Showing 3001 words to 6000 words out of 183750 words
min! Omar, wallahi sai naga bayanka. Sam baka da dadi maza suna can suna shiryawa matan da suke tare dasu dad'i Ni kana nan kana kashe ni da rayuwata, Wayyo Allah na, Wallahi sai ka rabu dani ko na gudu da Yarinyata kuma ina gaya maka sai na cire cikin jikina, Azzalumin mutum! Ina dalili."
Allah sarki haka ya fito daga dakin jikin shi a sanyayye, ya koma dakin shi, ina falon ya wuce, yana wucewa itama ta fito da zani a kirji, ta rufe ni da duka. Ban san me yasa Mommy take huce haushinta a kaina ba, sai da tayi min likis sannan ta barni ina jan zuciya.
Fitowa yayi da sauri ya dauke ni zuwa dakin shi.
#Mai_Dambu
8/30
*_ABU D'AYA_*
(MUKE SO)
💝💝💝
https://my.w.tt/azBiusUko8
~*OK NA SAUYA SUNAN LABARIN DA Abu daya muke so! Sabida wasu marubutan sunyi ABOKIN ABBANAH*~
3️⃣
Shigar dani dakin yayi ya ajiye ni a bakin gado, sannan ya shiga ban daki ya haɗa min ruwan wanka, yana fitowa ya shiga cire min kayana.
Yana ƙoƙarin cire min Kanta dan hannuna daya ya kumbura, kawai sai ganin mutane muka yi akanmu, lokaci guda suka rufe Abba da duka.
Sosai kamar zasu kashe shi, karshe suka wuce side bed dinshi suka kwashe duk wani takardu masu muhimmanci wanda kusan na Uncle Halwani ne. Suka barshi a gurin.
Duk ihun da muke wai Mommy bata ji ba sai bayan tafiyar su tashigo dakin.
Tana zuwa ta rufe ni da duka, kamar bazata kyale ni ba, sannan ta jani tare da wurgani d'akina,
Tun daga ranar ban kuma ganin Abbana ba, sai wahalar da take bani, abinci kuwa sai lokacin da yayi mata zata bani.
Kasancewar shekaruna basu kai wanda zai na iya fahimtar halin da Abba yake ciki ba, amma ina yawan jin ihun shi. Tare da niman ceto.
A cikin kwanakin da Bazan ce ga su ba, naji muryan mutane a cikin gidan mu, dan ko kafin faruwa haka ina yawan jin Mommy tana waya da Hajiya Larai takan zo, ko Mommy taje.
A ranar da abin zai faru tashigo ta ajiye min wani abu kamar kadangaren, ta bude bakin shi ina gani ta tura mishi wani abu a bakin, sannan tayi wasu irin surutai kafin ta tasanya bakin zare ta rufe bakin shi rub, sannan ta lullebe shi da wani dan kwalin kayana, sannan ta fitar dashi, daga d'akin.
Washi gari naji alamun hayaniya da kuka, ina zaune a inda ta ajiye ni, sai da Hajiya Larai tazo ta fidda. Cikin dangin Abbana, na koma gefe ina kallon su.
Ina kallon aka fidda gawan Abbana, aka kai shi gidansa na gaskiya, dama haka ne duk abinda ka gani a duniyan nan ai rudin duniya ce.
Yan uwan Abba sun so kwarai na shiga jikin su baki kowa na koma daki nayi ta zaman kad'aici.
Ranar da Abba ya cika kwana biyu a ranar Uncle Halwani yazo, zuwa Aunty Hussaina, abokiyar haihuwar Mommy ta fita dani.
Ina hango shi, naja ajiyar zuciya. Da gudu na isa gare shi. Buɗe min hannun shi yayi, na fada kirjinshi sai a lokacin na sake kuka, wanda Bazan iya cewa na meye, rungume ni yayi yana me matse ni a jikinshi, a hankali ya zare ni a jikinshi.
Duk tambayar da yayi min bana iya amsa mishi sai dai na girgiza mishi kai, anyi anyi nayi magana, Amma babu baki.
Immediately Uncle ya dauke ni zuwa Asibiti.
Tsaki Mommy tayi a ranta tana cewa zakuma dawo, dan abubuwa abinda zasu iya mata.
Haka ya gama wayo dani sannan ya dawo dani.
---
Tunda Mommy taga Uncle ya dawo ya damu dani, bata bi ta kanmu ba.
Har akayi addu'ar bakwai, a lokacin Hajiyar Abba taso tafiya dani, Mommy ta rikice musu da kuka, idan aka tafi da Ni, cikin jikinta kawai ya rage mata zata ta gayyara, don Allah a barni zata kula damu.
