Showing 114001 words to 117000 words out of 183750 words
hayakin kaikayi .
. kwanciya nayi akan cinyarta, ina sauke ajiyar zuciya,
"Ki zama jaruma! Mai tsayawa akan kafarta, ki zama mai iya sarrafa kome karki yawaita zama cikin b'acin rai domin lokacin ake samun galaba akanka.
..idan ranki ya ɓaci ki zama kin nemi Alkur'ani a kusada ke, Insha Allah babu shaidanun da suka isa cutar miki, amma wunin yau ko abin baki ci ba, Yumnah, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace.
"Karku tsannanta k'iyayya, karku tsannanta Soyayya! Sabida kowane yana iya juyawa zuwa daya bangaren, son da kikewa Halwani tana iya cutar da Lafiyar da rayuwarki, don Allah a sassautawa zuciyarki bata da laifi sai na so!"
Nasiha mai haɗe da fata tayi min, sannan tasani nayi alola, sannan na kwanta, ita kuma ta cigaba da addu'a, har lokacin barci yayi.
---
Kanshi a saman cinyar Hajiya, idanun shi a lumshe, damuwa ce kawai tayi mishi yawa. Kalaman Hardo ce take dawo mishi.
_Malam Amadu! Kayi hakuri kaje kayiwa mahaifiyarka biyayya, itama Yumnatu zamu bata wani cikin y'ay'an mu, idan kuma akwai abinda ka kashe mata ka gaya mana, zamu biya ka, ga wannan ka kaiwa mahaifiyarka, sannan ka gaya mata inji Ni nace mutunci madara ce!_
Jin kalaman yake kamar an buga mishi duguma, bude ido yayi kan yan uwanshi da suke zagaye dashi, ya tashi ya jingina da kujeran da Hajiya ke zaune.
Kallon su yayi sannan yace.
"Mamie ta lalata min rayuwa! Ta lalata min kome nawa! Hajiya anya Mamie ce ta haife ni?!"
Shiru yayi bai kuma magana ba, amma yana cikin damuwa sosai.
Cike da tausayin shi, mik'ewa yayi ya haura sama, inda dakin shi yake, ya tsaya.
Haka kawai, yake jin a ranshi ina ma da Omar yana raye, yau yayi rashin amini bai san akwai ranar da zai zubda kwalla akan mutuwar Omar ba, sai yau, kallon yadda sanyin hunturu ke kadawa, yake.
"Broh! Kayi hakuri, nasan Mamie zata aikata abinda yafi haka"
"Sarinah har naje na dawo banji muryanta ba....
Paid before read.....
Sai maganin Gyaran na mata zaku iya tuntubana ta wannan Number! Idan Baki shirya ba karki min magana! Da Manyan mata nake abu na 08130269641
ABU D'AYA.....muke so..
150 singul group! VIP 300 ta bank.Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga
200 singul grp! VIP 400 katin MTN..
Zaku iya tura shaidan biya ta wannan Number Zahran Addah Ramla +2347035133148 only Whatsp.
_ Idan kuma Alhubbih dayyia'n
Shima zaku iya biya ta Number! UmNass_
Acc No: 3051894647
Hajara Ahmad Hussain
Polaris Bank ga book din Alhubbi Dayyia'n zasu biya ta nan.... prize din iri daya ce, idan kuka biya ku tura shaidan ta gurin Zahrah+2347035133148
4️⃣3️⃣"Wallahi duk zaman da nayi da kwana ban saka Yumnah idanuna ba, ban san laifin da Mamie tai musu yakai haka ba sai da kakanta yake gaya min nayi hakuri nayiwa Mamie biyayya.
Daga nan na fahimci laifin mai girma ce, sai kudin da ya bani na bawa Mamie!, Tare da gaya min mutunci Madara ce!"
