Showing 183001 words to 186000 words out of 215266 words

Chapter 62 - BATUUL COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

1752

d'aya hankalinta ya gama yin inda akewa Batuul magani, so kawai take taji mey ke faruwa taji meye makomarsu, Mum najin an d'aga waya tace "Jainaba kome kikeyi ki biyo jirgi ki shigo Abuja yau, abin ya min yawa nikad'ai, komai dad'a lalacemin yakeyi", sheshek'ar kuka taji daga d'aya b'angaren, Jainaban dake kuka tace "Yaya kizo ki fitar dani cikin wannan masifa, na gaji da zaman gidan Idrees", Mum ta katseta tace "Mey kuma ya faru bayan wanda kika fad'amin", Jainaba na kuka tace "Banda duka babu abinda nakesha gurinshi, yasa masu gadi sun hanani fita daga gidan, duk ma'aikatan gidan ya koresu babu kowa cikin gidan nan sai ni kad'ai sai kace mayya, yaran ma ya kwashesu bansan inda ya kaisu ba gashi babu kud'i wajena bare in siya kati in miki waya kiji halin da nake ciki, kwakwaran motsi ban isa inyi shiba yanzu zaki ya fara hantara yana tamin habaici kan matar da zai aura", Mum da k'afafunta suka fara rawa jin bayanin Jainaba dawowa tayi kan gadon ta zauna taci gaba da cewa "Yaya ki taimaka kiyi koma menene cikin yau d'innan in samu in fito daga gidan nan, in yaso daga baya musan yadda zamuyi dashi", Mum da abu suka fara cakude mata tace "Ki kwantar da hankali Jainab kina jina, yanzun nan zan fita in San abin yin akanshi, yanzu haka ina wajen shashar nan, daga nan zamu wuce tareda ita, kwantar da hankalinki komai ya kusa zuwa k'arshe", Jainaba tace "Shikenan Yaya ina jira", da haka suka katse waya ta dafa kanta tana tunanin yadda abubuwa sukayi mata yawa lokaci d'aya, can ta juyo ta dubi Ajiddeh dake ta hawaye tace "Ki tashi yanzun nan muje musan abinda za ayi tunda kince yau za a gama mata maganin, Ya Allah mey nayi nake cin karo da masifu iri iri a cikin kwanakin nan", Ajiddeh tace "Mum bafa masifar da kike ciki, in ta tawa kike kije....", Mum cike da fusata tace "Dan uwarki bakida hankali ko?, ganin ina binki a hankali yasa kika fitsare har kike ce min indan taki masifarce in rabu dake ko toh bari kiji, mijin Jainaba aure zai k'ara kullum narka mata duka yakeyi a gida, Wanda zai auri Zainab ya fasa , matarsa da mukayi sanadin fitanta daga gidan ya maidata, Babanku yazo da wata mata gida yasa an gyara mata part guda ya zube mata y'an aiki, bansan tsakaninshi da ita kullum hankalina a tashe na tambayeshi wacece ita yace wannan ba matsalata bace snn gaki, akan wata can banza kikeson b'ata min