Showing 57001 words to 60000 words out of 183750 words
da ita."
Shiru suka yi kansu a sunkuye, hular su a hammata, kallon su yayi ya kalli Hajiya mika mata wayar shi yayi sannan yace mata.
"Kinga ke zaki iya fahimtar abinda nake nufi karb'a ki kira su. Kice musu su dawo min da ita, in ba haka ba wallahi zan kashe kowa."
Girgiza Mishi kai tayi cikin tausayin shi, tsaki yayi tare da barin cikin asibitin, yana fita wani me Mashin ya kwashe shi ya zub'e.
Haka yaji ciwo sosai, amma dan tsabar taurin kai, ya kasa hakuri dole shi zai je niman Yumnah.
Dakyar aka dawo dashi, akayi mishi treatment, sannan ana aka mishi abinda ya tsana alluran barci, ai kuwa dake jinin shi nada karfi sai da Ya zagi likitan kafin barci yayi gaba dashi.
Sai da yayi barcin awa hudu kafin ya farka, nan ya kuma baza jami'an tsaro aka tafi niman Yumnah, duk inda ake ganin Yan jagaliya duk an bi an kame su, kayan haushi wasu ma basu jagaliyancin amma haka Halwani yasa aka kame su.
Sau uku yana marin Linah, wanda kuma akan zafin Yumnah take yi, wasa wasa Yumnah ta b'ata a Gombe, da kanshi yaje ya ga yadda Mommy take fama da hauka.
Yana shiga ya kalleta, cikin bakin ciki, dan batai kama da wacce ta rasa Yar ta ba, shiru ne ya gifta tsakanin su.
Kafin ya fara magana, musamman da yaga tana kuka sosai.
"A da ina zargin ki? Amma ganin halin da kike ciki yasani jin babu fa'idar na zarge ki! Nasan rasa Yumnah ba ke daya bace ta rasata har dani.
Shin ko kin san su waye suka sace ta? Bi ma'ana ta wani siga suka zo gidan?!"
Kuka take sosai kamar ranta zai fita, amma taki magana, daga karshe dai, haka ya hakura bai kuma mata magana ba, san yasan bazata bashi amsa ba.
---
Sai da Ahmad yabi duk wata boda na kasar nan yana niman Yumnah, karshe sai ya daina shiga hidimar kowa, ya rufe kan shi yayi shiru, baya kula kowa baya tunanin aikin shi. Kawai abinda ya sani Yumnah,
Daga Mamie har Linah kowa shakkar shiga inda yake suke yi. Hajiya kuwa Addu'a ba dare ba rana, kuma anyi juyin duniyar nan ya koma Japan yace babu inda zai je a gombe zai zauna har sai an Sami Yumnah, kawai Hajiya ta sanya Masallatai da makarantun almajirai ana sanya shi a cikin addu'o'in su...
A cikin kwana goma da faruwar abin duk ya zama kamar mara cikekken hankali, aikin shima niman.
Daga karshe ganin laifin kowa yake, kamar da gangan suka bar mishi Baby. Ta b'ace.
Dakyar da Addu'a ya amince suka koma Riyadh, baya humm baya uhumm.
---
"Utta! Ban gane me kake shirin aikatawa ba, duk wannan azabar da na sha kace min aiki ya lalace kamar Ya? Uban me ya lalata min aikina."
Cikin wani irin angry face, ƴace.
"Ubanki ne ya lalata miki aikinki! Kaji yar abu kazan kaza, wata da ban san Wacece bane ta lalata min aikina, kuma ba a wani waje take ba a cikin kungiyar nan take, ga Yarki can ki sanya yadda zaki yi da ita!"
Zuba gwiwar ta tayi a kasa, sannan ta fashe da kuka tana fadin,
"Kayi min rai! Na tuba."
Shiru yayi sannan yace.
"Na kawo shawara? Yarinyar ki tana da taurin kai, don haka zamu had'a ta da babbar kungiyar mu, na na bakar kunama!"
