
Kanshi ya kifa jikin steering motar yana tunano stress d'in da ya shiga kwanakin nan, sam hankalinshi yaqi kwanciya da barin Batuul, ga wannan sarkin y'an rawan kan tazo zata k'ara mishi akan na da, iska ya furzar bakinshi ya tada motar yayi hanyar gida yana tunanin yanda zai shawo kan Ajiddeh ya bata hak'uri, parking yayi ya fito daga mota ya shiga gidan, kamar kullum tana nan kwance idonta a kumbure, tana ganinshi ta fashe da wani kukan, yasan hakan zai faru shiyasa ya shigo a shirye, rarrashinta ya shigayi da bata baki as usual don aikin kenan kullum, itakam murna cike fal ranta jin bayanin dasu Mummy sukayi mata a waya, sai da ta gama bashi wahala snn ta sauk'o kamar ko da yaushe, daga nan suka fad'a wata duniyar, ko masallaci bai fita ba nan gida yayi Magrib da Isha itakam tana kwance har saida yayi dagaske tukunna ta tashi tayo alwala ta had'e sallolin da duk ma babu nutsuwa cikinsu, tana idarwa ta dawo jikinshi ta shiga yi mishi wasu abubuwan amma gaba d'aya hankalinshi na wajen Batuul, so yake yaje ya ganta dan yasan ba kowanne abincin takeci ba sai kayan kwad'ayi amma fir Ajiddeh taqi kyaleshi, ita ko tambayar inda ya kai ta ma bata yi.
Kamar yadda yace kar ta tada ta batayi karambanin tada ta ba, k'asa ta sauk'o tana zagaye gidan tana yaba kyan da yayi mata, sai da ta gaji dan kanta ta hawo sama, bata dad'e da dawowa ba Batuul ta farka da mamaki take kallon Farida ta wara tace "Laaah yaushe kikazo, wa ya kawoki?" Farida tayi dariya tace "wannan baccin naki ai har a saceki baki sani ba, tun d'azufa kike kwance", "Wanne irin tun d'azu? Bai jima bafa da na kwanta" inji Batuul tana k'ok'arin sauk'owa, Sallah azahar ta d'auro alwala tayi daga nan suka sauk'a k'asa sukayi kitchen Farida sai santin gidan takeyi, Farida ce ta shiga had'a musu lunch Batuul kuma na zaune kan island d'in kitchen d'in, in no time Farida ta had'a musu spaghetti lasagne tanayi sunata shan hira, saida ta gama snn tayi musu serving a bowl d'aya, tana tunkaro Batuul dashi dariyar dake fuskarta ta d'auke ta toshe bakinta, Farida tace "A'a meye hakan" da k'yar ta samu ta iya bud'e baki tace "kin saka cheese bana so", da mamaki Farida ta tsaya kallonta Dan tasanta da son cheese, sabida itama ta zuba tace "Cheese d'in ne ya saki kamar zakiyi kuka?", ta bud'e baki kenan zata yi magana taji amai na yunk'uro mata, da gudu ta sauk'o tayi sama, Faridan ma a guje ta ajiye fork d'in hannunta tabita a baya tana tambayarta ko lafiya?, saida ta gama kwarara amanta a toilet snn ta d'ago a galabaice duk batada k'arfi, Farida duk ta rud'e sai hawaye take ta rasa yanda zatayi gashi ta baro wayoyinsu wancan gidan sabida tsabar masifan shi, kamo Batuul tayi daga toilet d'in ta wanke mata fuska snn suka fito, kan gado ta kwantar da Ita sai maida numfashi take, tashi tayi ta fita ta dafo mata noodles cikin lokaci kad'an, nanma Batuul turewa tayi tace batason kamshinshi, Farida duk ta damu tace "Besty wai mey ke damunki?, dama yana miki haka kuma yaushe kika zama allergic to cheese da har zai na saki amai",Batuul dai shiru tayi mata tana maida numfashi, a hankali kamar mai rad'a tace "Orange Juice zansha da Toast", da sauri Farida ta mik'e bata dad'e ba ta dawo riqe da abinda Batuul d'in ta fad'a mata, kad'an taci ta ture tace ta k'oshi, ta kwanta bacci, Farida kam kallonta kawai takeyi jikinta duk yayi sanyi, saida ta tabbatar baccin Batuul keyi sannan ta tashi ta sauk'a k'asa dan ta fara jin yunwa, sai a snn ta tuna da girkin da tayi musu, warming tayi ta tsiyayo juice tayi sama dashi, duk bayan