. kallon shi tayi na wani lokaci, kafin ta mai da idanunta, kasa ganin yadda Mamie ta shigo da farin ciki, tana tafiya tana murna, ta shiga babban falon gidan, da sauri ya juya tare da bari Sarinah,
Mamie na tsaye zata shige part dinsu, tana sauraron abinda Hajiya ke gaya mata.
"Me kika gayawa Iyayen Yumnah?"
Cikin rashin mutunci ta kalli Hajiya dakuma sauran mutanen da suke falon.
"Ce mata nayi indai iyayenta ba kwadayayyu bane, Kar ta aurar min d'a sannan dan na cireta daga rad'adi da zafin talauci na sayi soyayyar su da dubu dari biyu dan haka ina ga saura yar gidan Uwani itama haka zan mata gobe shegu kwadayayyun banza, kwadayayyun wofi."
"Garammmm!" Suka ji faduwar abu a bayan su, Sarinah tace.
"Yaya!!!" Da mugun karfi, kankace me gidan ya rufe, dole Rahbeel aka kira shi yazo ya duba shi tare da daura mishi ruwa.
"Hajiya don Allah kiyi wani abu! Wallahi damuwa tayiwa zuciyar shi yawa, shi yasa ya fadi jinin shi ya haura sosai,"
Shiru Hajiya tayi tana jin yadda kamen, har da wanda suke y'ay'an maza suna rokonta.
A jikin shi suka kwana. Kuma Hajiya ta haramtawa Mamie shigo mata Shashinta.
.washi gari.
Sammakon Hajiya tayi zuwa garin mu, ina kwance sabida zazzaɓin da yake damuna, ta shigo dakin.
Dakyar na tashi zaune ina gaishe,
Shafa kaina tayi tare da zuba min ido, kafin tace.
"Me yasa kika hana shi ganinki?!"
"Sabida iyaka tayi akan D'anta, kuma ta ambace ni da kwadayayya, ni da iyayena Hajiya it Uwa ce! Ni kuma matar da zai aura ce! Zai iya rabuwa dani, amma ita bazai rabu da ita ba. Kuma Hajiya ina ga kawai yayi hakuri inda gaske sona yake toh yayi min adalci, itace rokona dashi "
..abin gwanin tausayi duk yadda naso dakatar da kuka na, na kasa hayewa nake kawai, na kalli Hajiya da itama take kallona nace.
"Kin san Allah, Hajiya zan iya rayuwa dashi, amma bazan jure a wulakantani ko dangina akan shi ba! Duk da nasan bai da laifi ko daya amma ya san halin da mahaifiyar shi ta jefa shi ma rahama ce.
..hajiya ina son Uncle Halwani Sosai amma bazan iya daukar cin mutuncin ba, shi yasa na hakura da shi, tunda bashi ne autan maza ba"
Ina wannan maganar kuka nake sosai, itama shafa kaina take tana murmushi, sannan tace.
"Toh kiyi hakuri dan daraja na mana?!"
Kallonta nayi ina zubda wasu irin kwalla, sannan nace mata.
"Ki min adalci, a matsayin ki na kakar mu baki daya, yayi hakuri."
Mik'ewa tayi sannan tace "an miki adalci Insha Allah babu wanda zai kuma damunki da maganar halwani!"
Wani kukan ne ya taso min tana dariya tafito daga dakina da zata tafi aka kamo mata zazzaɓi da kaji, tare da Karyan man shanu, suka bata hakuri Baffa dan Azumi yace.
"Hajiya kuyi hakuri, Yumnatu yarinya ce. Kuma marainiya, bamu son muyi mata dole da zai saka tayi mana kallon dan ba mahaifinta bane, amma Insha Allah ni da Adam da kuma Jauro da harisu zamu lallabata, har ta amince,.idan kuma taki Allah ya gama kowa da rabon shi."
A haka tayi musu godiya sannan ta dawo gombe, ai kuwa yan koran Mamie suka shiga alakara tare da murnar an fasa auren shi da Yumnah, nan aka samu wata takira Kafaya ta gaya mata.
