Showing 144001 words to 147000 words out of 183750 words

Chapter 49 - ABU DAYA (Muke So)

29 Oct 2024

10662

hankali, tare da sanya ni cikin sabon damuwa, dake takafa hujja da an min fyade da aurena, kuma Linah tabbatar mata da babu abinda ya shiga tsakanina da Halwani, har rantsuwa ta nemi yi dan a yarda da ita.

Ta kuma daure mu, da jijjiyar mu, tare dasu Papa da Hajiya, kai duk wanda yasan da batun, sai da ta daure shi.

Dake meeting aka yi, ana cikin haka ta kira wani layi, sai ga Ra'isa, me ban ruwan flower. Na riyadh, ta kawo shi ya rantse musu cikin jikina na shine,

Wani irin abu naji yatsa min a wuya, ina kallon shi ya gama rantsewar shi, ban iya magana ba.

Bani da ikon kare kai a, baki daya kaina ya cushe da damuwa.
Ga cikin tunda aka fara wannan hayaniyar kamar an tunzura shi fitowa, domin yayi wani irin fita, ji make ina ma babu shi a rayuwata da na huta da ganin bakin ciki da idona.

Shiru falon yayi, can Hajiya tace.
"Toh mun ji,mun daura mishi cikin da ba nashi ba, kuma ina niman ku min Alfarma daya idan Yumnah ta haihu aka ga cewa ba dan Halwani bane, na amince ku kaita kotun musulunci a sauke mata haddin zina! Yumnah kin amince?"

A wannan lokacin da nake cikin tashin hankali, gyada mata kai kawai nayi, da ma zasu bi nawa da sun yanke min hukuncin na huta da bakin cikin rayuwa,

..... Da wannan rokon aka tashi, dake Hajiya tasa an ware min daki, kowa zai kwanta amma ban dani, zan zauna na dinga kallon cikin jikina, wanda sabida rashin kiba, da tashin hankali ya sashi fita sosai. Kuma babu wanda zai gani yace bai kai wata biyar ba, kuma duka-duka wata hudu ne.

Kawai ya fito ne, sosai.

........ Ina kwance akan abin sallah, naji kamar an tashe ni. Kudi da jakar kayana na gani a gefe na, kawai ina tashi na dauki kayan na fita tare da jan kofar na rufe, karar kofar ya sanya Hajiya lekowa ta window tana addu'a, bayan ta gama sallah na fitarta.

Buɗe kofar tayi tana kallon na kai hannu zan bude gidan tace.
"Ai ita fita duniya, ba lallai sai cikin dare ba, a koda yaushe zaka iya fitar ka, toh zaki iya zuwa na kara miki kuɗin guziri sai kishiga duniyar da hujja"

Nan ta shiga fada sosai tayi min, sannan ta kuma kara min da nasiha.
.....
Washi gari.
Ina kwancen, sai ga Linah, tana kallona ta kama dariya.
"Nazo ki bani laptop din Ahmad da yake gurin ki!"

Girgiza mata kai nayi tare da cewa.
"Baya hannuna."

Zare min ido tayi na juya mata baya dan bazan iya rigimar ta ba, dan matukar na cigaba zata iya kara min damuwa akan wanda nake dashi...
Paid before read.
#Mai_Dambu...
ma: 5️⃣"ki bani laptop din ko kuma abinda ake gudu ya faru?!"

Juyawa nayi ina kallonta, bakina ya gaza furta kome? A hankali a raina naji dama shi yasa yace min kar na bawa kowa laptop din.

Ashe abinda ya hango kenan! Toh me yasa yaki tsaya da kanshi, kallonta nayi a sanyayye nace mata.
"Babu laptop din shi a gurina!"
"Wato ba zaki bani ba kenan! Sai na saka an wulakantaki?! Tare da shegen dake jikinki!"

"Wallahi babu komai a gurina?!"

Duk barazanar ta bata samu kome a hannuna ba, haka ta gama zagayen ta tare da barin dakin.