rai, komai dan ku nake yinshi dan Ku samu farin ciki mai d'orewa amma bakya ganin k'ok'arina, yanzu babbar matsalar da muke ciki duk akanki sbd kin fifita miji da danginsa akanmu, har a samo mai magani bakiyi tunanin sanar dani ba", Mum ta fashe da kuka tace "In sha Allah na barwa Aliyu ke Hauwa, kafata ta bar d'akin nan toh ki manta kinada wata uwa", ta miqe ta zari Jakarta tayi hanyar waje, tana kaiwa bakin k'ofa zata bud'e taji an turo k'ofar, Abutturab ne tareda da Ammah suka shigo d'akin a tare, Ajiddeh na ganin yanayin sa durk'ushe a wajen ta saki wani irin kuka, cikin d'akin ya k'arasa shigowa, Mum da duk yan hanjinta sun kad'a ta dake ta dubi Ammah tace "Yanzu nake shirin inje in duba mai jiki, yarinyar nan ce take ta kuka nace addu'a zatayi mata", ko kallonta Mum batayi ba, Hannun Ajiddeh dake durk'ushe tana kuka ya kamo ya mik'ar da ita, cikeda kuka kamar ranta zai fita tace "Aliyu tsaya kaji Dan Allah, Let me explain kaji, wlhy Allah....", wani irin fizga da yayi mata yasa ta toshe bakinta da d'aya hannun nata, Mum da ta tunkarosu tana "Kai banza ina zaka kaimin y'a kake fizgarta haka", wani mugun kallo da ya jefeta dashi yasa tayi shiru ta matsa da baya, Har ya fita da Ajiddeh daga d'akin baice komai har saida ya kaita d'akinshi da yakeyin ayyukanshi kamin yayi aure, sake hannunta yayi yana kallonta da idanunshi da suka rine yace "Hauwa did you really hurt her? Kune behind suffering din Fatima all this while?", shiru yayi yana jiran jin amsar da zata bashi, ganin tayi shiru tana kuka yasa shi daka mata wani mugun tsawa yace "Answer me" har saida yasa Ammah yiwowa wajen tareda Mum, a kid'ime Ajiddeh ta kalleshi tana kuka tace "Am sorry, am so sorry, I wanted telling you Dan Allah kayi hakuri wlhy sharrin shaid'an ne, forgive me pls Aliyu", wasu hawaye ne masu d'umi ya shiga zirarowa daga idonshi, lumshe ido yayi ya bud'e ya kalleta snn yace "Get out of my sight, don't you ever cross my way not now not ever", tsananta kukanta tayi tana girgiza kai ta shiga matsowa kusa dashi tana "Aliyu you know I love you, karka horani da rashinka, I can't endure ko wane irin punishment amma banda rashinka dan Allah kayi hak'u.....", wani mugun kallo ya jefeta dashi da ya sata had'iye maganarta ya daka mata tsawa yace "I said get out", ganin yanayinshi tasan komai zai iya faruwa a lokacin, toshe bakinta tayi ta juya ta ruga a guje ta fice daga d'akin.
[11/15, 11:15 AM] β€ͺ+234 810 957 2036‬: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’