seconds sai ta kalli Batuul ta tabbatar tana lafiya, Batuul kam Bacci takeyi sosai, lokaci lokaci takan bud'e ido suna had'a ido da Farida zata sakar mata murmushi taci gaba da baccinta abin har tsoro ya fara bawa Faridan, Har magrib Batuul bata tashi ba sai da Farida taga gari yayi duhu snn ta tada ta suyi sllh magrib, tana farkawa tace "Yaa Abu fa?, bai dawo ba?", Farida tace mata "Ehh", take mood d'inta ya canja ta had'e rai tayi toilet abinta, koda ta fito kin yin magana tayi, Farida har saida ta gaji dan kanta tayi shiru, Kallonta Farida tayi tana murmushi dan ta kasa daurewa da sudden behavior nan nata tace "uhnnm Besty ko dai Baby za a samawa Yayana ne wannan rashin lafiya haka?", kunya duk ya rufe Batuul tayi kicin kicin da fuska tace "Baby kuma, wani irin baby, Malaria nake ya kama ni", dariya maganan ya bawa Farida tace "Ko ba Malaria ba, ai 9ja muke dole kice Malaria kikeyi", bata kulata ba dan ita rashin zuwan Abu ke damunta, itama Faridan badan ta yadda ta k'yaleta ba, haka ta zama wata shiru shiru har goman dare tana tsammanin dawowanshi amma baizo ba har sha d'aya har saida Farida ta gane, shima Abu gaba d'aya hankalinshi na kan Batuul, gashi ta zama so choosy akan abinci duk hankalinshi ya tashi
Washe gari da sassafe ya fito lokacin Ajiddeh na bacci ya tafi can gidan, a d'aki ya tadda Batuul kwance, kallo takeyi amma gaba d'aya hankalinta baya wajen, da k'yar ta samu bacci ya d'auketa jiyan nan, gaba d'aya haushinshi takeji, d'auke kai tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da abinda takeyi, hawowa yayi kan gadon ya d'agata cak yace "Wannan shariyan haka kuma fa? How is my baby?, ya fad'a yana shafa cikinta daidai nan Farida ta shigo riqe da d'an tray da glass cup a kai, had'e rai tayi ta k'araso ciki tareda gaisheshi, bai amsa mata ba saima harara da ya bita dashi, zumb'uro baki tayi tacewa Batuul "Ga lemonade d'in" ta juya zata fita, kai Batuul ta kad'a mata kawai dan kunyan yadda tazo ta samesu ta ji" Farida na fita ya juyo da Batuul yace "Hey bana son wannan silent treatment d'in mana, shout and yell yafi min da wannan shirun da kikemin", kamar ba da ita yayi maganan ba ta sake d'auke Kanta, a hankali ya fara mata magana yace "Hear me out, kinga Ajiddeh ce fa batajin dad'i shiyasa ban dawo ba jiya", kuka ta fashe mishi da ta shiga turashi daga jikinta tace "ai ni lafiyar ce dani, ka koma wajenta tunda nata lafiyan yafi damunka", dariya ne ya k'ufce mishi ganowa da yayi kishi ke damunta, nan ta k'ara k'arfin kukanta, janyota yayi jikinshi ya rungume ya shiga lallashinta, da k'yar ya samu tayi shiru, sai wajen 10 d'in safe ya fita siyo mata abubuwan da ta lissafa mishi zataci ya fita ya samo mata, lokacin da ya dawo gida a parlourn k'asa ya tadda Farida zaune tana kallon Tv yace mata "Ammah tace min Monday zakiyi resuming school dan haka nanda kwana hud'u zaki koma", tace "Ehhh", har ya fara tafiya tace "Yaa Abu wayoyinmu a gidanka, dan Allah ka kawo mana, koh jiya haka Batuul tayi ta amai kuma na rasa wanda zan fad'awa dan babu waya", har ranshi yaji aman da Batuul tayi dan yasan tana wahala sosai amma yaqi nunawa ya dake yace "anqi a kawo d'in, da uban wani ne ya saki bari can?", ya haura sama ya barta nan zaune, kullum haka yakeyi da sassafe zai zo ya dubata har sai ya sata yin bacci yake komawa wajen Ajiddeh, Ajiddeh ma bata sake mishi maganan Batuul ba, ko tambayanshi Ina take batayi ba, Dan Mummy tace mata ta kwantarda hankalinta cikin kwana biyu za ayi maganin Batuul, Farida kuma ce mata yayi ta koma Nigeria.