A razane Mommy ta kalle shi, kafin ta sake wata irin kuka domin matukar Yumnah ta faɗa wancan kungiyar rayuwarta ta lalace. Baki d'aya, zata zauna under control din Ammar ne! Cikin sauri tace.
"A'a Utta! Zakiyah ga Haja nan nawa ta miki?!"
Ta faɗa tare da kauda kanta,
" miliyan talatin!"
Ta faɗa kai tsaye?!
"Ba kaza bace? Kuma ki dubata Virgin ce! Ki kuma duba Suranta nan da shekaru idan ta goge zata iya rayuwa cikin aminci ki kara wani abu, sabida ko daga Halittar jikinta ba kowacce mace ke samun irin shi ba."
"Na kara talatin daga haka bazan kuma yin wani abu akai ba!"
"Ki kara ashirin zan bar miki ita a miliyan tamanin."
"Kin san inda zan kai ta ba lallai bane su yarda sabida."
Kallon ta Mommy tayi sannan tace.
"Sai kuma aka ce miki dole Thailand zaki kaita, ki nemi wani waje mana!"
Shiru tayi sannan tace.
"Thailand din dai! Chan yan iskan kasar nan suke zuwa suna farke kananun yan mata, amma ba damuwa zan kai ta gidan Jacob domin shi, yana harka da manyan Yan mata. Tunda kin ce Virgin ce zan amsheta a haka.
Amma yau zamu bar garin nan domin ina son na tsallaka Nijar da ita."
"Wannan aiki na ne! Kuma yanzun zan fara."
A take Hajiya Zakiya ta biya Mommy Kudin Yumnah, wacce ta sayarwa Halwani Miliyan dari hudu da kuma kamfanonin shi ya bata yau dan cikar Muradin ta ta kuma sayar da ita, zan ga yadda wannan kwamacal.
A daren aka fita dasu, har zuwa Jigawa dan ta me Gatari zasu fita, domin idan suka nufi katsina za a iya kamasu.
Tafiyar dare zuwa wayewar gari ya isar dasu, Niger Republic, bud'e idanuna nayi tare da saukewa akan saharar da muke ta haurawa.
Kallon yan kananun yan matan da muke cikin J5 dasu nayi, cikin mamaki nace.
"Ina ne nan?!"
Kallona wani daga cikin mutanen da suke tsaron yayi sannan yace.
"Beauty! Muna Nijar! Daga nan zamu shiga Libya gobe da safe, jibi kuma mu tsallaka zuwa Itali, gata a rabaku inda zaku fara aikin ku."
Ji nayi maganar kamar saukar aradu, a kaina kuka ne ya kwace min. Nace,
"Na shiga uku! Waye ya sace Ni?
Ya kawo ni nan?!"
Babu wanda ya kuma kulani a cikin saharan nan muka kwana, dole suka kashe motar. Sannan aka sauke mu, tanti suka bamu tare da nuna mana yadda zamu kafa.
Muna gama kadawa muka shige mutum biyu.
Dan akala mun kai mu ashirin a cikin J5 din nan.
Muna shiga tantin mu da wata yar jos, kallona tayi kamar bazata yi min magana ba, sai kuma ta miko min hannuna tace min.
"Laraba Salisu!"
Dama mamaki nace.
"Kina jin Hausa ne dama."
Gyada min kai tayi, sannan ta ja abun rufewa tace min.
"Ba shine a gaban mu ba, wannan itace tafiyata ta biyu, da farko an kai ni na dawo, yanzun kuma na fahimci ce ne rayuwata take, a can na dace na rayu.
Bazan iya bakar talauci da wahala ba, a cikin wata biyar zan maidawa Hajiya Zakiya kudinta, sannan na cigaba da kula da mahaifiya ta da kanena, domin sabida su nake raye a nan, dan haka kiyi hakuri kema da kike da kyau, kin san yadda suke niman masu kyau irinki kuwa.