88

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

A guje ta fice daga d'akin tana riqe da bakinta, ko Ammah dake shirin shiga d'akin bata lura da ba tayi wucewarta , hanyar staircase tabi zata yi k'asa taji an rik'ota, Mum ta gani riqeda hannun nata, kuka kawai take tana girgiza kai alaman ta sakar mata hannu, wani uban harara da ta bita dashi ta fincikota tace "Sallamamiya Ce mishin kikayi kinada masaniya kan abinda ya samu tsinanniyar yarinyar?, toh Dan Ubanki duk abinda ya biyo baya ki kuka da kanki tambadadda, In banda lalaci irin naki Dan uwarki har ya isa ya wulakantaki ina gidan nan?, banda sunci darajar gidansu nake daga shi har uwar tasa da na karta musu rashin mutunci, shashashar yarinya, yanzun ma bata baci ba muje in keh baki iya kare kanki ni zan yi, wlhy ban san asarar haihuwa nayi ba da na zubdashi tun kamin kizo kina cusa min kuttu", ganin Ajiddeh na k'ok'arin k'wace hannunta yasa Mum cikeda fusata tace "kinsan Allah in baki kiyayeni ba sai naci mutuncinki, yarinya ana neman k'watar miki y'anci kina neman yi min tijara? Kuma wlhy kika kuskura kika tozartani saidai gidan wata uwar bani ba, tsine miki zanyi ki k'arasa lalacewa kibi duniyar gaba d'aya", ta fizgota sukayi hanyar d'akin, kan kujera Ammah ta tarar da Abu zaune ya dafe kai yana kallon marbles d'in d'akin, hannun Ammah da yaji jikinshine ya sauk'ar mishi da nutsuwa, hannayenta duka biyu tasa ta tallabo kanshi tareda shafa kanshi tace "Are you okay?", ido ya lumshe kamar maijin bacci da k'yar ya bud'esu yana kallonta ya girgiza mata kai alamun "Yeah am fine", kan nashi ta sake ta kamo duka hannayenshi tace "Badai dukan yarinyar nan kayi ba ko Aliyu, naga ta fice a guje tana kuka", ya kalli Ammah for some seconds snn ya bud'e baki da k'yar yace "I just don't want to see her anywhere around, not now not ever", Ammah da taji dad'in maganganun shi taja wata kujerar ta zauna tace "Alhamdulillah, Allah yayi mana tsari da masharranta, tayi maka admitting d'in sunada hannu ciki koh?," ido kawai ya lumshe ya bud'e dan gaba d'aya hankalinshi na wajen Batuul, ganin baison zancen tace "Ba komai ai ka kwantar da hankalinka, zamu jirayi hukuncin Abui, muji ya za ayi dasu, amma albasa batayi halin ruwa ba dan mahaifinta ba halinsa ba kenan, kuma nasan in har yaji wannan ta'asa da sukayi sai ransa ya b'aci, baiwar Allah yarinya k'arama da ita sun sata cikin azaba, mey sukeso mucewa Maryam ya sami y'arta?", ta matso kwallar dake idanunta tace " koma dai menene dukdai nina jawo shi tunda yarinya na gaban iyayenta hankali kwance nasa aka nema maka aurenta, bayin Allah ba tareda second thought ba suka bamu, Allah dai ya mata katangar k'arfe da mugaye", har Ammah ta gama magana bai bud'e bakinshi yace uffan ba, tunanin Batuul dake dad'a yi mishi yawa yasa ya zame hannayenshi cikin na Ammah ya mik'e yayi hanyar k'ofa, hannu yasa zaiyi sliding k'ofar yaji an rigashi ta d'ayan gefen, Mum ce janye da Ajiddeh ta shigo tana sababi, "Har mu za ayiwa sharri, Bilki kinyi kad'an kuma wlhy hukumace zata rabamu daku, wato tun kiyayyar da kikemin muna yarinta shine ya koma har kan y'ay'ana sai kin bisu da sharri ko, mu za ayiwa k'azafin yiwa wata figaggar yarinya can asiri, billahil azim sai kinyi Dana sani", Ajiddeh da damuwa ya cika ta rasa inda zata sa rai taji dad'i zubewa k'asa tayi tana kuka, Mum ta dubeta tace "Sun sallameki kin zama bakida amfani shine suke tunanin muma munyiwa wata can ko, kai kuma d'an mace an tura maka karuwa kanata cin amanar y'ata shine Dan Allah ya kamaku zaka lak'awa y'ata da bata san zance ba", ido Abu ya rintse yana fisting hannayenshi jin ta dangana Batuul da karuwa, kai