Showing 6001 words to 9000 words out of 215266 words
zaki min halin naki ki qi zuwa, Batuul batace komai ba har suka karasa ciki ,tacewa Farida Ammah da Abui da Sadiq fa ?
"Ammah da Sadiq basu dawo ba inaga Sun tsaya wajen Ayyi, Abui yana Shehuri, Nida Yaa Abu ne a gida kawai shima yana sama,
Batuul tace "okay",
sama suka haura suka isa dakin Faridan, suna shiga ta cire gyalenta ta ajiye a akan gadon ta juya inda fridge din dakin yake zata dauki Fanta, tana budewa taga babu Fanta à fridge din, "kinsan zanzo shine baki saka Fanta a Fridge dinki bako, sai tarin bakaken drinks da kika ajiyewa mutane(coke),ni na sauka fridge din kasa in dauko, batajira jin abinda Farida zata ce mata ba ta sauka ta isa dinning area ta bude standing fridge din zata dauki Fanta taji wata Murya cikin sanyi an Ce "Farida kawomin bottle water daya", bugun zuciyantane ya k'ara tsananta, Bata juyo ba kuma batayi magana ba har sai da ya k'ara maimaita maganar amma yaji shiru, ransa ne ya b'aci ya taso yaga abinda takeyi da har ya hanata amsa mishi, yana zuwa ya fizgota da k'arfi da har saida ta fada kirjinshi kamin yayi sauri ya janyeta
💖💝BATUUL💖💝
6
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
tsayawa yayi ya na kallonta ita kuma kanta à kasa, ba a Jin komai sai bugun zuciyanta da ya kara tsananta, riqon da yayi mata ne da kuma bugun zuciyanta yasa hawaye taruwa à idonta, kiciniyar kwace kanta ta fara yi daga wajenshi amma yaki saketa, Dumi yaji a hannunshi ya juya yabi hannun nashi da kallo, hawayen da ya gani ne yasa shi sakinta a hankali ya juya mata baya, juyowa ya sakeyi zai yi mata magana yaga bata wajen,
Parlour ya koma zauna yabi stairs din da ta hau da kallo, lokaci daya ya shiga kwada ma Farida qira, A bakin kofa ta kusa cin karo da Farida, Farida tace "kinga abinda nake gaya maki, I Wonder why he is calling me yanxu" bata karashe maganan ba ta ta riqe Baatul tana tambayarta "Why are you sore ? Mey ya sameki kuma idonki ya canja , kamin ta bata answer ta sukaji ya sake kwada ma Farida kira, bata jira cewan Batuul ba ta sauka kasa tace "Gani Yaa Abu" a nutse yace "Who is she ? I mean that lady, doesnt she talk ko kuma gaisuwa ne bata iya ba ? A zuciyanta cewa tayi "Innalillahi wa inna illaihi rajiun, Yaa Abun nan komai ba a yi mishi daidai, in nayi magana yace na cika surutu, yanxu kuma Batuul bata yi magana ba zaiyi fada" Tana cikin tunanin taji yace "am i not asking you ?"
