Showing 162001 words to 165000 words out of 183750 words
matsa ka bani guri na wuce!"
"Idan naki fa!"
Ya tambaye ta, tare da tsareta da ido.
Cikin sanyin murya tace.
"Rayuwar abin cikinta zaka Duba, don Allah mu kaita Yola daga nan ka cinye ni danye na amince."
"Hmmm!" Yace mata,
"Amma da Sadeeq ne ko wanin shi sai inda karfin shi ya ƙarfinka ya ƙare!"
"Abokin arziki ne! Itama bakin taimaka mata nayi ba, gani nayi kamar anfison yarinyar dani ne, tunda sabida ita kika yada zango anan dajin. Kuma Kinga mijinta na nimanta, amma kika hana shi."
"Toh idan ma na bashi ita bazata bishi ba dan shi baya ganin mu ita kuma tana ganin mu, kuma bazata tab'a bin shi ba, taya zamu bayyana mishi ba tare da ya razana ba, kaga muje kawai dan Ni ban cika son mita ba."
Ba tare da bata lokaci ba, ita ta gyara kayan jikin Yumnah, sannan ta dauketa suka bar dajin da ita.
....... Awa biyu, ya isar dasu forest din da yake bayan Mansion din Lamidon estate dake garin Yola domin jinyarta...
(Sorry na kawo muku Zuljah wa Imran!🤭)
#Mai_Dambujeeee
8/30/20, 9:42 PM - Ummi Tandama: ⁶?. Suna isa Sadeeq yana karasowa gurinsu, kallon Yumnah yayi da cikinta ya fito yace.
"Sati biyu da suka wuce naga sanarwan ana nimanta, tab'a wata biyar da suka wuce, a ina kuka samota?!"
"Toh gata nan Sharrin uwa yake bibiyar ta, dan haka sai ta zauna a hannun ka, muje ka haɗa mata magani, Kinga Zuljah taimaka ki dauketa, Dan Matar wani ce babu amfanin mu dauketa."
Haka kuwa aka yi, suka dauketa zuwa dakin Amrah, wacce taci kuka har idanunta sun kumbura, kallon Zuljah tayi cikin mamaki.
"Daga ina kuke?"
Shimfid'a Yumnah tayi , tare da bata labarin abinda yake faruwa, ta tausaya mata sosai.
Can suna tattaunawa, Sadeeq da Imran suka kawo maganin da za a fara mata amfani dashi, tare da zare zoben da ya matse hannunta sosai.
----
Yau ma kamar kullum, ya gama.
Mamie sun gama hada munafuncin su kenan, zata haura sama, kawai ta taka abu koda ta duba sai ta ga ƙayar kifine.
Tayi mamakin ganin shi a gurin dan haka ta cire, tare da hawa ta wanke kafarta tasa magani. Ta kuma cigaba da abinda yake gabanta tare da kiran Linah tana gaya mata yadda suka yi da matar Rahbeel.
Bayan sun gama, ta kwanta.
...... Cikin dare zogi ya ishe ta tun tana barci taji kafarta yayi mata nauyi, dan haka ta mike tare da yayye bargon, me zata gani kafarta ta gani kamar bokiti tsabar girman shi yayi bak'ikirin.
Ihu ta tsalla gashi ita daya a cikin daki, ihunta dije taji ta hauro sama da gudu, tana zuwa kawai taga kafar Uwar dakin ta.
Ai a cikin abinda bai fi minti biyar ba, ta fita zuwa shashin Hajiya ya gaya mata, sai gasu tare da Halwani.
A daren suka kaita asibiti.
Kamar mahaukaciya take surutun abinda zata aikata Khuwailah, tare da kara b'atar da Yumnah.
Haka ya rike kanshi yana kuka, tsabar wahalar da take sha, har fadan abinda ta shiryawa Safiyyah, tare da rabata da Papa..
.Mugun Abu iri iri, sai da tafallasa kanta, da duk irin qoqarin da tayi gurin lalatawa Yumnah suna.
. alluran barci Rahbeel yayi mata domin abin kunyar yayi yawa.
Tare da tashin hankali, har kunyar fita waje yayi a cikin asibitin.
.....washi gari aka duba kafar ta lalace, a cikin kwana ɗaya tal, dan dole suka shiga da ita aikin gaggawa, domin sun fahimci tana dauke da diabetic, babu yadda zasu yi idan basu cire kafar ba, haurawa ciwon zai yi dan haka Halwani ya saka hannun, aka yanke kafar.
Papa kan cewa yayi babu ruwan shi, ta karata can.