yasa zai fice daga d'akin Ammah ta rik'oshi ta jawo shi gabanta tace "Abutturab inajin aure ne ya had'aka da y'arsu tun farko, inaso yanzun nan ba anjima ba ya rabaka dasu, mey za ayi da mugun iri irin wannan?, maza sallamar musu y'arsu, Allah ya had'a kowa da rabonshi", a firgice Ajiddeh ta tashi har wani dishi dishi take gani tazo gaban Ammah ta had'a hannayenta duka biyu tana kuka tace "Ammah Dan Allah kimin rai, nasan ban tab'a zame miki sirikar kirki ba, babu abin arziqi da na tab'a yi miki amma Dan Darajar Annabin tsira da aminci kar kisa ya sakeni, nasan ko bai sakeni ba tunda yace bai kuma son ganina nasan mutuwa zanyi, ki yafemin, ki roka min yafiyar Batuul ki rok'a min yafiyarshi in mutu da aurensa akaina, badan halina ba sai dan nasan ke uwace ta gari mai halin dattako, inayiwa d'anki son da bansan adadinshi ba a rayuwata", sanyi jikin Ammah yayi amma ko kallonta batayi ba tace "Babana ina jiranka, ka sallamesu su bar min gida", Jiki a sanyaye itama Ajiddeh ta kalleshi amma ko kallon inda take baiyi ba ya karb'e hannunshi daga rik'on Ammah ya fice daga d'akin, Duka Mum ta d'aka mata tace "Dan uwarki sai ki tashi tunda ke asararriyace, ban taba sanin ke mara hankali bace sai yau, har uwarsa ta bud'i baki tace ya sakeki uwar mey zaki zauna yi gidanta, kike wani cewa keh kinsan uwace ta gari ita, da y'arta ce baza ta tsaya....", ko kallonsu Ammah batayi ba ta fice daga d'akin itama, a guje Ajiddeh ta biyo Ammah tana ci gaba da magiya, Sau d'aya Ammah ta dubeta tace "Ba yafiyata zaki nema ba, wacce kika cutar zaki tambaya ta yafe miki", har ta sauk'o k'asa bata dena binta abaya ba, Abui da Farida tare suka fito jin hayaniyar Ajiddeh da Mum, kallon Mum yayi yace "Bilkisu lafiya?, mey ya sameta?", jin muryar Mum sukayi tana cewa "Ki fita harkar k'ananan mutane kizo mu wuce, kema uban ki nada gidan", Abui ya kalleta jin mey take fad'i snn ya kwalawa Abutturab k'ira, ba b'ata lokaci ya fito d'akin da Batuul ke kwance, yana ganin Ajiddeh ya had'e rai, Abui ya dubi Ammah yace "Mey yayi mata kina wajen baki hanashi ba", Ammah ta had'e rai ta tab'e baki tace "cewa nayi ya saketa", Abui ya dubeta da kyau jin abunda ta fad'i yace "Kan wane dalilli zakisa ya saki matarsa?, kaji shirme, kai Aliyu da hankalinka zaka saki matarka, kuskurene tayi kuma yarinya Allah ya tashi kafad'unta sai dai fatan Allah ya tsare gaba", Ammah ta fashe da kuka tace "Abui ya saketa kawai, dubi fa yadda suka cutar da Fatima amma uwarta ke musun sharri mukayi musu har da cewa k'ara zata kai mu munyi musu sharri", Sai lokacin Farida ta fuskanci kan zancen, Ajiddeh ta duba da wani mugun kallo ta tab'e baki ta matso wajen Ammah, Mum cikeda masifa tace "Yo ba Sharrin kukayi mana ba, wacece Maryam ma bare Fatimar har a wani yi mata asiri, kai kaga", ta nunawa Abu yatsa taci gaba "In ka fasa sakin nata baka cika haifaffen d'an bilki ba", Abui da mamaki yake kallon Mum, Abutturab da tunda yazo ya kasa d'ago kai a hankali cikeda nutsuwa batareda ya kalleta ba yace "I don't need a second thought, get out of my sight before I loose my cool, before you regret ever knowing me", yana fad'in haka ya juya batareda yabi ta kan kowa ba", Ajiddeh na jin haka ya fito daga bakinshi kuma a gaban Abui tasan zamanta gidanshi ya k'are, har wani dishi dishi take gani ta miqe tayi waje cikin hanzari batareda ta kula kowa ba ta fita a guje, Mum ce ta bita a baya tana kwala mata k'ira, girgiza kai Abui yayi yace Allah ya kyauta yayi sama , bayan kamar minti biyu Mum ta sake shigowa ta nuna Ammah da d'an yatsa tace "duk mey zai Samar min 'ya wlhy ki kuka da kanki", ta juya ta fice fuuu kamar wata iska


