Showing 147001 words to 150000 words out of 183750 words

Chapter 50 - ABU DAYA (Muke So)

29 Oct 2024

10689

kuma sai na kashe shi.

"Mommy! Ki bani D'ana, don Allah karki cutar min dashi, shine gata na."

Dariya ta saka mai mugun cika kunne, kuka na saka tare da ce mata.
"Ki bani d'ana don Allah ki bani d'ana"

A zahiri kuwa, ina yunkurin farkawa, sai su ga na kuma rufe idanuna, ina ƙoƙarin d'aga hannuna sama, bakina na motsi.

Sai na maida, dole tasa hajiya zuwa kaina ta fara tofa min Addu'a, kafin na farka cikin ikon Allah.
.dukda idanuna basu gama washewa ba, amma ina ganin yadda Mommy take cilla min Yarona sama, tare da walagigi dashi. Sai kuka yake, sai na yunkuri zan tashi a mai dani, suke sai su dauka ko zanyi irin abinda masu sarkewar Hakori suke ne.

Wani ranar halin da nake ciki kenan, har sai da d'am uwan Hajiya yazo a lokacin ne ya shiga karanto min wasu addu'o'in, tare da almajiran shi, a hankali na buɗe ido na. Nace,
"Hajiya! Abinda na haifa zata kashe min."

Shake wuyana Tayi, tana huci, tare da fadin "ke har kin isa, ki gayawa mutane zan kashe miki d'an?!"

Buɗe hannunta nayi,.cikin ihu da akaraje, tayo kaina.
"Wai Mommy! Meye nayi miki ne? Meye na tare miki ne?

Ga baki daya kin hana rayuwata sukuni meye kike so! Wallahi ko mutuwa nayi Halwani ya haramta miki, balle kuma ina raye. Muguwar mata kawai, wacce babu nufin Alkhairi a zuciyar ta,"

Cikin jin haushi tayo kaina, dan dole ta juya sabida karfin addu'o'in da suke min, tace min.
"Zamu hadu! Baki sha ba."

Tana b'acewa ina bude idanuna, sannu suke min. Ina binsu da ido kawai dan ban san me zan ce musu.

.... Har wani washi garin ina jin ciwon wuyana, dan abinda aka bani nasha Bai taka kara ya karya ba, kamar nayi kuka haka nake ji.

Tunda na farka, naga sauyin kaddarata, wani irin kulawa ake nuna min me cike da tsantsar soyayya da kauna, ko ya nayi motsi zasu tambaye ni ina ke min ciwo? Meye nake so.

.. .har kiran Sarinah aka yi ana ce mata.
"Ga Maman Baby Boy! Ya Kika ga mulki, sai ma Kinga yaron, wow yadda kika san Bro"

Ire-iren waɗannan abubuwan ya sanyani jin tsoron Allah a lokaci guda ya shige ni.

Cikin Abinda bai fi kwana biyu ba, ya sanya masu tsanata zuwa kaunata, tare da wani irin mutuntawa, kullum za a zo a matsi nonona, a saka a cikin wani abu mai rike zafi akai mishi.
Ina zaune Mamie tazo da kawayenta, tana gabatar dani. A matsayin D'anta da ta haifa mata cutie baby boy, nan kuwa suka min fatan Alkhairi da kuma kyauta aka sanya nurse ta dauko musu babyn dake Hajiya bata nan.

Haka suka gama binshi da Wow babu masha Allah Barakallah. Ni kuwa da zasu tafi nace musu.
"Ku bani d'ana nayi mishi Addu'ar da Manzon Allah ya bamu, gudun mugun baki, mugun idanu, da mugayen mutane da aljanun, dan a yanzun yafi bukatar addu'a na"

.ba musu daya matar ta mike min shi, bayan na rungume shi a kirjina na kalli Mamie.
"Zaki iya yin daya ki fada rijiya, amma bazaki taba tsalle dubu ki fito ba, daga yau karki kuma sanya kazamar hannunki akan Yarona, d'a bai fi d'a ba. Haka uwa bata fi Uwa ba, ki rike Halwani na Iri Annur!"

Na gaya mata haka, a fusace.
Cikin takaici ta juya, saka hannuna daya nayi a bakina, tare da ce mata.
"Shiiiiii! Keep quiet and get out, Annur Yarona ne! Ko kin manta Halwani yace na nima mishi Ubanshi, ra'is Bai isa ya min cikin D'an so ba, amma ban sani ba ko inda Anyi gwajin jini, Hajiya Basirah kar na kuma ganin ki anan idan ba haka ba.