Zaki yi arziki, sosai zaku ki samu daukaka."
Cikin mamaki nake kallon ta, tare da ware idanuna akan ta, ina mamakin wannan al'amarin, a sanyayye zuciyata ta kama rawa nace mata.
"Wacce irin sana'a ce haka?!"
Kallona tayi sosai, sannan tace.
"Karuwanci! Da kuma duk wani abinda zai iya jan hankalin maza dasu!"
A firgice tace.
"Karuwanci???! Abinda ake kirana dashi? Yau ya tabbata a kaina waye yayi min wannan yankar kaunan,"
Na fashe da kuka, jin ihu a tantin dake gaba da namu, ya sani tuma tsalle zuwa jikin Laraba,
Jikina na rawa cikin tsoro da firgici, nace mata.
"Meye?!"
Hannun tasanya a bakina muka dauke numfashi, can muka ji mazan da suka kawo mu, suna dariya.
"Kai wancan tayi karama bata da armashi, wancan kuma tayi zaki da yawa,"
"Eh dayan tafi dad'i amma Ni wannan yar kyakyawan nake nima ban san inda aka tura ta ba."
Ina jin haka na shige jikin Laraba nayi luff, har Suka gama nima na basu same ni ba, sannan suka bar tantin,
Washi gari da safe, sai ga Hajiya zakiya, tana zuwa ta shiga duba abinda ya faru, ranta yayi mugun b'aci, domin a cikin mu ashirin da daya a yiwa goma sha bakwai fyade, abinda ya ja mata asara yarinya daya ta mutu, biyu kuwa tsabar an musu zalinci sai da aka fatattaka su.
Lumshe idanun ta tayi, sannan ta sanya aka tara.
Juya baya tayi tare da cewa.
"Ku buɗe musu wuta, ku bar gawarwakinsu a cikin sahara, suma yaran da bazasu moru ba, a Barsu a saharan su Mutu."
" Akan me za a Barsu a sahara su mutu? Ke wacce mara imanin ce? Toh yadda kika kwaso mu a gaban iyayen mu dolenki kiji damu, muguwa kawai."
Juyowa tayi ta kalle ni, taga babu tsoronta a idanuna, ga mutanen da suka yi fyaden za a harbe su.
Dawo dani baya Laraba tayi na kwace hannuna ina kallonta.
Takowa tayi gaba na, ta d'aga hannu zata mare ni, taga na zuba mata ido babu tsoro ko kad'an a idanuna. Sai ta fasa.
"Zan kyale ki! Amma zan gaya miki abinda zai dawwama yana çaccakar ruhinki da zuciyarki har karshen rayuwarki!
Abu daya muke so Ke da uwarki? Kin san meye abin? Sabida shi take azabtar dake, sabida shi take sabida shi ta lalata rayuwarta dan ta same shi, shi kuma ke yake so?
Kin san ina zan kai ki? Kin san waye haka? Toh Halwani ne? Ahmad Halwani sabida shi mahaifiyar ki take wahalar dake? Sabida shi ta sayar dake, sabida shi ta sayar da Darajarki! Sabida shi danginki suka tsane ki? Shine rokon ki bar mata shi ita ta aure shi, kika ki amincewa.
Uwar shi da matar shi basu kaunarki sabida shi, kinga kenan dole ki sadaukar da rayuwarki domin na Mahaifiyarki domin itace kawai zata iya ji da Matar shi."
Dariya me hade da kuka nake, cikin wani irin yanayi na bakin ciki da takaici, nace.
"Ni bazan yi karuwanci ba! Sai dai ke kiyi ko ita Mommyn tazo tayi amma wallahi na rantse miki da Allah bazan bawa wani namijin kaina ba, sai mijin da zan aura."
Bushewa tayi da dariya sannan tace.
"Yaro man kaza! Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare! Muna nan dake zaki amsa kin amince."
"Har abada bazan tab'a zina ba!"