Shiru nayi ina nazarin abinda ya faɗa min. A ranar da zan bar Qatar, dan ya turo min sako ta wayar Zein!
_Kada kiyarda ki buɗe laptop din! Zasu yi amfani da address dina, karki bawa kowa.! Don Allah koda zamu rasa kome na mu, karki bada laptop din, idan na mutu karki min kuka! Ina sonki_

Toh me yasa ba zai kirani ba, yake bari ana wahalar dani.
Share kwallar idanuna ayi sabida ganin Linah, ta wuce ta bayan d'akina, fitowa nayi nabi ta baya, zuwa gurin da take.

"Babu komai a hannunta! Kuma bana tunanin komai a hannun kunsan ba karamin shu'umin mutum bane! Kawai zan dawo amma dole zan tsaya dan naga akwai matsala a nan sabida Dad dina yaki bada hadin kai so yake kason shi yafi na kowa yawa."

Kashe kiran tayi, nayi maza na koma baya.
Wasu irin hawaye ne suka zubo min, Jacob shine ya fado min toh ya zanyi da cikin jikina? Dole akwai wani abu! Kafin na haihu zan iya rasa shi.

Ji nayi kamar zuciyata zata fita.
Kiran Zein nayi cikin kuka nace mishi.
"Meye kake ƙoƙarin boye min? Ina mijina?"
"Kinga Yumnah! Ban san kome ba!"
Kashe kiran yayi can sai ga Rahbeel, amsar wayar hannu na yayi cikin fada yace.
"Ya ana ƙoƙarin gano ainiyin gaskiyar alamarin kina kokarin ganin kin b'ata mana aiki, ince duk sabida kece da kin bada laptop din da ake zargin ya baki da bai fito bane.

Duk halin da Halwani yake ciki duk sabida kece. Ki bada laptop din da ya baki."

Wani irin kuka ne, ya kwace min, wato na basu shine matsalar su.
"Toh ni babu laptop din a hannu na"
"Karya ne! Yana hannun ta. A duba dakin za a samu." Inji Mamie!
Lokaci guda kowa ya juya min baya, Hajiya ta kasa yin komai, sabida tashin hankali.
"Yumnah basu laptop din shi"
Kauda kai nayi sannan na ce mata..
"Baya hannuna!"
Da gaske baya hannuna ne! Yana Qatar, tun zuwana can da kwana biyu, ba tafi wani banki na ajiye a can.
Sun gama dubawa basu samu ba, dole suka fita. Kowa na mamakin abin, kuma sun tabbatar yana hannuna, sannan duk abinda zasu yi sai dai suyi amma babu su babu laptop din shi.
Bayan fitar su, aka turo min Khuwailah, nan ta shigo muna cikin hira ta jefo min tambayar akan laptop din.

"Zai yi kyau! Ki tsaya inda muke, domin babu abinda zaki ji a bakina, laptop babu shi babu a hannuna, ban san ya zan yi muku ba, hala idan na fara shirin barin gidan nan zaku yarda dani."

Haka ta koma ta gayawa mijinta babu a hannuna, ban san dalilin da yasa ake niman laptop din ba, amma koma meye abin nada muhimmanci.

Bayan kwana biyu, jami'an tsaron daga Abuja sun zo, niman laptop din, basu samu ba. Dan haka suka tasa keyana, zasu tafi dani, abinda ya gaya min shine ya faɗa min.

_Za a biyo laptop din, kuma zasu dauke ki! Ita mace ba ana ajiye ta, dan girki da a kwanta da ita bane, a'a kawai an aureta ne dan an san duk wata hikima a sarrafa girki ta iya. Dan haka kamar yadda ake sarrafa kayan miya a tukunya kema sai ki hada musu zafin kai, ga wannan wayar na bude miki Whatsp da Facebook, IG da Tweeter, dan haka a duk lokacin da suka zo, abinda zaki yi anan_

_Shine, zaki daura abinda yake faruwa ne. Sannan idan kin je can. Zasu nemi baki wahala, kafin nan abinda kika daura zai zama abin yayatawa, tare da duba lamarinki na yarinya mai ciki. Karki manta, kiyi haka domin abin cikin kine, dole kema ki zama Ni! Indai da gaske abu daya kuke so!_



Kallon su nayi, cikin niman rigima, nace.
"Kunga! Ku tsaya nasha agwaluba!" Kallona suka yi, ai kuwa na b'ata rai nace.
"Matar aure da ciki kuka dauko! Dan haka dole a nima abinda zan iya ci, sannan idan kan sami aya da kwakwa kai har da dabino, tare da dinya, sannan ku duba min, madarar fura da nono, na Admiral."