Wallahi bindigata da take cike da harshashi, zan zuba miki a goshinki, kuma bazan ji kome ba, tunda abu daya muke so"

Mata najin batun mutuwa, bayan fitar su Hajiya ta zo ta ganni da yaron shine take tambayana taya yazo, dariya nayi cike da jin kunyar ta.

Ajiye shi nayi na sauka a hankali sai da na shiga ban daki na fito, sannan na gaya mata yadda aka yi yazo, shiru taya, a ranta tana cewa.
_Za ayi tsiya kuwa dan nasan Yumnah ba bar miki D'anta zata yi ba, tunda Tasan ba sonta kike ba_

Satina biyu aka sallame ni, har da Yaron, yanzun matsalata yadda zan gano meke faruwa, zoben hannuna na juya ina kallon shi, duk wani kulawar da ake bani, bai hana ni jin ina da mijina yana nan ne.

Anyi walima, inda yaro yaci Sunan Abbana, dan suna zuwa aka fara min alaye wai Mamie tace a sanya mata sunan Babanta Takwarata Rahbeel.

Dariya nayi, sannan nace mishi.
"Wai Ai sunan shi Umar Faruq! Dan tuni na mishi huduba! Idan yayi musu Akira shi Annur! Idan bai yi ba, zaku iya barin shi da Faruq ko Umar, sannan ka haɗa min duk wani abinda ka sani akan mijina, idan ba haka ba.

Ba zan iya dakatar da zafin da nake ji ba, akan shi."

Sake baki yayi yana kallon yadda na ke gaya mishi magana kai tsaye, babu wani jin kunya, ina ruwa na da kunya, waye shi da zan tausassa mishi harshe, tab! Duk wanda yayi min abu ina da ciki sai na rama.

Bayan kwana biyu, kawai Mamie ta tsiro iskanci, sai a turo a karbi yaron, ya wuni can a barni da ciwon nono, koda na tura ko naje da kaina bazata bude min kofa ba.

Ran Hajiya ya b'aci dan nonona sun kumbura sosai har sun samun zazzaɓi, taje ta sami Papa da yaranta tayi musu, rashin mutunci tare da musu barazanar zata kwashe musu albasa mai lawashi, dake suna gudun b'acin ranta, nan aka je gurin Mamie ta bada yaron, tace bazata bada ba.

Tun da take bata tab'a ganin fushin Hajiya ba, tace mata..
"Ki rike Yaron!"
Sannan ta ja hannuna zuwa gidan.
Sannan ta rufe gidan, akayi juyin duniyar nan Hajiya ta bude gidan taki, ga yaron shima kamar ya san ana rigima, sai kuka yake.

Tun karfe uku ake abu guda har tara na dare, nima tun da na shiga daki nake kuka, sabida bango dalilin da Hajiya zata kafe ba, tunda yaron yayi kuka har yayi shiru.

Ga nonuwana sun cika, har yana tsirtuwa...
Sai da suka je can wani gida a karshen Layin suka dauko wani dattijo,ashe abokin kakansu Uncle ne.

Shi yazo yayi mata magana tare da niman alfarma, akan tayi hakuri haka ba zai kuma faru ba.
Shine dake tana jin kunyar shi ta bude ta amshi yaron.

Tun da amshe shi, ta kuma kafa dokar, kar wani ya kuma zuwa ya amshi yaron, ina kwancen. Ta kawo min yaron.

Zama tayi a bakin gadon, tana murmushi tace.
"Ina da son kai ko? Gashi abinda nayi badan kai na bane, dan kece. Ai nasan da na amshi yaron, gobe Insha Allah zata kuma amsar yaron bazata dawo dashi ba, kuma daga haka zata rabaki da shi.

A duk lokacin da zamu yi abu, mukan iya manta da son ran mu, da abinda muke jin tausayin shi, sai mu boye soyayyar mu da.
Mukewa abu dan haka sai mu saka toka a idanun mu dan cimma wata manufar mu.

Kiyi hakuri! A matsayin ki na uwa na d'aga miki hankali, na kuma sanyaki damuwa, ki yi hakuri domin ke da d'anki nayi haka, banyi dan son raina ba. Abin zai miki yawa, taya za a nisanta ki da Ubanshi kuma a kuma nisanta ki dashi, babu adalci."