"Yarinya kenan! Ai kinyi keda Halwani, sau nawa yana kwanciyarshi dake, ko na nuna miki ne?!"
Rintsa idanuna nayi wasu irin kwalla na zuba da mugun zafi, sannan tace.
"Maza ku zuba min kowa a mota! Sannan suma wadancan a zuba su a mota, idan sunkai labari shikenan, sun ci albarkacin ta.
Ke kuma muje dake, dan ina son naga karshen taurin kanki!"
Wayyo Allah na! Alqur'an zan fita yawon sallah 🤭🤣🙄🤔 idan na dawo da wuri zaku ga Update Idan kuwa na hantse sai dai ku makale a kwalelen jira! Libya 🤦.....
_Muna sayar da in gantattun magungunan mata har da na Maza! Kai hatta na Infection! Bom-bom! Hips! Boons! Tare da hadin amare! Ku sani bayan hadin amare da yake 16k kowani maganin mu 5k ne! Har da kazar amare! Zamu kai muku ko ina a fadin kasar nan! Har Nijar muna kaiwa_
Acct: 0472282105
Ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk
Ranar:10/August/ 2020/ Insha Allah zan gama free Pages! Wannan karon abin da sauki babu tsawallawa, domin dubi da halin da muke ciki! Na sakawa book din 150? ta bank idan kuma VIP ne 300? ne,
Naga har yanzu wasu basu fahimci yadda ake saya ta katin ba! Idan katin Mtn ne 200 ne! VIP 400 ne, katin mtn kenan
Ba yabon kai ba.Acct: 0472282105
Ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk! 08130269641 ta nan zaku tura min evidence🖕
*_ABU D'AYA_*
(MUKE SO)
💝💝💝
_Barka da Sallah_
2️⃣7️⃣
Kwace hannuna nayi, cikin murmushin bakin ciki, nace.
"Ba zaki tab'a ganin karshen taurin kaina na ba! Ba dai Ni ba, Insha Allah na fi karfin karuwanci.
.ku da ya zame muku, dole dai.
Amma ni Bai zame min dole ba, Insha Allah sai Ubangiji ya nuna muku iyakar shi, tun anan duniya zaku tagayyara, Kuje lahira ku lalace.
Insha Allah sai kunyi muguwar karshe, bila sai tafi ku daraja, ba dai duniya kuka zab'a ba, ai wanda ba a haifa ma ba, tana jiran shi balle wanda yake cikinta."
Daga haka na bi bayanta muka shiga motar da ya kawota, wurga min wani mayafi tayi tare da nuna min yadda zan daura, mai da mata abinta nayi na daura dankwalin kaina.
Ya zamana fuskana ake gani, wato munyi wani irin tafiya mai mugun wahala, kafin muka isa garin da yake boda da Libya,
Tafita suka gama magana da jami'an tsaron kasar, suna gama magana aka bude mana hanya muka shiga yankin tripoli.
Kafin mu isa cikin ƙasar sai da muka hadu da yan ta'addan da ake gwagwarmayar yakin kasar. Abin mamaki yadda aka bude motar bayan mu akayi ta kwaso musu kayan abincin, magungunan.
Da wasu abubuwan Amfani, sannan suka hada motar mu da wasu yan ta'addan suka rakomo.
Daga nan kuma tripoli, aka sake shirya mu a cikin jirgin ruwa, wanda zai tsallaka damu, Italiya, yan mata biyun da aka yi musu fyade daya muna shigowa tripoli ta mutu, dan haka sai da dare aka shirya mu, sannan aka ɗauki gawarta aka wurga cikin ruwa.
Karki manta tafiyar da za ayi Ni kadai ce Hajiya Zakiya ta dauke ni a jirgin ruwa mai kyau, sauran yan matan da mazajen dan an kashe wadancan,
Sannan masu tukin jirgin gudun kar su mata asarar sai da aka musu horon wata biyue.