Dangin Abba sun so ki, amma Uncle ya saka baki, dole suka hakura dani, amma suna jin a jikinsu babu Alkhairi a zamana da ita.
Bayan sati biyu da rasuwar Abba, dan Mommy taki sakin jikinta ta nuna she is getting better, Kawai she always says that Bata da lafiya.
Atleast dai sai da ta haifi babyn da bai kai month d'inshi ba. She suffer from dogon labour da tayi. Amma da ta tuna ta gama takaba, sai ta watsar da kome.
Bayan haihuwar ta ne, da kwana biyu. A ranar da ta cika kwana biyu ne naga Uncle ranshi ya b'aci sosai i did know what happen but naga ya bar gidan cikin damuwa, ina tsaye a window ina kallon shi, ya juyo ya yayi ya kalle ni sannan ya girgiza kai bai kuma jiyo ba.
Ya fita daga gidan, ina rike da karfen window, rankwashi na Mommy tayi ban san lokacin da na sake fitsari ba, ina me tsalle.
"Yar banza me mugun nufi, sai da kika min sanadin tsiya." Haka take ta dukana.
Wuya bata kisa, haka zaman mu ya kasance da Mommy Ina Cin Ubana sosai.
Ko wata biyu ba ayi da rasuwar Abbana ba, Mommy ta tsiro da wani irin hali na daban.
Bata zaman gida, haka zan wuni da yunwa wani lokacin na kwana, yan uwan Abbana sun zo dauka na taki basu ni.
A hankali rayuwar ta mike, idan ka gani sai ka dauka ban kai shekara tara zuwa goma ba, sabida karancin abin gina jiki.
Makaranta kan tun Abbana tun Abbana yana raye.
---
Tokyo...
Kwance yake, idanun shi lumshe karar alarm clock ne ya sanya shi bude idanun shi, kyakyawan idanun shi sauke akan Hoton Yumnah tana murmushi rungume da wani katon Teddy din Panda, yalwatattacen gashin kanta ya sha kitson kalaba, wanda aka jera mishi beat, tana murmushin ranar birth day ɗinta ne.
Kafa mata ido yayi, yana murmushi sannan ya tashi zaune. Wani murmushi yayi wanda dimple Point d'inshi da yake guri uku sai da suka lob'a.
Wata kumatun shi, sai wanda yake a habb'arshi. Lashe bakin shi yayi wanda suka kasance light pink, ziro kyakyawan leg din shi yayi kasa, tare da sanya room slipes. Fari tass.
Sai kayan jikin shi, suma farare tass suma masu tsantsi, kasancewar yadin silky ne, gaban rigar a buɗe take, dan bai sanya botirin rigar ba.
Ban daki ya shiga, ruwa ya tara a Jacuzzi, a hankali ya zuba turaren wanka, a hankali ya shiga cire kayan jikin shi, sannan ya shiga ruwan.
Giant body d'inshi ne ya bayana, wanda ya buɗe sakamakon d'aga karfe, ga dai yanayin shi, mai sanyi ne amma kana ganin shi kasan akwai alamun karfi a tare dashi.
Lumshe idanun shi yayi, can ya ware idanunsa akan kofar ban daki, b'ata fuskar shi yayi tare da tsare kofar da manyan idanun shi.
Knocking din kofar ban dakin akayi, ya sanya shi gyaran muryan shi yayi.
Wanka yayi sannan ya fito bayan ya wanke jikinshi, ya dauko bathtube d'inshi ya saka, tare da daura gashin kanshi da wata karamin towel.
Kamshin showel gel din da yayi wanka dashi ya cika ban dakin, har zuwa cikin bedroom dinshi.
A sanyayye yake tafiya, kamar ba namiji ba.
"Mr Halwani!"
A kaikace ya kalleta ba tare da yace mata kome ba, yaje gaban mirror yaja stool d'inshi, hand drie ya jona, ajiyewa yayi sannan ya warware towel d'inshi ya shiga busar da gashin kansh.
"Wai meye nufinki dani? Yau wata biyu da auren mu, amma ko...."
Kashe hand drie yayi, tare da mik'ewa ya wuce closet d'inshi ya danna yar tap din jikin kofar, buɗewa closet din yayi, ya shiga niman inner wear din shi, boxes d'inshi da singlet dinshi, a hankali ya fidda su tare da wata dark blue American suit.
Ciro su yayi a hankali ya ajiye su a saman india bed d'inshi, Wanda aka yi shi da zallar whiter woods.