----
Ga baki daya yan kungiyar Utta dashi, aka wayi gari sun kama da wuta, a gurin tsafin su. Har da Ammar, Hajiya zakiya ce ta sha bayan tayi ta tonawa kanta asiri. Haka akaita bugawa a jarida, dan haka da Uncle ya sayi daya.
Yaje har inda Mommy take ya wurga mata ya fita abinshi.
----
Bayan wata uku..
Lafiya na samu, sosai duk wanda yaga Yumnah zai sha mamakin yadda ta koma, sai dai bata magana, kuma koda ka tambaye ta daga ina tafito sai kuka.
"Yan mata! Zo mu shiga kitchen, kafin Abbi ya dawo." Inji Amrah.
A hankali ta mike sabida nauyin da cikin ta yayi, tunda suka shiga aka fara girkin.
"Kin gama makaranta ne?!"
Idanun tane ya cika da kwalla, ta girgiza kai.
"Toh me yasa?"
Kuka ne ya kwace mata, tana son magana amma babu bakin magana, dan haka ta kai hannunta gemunta, tare nuna alamar namiji tayi, sannan ta kuma sanya hannunta a kirjinta, alamun nono, ta kuma made hannun ta kama juya shi kamar me renon yaro, sannan ta fara bata labarin abinda ya faru..
Hatta kaita thailand da dawo da ita da Halwani yayi.
Kuka sosai Amrah take, dan tausaya mata, sannan take gaya mata, ita bayi sa'ar Uwa ba, sabida ta tsaneta, bata sonta rayuwarta take bukata.
Sannan ta kuma ce ta rabata da mijinta, yana sonta sosai. Ta kulla hannunta sannan tayi mata alama zuciya, tace.
Duk ya mallaka mata, zuciyarshi. Kuma baya fushi da duk abinda tayi, dan haka don Allah su maida ita gida ta haihu...
Don Allah karsu bari ta haihu basa tare alkawarin da yayi mata kenan.
Shigowa yayi cikin Kitchen din, ƴace.
"Wato kina son komawa wajen mijinki ko?! Bayan naga shi din tsoho ne!"
Girgiza kai tayi tare da raba hannunta tace. A'a da hannunta biyu, sannan ta zagaye fuskarta da tafin hannunta, alamun mijinta kyakyawan ne.
Tana murmushi, ta kuma ce mishi, yana da kirki, sannan yafi shi tsayi, wato Uncle Yafi Sadeeq..sannan yana da karfi alamar yana da kirar jiki me kyau.
Sannan baya da fada, yana da hakuri. Shi indai ba da ita bace baya magana don Allah su maida ita gurin shi, yana can a dame.
"Shi kenan! Zamu kai ki gobe Insha Allah, dama sabida lafiyarki muka barki tukun yanzu kan Insha Allah ba Mutum ba aljani ba bazai iya miki kome ba, kai hanyar da kika bi bazai bi ba."
Wani irin farin ciki ne, ya kamata sai godiya take musu, saboda zasu maida ta gurin Uncle..
----
Lokacin da Mamie ta farka, ta sami kanta a wani daki ne yaran zagaye da ita, zogin da take ji ne. Yasata tambayar su tayi tare.
"Me yasa mi kafata? Taya haka ya faru dani?"
Dakyar Uncle ya bata labarin, abinda ya faru aikuwa ta tsalla ihu, tare da suma.
Tun daga lokacin ta zama kamar mahaukaciya, haka suketa lallabata, har aka sallame ta. Banda Halwani babu me zama ya kula da ita, cikin kwanciyar hankali.
.....
Yana zaune na Office d'inshi nan, cikin gidan shi, aka mishi sallama yayi baki, cewa yayi a shigo dasu, falon baki, haka aka kai su can.
Kamar bazai fita ba, ya daure ya fita. Yana isa ya hango matashin mai kudin nan na yola, cikin mamaki ya isa da sallama ya mika mishi hannu suka gaisa, daga nan suka fara tab'a hira yace.
"Mr Sadeeq Lamido Sadeeq, yau kai ne a gidana? Gashi gidan babu kowa sai ni bari na kawo maka ruwa, sannan Madam"
"Haba barshi kawai yanzun zamu koma, mun zo maka jajje ne, kuma toh bamu san yadda zaka dauki abin ba, duk da cewa.
Ba wani abu bane, amma mun kawo maka wata mata ce, ko itace wacce kake nima."
Fita Amrah tayi ta shigo da Yumnah, tana. Shigowa ya mike jikin shi na keerrma, yace.
"Don Allah, ki daina min gizo. Tunda baki kusada dani"
Bakinta na rawa, gashi dakyar take daya kafa, tace.