Shi kansa tekun akwai ƙatuwar halitta kifi, shark wacce zata iya ban gaje jirgin ta kifa, sannan koma daya suke da mutane.
Idan kuma Teku bata so ba itama zata iya anbaliyar lakume mutane, a gaskiya muna cikin wani irin yanayi. Koda yake Ni bani da matsala masu matsalar su Laraba.
---
Nasiha Hajiya take mishi mai shiga jiki, tare da bashi labarin wasu daga cikin bayin Allah, wanda Allah ya jarabce su da jarabawa suka yi hakuri Allah ya biya su da abinda ya fisu.
Duk yadda Uncle yaso sakewa abin yaci tura, yaso abar shi a kasar ya kara bincike Hajiya taki sam, dan Amadadin haka sai ta fahimci Mommy Yumnah tana yawan takura mata da maganar ko zai duba halin da take ciki ne ya aureta.
Wannan dalilin ya sanya ta sashi a gaba suka bar garin Gombe zuwa Abuja satin su daya suka wuce Rayidh, duk wani harkokin shi ya ajiye ya dawo gida da zama.
Baya kwana biyu bai shiga Makka ba, wannan kwalisar. Da gayun shiga irinta zaratan maza duk babu shi, kana ganin shi kaga namiji amma bai jin yayi kome.
Idan yaje yayi dauwafi zama yake ya zuba dakin ka'aba a gaba da kallo, cikin rashin kuzari.
Haka zai ta Addu'o'in, yana tuna lokacin da suka shigo da ita, kanta a sunkuye inda yake zaune tare suka zauna da wata Yar lebeness, Kallon matar tayi cikin murmushi sabida tana dauke da yarinya mai kyau.
Cikin harshen turanci tace mata.
"Babynki tayi min kyau."
Mika mata Babyn,
Motsawa kusada Ita yayi, cikin murmushi yace.
"Baby! Auntyn Baby. haka zaki haifa mana baby Mai kyau da haduwa irin wannan.
Mai kiga gani idan na nima miki irina mutumin kirki?!"
Kallon shi tayi, tasake dariya me ban sha'awa, sannan tace.
" Ka bar kiran kanka mutumin kirki, domin kuwa baka cika mutumin kirki ba, yana da kyau ka fahimci haka?"
"Me yasa bazan kira kaina da mutumin kirki ba?!"
" Ba wai baka da kirki bane! A'a lokaci guda ka tashi daga haka ka maida kanka mutumin akasin haka, kai mutumin ne mai amana, da gaskiya amma dare daya ka tashi daga haka ka koma mara haka.
Ban san me yasa jikina ke rud'an ka ba, amma iya akan shi na fahimci halinka kana da dabi'un son Kai."
Ajiyar zuciya ya sauke, tare da sunkuyar da kai, ina ma zai ganta yayita bibiyarta har sai ta yarda da irin halayyar.
---
Kwance suke da Yusha'u wanda ya gama abinda ke so da ita, a hankali ta janye jikinta, sabida barcin da yake, wanda ta goga mishi wani hodar sihiri.
D'akin tsafinta ta isa ta shiga tare da rufe kanta.
Yanka hannunta tayi, tare da ɗaukar wani babyn roba, na mace da namiji.
Wasu irin surutai take, tana aiki jikin yan babyn roban, sai da tayi musu tsakani mai mugun rata, sannan ta kuma cigaba da abinda take.
Tana gamawa da aikin, aikuwa kamar wanda aka jona lantarki aikin ya tarwatse, cikin bakin ciki ta kuma hada wani aikin.
Ya tarwatse. A na karshen ne tayi shi da wani sabon yanayi, tare da saka babyn robar a cikin kasar wani irin ruwa, sannan ta dauko wasu babyn robar ta zagaye Wadatacce inda tasaka babyn.
Sai ya zamana gurin kaman prison, haka ta gama abinda zata yi, mik'ewa tayi bayan ta kwaɓe kayanta tayi tsirara, ta gama birgima a gaban gumkin da take gaban