Komawa yayi gaban mirror ya shiga shafa, lotion na Mai sanyin kamshi na kamfanin lux, kuma dama da showel gel din shi yayi wanka.
Roll on da body spray ya fesa, sannan ya shiga sanya kayanshi, d'ago kai yayi ya kalleta sannan yace.
"Please out!"
Ba musu ta fita, Binta yayi da ido tausayinta ne ya kama shi.
Zama yayi a bakin gadon tare da zuba tagumi yana nazarin abinda yake hanashi zaman lafiya da matar shi.
A yanzun wannan auren shi na biyar kenan, kuma duk case daya ne.
Hawayen bakin ciki ne ya sauko mishi, kallon hoton Yumnah yayi a hankali ya nemi b'acin ran shi yayi duk ya rasa su.
A sanyayye ya shirya tsaf, sannan ya sanya turaren pure oud wood ya saka wanda ya gauraya dakin da kamshin sa me dadin.
Sannan ya dauko wata takalmi ta kamfanin Channel, ya saka tare da Black sack, sai agogon shi na silver wanda kwalbar da ta rufe saman agogon ta kwalbar diamond ce, a hankali ya dauki yar karamar briefcase din shi, ya fito a sannu yake takawa, baka ce ya kai 46 years ba, har zai fita ya koma bakin side bed din shi, ya dauki yar memo da yayi yar Rubutu a jiki, ya cire shafin da yayi rubutun ya fito a hankali yana sauka daga step....
#Mai_Dambu...
8/3💞💞
*_ABU D'AYA_*
(MUKE SO)
💝💝💝
This page is for You Min Sayeed ne Noor! Uwar dakin Mommy da Hajiya Larai...😜
😍 Nabilah Hayatu special Greet to you! Ya za ayi da halin Mommy!🤣
https://my.w.tt/gVdJICUTp8
4️⃣
Sound's din Shoe din shi da yake bada wani taf-taf- har ya iso kasa, kallon dinning room din yayi tare da kawar da kan shi daga kallon dinning room din.
"Mr Halwani!"
Kallonta yayi bayan ya shigo tsakiyar falon gidan, wanda yake zagaye da wasu Italian fashion cushi.
"Please! Ka saurare ni! Idan bazaka mu rayu a igiya d'aya ba Why not ka sallame ni! Ga abinci can daga daga Sarinah!" Ta faɗa mishi,
Nufar Dinnig room din yayi, abin tausayi ita taja mishi kujeran, ya zauna bayan ya ajiye briefcase din shi, sannan ya gyara hannun rigarshi.
Da kanta tayi serving din shi, inda ta zuba mishi honey chick, tare da Chinese chips sai green tea Wanda ta zuba mishi apple honey, gefe guda kuma toast bread ne, da fry sauce egg.
Ta had'a mishi, a hankali ta ajiye mishi normal spoon da fork, sai tissue paper da ta ajiye mishi.
Duk sai yaji ba dad'i, b'cos tana hidima dashi ba tare da tasan halin da yake ciki ba, ko wanda zai jefata.
Takardan da ya fito da ita, wanda ba kome ne a cikin shi ba sai kalman saki, damke takardan yayi.
Ya fara cin abincin, yana kallon yadda take siyayya mishi orange juice Wanda ta d'iga mishi alvera, Hannun shi ya kai zai dauki cup din tariga shi dauka.
Sake mata yayi, a hankali ya ajiye mata takardan nan, sannan ya amshi ruwan ya kurba. Kafin ya mike da sauri. A sannu ya motsa da lips d'in shi yace.
"Am sorry Mayah!"
Daga haka ya saka kai ya fita a gidan, a hankali ta warware divorce paper din, abinda idanunta ya hango mata shine.
*Am sorry! Mayah Malik, na sake ki saki biyu*
Ahmad Halwani Nafada.
Hawaye ne ya zubo Mata daga idanunta, karar da yaji wayar ta yayi ne ya sanyata duba wayar.
Text message ne, tana dubawa taga abin mamaki, zuzzurutun kudin da ya turo mata, is too much wato dan karta zarge shi da son kai shine ya mata irin wannan sallamar
Dakin ta da yake sama tashi Allah ya gani dama auren biyayya ne, domin tana da wanda take so, aka sanyata auren Halwani.
Tattara kayan ta tayi, sannan ta kira Sarinah ta gaya mata, abinda ya faru.
