Showing 159001 words to 162000 words out of 183750 words
"Naji zan karasa aikina amma kaima ai baka tashi da wuri ba, kuma nasan yanzun kowa ya hallara a can."
Juyowa ni yayi tare da zuba min ido.
"Kiyi hakuri! Kinsan me? Haka kawai nake ji a jikina zamu rasa juna! Shi yasa da naji haka na maza na kwala miki kira, jirani a nan har na shirya"
Haka na zauna, ina kallon shi, ya cire towel ɗin. Tare da saka boxes ɗin shi, murmushi nayi nace.
"Kana da jiki mai kyau! Shi yasa baka girma"
"Allah ko?"
Ban kuma magana ba, sai dai. Ce mishi da da nayi ina zuwa, da sauri na fita, ina zaune falo naga babu Zoben. Haka na dawo dakin na fara ji a jikina zoben babu Alkhairi a tare da shi, dan haka na cigaba da taimaka mishi ya shirya, muka fito.
Tsaf muka gyara ko ina dashi sannan muka fito, tunda muka nufi gidan sunan nake jin yin kuka, haka na fashe mishi da kuka sai da nayi ya isheni sannan ya bani abu na goge fuskana, muka nufi gidan dan tsayawa yayi nayi kukan.
Tunda muka shiga gidan ake mana tsiya, tare da zolaya ban damu ba na wuce dakin Hajiya wanda yake cike da Y'ay'an yan uwanta, anan wata mata take cewa.
"Wannan ba yarinyar nan da ta tafi karuwancin nan bane? Naga ta girma sosai!"
Kasa tashi nayi, tsabar tashin hankali, ina jin wata nacewa.
"Ai kazamar gado tayi uwarta sana'ar kenan, Kinga ai ba wani abu bane, dan ita tayi."
Wani irin kuka ne ya kuma kwace min, dakyar na nufi kofar ko gabana bana gani, ashe Hajiya na ban daki, lokacin da suke wannan maganar da sauri ta fito har tana Fad'uwa.
"Amma kunyi asara! Mugun asara ma, mugaye azzalumai marasa yarda da ƙaddara, maza ku fice min a gida ko na kira mijinta ya fidda ku, tunda ku Allah ya halicce ku baku da abin fada wani keda ita, kuke Allah ya bamu yawan rai da lafiya, sai kunyi kukan da yafi sautin ta, idan itace ya zanawa kanta zanen kaddarar ta, zaku gane idan kuma Ubangiji ne yake zanawa zaku gane.
Kufita kafin rayukan ku ya baci."
Ta faɗa haka tana jan haki, hawaye na zuba daga idanunta, haka suka fito basu ba hatta sauran yan uwansu sai da suka ji babu dad'i.
Ina fita, Aunty Marwanatu na min magana dan naga Annur a kafarta, shafa kanshi nayi ban iya bata amsa ba, shima gogan ya shigo gidan yaga nayi bayan garden da sauri, ya ke tambayar su.
"Lafiya me ya faru?!" Fitowar ƴaƴan yan uwan Hajiya suna mita tare da ganin laifin mutane biyub da suka aibanta Yumnah suke anan yaji abinda ya faru.
Da sauri yabi bayanta, amma sai me! Wayarta da takalminta tare da gyalenta duk suna gurin, amma ita kam babu, alamarta.
Da sauri ya fito yana haki, yace.
"Bata fito ba? Bayan shiga na,"
Kamar hadin baki suka ce.
"Wa????"
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Ya Allah idan barci nake karka bari wani ya taddani, Ya Allah karka farkar dani daga wannan mugun mafarkin."
"Halwani lafiya?!"
Kallon su yake kamar wanda ya tashi daga cutar makanta, a hankali yace.
"Da gaske bata fito nan ba?!"
Wani irin duka kirjina shi yayi daga nan ya zube akan gwiwar shi, tare da dafe goshinsa, kirjin shi kamar zata fashe zuciyarshi tayo waje, da sauri Aunty Taslima ta shiga garden din, itama gyalen da takalmi kawai ta gani tare da waya a can ya she.
Da sauri tafito tare da cewa.
."jama'a Yumnah tab'ata...... ..
#Mai_Dambu....
a: 6️⃣2️⃣. "Kamar Yumnah ta b'ata? Yarinyar da yanzun ta shiga gurin?!"
Kasa Magana Taslimah tai, kafin kace me gidan ya rufe da tashin hankali, aka shiga niman Yumnah.
Dakyar ya mike, tare da wani irin tangaɗi, gurin motar shi ya isa, kafin su fahimci me yake shirin aikatawa, tuni ya fada tare da fincikar motar.
...... A guje ya fita kamar wanda yake da yakinin ganinta a waje, gudu yake zubawa, mutane sai bashi hanya suke dan suna zargin ya shawo ne.
Bai tsaya a ko ina ba, sai gidan. Mommy mahaifiyar Yumnah, ranshi ya gama b'aci. Matakin da zai dauka akanta matukar ta rena mishi hankali ba na wasa bane!