"No Yaa Abu bata jin dadi ne shiyasa bata gaisheka ba, Ce mata ya sakeyi "daga ina take"? "Batuul cefa kawata tun muna Centagon wacce ka kaini gidansu a Maitama last year da ka dawo har kace bazan kwana ba",
Hannu ya daga mata alaman ya isa,
"ki miqomin ruwa a fridge", a kan center Table din gabanshi ta ajiye ta juya ta bar falon
D'aki ta nufa, tana shiga ta tarar da Batuul à tsaye tana riqe da jaka da gyalenta a hannu, "Zan tafi gida"
"Ban gane zaki tafi ba saboda mey" Farida ta tambaya , Yaa Abu yayi miki fada ne dan nasanshi da yiwa mutane fada, "Ni baiyi min komai ba kawai zan tafi ne"
"In kinje toh mey zaki cewa Aunty ya dawo dake bayan kince har dare zaki kai " kuma in Ammah ta dawo mey zan fada mata ? That kinzo har kin koma ? If Yaa Abune baza mu sake bin hanyan da yake ba nima haka yake min
"Toh naji bazan tafi ba amma baza muje inda yake ba " Farida ta kyalkyale da dariya tace,
"Keh da kika ce zaki fada mishi ina gulman shi yanxu kuma ke da kanki zaki qi bin hanyan da yake "
"Ni ki rabu dani, kuma ai ni babu abinda yayi min kuma zan fada mishi din ai", haka suka ci gaba da hira har Batuul ta manta da Abutturab na gidan
Yana zaune a palo bayan ya kurbi ruwan da Farida ta miqo mishi, tunani yayi na lokacin da Baatul ta bigeshi a masallaci da yadda tace mishi sorry har yanxu da ta zo gidansu yaga hawaye a idonta, hawayen da ya tuna ne ya sashi ajiye ruwan yana fadin "Damn it" à hankali, "does shi always cry"? Yana cikin tunanin yaji an bude kofan palon , Ammah ce tare da Sadiq a bayanta suka shigo suna hira, ciki suka karaso suka zauna a palon, Abu ne yayi musu sannu da zuwa, Ammah ce tace "baku tsaya anyi hawa bane da ku "? "Ehh naso mu zauna sai kuma na fasa amma Abui yana can" , "Muma munje mun duba Ayyi ne, sannan ta kwalawa Fanne kira,cikin hanzari Fanne ta karaso tacewa Ammah "sannu da zuwa,Gani"
"kije ki duba min Farida kice mata mun dawo, sama Fanne ta haura ta fadawa Farida sakon da aka bata sannan ta fita, Farida tacewa Batuul "muje ki gaida Ammah nasan baza ta hawo palon sama ba shiyasa ta sa a fadamin"
"Ni sai kinje kin duba in Yaa Abu baya palo tukunna zanzo"
"Farida tace you are kidding me,taso mu tafi ai in Ammah tana nan bazai yi komai ba" Hannun ta Farida ta jawo suka sauko k'asa, lokaci daya ta d'ago kanta suka hada ido hudu dashi, ta dauke nata da sauri ta karaso cikin falon ba tare da ta kallesa ba suka iso gun Ammah, Farida da gudu ta karasa gun Ammah tana fadin "shine Ammah kuka qi dawowa da wuri inata jiran ku, Ammah bata yi mata magana sai Batuul da ta cewa " A ah Batuul yaushe kikazo, su Aunty na lafiya ? Ashe kunxo, Aunty da mukayi waya tace mayb baza ku zo ba dan Baba na aiki, anyi sallah lafiya ? Batuul da murmushi a fuskanta ta k'arasa wajen Ammah ta zauna daga k'asa sannan tace Alhamdulillah, ta tambayeta ta karfin jiki, "Alhamdulillah Batuul, kun gama karatu lafiya ? Next two weeks zakuyi graduation dinku ko ? Da "Eh" ta amsawa Ammah, Ammah tace "Allah yasa kuyi a sa'a, suka amsa da Amin dukkansu, Sadiq ne ya cewa Batuul "Wane school kikayi applying admission ne , ko har yanxu oxford din zakije ya k'arasa maganan yana dariya, Batuul tace " ban sani ba ko Baba nan yake nema min but if ban samu ba may Baze ko Nile zai kaini dan bayason inyi nisa, Sadiq yace "ai dama oxford makaranta masu ilimine ko da yake ai kema kina da ilimi you can do it", tayi murmushi tace kai Yaa sadiq"
Abutturab na zaune yana kallon TV amma duk hankalinshi yana kansu, tunani yake yaushe ma suka santa and everything about her,wai har Sadiq ma yasan makarantar da take son zuwa, tab'e baki yayi ya ci gaba da kallonshi, Ammah ce ta tashi ta hau sama, yan matan ma suka bita, da ido ya bi bayanta har saidai suka shige ciki
7:20 na dare duka y'an gidan na kan dinning suna dinner,Abutturab ne kadai baya nan Ammah ce ta tacewa Batuul "kwana zakiyi amma ko" Batuul tace "a ah Amma zan tafi yau, yanxu ma Ahmad nake kira baya picking, shi zaizo daukana Ammah tace , "No ai ba sai kin kirashi ba , gasu Sadiq sai su mayar dake bari a gama dinner, Toh kawai tace dan batason yiwa Ammah musu
Abui ne yace "su tafi da Abutturab dan yanxu zamu fita da Sadiq", mik'ewa yayi yacewa Batuul in taje gida ta gaida Baba, tace mishi yayi ta trying number dinshi its not going" Ta amsawa Abui da "Toh" sannan ya ciro rafar kud'i daga aljihunshi yace ga Barka da sallahn ta nan,tayi godiya.