---
"Mommy!!!" Kira nake mata amma bata ji ni ba, sabida rayuwar da ta zab'awa kanta,
Halin Mommy ya sabunta kanshi dan ta koma mara tsoron Allah,
Haka na gama ihu bata fito ba, sai da suka gama sab'awa Allah sannan ta fito, tazo ta zuba min duka a gadon baya kana ta tura min wani bushashen ruwan semo.
A yanzun da jikina ya saba da duka, ban ji kome ba burina na ci na koshi.
Haka nayita tura abincin, har na samu ya shiga cikina, murdawa cikina yayi, saboda yunwar da take cina,
Wani wahalallaliyar gatsa nayi, aikuwa ta buge min bakina, tana faɗin.
"Yar banza ne zuciyar mage! Sai na rabaki da duniya.". Komawa gefe nayi ina ajiyar zuciya, idan da sabo ai na saba da abinda take min.
Ni bana makarantan boko ba, Ni ba Arabic ba, gani nan zaune sai yadda tayi dani.
Wani matashin saurayi ne ya fito falon, sanye da gajeren wando, yazo ya kalle ni.
Tsoron shi ya sani, kame jikina ina sunkuyar da kaina.
"Baby! Har ka fito?!" Tace mishi,
Bai bata amsa ba ya tako inda nake, durkusawa yayi a gaba, ya shafa fuskana. Sannan yace.
"Yan mata! Ya sunan wannan abin?!"
Cikin jin haushi tace mishi.
"Baby! Meye na tambayana, Kawai ka shirya yau zamu je...."
A zafaffe ya juya mata, ita kanta sai da ta tsorata, mik'ewa yayi, sannan yace mata.
"Yarinyar tayi min? Da na ganta tun dazun da babu abinda zai shiga tsakani na dake.
Haka meye sunanta?! Nace ba wani shirme na tambaya ba."
"Baby Yumnah!"
Ta bashi amsa a takaice, tana b'ata rai.
D'ago ni yayi sannan ya zaunar dani a saman cinyar shi, duk na gama razana.
"Shekarunta nawa?!"
"But Baby?!"
Cikin tsawa ya dakatar da ita, shiru tayi tana zare idanu,
"Shekarunta?!"
"Goma da watanni!" Ta faɗa mishi kamar zata yi kuka.
"Hmm!"
Ƴace, sannan ya mik'e, ya ajiye ni tare da komawa d'akinta, d'aga hannunta tayi zata rufe ni da duka, daga dakin ya buga mata tsawa, dole ta ajiye hannun, yana fitowa ya kalleta, bayan ya saka wata sarka me hoton ƙatuwar kunama!
"Ki sani! ITACE sa'arki ! Matuƙar kika tunzura akanta kome naki lalacewa zai yi, duk da kinyi ƙoƙarin rufe bakinta, amma haka ba zai samu ba, dan zata yi magana wata ranar, sannan matukar kina son mu dai-daita ki ajiye k'iyayyar da kike mata.
Inba haka ba, zaki rasa abubuwa da yawa, dan akwai..."
Riko hannuna yayi muka fitar daga gidan, wata mota mai shegen kyau ya saka ni, muka fita daga gidan, wani gidan cin abinci ya kaini, yasa aka zuba min abinci, takura kaina nayi a gefe dakyar ya bani da hannun shi naci.
Rabona da cin abincin mai dadi har na manta, haka na dinga karb'a kamar mayunwancin dama da yunwar, sai da na koshi ya kaini gurin wanke kai aka wanke min kaina, ya fita tass kwarkwata da amodari duk ya fidda min su, samnan aka gyara min kan muka dawo gida.
Tunda ya shigo dani, gidan ya sanyata ta haɗa min ruwan wanka, kafin naje nayi da kaina, da na gama ina fitowa naga kayan da ya ware min nasaka.
Shigowar Uncle Amar ya sama min yanci, domin Mommy tana jin tsoron shi, sannan kuma da kanshi yake kaini makaranta.
Zanje na dawo ya kuma bani abinci.
Abin yana masifar mata ciwo, dan koda ya tafi Mexico sai da ya bar min masu kula da ni.
Dan haka bata da ikon takura min, domin akwai abinda ban sani ba, kawai zuwan Uncle Amar yasa ni, fahimtar daga Mommy har Hajiya Laraih suna masifar tsoron shi, bayan tafiyar Uncle Amar, mommy tayi samarika da yawa, wanda suna gani nan zasu ɗaukar wa kansu dawainiyyar kula dani, sabida farin jinin da Allah yayi min.
--
"Utta! Ka sanya baki Amar ya rabu da Yumnah, bana son Yana kulata Ni Inda hali ma a sanya mata bakin jini da kin