Bayan kwana uku ana gobe Farida zata koma da yamma Batuul na baccinta a d'aki ita kuma Farida na gefenta tana chatting da Affan d'inta sai murmushi takeyi abinta, a firgice Batuul ta farka tareda sakin k'ara, Farida dake gefenta ta mik'e a rude ta rik'ota tana tambayarta ko lafiya, kasa yi mata magana tayi sai riqe cikinta da tayi ta sulale k'asa tana yarfe hannu, hankali tashe Farida ta shiga neman layin Abutturab dan ko 2hrs baiyi da barin gidan ba, baccin ma da takeyi ajikinshi tayi snn ya kwantar da ita ya fita, kullum a rana yakan shigo sau biyar kuma da sassafe yake shigowa, watarana sai dai ta farka ta ganta a jikinshi, kwana ne kawai bayayi, kuka Farida ta fashe da ganin har ya katse bai d'auka ba, a karo na biyu ne da ta k'ira yana fara ringing ya d'aga, cikin kuka ta fad'a mishi abinda ke damun Batuul, bata gama ba ya katse wayan cikin tashin hankali, in few minutes ya iso kamar dama can yana area, a guje a ya hawo sama, ganin Batuul riqe da cikinta tanata murk'usu ya sake tada mishi hankali, nan ya rungumota ya shiga tambayarta mey ke damunta taqi cewa komai sai kukan da takeyi tana riqe da cikinta duk yanda yaso tyi magana batayi ba sai juye juye da takeyi, Shida Faridan duk hankalinsu tashe yake sosai, ganin sae gaba abun yakeyi duk ya rud'e, Farida daketa hawaye tayi k'arfin halin cewa Yaa Abu mu kaita asibiti Dan Allah kar wani abin ya sameta, sai lokacin tunanin Hospital ya fad'o mishi, ko second d'aya bai k'ara ba ya d'auke ta cak yayi waje da ita, mota ya sata shima ya shiga yaja motar duk hankalinsa tashe, a gurguje doctors suka karb'eta suka shiga dubata, duk iya kwarewarsu sun nuna amma basuga komai ba, haka suka hak'ura suka yi mata allurar pain reliever suka k'ara mata ruwa Dan ganin yanda taji jiki ta jigata, har ta fad'a daga d'an lokacin nan, likitocin na fita ya taso ya rungumeta yana sake tambayanta ta fad'a mishi inda ke mata ciwo, duk yanda yayi da ita k'in cewa komai tayi sai kukan da take tana juye juye, iyakar rudewa ya rude, Farida har fuskarta ya kumbura tsabar kukan da tasha, shikam ji yakeyi kamar ya cire mata ciwon ya dawo dashi jikinsa, Farida ce ta matso gaban gadon ta riqe hannunta d'aya ta shiga tofa mata addu'a a hankali, ta kusa minti sha biyar tana mata addu'a, ko Abutturab baisan abinda takeyi ba, a hankali ta fara tsaida kukan da takeyi jin ta fara samun relieve har dai tayi shiru tayi lamo jikinsa tana sauk'e numfashi, a hankali ya d'ago kanta yana kallon idonta da ya kumbura tsabar kukan da tasha, cikin sanyin Murya yace "Fatima don Allah tell me mey ke damunki, ina ke maki ciwo?", kyar ta iya bud'e baki tana nuna masa cikinta tace "cikina kemin wani iri", rungumeta yayi tsam jikinshi kamar wacce za a k'wace ya dinga rad'a mata sannu a hankali.