Haka nayi ta basu wahala, dan bakar fitina har masa nace a nima min, kamata yayi ace min isa abuja karfe biyu, sai gashi har uku saura bamu bar Gombe ba.

Duk wannan abin ina ta tura sako, face book tare da fadar yan sanda sun dauke ni, ba tare da nasan abinda nayi ba, sai yawo ake dani da aurena.

A hankali aka fara samun masu zuba sakona, tare da comments, lokacin guda wasu suka fara share. Kafin wani lokaci maganar ya zama na yayyatawa, a Media haka ya d'aga hankalin su, take aka kira su dan har mun isa airport, cewa aka su mai dani.

Dariya nayi lokacin da naga sun mike hanyar gida, yalo na kai bakina, nace.
"Abu mai sauki ne! Kama barawo amma abu me wahalar gaske shine samun hujjar ka mashi.

Ban san inda mijina yake ba, amma har yau ina jin shi a raina, dan haka kuyi kokarin kare kimar matayenku, nima da koyarwa shi nake jin Ni wata ce."

Tunda suka kawo ni, har cikin gidan, suka tafi. Shiga cikin gidan nayi tare da zuba musu ido. Idan kunne na, da idona basu min karya ba.

Mommyna da su Mamie na gani, sun fito. A razane ta kalli cikin jikina, jinjina kai tayi tare da kwafa.

Tunda ake cikin wannan tashin hankalin, babu irin na yau, domin kuwa. Kusan kwana akayi a kaina , ina mugun mafarki tare da ihu. Sosai abin ya fara niman tab'a lafiyata da abun cikina ɗan garin boya na fadi akan cikina.

Jini ne ya shiga zuba, dole aka wuce dani asibitin Dr Bello.
Wannan abun ya dame kowa. Dole aka daura min ruwa. Tare da sanya min abu aka daure hannuna da kafana.

Sabida lokacin da na farka kiciniyar sauka nake, zan fado shine aka daure ni.

Wahala ka shiga bani, ta hanyar firgita, da taimakon tsorata ni da Mommy take, suka shiga sai na fadi inda laptop din yake, fir naki magana.

A cikin maganar da Linah bata gaya min, anyi auren sune, domin a rufe mishi baki, shi kuma da taimakon wasu Mamien shi, suke kome.

Ni laifina da suke ganin, da kuma yunkurin su na hana ni shiga rayuwar shi, sabida yana sona, kudin da Mamie take samu abubuwan da ake bana wasa bane. A cikin masu hannu abinda suke aikatawa har da Mommy na. Ita kan dama son da take mishi yasa ta, bani wahala. Ga kuma cikin jikina wanda take ganin yana kuma cusa mata haushi.

Su Mamie kuma, da zan basu laptop din, zasu cire sunayen mutanen da ake zargin su, da shigo da haramtacciyar kwaya, tare da safara da mata da yara kananu, wanda dama kungiyar su Mamie yana cikin masu wannan sana'ar.

Sanan nice na tafi can aka dawo dani, dan haka akwai abinda na sani, a can ɗin gudun kar na fada mishi idan binciken haka ya taso shine suka kunna mishi wuta daga ofishin su, duk sabida mun hadu a cikin abu daya muke so.

Iya azaba na azabtu, amma bana jin zasu sani magana, dan dama na taurari tun a thailand.

Da suka ga naki magana dole suka barni haka, tare da sallami ni, zuwa gida.

Cikin jikina babu abinda ya same shi, kuma gashi dama Ana zargina akan cikin, idan wani abu ya sami cikin, Mamie sunyi riba dani.

Sai da ta kai kowa ya daina min, magana. Sai hajiya kad'ai ke kula ni.
Ina cikin damuwa sosai, bani da yancin fita koda falone, kullum ina daki kamar mayya.