"Uncle! Nice Baby Yumnah."
A hankali ya karasa gareta, tare da bude mata hannu, ta shiga, duk da cikin ya tokare shi.
Juyawa yayi cikin juriya yace.
"Na gode kun dawo min da farin cikina, ban san me zan iya biyan ku dashi ba, amma ina muka fatan Alkhairi."
"Auuuwu dama kina magana kika mana shiru?!"
"A'a Ammih, ina ganin shi maganar yazo min"
Na karshe cikin Kuka, rike ni Uncle yayi sannan yace.
"Toh muje family house din mu, sai ku samu ganawa da iyaye na!"
Dukkan mu, muka nufi can gidan Hajiya, Ni da Uncle muka shiga gidan, duk wanda ya ganni sai ya shige gidan, kafin mu shiga kowa ya fito.
Ihu da murna kawai ake, sannan da aka nutsu, suka bada labarin abinda ya faru, sannan Ni kuma aka juya kaina.
Akan na basu labarin abinda ya faru, share kwalla nayi sannan na fara da cewa.
"Lokacin da na fita daga dakin Hajiya, ina kuka. Kamar zan dauki Annur sai na fasa, kawai na tafi Ni daya na, ina zuwa garden din sai naga zoben da Uncle ya hanani dauka, tunda na ganshi naji ina son zoben, Ina ganin shi kawai na dauka.
Tunda na saka a hannuna, naji kamar ana juya min duniyar baki daya, tare da kwala min kira .
Tunda na fadi a gurin ban kuma fahimtar inda nake ba, kawai na farka ne sakamakon tsawar da aka daka min, naji ana jan zoben da hannuna.
Tunda na fara tafiya bana cin kome sai ya'yan itace, shima wurgo min ake naci, sai ruwa shima kawai ina fara jin ƙishirwa, za akawo min shi bakina a zuba min sannan a ture ni!!!"
Shiru nayi,.kafin ma kuma fashewa da kuka, ina gaya musu irin wahalar da nasha, tare da tafiyar da nayi har yanzun kafafuna suna nan da ciwon da k'aya yaji min,"
Mik'ewa Uncle, ya fita can ya dawo, sannan yazo na cigaba da basu labarin irin bakar wahalar da nasha, da tafiyar da nake, ga laulayi, kuma kome dare kome rana haka zan ta tafiya,, bana barci bana ina kwanciya.
Har Addu'a nake Allah yasa na mutu da bakar fitina da nake fuskanta, babu ranan da baza a min tsawa ba, kuma bana ganin me min tsawa, Uncle! Uncle!! Uncle!!!, Don Allah ka boye ni yadda babu wanda zai kuma.
Cutar dani, kaji Uncle na gaji idan haka ya cigaba da faru mutuwa zanyi."
Rike min hannu yayi cikin nashi, yace.
"Kina tare dani babu wanda zai kuma cutar dake Insha Allah."
Sosai kowa suka tausaya min, aka yita min jajje, dasu Ammih zasu tafi muka rakasu tare da musu godiya.
Bayan tafiyar sune, Hajiya tace min na wuce, na wuce d'akinta.
Shi Uncle Yana tsammanin zamu tafi ne.
"Hajiya ya haka?! Ni da zamu tafi tayi jinyar jikinta, kafin ta haihu."
"Ai toh ai baka gaya min bane, amma tunda ka gaya min jeka Allah baya bamu Alkhairi, kuma zan kula maka da ita kamar yadda kake so."
"Hajiya ni fa da Matana zan tafi, inje na!"
"Kaje ka Zunguro mata Haihuwa ko? Ba dani ba jeka idan ta haihu tayi arba'in kazo ka ɗauke ta."
.cikin jin haushi yace.
"Wallahi babu inda zani, kawai Malama ki bani matana na tafi da ita?"
"Toh wallahi ko uwaka baka bata isa ba, balle Ubanka kafita ka bani guri ko na sab'a maka, sakarai Kawai"
Rigima ta barke tsakanin Uncle da Hajiya, ta bashi ni taki shima kuma yaki fita yana masifa, karshe yayi zuciya da ta bashi haushi, ya bar gidan.
Tunda ya fita, ta kira Rahbeel tace ya rubuta min abinda zai kara min kuzari da karfin jikina.
---
Kulawar da ake bani babu iyaka, gashi har yau saukar Alqur'ani ake da yanka, tare da sadaka maganin masifa.
Sosai abin ya tasirantu, domin Mommy kome na aikinta ya lalace, dole ta fara nazarin abinda zata yi na gaba.