Daga cikin maganar ta, na fahimci cewa, tana matuƙar kewar Jikarta, sosai tare da matukar bukatar ganin shi.

Kasa magana nayi, nayi shiru ina nazarin abinda yake faruwa, tabbas akwai matsala, toh waye zai gaya min halin da yake ciki.

....
A hankali rayuwa take Gara mana, rashin mutunci kuwa Hajiya da Aunty Safiya da Taslima nake ragawa, har Khuwailah, bana kyaleta. Yarona kuwa yana samun kulawa, kuma babu wanda ya isa takani na kyale shi.

Muna cika wata shida, na shiga hada mishi abincin Ni kuma na fara bindidigin Linah, duk wata motsinta tare da taimakon Zein da Jim, mijin Sheena.

..... Karshe Annur yana cika wata tara na cire shi a nono, tare da barin gidan, dare daya ba tare da na ce wani abu ba.

---
Thailand na nufa, inda na sami Jacob, Dan nasan babu yadda za ayi bai san wani abu ba.

Ƙamar Yadda nayi tunani, amma yaki gaya min, dole sai da muka isa gurin. Lucefe, shugaban Panda, shi yake gaya min abinda ya faru, sannan an san na shigo Thailand fita na shine tashin hankali.

"Zan fita kamar yadda, kake tunanin bazan fita ba, kawai mijina zaka gaya min inda yake." Na gaya mishi.

Jakar da nazo dashi na wurga mishi.
"Mijina kawai nake son sanin inda yake"

Tashi yayi sannan ya zauna kafin yace min.
"Lokacin da aka kawo ki! Wasu mata biyu sun zo, daya tace ita ce Mahaifiyarki! Sai daya tace mijinta shine zai aure ki, dan haka suke so a badda ke.

Bayan nan sun zuba kudi sabida sun nuna min akan abu daya suke so! Kuma hankalin shi yana kanki! Sannan bayan yazo ya dauke ki, an bashi wani aiki wanda matar shi da Thomas drugs Suka kashe wani da yake Office din mijinki sabida ya shiga zargin da dole zaki rabu dashi, duk abinda a ke sabida ke ce! Sun kuma sanya kowa na jikin shi ya ajiye aikin da yake ne, sabida a kuntatta musu.

Abu daya ake nima a hannun mijinki, shine wasu bayanai da ya dauka lokacin zuwan shi. Saudiyya bayan aurenku, ya dauki bayanin daya daga cikin crown prince! Zein Asood. Har da shi a cikin masu farautar mijinki, sabida ke! Dan haka ki bar garin nan dan zasu iya kashe ki, dan duk abinda suke dan ki bada laptop din nan ne. Sannan Mahaifiyarshi tasan kome."

Sake baki nayi hawaye na zuba daga idanuna, na kasa fahimtar kome a cikin duniyar nan.
"Toh meye Zein din yake aikatawa?!"

"Yana cikin masu taimakawa kungiyar ta'adanci da suke yaki. Babban dan ta'adda ne, mijinki bai san da haka ba, burin shi idan ya aure ki zai ajiye kome! Sabida ke, sai gashi an shigo mishi da Dilshad, kuma sabida a hanaki sukuni ne, mijinki yanzun haka yana Syria, anan suke ajiye dashi, lokacin da jami'an tsaro suka zo niman laptop din, da kin basu zasu kashe miki mijine!

Kiyi nazarin Yadda zaki fidda shi. Amma dole kije da kanki. Aikin mijinki yana da hadiri, matsalar sabida Abu daya kuke so shi yasa abinda za a miki shi ya amshi hukuncin."

Juyawa nayi tare da barin gurin, dan sannan shima ba tsira yayi ba....
Inda ake fita da mata......don Allah kuyi hakuri! Kunsan karshen sati 🤔 🙄 dan abu kadan za a fara mita....
#Mai_Dambu...
?. Ta barauniyar hanyan da zai fitar dani, tsibirin lankabi muka fito, daga nan muka fito Ma,laysia.

Kwana na biyu, a cikin kasar, na samu jirgin da zai kaini ƙasar Qatar, na isa da dare. Kuma nasan Zein yana sane da haka, washi gari da hatsin na tafi bankin na dauko laptop din da ake nima, na bude na cire musu daga security code.