........
Damuwa na karuwa, tashin hankalin kullum kara yawaita yake, domin kuwa sai da suka sani na amsa yana hannuna, a lokacin ne naga tashin hankali, ga cikin jikina da bai wuce wata bakwai ba.

Tunda na amsa yana hannuna, kullum sai an zo tambayana yana ina ne? Nan ma bani da wata amsa sai dai nace musu.
Yana cikin dakina, haka mahaukata zasu wargaza dakin basu gani ba, zasu mai da kome gurin zaman shi.

.karshe a bini da harara, kowa ya gama gajiya da abinda nake Mishi, ranar kam ma cewa nayi ai yana korea, mahaukatan nan, sai gasu nan zasu tafi koda yake sun tafi, kawai na kyale su suka gama wahala sannan suka dawo kamar zasu harbe ni.
......
Papa ne ya shigo dan shima ya gaji da abinda yake faruwa.
"Yumnah! Ki gaya min inda laptop din yake, baki gaji bane da damuwar mutane, kullum jami'an tsaro suna hanyar zuwa gidan nan! Ki bamu Laptop din nan don Allah"

Maganar Uncle ce ta fado min.
_Duk wanda yazo karki Bashi! Duk abinda zasu miki karki yarda dasu, domin suma ana musu barazana ne dan su bada, karki yarda ki basu, laptop din Yana kunshe da abubuwa na masu amfani, da kundi na masu laifi, don Allah karki basu. Insha Allah wata rana zan zo da kaina. Amma ki a dana min shi_

Wannan abin ya dame ni, sosai bayan abinda Kafaya ta gaya min ban yarda iya shine ake zargin Uncle dashi ba! Kawai wanda suka sani ta faɗa bawai gundarin abinda ya faru na.

Na fahimci cewa kawai damuwar su a basu laptop din ne, amma ba wai abinda yake faruwa bane ake niman akan shi ba.

...
Sau biyu Ina ganin Mommy, a cikin gidan, kuma zuwa na biyun shine wanda tazon da cewa.
"Nasan kina sane da abinda yake kawo ni, da kuma abinda nake miki, abinda nake so shine a ki bar min Halwani zan dawo dashi duniyata, Ni daya."

"Ai ba duniya ba! Ko karkashin kasa zaku shiga ba zaki tab'a samun shi ba, dan shi nawa ne Ni daya.....
Paid before read...
8/30/20, 9:39 PM - Ummi Tandama: 6️⃣ Babu wanda bai ji haushi na ba, ga takaici ga bakin ciki, nima haka naji lokacin da suke shegen ramin cikin jikina,.

Yawan damuwar da na sawa raina, ya sanya ni fara cikin baya da mara, kusan lokaci guda.

..ganin haka Hajiya ta kira Baban Khuwailah, shima yazo tare da wata nurse, Muka nufi asibiti. Dukda dogon binciken da suka yi sanun samu bazan iya haihuwa da kaina ba dole sai sun min aiki.

Papa ne ya saka hannun, daren juma'a aka cire min dan mitsitsin yaron da ya kusan sanya family su Uncle hauka, sabida wani irin kamar da suke da Uncle.

.wato familyn suna da chindo, dan haka basu cika barin shi ba, dan naga shaidan haka a hannun Uncle, toh na yaron shi kam bazan ce kome ba, domin kafar shi na dama, shida ne haka hannun shi ma, kafar shi na hagu shida ne tare da hannun su kan su, basu samun masu shida shida.
Sai tsakanin wuyar Uncle, akwai wani baƙin tawadar Allah, toh shi kan Yaron, har gurin fuskar shi. Iya haka ma yasa mamie jin wani mugun kunya da tsoron abinda mutane zasu ce mata.

Lokacin da Linah taga yaron, dan sunje har gurin da yaron yake ana hanasu daukar shi.

Da bakin cikin haka ta shigo dakin da nake, taga Hajiya da Maman Khuwailah suna magana akan halin da nake ciki, kallon su tayi sannan ta fita.

....... Sai da na kwashi wasu awowi. Koda na farka Mommy Naga tare da Yarona, mika hannu nake ta bani dani Yarona.

"Kin ketare iyakata, ba zaki tab'a ganin Dai-dai ba, sai d'ai-d'aita ki, shi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login