ππBATUULππ
77
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tana nan rungume jikinshi har tayi bacci, a hankali yaji numfashinta na sauk'a kad'an kad'an alamun baccin nata ya fara nauyi, ajiyar zuciya ya sauk'e amma har lokacin tana nan kwance jikinshi bai kwantar da ita ba, sai bayan 15mins snn a hankali ya d'an d'agota daga jikinshi ya kwantar da ita kan gadon, kallon k'aramin cute face d'inta ya tsaya yi yana lumshe ido, ciwon rana d'aya amma duk ta fad'a ta rame, dama can ba wani jikin bane da ita, sai haske da ta k'ara, yafi five minutes idonshi na kanta daga baya ya d'auke idanunshi ya sauk'esu kan Farida dake tsaye gefe duk tayi sanyi yace "Taci wani abune bayan na fita?", kai ta girgiza mishi a hankali tace "Babu abinda taci, ko baccin daka sa tayi ma fa bata tashi ba, kawai ina kwance naga ta mik'e ta riqe cikinta, shine tace yana mata ciwo ne", kallon Farida kawai yakeyi har tayi shiru snn yasa hannu cikin gashin kanshi masu santsi ya bajesu yace "take care I will b right back", daga haka yayi exiting d'akin, har ya dawo bacci Batuul keyi, Farida na zaune kan kujera ta jingina kai ta baya ta tsura ma Batuul idanu, tausayinta kawai take cikin ranta, ji takeyi kamar ta fasa komawan gobe ko kuma su tafi tare, motsin k'ofan da taji ne yasata duban wajen, Abuturrab ne ya shigo riqe da paper bags a hannyenshi har ya k'araso cikin d'akin snn Farida ta miqe tana mishi sannu da zuwa ta anshi kayan dake hannun nashi, zama yayi daga kan kujeran idonshi nan kan Batuul d'in, sai da Farida tace mishi sannu da zuwa yaya snn ya dubeta ba tareda ya amsa ba ya jeho mata tambayar "Ta tashi bayan na fita?", kai ta kad'a mishi tace "No! Bata tashi ba, baccinta takeyi tun d'azu" bai ce komai ba ya juya ga kallon Batuul d'in da yakeji kamar ya cire mata ciwon gaba d'ayanshi ta huta, hannunta da babu drip ya kamo cikin nashi ya rik'e gam yana jin wani feeling na circulating dukkanin nerves d'inshi, a hankali ya juyo ya dubi Faridan yace "Kinci abinci ne?", ta kad'a mishi kai alamar a'a, yace "gashi nan ki duba packs d'innan", yayi mata nuni da bags d'in da ya shigo dasu, bags d'in ta janyo ta shiga bubbud'esu, tab'e baki tayi ganin irin abincin da ya siyo musu, ita bata cika son jagwalgwalon turawa ba, daga k'arshe dai pasta with Lamb ragu da cauli flower crisp ta ciro ta ajiye gefe, kallon Abu tayi tace "Yaa Abu in ciro maka?", kamar me nazari yake kallonta snn ya girgiza mata yace "No am okay", batayi mishi musu ba ta koma kan kujera ta shiga cin abincinta, sai da ta gama tayi disposing packs d'in yace mata ta mik'o mishi ruwa, Fridge d'in d'akin ta bud'e ta mik'o mishi bottle d'aya bayan ta bud'e, har lokacin hannunshi na cikin na Batuul, yana jin yadda pulses d'inta ke kaiwa da komowa, basu fi thirty minutes ba bayan nan ta bud'e lumsassun idanunta a hankali, kanshi tafara