Sannan na dauka na kai mishi, gidan shi. Tunda na shiga na samu Dilshad bata nan, na sha jinin jikina, sun sami matsala. Fitowa yayi daga dakin shi dake sama, yana murmushi. Yana gama saukowa ya iso gabana, ya zuba min ido sannan yace.
"Har ila yau kina nan a hadenki, ko zamu sha ruwa!"

Ya kashe min ido, murmushi nayi sannan na gyara zama na, nace.
"Haduwata da Halwani ya rabani da shan ruwan, ga sakonka. Mijina nake buƙata!"

"Taya zan tabbatar da mijinki kike bukata! Bayan banga madarar sha'awa a kwayar idanun ki ba!"

Takowa nayi gaban shi, sanan nace.
"Shi din mijina zakine! Baya ci sai ya farauto! Sannan yaci yabar sauran namun daji, shi baya cin abincin kowa nashi yake ci."

Dariya yayi sannan yace..
"Kenan! Iya shi ya amshi tayin ki."
D'aga mishi kafad'ana nayi tare da cewa.
"Ga zahiri!"

"Amma kin san ina sonki?!"

"Gaskiya ban sani ba, tunda duk masoyin asali, adalci aka sanshi da shi, ba rashin adalci ba, zaka bani mijina dan ina son mu koma gida dashi."

Saka hannu yayi ya amshi laptop din ya shiga duba abinda yake buƙata, sannan ya d'ago min kai yace.
"Mijinki na cikin gidan, shikenan!"
Tashi yayi tare da bud'e wani kofa, tun da ya shiga bai fito ba. Can sai gashi dauke da Uncle a kafad'arshi. Da sauri na mike na tare su. Kamar zanyi kuka.

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Sannu."
"Yumnah! Kece? Me kika kawo musu ba dai laptop din bane."

"Kayi hakuri!"
"Me yasa kika kawo musu?!"
"Rayuwarka nake buƙata, idan ka tafi zanyi maraici sosai, bani da Uba bani da kai toh da waye zan rayu?! Don Allah karka sare min gwiwa."

"Toh masoya! Allah ya kiyayye hanya," ya fada tare da dariya.

. Dakyar muna bar gidan, dan banyi tsammanin zai kyale mu ba, daga nan masaukina isa tare da kwashe kayana, na kuma komawa banki na dauki Abinda ya rage min, muka tawo airport.

Cikin damuwa nake kallon hanya dan na kosa jirgin mu ya tashi, cikin ikon Allah muka tashi, har mun cilla gajimare sai ga Zein, ya biyo bayan mu.

......
Ajiyar zuciya na sauke tare da daura kaina a kirjin shi, nace.
"Ga laptop din Agent Nan ban Basu ba!"

A hankali ya bude idanun shi, wani irin murmushi ya sauke min tare da kwalla, yace.
"Shima yasan zai yi wuya ki bashi laptop din, shi yasa ya min alluran da zai lalata min kwayoyin halittar jikina,."

Zubda kwalla yayi, wani irin kuka ne ya kwace min.
"Sabida me yasa yayi maka haka?!"
"Sabida yana matukar sonki! Kinga kuma idan na mutu shikenan zai same ki"

Dafe goshina nayi, muna tafiya jikin shi ya fara wani irin rawa, dakyar muka isa Dubai. Anan aka kwantar dashi, ban gayawa kowa ba, daga Sarinah sai Hajiya. Dan sun fi kowa damuwa da halin da muke ciki.


Jikin ba sauki, dole suka tura mu, New York. Dan sun tabbatar akwai wani kwararre likitan matsalar shi, kuma Insha Allah za a dace, tun a can aka mana hanyar samun shi dan yana yawan tafiye-tafiye.

Sati Daya muka shirya da taimakawar Sarinah da mijinta, tare da Hajiya, muka nufi can. Tunda muka isa aka fara waje waje. Ana diban jinin shi, fitsarin shi.

Babu abinda basu diba ba, ya fara aiki akan shi.

Magani aka fara mishi na antibiotic. Allurai, da ruwa. Idan ciwon ya tashi har kaga kaman bazai tashi ba.

Babu wanda yasan da wannan abin, Mamie tana can ana shirya tsiya.

----
Kallon hoton Annur nayi wanda Hajiya ta kawo min hoton shi ya ya tara kumatai, kamar shi da Uncle ya b'aci.

----
Gombe.
Sun nutse kogin masha'ar su kawai. Hajiya Atika ta bude d'akin mijinta, me zata gani Ummi Yarta da mijinta.

Ja da baya tayi, kafin kace me ta falla wata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login