Showing 165001 words to 168000 words out of 183750 words

Chapter 56 - ABU DAYA (Muke So)

29 Oct 2024

10688

Don Allah ku bari idan nan da karfe tara bata haihu ba ku mata, amma zata iya da kanta."

...dakyar aka barshi ya shigo dakin, zama yayi a kujeran da yake kusa da gadon.
."Baby na! Wai ba zaki iya ba, don Allah ki daure mana, bana son aikin nan kinji, ai na gaya miki tare zamu yi kuma gashi nan nazo muyi nakudar tare."

Gyad'a mishi kai nayi tare da rike hannunsa.

Wasa wasa, aka yi sallar magrib, dakyar ya tafi masallaci,

Sun tafi masallaci, yana dawowa ya shigo d'akin ya samu har yanzu. Addu'o'in kan babu wani ba a bani ba, muna zaune lokacin isha yayi.

Kamar ba zai tafi ba, yana saka kai waje, suka zuba mishi ido. Tare da tambayar shi, bai basu amsa ba, kawai ya Barsu ne a gurin.

Yana fita kamar an korashi shi, sai ga Haihuwar gadan gadan, kiran shi nayi amma baya nan karshe Rahbeel ya shigo min, duk da ciwon da nake ji, cikin masifa nace.
"Fitar min a daki bana son ganinka ka nimo min mace ba dai kai ba"

Abin ya bawa kowa mamaki, fir naki ya duba min, dole wata babban Nurse ya Kira tana shigowa, ina sauke ajiyar zuciya bayan ƙatuwar yarinya na ta fado daga jikina.

Tare da mabiya.
"Sannun! Ai dole ki wahala, kin ganta fa, babbar mace kamar ta haƙa."

Tana cikin yanke cibiyar, cikina ya murda, kafin nayi mata magana na kuma sauke wata yar, wacce kukanta ya karaɗe dakin baki daya, dan na farkon bata yi kuka ba.

Kuma suma basu san na haihu ba, gyara yaran tayi sannan ta fita ta gaya musu, shiru suka yi ana jiran ya shigo.

Yana shigowa ya kalli agogon falon, zama yayi cikin mutuwar jiki, yasan dole aikin dai zasu min, baya son aikin nan.
"Congratulations! Baban biyu,?!"

"Ta haihu ne?!"
Ya tambaye su a raunane, murmushi Aunty Taslima Tayi tare da nuna mishi dakin, kasa tashi yayi, hada hannun shi yayi ya fara. Zabgawa Ubangiji kirari, tare da yabon Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, yayi addu'o'in sosai sannan ya mike zai je dakin akan rike shi..
"Dalla malam! Karka je ka rigani ganin jariran"

Cikin jin haushi ya juya tare da cewa.
"Hajiya meye matsalar ki dani ne? Matar nan dai tawa ce! Kuma yaran nawa ne! Toh dalla go gefe, kin hanani mintin zuciyata na hakura, amma banda wancan Yaran."

Rikota yayi suka shiga tare, an gama duba ni yaran ake gyarawa, Ni kam ina sauka barci yayi gaba dani, dan haka bazan ce ga tabbatacciya abinda na haifa ba.

.....
Zama yayi yana kallona, kamar zai cinye ni, murmushi yake kawai.

Har karfe goma,.yana zaune a gaban gadon, bayan a canza min d'aki ya koma gida, washi gari da asuba sai gashi baya fa ta yaran nice damuwar shi.

Ban farka ba sai karfe takwas, sannan aka hada min ruwan wanka, me zafi na shiga nayi wanka ina fitowa ya gama hada min abin karyawa, zama yayi yana kallo na.

Ina karyawa, a hankali yake min yan tambayoyi,tare da jin ko ina da Matsala nace a'a.

..... Bayan karfe biyar na yammacin ranar Lahadi aka sallame mu, muka dawo gidan, sai lokacin ya dauki yaran yayi musu hudu ba.

Hassanah sunan Hajiya ya saka mata, Hussainah kuma sunan Maman Mamie! Fatima da Aisha, Fatima wacce sunan Hajiya muna kiranta da Anum(Wato kyauta Allah) Hussainah Aisha muna kiranta da Anaum( Albarkan Ubangiji)

Duk da naso abarsu da sunayen su Sarinah taki amincewa, wai a'a sake musu suna.

.....
Tun kafin Suna, Uncle take hidima, daga Can garin kakanni na, an kawo sa! Da kuma raguna guda biyu, manyan. Sai kaji da zabi, tare da agwagwa. Nace wallahi bani cin agwagwa.