Saukowa yayi daga stairs sanye da grey sweats da farin shirt hannunshi rik'e da key din mota, Ammah ce ta tareshi tana tambayanshi inda zashi,yace mata shehuri zashi, Ammah tace mishi "zakayi droping Batuul a gida , shi ya manta da yarinyar ma saida Ammah ta ambaci sunanta , cewa Ammah yayi "Sadiq fa baya nan ne, "tace sun fita da Abui, iska ya fitar daga bakin shu snn yacewa Ammah " a kirata mu tafi, am in a hurry, Fanne Ammah ta kwadawa kira tace taje ta kira mata Batuul ace ta fito su tafi, fitowa tayi bayan Fanne ta fada musu sakon Ammah, wannan karon babu gwagwaro a kanta sai gyalen kawai ta yafa,tana saukowa Ammah ta tambayeta ta shirya ? Tace "ehh" Toh ga Abu nan zai kaiki gida" Ido ta wara ta dubi inda Abun ke zaune yana jiranta
💖💝BATUUL💖💝
7
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
A hankali take tafiya sabida yadda bugun zuciyanta ke k'aruwa, tana zuwa bakin k'ofa ta juyo ta kalli Farida da pleading eyes ko zata rakata amma sai taga tana d'aga mata hannu da wide smile a fuskanta, Ammah ta sake juyawa ta duba taga ko tana wajen, itama hannu ta d'aga mata tare da mata murmushi, horn dinshi ta sake ji da k'arfi , murda kofan tayi ta fita daga palon har ta k'arasa wajen da motocin gidan ke pake, rasa wanne motan yake ciki tayi sai da taga ya dallo hasken motan daidai inda take tsaye tukunna ta k'arasa amma bata bud'e ba, tsayawa ta sakeyi tana contemplating gaba zata shiga ko baya ? Ranshi ne yayi mugun b'aci ya sake danno mata horn din da k'arfi, kofan dake gaba na gefen driver ta bud'e ta zauna ba tare da tace mishi uffan ba, tada motar yayi sai da sukaje gaban gate kamin mai gadi ya bud'e mishi gate bayan yayi mishi horn ne ya jeho mata tambaya ba tare da ya dubi inda take ba yace "wane anguwane", a hankali cikin sanyin magana tace mishi "Lagos street", tambayanta ya sakeyi " Which side of Lagos street? , "In munje area din zan nuna maka" Baisan Lokacin da ya juyo ya watso mata wani irin kallo ba, a ranshi fadi yake "Is she kidding me, muje zata nunamin, bata san ma hanyan gidansu ba kenan" bai ce mata komai ba ya fita daga gate din gidan ya d'au hanyan anguwan da ta fada mishi, tafiya sukeyi babu wanda ke cewa kowa komai sai k'ira'ar Juhanny dake karanta suratul Qasas da k'arar air conditioner, gaba daya hankalinshi na kan tukin da yake , Batuul kam skirt din jikinta ta riqe da k'arfi har hannunta na yin gumi saboda kwata kwata she is not comfortable, Allah Allah take su k'arasa gida, wani hanyan Lagos street din yabi wanda bata tab'a bi ba har suka isa, suna zuwa ya sake tambayanta " Ta ina gidan yake" juyawa tayi tabi window motar da kallo taga bata san wajen ba, a hankali tace mishi " ba nan bane fa" , wani kallon ya sake watso mata wanda yayi saurin sata sadda kai k'asa , tare da gangarawa gefen titi ya tsaida motan, dago