Yana komawa d'aki ya d'auki Batuul cak a hannunshi ya rungume ya fito da ita, ganinshi riqe da Batuul Ammah ta tambayeshi "lafiya ka d'aukota, ko ta tashi ne?", kai ya kad'a mata yace "Inaso ne ta huta a saman" snn ya k'ira Farida ta biyoshi, yana shiga d'akinshi ya kwantar da ita kan gado, dai dai nan Farida ma ta shigo, yace "Je ki samo mata kaya mara nauyi, I want her to change", kai ta kad'a mishi tace "okay", ta fice, ya kurawa fuskan Batuul ido y'ana kallonta a hankali ya kamo siraran yatsunta ya kai bakinshi ya manna mata kiss yace "I love you Batuul", kamar taji abinda ya fad'a a hankali ta bud'e ido ta kalleshi, ido ya lumshe ya bud'e yana so ya tabbatar dagaske ta farka, da sauri ya matso yana riqeta yace "Alhamdulillah, am glad kin farka", murmushi tayi mishi ta shiga k'okarin tashi ta zauna, shima d'in murmushin yayi mata ya rungumeta jikinshi yana lumshe ido yana shak'ar k'anshinta da yakeso a koda yaushe, jin yaqi saketa yasa ta d'an turashi, ya d'agata daga jikinshi yana kallon fuskanta, hawaye ya gani cike da idonta kuma har lokacin da murmushinta a fuska ta k'arewa d'akin kallo tace "Yaa Abu inane nan?", ya dad'a matso da ita kan cinyarshi yace "Cry no more kinji, baza ki sake kuka ba sai na farin ciki In sha Allah, We are home, and you will be safe here in sha Allah", Farida ce ta shigo riqe da kaya a hannunta, watsar da kayan tayi ta fasa ihu ta hawo kan gadon ta k'ank'ame Batuul tace "Alhamdulillah, omg Batuul am happy kin warke, don't fall sick Dan Allah kinji?", sai kuma ta fashe da kuka, Abu ya kalleta yace "Keh mey haka, kin shigo kina ihu, ina aiken da nayi miki?", Farida ta cunno baki tace "Yaa Abu am just happy my friend is well again", Batuul tayi murmushi ta kamo hannunta tace "Yeah Alhamdulillah, am feeling much better now, Ammah fa", zata bata amsa yace mata "Leave", ta zumb'uro baki ta sauk'o daga kan gadon, Batuul ta kalleshi da idanunta da sukayi raurau tace "Yaa Abu mana, let her stay", bai kulata ba ya sake kallon Faridan data fita kamar mai shirin karya k'ofan, ya kalleta yace "Baby you hungry ko?", kai ta girgiza mishi, hancinta ya d'an ja yace "Nasan kina jin yunwa, and my lil champ too", ya kai hannu kan mararta, sam ta manta da wani ciki a jikinta sai yanzu, murmushi kawai tayi mishi, yace "Let's freshen you up, sai kici abinci", tace "Ni bacci zanyi, am not hungry", tashi yayi ya tattare kayan da Farida ta watsar snn ya dawo kan gadon ya shiga k'ok'arin cire mata kaya, hannunshi ta riqe tace "Zan cirefa", kamar baiji mai take cewa ba yaci gaba da abinda yakeyi, cak ya d'agata yayi toilet da ita, wanka yayi mata tayi brush snn tayi alwala ya d'aukota suka fito, shi ya shiryata ya canja mata kaya, a lokacin Ammah da masu aikinta suka shigo da abinci, ba abin mamaki bane dan tasan irin son da Ammah ke yi mata tun kamin ta auri d'anta, ranan ko Sallah Abu bai fita ba a d'aki yake yinshi ya jasu jam'i, lokaci lokaci Ammah ke shigowa dubata, da daddare ma shi yayi mata wanka ya shiryata cikin kayan bacci snn ya tofa mata addu'a tareda ja mata bargo,wutan d'akin ya kashe ya jawota jikinshi yayi pecking lips d'inta yace "Have a sound sleep Haya", sake shigewa jikinshi tayi, a hankali kamar mai rad'a tace "Ban ganta ba duka yau?, ina ta tafi?, kamar baiji abinda tace ba ya dad'a gyara mata kwanciya yace "You need rest, kiyi bacci", sake maimaita mishi tambayar tayi tace "Yaa Abu mana, she needs to know na warke, ina Ajiddeh?", jin ambaton sunan Ajiddeh yasa yaji abubuwa da dama na taso mishi, hannunta ya kamo cikin nashi yace "Fatima Kiyi bacci Dan Allah", k'ok'arin tashi ta shigayi tace "Toh ina taje mana, I just need to know", a fusace ya janyota yace "I will slap you right away in baki kwanta ba, bakisan you are still weak bane? komawa tayi ta kwanta, ajiyar zuciya yaji ta sauk'e, yaja d'an tsaki, bada son ranshi yayi mata fad'an nan ba, so yake ya dena tunawa da Ajiddeh, gabanshi har fad'uwa yakeyi in ya tuna abinda tayi, he have to caution Batuul d'in da kanta ta dena tuna mishi da ita, atleats for the mean time, ajiyar zuciya ya sauk'e ya rungumota jikinshi yace "Am sorry Fatima", bata ce mishi komai ba, hakan yasa ya mirginota tana fuskantarshi yace "You should rest Fatima Dan Allah, I love you"

[11/22, 11:21 PM] β€ͺ+234 803 698 6494‬: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






89






By

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login