Tunda aka turo Mamie tazo taga yaran, kasa hakuri tayi cikin damuwa tace.
"Kuma kece kika haife su?"

Hajiya da Bakar magana tace.
"A'a tsinto su tayi a bolar asibiti."

Daga haka bata kuma magabata ba, ta fita amma har yau tana jin ciwona a ranta.

Ina zaune na saka tuwo miyar kuka, tuwon ma na dawa, sai tura baki nake Hajiya ta fita ta barni a dakin, Linah ta shigo.

Kallona tayi taga yadda na murmure, tsaki taja, sannan tace min.
"Akuya uwar Haihuwa! Toh ayi a hankali dai, kafin gaban ya gama zazzagowa. Dan namiji a yanzun mace yake bukata ba tarin haihuwa ba."

Dan haka kina nan yana can yana lashe ni."

Dariya nayi sannan na gyara zama na, nace mata.

"Eh ai nice na bashi hakurin ya lasheki dan girman Allah, kisan irinmu sweet 16-17! Dadin tsiya ne damu, dan haka karki damu kanki nice nace yayi maneji dake kafin na dawo."

"Ke har kin isa cewa ayi maneji dani"
Saka hannun nayi a bakina tare da nuna mata hanyar fita nace.
"Yarana suna barci, bana son koya musu hayaniya please out"

Kasa magana tayi tare da zuba min ido, ranta na kuma b'aci Ni banji kome ba, tana fita suka haɗu da hajiya.
"Bana son Fitina! Kar na kuma ganin ki a a nan, dan zan sabawa mijinki."

Hajiya ta gaya mata haka,

Ana gobe suna, ya shigo min da kayan fitar suna, har ya bani wata lace Wacce yayi mana, mu biyu da kafaya, sai shi kuma yayi shadda.
Dake ya bar Hajiya a falo zama yayi kusa dani, tare da saka hannun shi cikin rigana, yana shafa nonuwa na, yace.
"Ina kewarku sosai!"

Zare hannun shi nayi tare da sake murmushi nace.
"Kai Uncle! Kai da kake da mata."

Rufe min baƙi yayi sannan yace.
"Ko wacce da matsayinta da kuma kimarta, don Allah karki kuma min magana akan haka."

Gyada mishi kai nayi, muna cikin haka me lalle ta shigo ta fara min.

. .. bai kuma dawowa ba sai dare, zamu kwanta yazo yayi mana addu'a, bayan ya sumbaci goshina da na yaran shi.

Sannan ya tafi, ya sami Kafaya tana kuka, akan itama yayi mata cikin ta haihu dan tunda ya kawo mata kayan fitar suna. Suka yi rigima sosai.

Bai damu ba ya fita abin shi.
Washi gari.
Bayan ya dawo sallah asuba ya kirani yake gaya min zasu yi walima, na tambaya mishi Aunty Taslima da Sarinah sun gama abincin walimar ce.

Sarinah tazo, tun ranar da muka cika kwana uku, dan haka na fito, na tambayeta, tace eh bari ta kira shi.

Karfe sha daya, aka kawo min mai kwalliya, na zauna ta gyara min fuskana, tana gamawa, yana shigowa da me hoton, haka na dauko yaran masu matukar burgewa aka yi mana hoto dasu.

Shigowar Linah ya kirata akayi hotunan da ita, kasa boye b'acin rainta tayi Ni kuma nayi ta murmushi, ina son cin abinci amma ban samu ba, kawai na shige dakin dake gefen na Hajiya wanda aka sauke baki, na zauna zan fara ci, sai ga Ammih Amrah, naji ana ce musu ina dakin nan, da sauri na mike.

Tare da buɗe musu kofa na fada a jikinta, ina dariya sai kuma kuka.

Shigowa tayi tare da matar da ta taimake ni a daji, wato balarabiyar nan.

Abinci na fita na kawo musu dukda ba a gama na gidan ba, wanda akayi na walima na kawo musu, nayi ta jera musu a gaban su.

Kallona Ammih Amrah tayi, sannan tace.
"Sannun Babyn Uncle irin wannan kyan haƙa, ko Zuljah? Dubeta kamar bata haihu ba."

Murmushi nayi sannan na mike zan dauko musu yaran, Ita matar nan dai ta rike hannuna.
"Koma ki zauna! Murna yasa zaki fadi, baki san gidan nan cike yake da masu kokarin kin fadi ba?