---
"Uwani kwaɗayin ki bai isa ki hakura ba, ai Kinga wacce tasan Darajar kanta da iyayen ta sun janye matakin aurawa dana kuma idan ba kwadayayyun ba, toh ahir din Yarki in ba haka ba zan wulakantata!"
Dariya Maman su Khuwailah ta saka gashi gidan an cika ana aikin biki. Kawayenta da Yan uwanta.
"Waye ya gaya miki ja da baya da rago yayi tsoro ne? Shirin aikata Alkhairi suke! Khuwailah da Yumnah kaman sun auri y'ay'anki kuwa.
Banda hauka da rashin kai, kina nan za a miki kishiya amma kina bin kan mutane da masifa, wallahi idan baki fita min daga gida ba zamu miki shegen duka."
"Ohooo! Yarki da ma ta gama karuwanci shine aka zo za a likawa yarona"
Fada sosai ya kaure, Khuwailah na Gidan gyaran jiki aka kirata aka gaya musu, babu shiri tazo taga yadda Mamie ke kora rashin mutunci, kiran Rahbeel tayi cikin damuwa da tashin hankali ya iso, yana shigowa yaga yadda ake dambarwa da Mamie.
"Kazo kayi waje da ita."
Takowa tayi gaban shi, tare da riko hannun shi har gaban Mamien. Wani irin takaici take ji, bakinta sai rawa yaƙe.
"Gashi nan! Ba dai Sharahbil bane? Ga d'anki nan! Amma yau bazaki bar gidan nan ba, sai ya biya ni matse ni da tsotse ni da yayi ko kuma wallahi na Bankad'a abinda baki sani ba akan Mah Naz da Mah Liqah."
Ta faɗa da mugun karfi sai da gidan ya dauka.
"Meye kika dauki Yaranki? Bugun aljanna ko? Mazan da suka fi dacewa da Y'ay'an masu kuɗi? Sune shafaffu da mai?"
"Hajiya kina abinda kika gadama, idan kin watsar da auren Yaranki toh ai bazaki iya watsar da na mijinki ba, Huwailah wuce daki, Allah ya kaso miki Manzon sauki Sharahbil, kuje babu kome Insha Allah biki yanzun haka fara, dan ta watsar da na Halwani sai take ganin zata iya wannan haukar.
Bata san cewa mu kaifi daya bane, Bama magana biyu. Zaki iya fita ranki shi dad'e Gimbiya"
Inji Baffa Nasir,
Cikin masifa ta juya gare shi zata fara yace mata.
"Wallahi yau ni na dakatar da Habu sake ki, Tunda yaji abinda kika yi akan Yar abokin Ahmad, Ni na hana ya sake ki, kuma kika Kuskura kika zage ni, tabbas wannan shine abinda zaki yi a tsakanin aurenku.
. Idan kina ganin karya ne, bismillah!"
Kwafa tayi tare da barin, gidan ita kuma Khuwailah ya tura aka kirata ita da Rahbeel, yayi musu nasiha tare da nuna musu bambanci halayyar shi da na sauran mutane wani bai tunzura shi ya fasa abinda yayi niyya, sannan suma sun je har garin su Yumnah, anyi magana da iyayenta sun fada musu gaskiya Mamie tace zata kashe Yumnah, kuma basu ga laifin su ba.
Dan sun san ita daya ce suka mallaka, tunda mahaifinta ita daya ya haifa, nasiha yayi musu mai shiga jiki.
Sannan ya bar gidan, dan dama matar shi Maman Sadeeq itace ta kira shi.
---
Kwanan Halwani biyu ya warware, basu sani ba ya dauki key mota daga shi sai kayan barci, sai garin mu.
Tunda yayi sallama, aka mishi iso zuwa dan wani daki a zauren gidan, ya zauna Hardo da kanshi ya shigo suka gaisa.
Sannan ya kalli Hardo.