kanta tayi taga ita yake kallo yana jira ta k'ara yi mishi bayanin ina ne idan ba nan ba, ce mishi tayi "Ni ban taba ganin nan ba a anguwanmu, mu koma gidanku sai in nuna maka daga farko inda hanyan gidanmu yake ko kuma in qira Ahmad sai ya d'aukeni a can" sai da ya bari ta gama magana bai ce mata komai ba sannan ya tada motan yaci gaba da tafiya, tsaki yayi tare da duba agogo yaga k'arfe takwas 8 daidai, Sun kusa minti talatin suna yawon neman hanyan gidan basu samu ba, ita dai babu abinda takeyi sai addu'a gashi tana ta k'iran number Ahmda baya d'auka, sai da ya gaji da yawon neman tukunna ya sake tambayanta "For God's sake tell me where your house is" cikin kakkausar murya yayi mata maganan, take jikin ya fara b'ari hawayen dake mak'ale ya k'arasa gangarowa, shiru tayi ta kasa ce mishi komai, magana ya sake yi " Are you this dumb naji Sadiq na cewa kina da ilimi", tsaki ya sake ja yace mata "okay tell me right now cuz you have wasted my time alot", ce mishi tayi "Nifa ban gane hanyan nan da ka bi ba, ba ta hanyan nan muke bi ba mu in zamu....., bai bari ta karasa magana da ta keyi ba yace mata "GET OUT" da k'arfi, kai ta d'ago ta kalleshi dan ta k'ara tabbatarwa da gaske yake, ce mata ya sake yi "I SAID GET OUT", kasa yin komai tayi a lokacin saida ya mik'a hannunshi ya bud'e mata k'ofan sannan ya k'ara ce mata "OUT" ko ledan da Ammah ta bata bata tsaya dauka ba ta bud'e motan ta fita, tana fita ya fizgi motan kaman wanda zai tashi sama
A wajen Batuul ta tsaya ba tare da tasan abun yi ba, ga tsoro da ya cika ta, tsoro ma takeji tayi motsi dan gani take wani abun zai kama ta, kuka ta saka a hankali tana k'iran Baba, wayanta ta ciro ko xata ga mis cal din Ahmad amma taga bbu, takaici yasa ta ki kiransa kuma mayar da wayar cikin jaka, tsugunawa tayi a wajen ta kifa kanta a cinya ta ci gaba da kuka dan ita bata ma san inane nan ya kawota ba, gashi anguwan babu commercial vehicles bare tace zata hau d'aya ya kaita gida, shirun da anguwan yayi ne yasa ta d'ago kanta ta sake dubawa ko zata samu mafita, da taga babu yadda zatayi ne ta yanke shawaran kawai ta tashi tayi ta tafiya ko zata samu yadda zatayi,
Tunda ya bar wajen hankalinshi yake kanta, tuk'i yake cike da damuwa, "yama za ayi mutum yace baisan hanyan gidansu ba idan ba rainin wayo ba"? Tambayar da ya yiwa kanshi kenan tare da jan tsaki, Tunawa da yayi da fuskanta da yadda hawayen ke gangarowa daga idonta ne yasashi saurin taka brake da k'arfi, mutane ne ke ta yi mishi horn amma bai kulasu ba, parkin gefen titi yyi, lkci daya yace "ta ci sa'ar nasan darajar human" wayanshi ya d'auko ya lalubo number Farida ya k'ira, tana d'auka yace "ke inane anguwansu k'awarki", ce mishi tayi "lah Yaa Abu har yanxu baku k'arasaba" a tsawace yace "Tell me what i asked you and dont question me" ce mishi tayi "Lagos street ne behind Leventis, Yaa Abu wani abune ya faru" bai jira ta k'ara magana ba ya katse wayan, yana ajiye wayan ya juya motan hanyan da ya bar Batuul a wajen, yana isa inda ya bar ta ya duba yaga bata nan sai d'an kwalinta da bata san ya fad'i ba a kasa gun, fitowa yyi ya dauka ya jefa bayan motanshi, a hankali ya dinga bin hanyan, daga can ya hango ta tana tafiya tana share hawayen dake zubowa a idonta, karasawa yayi inda take yayi mata horn, bata juyo ba sai ci gaba da tayi da tafiya da sauri, wani horn din ya sake mata amma bata juyo ba sai ma sauri da ta k'ara sabida tsoro, gabanta yaje ya tsaya da motan, bude mata k'ofa yayi yace mata "GET IN," ko kallonshi bata yi ba taci gaba da tafiya, fitowa shima yayi daga motan yabi bayanta dan ranshi ya soma b'aci, yana isa wajenta ya kama hannunta ya jawota har wajen da yake, fixge hannunta tayi da karfi tace "dole ne sae na shiga motar ka malam" bata ankara ba sae ji tayi sa ka ta cikin motar, yyi banging kofar snn ya zaga ya shiga ya tada motan ya bar wajen, kuka ta dinga yi a motar uwa wata karamar yarinya, kara gudunsa yyi had'e da dukan steering wheel din motan yace "Damn it" sae kace warce ya sato, a ranshi fadi yake "Duk su Ammah ne suka jawo masa yana xaman xaman sa" gnin har lkcn bata fasa kukan da take ba yasa ya bude pidgin din motar ya dauko handkerchief ya miko mata, kin karb'a tayi, wani haushi ya kuma kama sa ya mayar da handki din, wani gida suka kusa wucewa tayi sauri tace mishi ga gidanmu nan, brake ya taka yayi horn a gate din yana jira a bud'e, bata jira an bud'e ba ta fita da sauri ta shige gidansu, bin ta da kallo yyi cike da bacin rae, yafi minti goma a k'ofar gidan ba tare da ya tafi ba, idonshi ya fad'a kan ledan dake ajiye, d'auka yayi ya fito yayi sallama da mai gadin ya mik'a mishi yace mishi na Batuul ne, k'iran sunanta da yayi ne ya sashi jin wani iri ya juya ya koma mota ya tada ya tafi.
💖💝BATUUL💖💝
8
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tana shiga gida hanyan garden tayi ta wanke fuskanta da kyau dan kar a ce tayi kuka, da sallama ta shigo palon, ba kowa sai Aunty da Aabid a hannunta tana bashi madara, karasawa tayi cikin palon zata hau bene bayan ta cewa Aunty ta dawo taji Aunty tace "Batuul zo nan, mey ya sami idonki ya canja kala, kuka kikayi" da sauri ta ce " a ah Aunty kaina ne yake ciwo tun da naje, nace zan dawo ma Ammah tace in bari sai da yamma a dawo dani, tana gama maganan ta hau stairs da gudu, da ido Aunty ta bita ba wai dan ta yadda da abunda ta fada din ba, tana kaiwa last stair case din taji sallaman mai gadinsu ya shigo da leda wai a bawa Batuul inji mutumin da ya kawota, Aunty ce tace ya ajiye, yana ajiyewa ya tafi abunshi, Batuul kam tsayawa tayi tana kallonshi har saida ya ajiye ya fita tukunna ta tab'e bakinta ta tafi , dan ita