Akwai wata da aka turota ta kawo miki kayan suna daga Mahaifiyarki, kada ki amsa, kuma karki sake ki bari akai d'akin, hmmm! Basu san da wacce suke tare ba. Maza kije karki saka kayan da mijinki ya kawo miki, domin an zuba miki wani abu akai idan kika saka zata iya maye gurbin ki a yi shagalin da ita. Jeki dauko yaran."
.jikina a mace na fito, na rasa yadda zanyi na gane matar da aka turo dan ta kawo min sharri.

"Yumnah! Sannun ga aikarki daga Hassanah, wai a kawowa takwarorinta."

Akwati guda, kallon matar tayi, ina jin muryan Umma Zuljah, tana cewa.
"Kice mata kin gode baki bukatar shi"

Girgiza kai na nayi sannan nace mata.
"Na gode! Ki mai da mata bana bukatar su a wadace nake!"

Daga haka nan Kuma kulata ba, nayi shigewa gurin su Mah Naz, na dauki Anum a kafad'ana, sannan na kuma cewa.
"Don Allah mah Naz, bani Anaum."

Haka na hada su, tare da barin d'akin, na nufi dakin su Ammih Amrah, na mika musu yaran, addu'a sosai Umma Zuljah tayi musu......
#Mai_Dambuje
?. Na kai musu yaran suka musu addu'a, karfe biyar suka bar gidan bayan sun gama gaya min abinda zan kiyayye, a bangare guda suka nuna min burgewa ta.

Yadda bana fitar da kishina, a fili. Kuma sun bani labarin kansu da irin halayyar mazajen su, kana da irin gwagwarmayar da suka sha a rayuwarsu, Musamman Ammih Amrah.

Bakar mace azurfa, kenan inji Umma Zuljah. Bayan tafiyar su muka cigaba da hidimar suna har dare.

..... Karfe goma, na fito wanka hannuna rike da towel karami Ina goge gashina da ya gwaguye, sabida wahalar da nasha lokacin da na b'ata, sam idan aka kutsa min ko dokin wuyana baya zuwa.

Samun su nayi da hajiya, ban san me suke tattaunawa ba, kawai dai ya bani umarnin na saka kayana, mufita zo falo.

Kallon shi nayi ya kauda kanshi, ba tare da wani damuwa ba na kitsan, sannan na fito falon.

Kawu na tare da matar shi da Aunty Hussainah, juyawa nayi zan koma cikin dakin, yace min.
"Karki kuskura ki koma cikin dakin nan"

"Ban san su bane, kuma kadda a basu yarana, dan ban san da wata manufar suka tawo gare ni ba!"
Na sa kai zan koma cikin dakin.
"Ban isa dake ba kenan? In na isa dake ki fito ku gaisa."

Wani irin kuka ne ya zo min, cikin bakin ciki, na dawo tare da jingina kaina da bango.

Ina shashekar kuka.
"Tun tasowa ta, babu wanda ya wanke kafar shi yazo inda nake, kullum bata goyan baya suke, basu damu da halin da nake ciki ba, zan rayu ko zan mutu, burin su a ɗauki abinda ba zai kare su da kome ba a basu.

Ni Ko oho, kawai yar uwansu suka sani, bani ba tunda nayi musu karan tsaye a rayuwar yar uwarsu.

Badan na sami mijin da yake yina ba, da bansan yadda makomata yake ba, zan iya samun farin ciki a gurin kowa, amma banda ahalin Mahaifiyata, suje bani son ganin su. Kawai suje, zumunci yayi rauni a zukatan mutane, kawo sai kana dashi zayi dakai.

Tun yarinta na, na fahimci ta Yar uwan su, suke bata ni ba, yau gashi sabida dalilin da babu hujja sun dibo jiki sun zo.

Taya zan fahimce su, bayan nima bawai fahimta na suka yi ba, kawai bana bukatar su.

Wanda suka dace na bukata suna can akko..don Allah suje ga hanya nan bani son Jin kome daga gare su."
Na kai aya cikin kuka da b'acin rai,
"Gaskiya Yumnatu ta faɗa a wannan zamanin zumunci yayi karanci a zukatan al'umma.

Idan baka dashi kare yafika daraja, yarinyar nan taga rayuwa da kun tsaya mata lokacin da take buƙatar ku, wallahi bazata dauki matakin kin jinin ku ba, amma daga ku har Hassanah kun sabunta rayuwarta da k'iyayyar ku. Allah ya kyauta."

Kasa magana suka yi, dukkan su jikin su a mace, badan kome ba sai iya gaskiya ce babu sharri a cikin sa.