"Nazo ne! Ka tausaya min,ka bani ita wallahi bazan tab'a zalintarta ba, kuma a duk lokacin da aka sami akasi, Insha Allah bazan juya mata baya ba, zan mata adalci iya karfina, Hardo bafa a gida daya zata zauna da Mahaifiyata ba, ba zata zauna a gida daya da kowa ba, daga ita sai ni, dan sonka da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka min adalci ka bani ita, don Allah."
Yadda yake rokon Hardon duk sai yaji jikin shi yayi masifar sanyi, ga kaunar shi da yake da Yumnah, ga kuma amintar shi da Umaru. Mik'ewa yayi sannan yace.
"Ka kawo kuka inda ya dace! Bari na turo maka ita."
Ina kwance duk na gama hakura da zan kuma ganin shi Hardo ya d'aga labulen yace min.
"Bingel! Ki Kai min ruwa dakin zaure."
Dan yasan idan yace na kai mishi bazan fita ba, zuwa dakin matar shi nayi na amshi ruwan na kai dakin da sallama na shiga kamshin turaren Chor.
Yayi min maraba da zuwa ban ganshi ba, amma tabbas turaren shi ne, rufe kofar da aka yi yasani juyawa da sauri.
Sake ruwan nayi cike da mmki, nake kallon shi.
Sai zare idanun nake, tab'e baki nayi tare da kauda kaina.
"Baby Yumnah! Gani a gabanki kafaffuna dukkan a kasa zan durkusa miki! Don Allah ki amince da ni bazan miki rashin adalci ba!"
Ganin zai zube a gabana na tare shi da cewa.
"Kayi hakuri karka durkusa min, kawai kaje kaiwa Mamie biyayya, bawai bana son kasancewa da kai bane, gani nayi akwai masu fushi da fushin wani akanka ne!
Ko ya-ya suka samu mafaka toh cutar dani zasu yi dan haka kaje kawai ka zauna da Yar Vice president daughter."
Takowa yayi gabana yana matsowa ina matsawa har muna isa bango, janyo ni yayi yana kallon cikin idanuna yace.
"Ki saurare ni mana! Kiyi hakuri kinji"
Kokarin kwace kaina na fara tare da ture shi, sannan na zabga mishi harara nace.
"Bana son karuwanci, kazo kana tab'a ni, dan nan gidan mutanen kirki ne ba Masu son kansu ba,
Basu da wata dogon buri sai na wanzan da farin ciki a tsakanin yaransu, dan haka ka tafi bana son ganinka, kaje bana son ka wai dole sai dani zaka rayu!
Idan babu kai ni zan iya rayuwa, kuma nayi au....."
Ajiyar zuciya n sauke, gani da kaunar kiss, dif na dauke wuta.
Rike rigarshi nayi, cikin wani irin kewar shi, har ina d'al-d'algal, ina kuma rike wuyar shi, Hadani da jikin bango yayi, ina tunawa da abinda Mamie ta gaya min na kwace kaina, tare da fasa mishi wasu irin bakaken magana, wanda tunda na fara idanun shi yake rufe, har Baba Sunusi da yazo juya, yana jinnu.
Ran shi ya b'aci shima, komawa yayi cikin gida ya tara iyayen shi yayi.
"A gaskiya bazan boye muku ba, sonda muke nunawa Yumnah tayi yawa! Karku manta shima namiji ne zai iya juya mata ya rama abinda tayi mishi. Kuma zuciya bazata ji dadi ba.
Sannan kuna tunanin dan uwar Amadu tace muku makwadaita sai ku ce bazaku bashi auren Yumnah ba, ai amfanin girma hankali yau da Umaru yana raye bazai fasa ba, sai dai ayi uwar da za ayi.
Dan haka aure babu fashi idan yaje ya turo mana dangin shi a fara shirin bikin."
Duk yadda soka so hana shi da nuna ai marainiya ce, nan yace musu munafuka ce, idan anyi auren zaku ga yadda karshen k'iyayyar zata koma, sannan tana hauka ne da zata ce sai yayi shadi.