Dangin Uncle, sun shiga alamarina sosai, domin ganin yadda cikin jikina yake kara girma yana kara sanya su murnan ko yan biyu ne.
Dan haka suka sa Uncle ya kaini aka duba cikin aka ce daya ne, amma basu fidda tsammanin ba, kawai kulawa ake bani.
...... Wata na biyu da dawowa, Mahaifin linah ya kawota da kanshi tare da niman maida auren Uncle da Linah, ban san ya suka kare ba, amma naji wai an maida auren su, dan Uncle ya kasa nuna musu baya yinta, zama nayi na fashe da kuka.....🙆🏻♀️? Don Allah yaushe Chakwakiyya zata kare ☹️😒
#Mai_Dambu
"sannun sakarya! Nuna mata kina kishinta, ta samu abin yakarki dashi,.nunawa zaki yi baki damu da yinta ba.
Yumnah! Koda wasa karnaji kar na gani kuka akan kishiyarki ta dawo, toh bari kiji wannan karon anan cikin mu zaku gwabza, kowacce ta kwaci kanta, har zaki mata kuka yaushe aka haifeta?
Kul na kuma ganin hawayenki masu tsada da daraja sun sauka, ki samu ki dire wannan cikin shine fatana bawai ki zauna kina bare bakin ki ba."
Haka na daure bawai dan bana jin yin kukan bane, kawai daurewa nayi, har washi gari ban ganshi ba.
Sai wajen karfe biyu suka shigo da Rahbeel, sau daya na kalle shi, tsabar kishi kawai naga kamar har wani haske ya kara, ban kuma d'agowa bai kaina na kasa ina wasa da cokalin da nake cin taliyar gargajiya.
Zama yayi tare da saka hannun shi, ture hannun nayi. Tare da sauke wani irin kwalla me zafi.
D'ago haɓɓana yayi, tare da sake bakin shi.
"Toh meye na kuka, Kinga fuskarki ya muna min alamun jiya baki yi barci yadda ya dace ba, karki manta jininki yana sauka fa!"
"Toh ina ruwanka dani! Kaje can me sabon Pussy kun kwana kuna cin kanku like a food."
Murmushi yayi yana kuma kallon bakina da suke rawa, kamar wanda aka cillani cikin ruwan sanyi.
....niman hada fuskana da nashi yayi, na buge hannun shi. Ina zubda kwalla.
"Please ka kyaleni mana, ko na kira maka Hajiya ne!"
Kwaikwayon muryana yayi, yana dariya.
..."Kinga bana son wannan rikicin, tunda bawai nayi miki wani abu bane, kawai abinda na sani, zan yi adalci a tsakanin ku, and Bana son damuwa please, Yaushe kika koyi zafaffa kishinki ne? A sanina baki da zafin kishi koda kina dashi kina da kokarin dauke kanki, don Allah ki tafi a yadda na miki shaidan karki karkata wani hanya na daban.
Idan wani abu ya same ki bazan yafewa kaina ba, sabida na sanya ki a damuwa, sannan dube cikin nan naki, me yasa? Don Allah kike daura damuwarki da yawa, ki rufa min asiri ki sauka lafiya."
Wata uwar harara na mishi,.tare da kauda kaina, hannun shi naji yana shafa cinya ta nayi maza na buge tare da b'ata rai.
.dan dole ya kyale ni ya murmushi, ga baki daya naji ya bani haushi, haka ya gama zaman shi har zai fita yace.
"Toh ba ga irinta ba, da kin san kina kishina Hajiya ta kwace min ke! Gashi min zo kina jin haushina, kawai yan mata. Taso mu tafi."
Sunkuyar da kaina nayi ban iya d'agowa ba, sabida ina jin zafin shi, banda shirme irin nawa gani nake kafin na haihu na koma, ta shanye duk wani dadin..
... babban burina shine na sauke nauyin da ya addabi rayuwata, wato cikin nan dai, gashi naga alamun ba zai yiwu na dauke shi ba.
Dan na wuce watanni Haihuwar ma da yan kwanaki,
Ranar wata asabar, da safe na tashi da ciwon nakuda, tun ina b'oyewa Hajiya har ta kai karfina ya fara kasa haihuwa bai zo ba, dan dole na gaya mata halin da nake ciki, babu bata lokaci ta kira Uncle, da kanshi ya iso. Muka nufi asibiti.
Tun karshe tara na safe, muke asibitin, har karfe biyar na Yamma, kawai Rahbeel ya kawo takarda wai Uncle ya saka hannu a shiga dani aiki.
Idanun shi ne ya cika da kwalla yace.
"Zata iya!