Haka suka mike tare da mana sallama, tunda na koma daki nake kuka, ji nake kamar na bisu.
Bayan tafiyar su ya shigo min da yaran, ya samu na kwanta, ina sauke ajiyer zuciya.

Sauke numfashi yayi kafin ya fara magana.

"Bai dace ba abinda kika aikata fa, karki manta jininki ne! Sannan kuma."

A hankali na kira sunan shi, juyawa yayi yana kallona, sannan na fara magana a hankali. Tare da mishi misali, da shi kanshi.

Sannan nace mishi.
"Mu kwana lafiya!"

Wannan abin ya matukar kashe mishi jiki, sannan ya mike tare da barin dakin, nayi kuka sosai bayan tafiyar shi, domin na fahimci yana da saukakkiyar zuciya.

Shi mutum ne da zai yi wuya ka kama shi da kuskuren ba tare da ya baka damar gyarawa ba.

......
Tun zuwan su, kullum Kawuna yakan zo ganin yarana dani, yawan zuwan shi baya shigowa cikin gidan, a kofar gida yake tsayawa, ranar da na fita nace mishi.
"Kawu ka shigo mana! Ai babu dad'i tsayawa a wajen."

Murmushi yayi sannan yace.
"Yasu Hassanah suke, karki damu dani, jikokina nazo gani..kuma ina kara baki hakuri da wofantar da.."
."zuwa daya, zargi yanka darsu, na biyu kokwanto, na uku domin gyara kusakura ne, wallahi bani jin kome akanku ka shigo cikin gidan."

A hankali ya shigo cikin gidan, na shiga mishi hidima bayan sun gaisa da Hajiya na bashi yaran, ya kalle su, kuka naga yana yi sosai, tare da rungume si,.

"Kiyi hakuri! Allah zai miki sakayya, bazaki tab'a Fad'uwa ba, Insha Allah"
Ajiye min yaran yayi, sannan ya fita, bin bayan shi nayi.

Na same shi ya buga machine din shi zai tafi duk tasha duniya,
"Ki koma gida, kina jego!"

Haka na juya zuwa cikin gidan,

Tunda na zauna nake nazarin meye amfanin dukiyar da nake dasu indai bazai zama gayawa dangina na ba.

Sai dai ban san matsayin dukiyar bane, tunda bata halal aka dame su ba.

Dan haka na shi damuwa sosai, tare da tuninan yadda zan fadawa Uncle ɗan yanzun kunyar rayuwata ta Thailand nake.

....... Lokacin na tafiya, rayuwa na kuma mik'ewa, dan haka na sami Uncle da maganar, Kawuna.

Bai ce min kome ba, yace min idan na matsu abin na dawo d'akina, Ni kuwa ya bani Haushi naki magana, duk da kullum sai yazo ya lallube ni.

Domin Hajiya gyangyadi take abinta, kai ni zargin shi nake da saka mata wani abu a cikin abin shanta.

. Domin kuwa yana kawo mata furar admiral. Tasha daga nan kuma zai shigo yayi lalube ni sai ya rage zafi.

Idan ya kuma gida suyi ta faɗa da matar shi, karshe dake kunya yayi mata tashin gwaron zabi, ta kawo karan shi wai tun da ta dawo baya bata hakkin ta, karshe da tayi magana yace basir ya tsiro mishi.

Sannan kullum ya koma gidan sai yayi wanka, ita bata sani ba ko har nima ya gaya min yana da basir.

Kirana aka yi da niyyar tambaya, murmushi nayi ina kallon yadda yake gumi, cikin damuwa karara nace masu.

"Eh ya gaya min yana da basir, kuma yana zuwa gidan nan na dafa mishi maganin sai yasha yake tafiya, bayan nan ban san kome ba, idan aka duba halin da nake ciki na jego."

Ina lura dashi ya sauke wata B'oyayyen ajiyar zuciya, tare da min fuskar Tausayi.

"Munafuka! Wato ke har kin san dadin miji bari ki rufa mishi Asiri."
Juyawa nayi ga Mamie da take wannan maganar, na sake mata murmushi nace.
"Mamie! Halwani dai d'anki ne! Mu kuma bare ne, dan haka idan na yi abinda bai dace ba, har abada zaki ta kallona ne da haka, idan kuma nayi wanda ya dace bazan tab'a burgeki ba.

Matukar zan suturta mijina, bana bukatar taimakon kowa sai na Allah, dan haka shi suturana ne, Ni kuma garkuwar shi ce, Allah ya baki hakuri."

"Girma ya dai fadi, ace akan d'anka sai surukarka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login