Fada sosai, yayi kafin suka tsayar da magana.
"Kana tunanin zaka aure ne, a banza. Zaka same ni a banza. Toh idan kuwa kace haka ne kayi kuskuren ka nuna min mazantakarka ta hanyar shi ga shadi, idan ka tsallake nayi tunanin akan makomar ka dani!"
"Shadi fa?!" Ya tambaye ni,
"Bai maka bane? Ko baka ji abin bane da kyau na kuma mai maita maka, idan bazaka iya ba, jeka kuma koda an baka aurena wallahi bazan tab'a kallon ka a matsayin namiji ba, toh tsaya ina mazantar take, in da gaske kake dole ayi idan bai maka ba, You can go"
Daga haka nayi ficewata nabarshi a tsaye, fitowa yayi sallama da hardo yace ya turo iyayen shi, girgiza kai yayi sannan yace.
"Hardo a d'aga bikin zuwa nan da wani lokaci, Yumnah tace sai nayi wasar Shafi zata amince da mazantaka na,"
Zaro Ido Hardo yayi, tare da cewa.
"Amma yarinyar nan anyi yar banza, sai da ta gaya maka batun shadin nan toh wan Ubanta yace ba za ayi ba"
Dariya yayi sannan yace.
"Za ayi fa,"
Dan haka Ardo ya tura aka mishi Baffa sunusi suka yi magana da Uncle, Shima ya kafe zai yi ai shi yana cewa.
"Ai Nima Bafulatani ne! Kuma zai yi a daga bikin nan da bad'i sai ayi kafin nan na shiryawa shadin da kyau, amma don Allah a barnita yazo bikin Khuwailah."
Murmushi Ardo yayi sannan yace.
" Amma ya zaka yi da iyayen ka?!"
"Wannan ba matsalar su bane, tunda muka iya yin al'adar wasu dan niman aurensu, Na Yumnah ce bazan yi ba, ba shi take bukata ba, nayi kuma an gama"
Sosai yayi musu bayanin da suka gamsu, sannan yayi musu sallama,
tare da barin garin yana nazarin shadin da nace, har ya isa gida. Babban damuwar shi yadda iyayen shi zasu dauki batun musamman Mamie,
Koda ya isa bai gayawa kowa ba, Sai Baffa Nasir. Shi ya iya gayawa tare da nuna mishi bukatar ya gayawa mutane yadda zasu fahimta.
Dariya yayi sannan yace.
"Yarinya mai basira! Wato tunda ka iya auren bayarabiya, kayi al'adar su. Shine itama bari ayi anata. Toh zaka iya jure itacen da suke zubawa mutane? Da zafi fa."
Shafa kanshi yayi sannan ya mike tare da cewa.
"Karka damu Baffa! Indai kowa ya amince da shafin babu matsala zan iya jurewa har zuwa wannan lokacin.
Shi yasa nima nace a bar bikin dai shekara mai zuwa, kasan sabida me? Sabida yanzun bata san girman sonda take min ba, just 15 yar fa, kaga next year tana da 16yrs. Kuma nasan kafin zuwa wannan lokacin ta fara hankali
Zata iya yarda da ina sonta a yanzun kuwa idan aka yi zata dauka na damu da wani abu nata ne, shi yasa na yarda na amshi sharadinta, amma idan nayi biris zata kasance cikin damuwa, me yasa nayi tafiyana ashe ba sonta nake ba, tunda na tafi. Sannan har naso a barta tazo bikin Khuwailah amma fir yaki yace zata rasa kimarta."
"Mutanen sun san darajar kansu, suna da kokarin kare kansu basu son ka rena su, kuma sun iya amsar bakin su, dan haka na hakura shekara mai zuwa ayi kome a tsanake kafin nan hala Mamie ta nutsu."
Sun jima suna tattaunawa, kafin Yabar gidan yana jin wani irin farin ciki kamar an bashi Yumnah.
.......
Lokacin da