.dan haka yana shiga ya same ta, tana zukar shisha.
.Gaban kayan kallon yaje, ya ciro wayar dake hade da wani receive, tana kallon shi ta zata ba zai iya abinda ya saka kanshi ba, kawai ya shiga zane ta.
Dukarta yake tare da ina ta kai mishi Yumnt, tsabar dakuwa. Sai da fuskarta ya farfashe. Taki magana waya yayi tare kiran yan sanda aka zo, suka tafi da ita.
Koda ya koma gida, kai tsaye part din Mamien su ya isa yana shiga, ya zuba mata ido.
A hankali yake takawa yace.
"Ina matata? Mamie ina kuka kai min Matana? Wallahi matuƙa baki yi magana ba! Na rantse zan yi abu!"
"Zane Ni! Kamar yadda ka zane Hassanah!" Kauda kai yayi cikin baƙin ciki.
Har ya juya zai fita, ya dakata da cewa.
"Ince ni kika wulakanta Mamie? Kika raba ni da matana? Ba komai zan barwa Allah kome yayi ikon shi kamar yadda ya saba"
Bai sake magana ya fita daga gidan, duk yadda yaso jurewa sai da ya suma.
Asibiti aka kai shi, cikin gaggawa, nan aka shiga niman ceto rayuwar shi, dan zuciyarshi tana kokarin neman kin bugawa ne, sai da suka saka mishi bututun shaƙar numfashi. Kafin numfashin sa dai-daita.
Sai da aka share kwana uku, ana niman Yumnah babu ita babu labarin, hankali kowa ya tashi Hajiya ma tayi kuka tare da yin Allah ya wadaran ƴaƴan ƴan uwanta.
----
Tafiya kawai, take a cikin dokar daji tare mika hannuna kamar zata kamo wani, amma babu kowa, kafafuna sun kumbura, har suna tsagewa, tafiya kawai take. Ita kanta bata san ina take tafiya ba.
....kuma gata nan dai kamar mai hankali kamar ba me hankalin ba.
...... Ko ciwon kafarta bata ji, tafiya kawai take, idan ta gaji sai ta zauna a jikin bishiya, ta kwantar da kanta tana haki, dan barcine ya saceta, kamar wacce aka daka mata tsawa ta mike zubur ta cigaba da tafiya.
Hawaye na zuba a idanunta, tafiya kawai take, ga yunwa ga ƙishirwa, amma bata da ikon tsayawa.
---
A ofishin yan sanda kuwa Mommy ta sha mugun wulakancin, wanda bata tab'a tsammanin sabida Yumnah za a mata ba, domin CP Ibrahim yace kar a raga mata, idan bata fadi inda Yumnah take ba, ta zata wasa ne sai da suka fi dinga kwara mata ruwan sanyi tare da dukarta kamar mahauta.
Amma taki magana dan gani take, kamar zasu kyaleta amma suka ci-gaba da mata Izaya, gata da taurin kai. Suma suka nuna mata gaban samu,
....... Kwanan Halwani daya ya farka, cire karin ruwan yayi ya wuce ofishin yan sanda, tunda ya isa, ya kalli Mommy da taci wahala, kanta a cinyarta ta koma kamar marainiya.
"Ku sake!"
Haka suka bude mata ta fito, a sanyayye ya nuna mata hanya ta fita.
"Ki jirani a jikin motana"
Gyada mishi kai tayi tana dingishi.cika report yayi na ya janye tuhumar da yake mata, sannan ya kuma mika musu na goro.
Kin amincewa zuciyarshi yake, kawai domin yasan idan ya aikata haka, Yumnah bazata yafe mishi ba. Zai zama me mugun son kai.
Kasuwa ya wuce ya sayo igiyar da ake daure saniya, sannan suka shiga tafiya, sai da suka bar gombe kamar zasu nufi Yola, ya yanka da ita wani daji.
Da gudun gaske, har cikin tsakiyar dajin ya shiga da ita, ginin gida ne a cikin dajin, bai kalli inda take ba,. Ya fito da sauri.
Ya shiga gidan ya buɗe, sannan yazo ya mata jagora ciki, bayan ya kwashi kayan aikin shi.
Yana shiga ya wuce wani daki ya bude mata kome, sannan ya fito falon, ya shiga hada abinda yayi niyya.
Bayan shigarta da minti talatin sai gata sanye da wani irin rigar barci., Kauda kai yayi tare da zubawa igiyar da yake zargawa a saman fankar falon.
Yana gamawa ya juya ya zuba mata ido cikin murmushin takaici.
"Wowwww! You look sexy. Ka raso mana."
Da sauri ta karaso zata rungume shi yayi maza ya zamee tare da tura kanta cikin igiyar ya matse wuyarta.
Waje idanunta suka fito tare da tari, bai kulata ba, ya wurga igiyar sama, tare da zarge ta.
"Ina kika kai min mata na?!"
Dariya ta fara kamar Mahaukaciya, sake jan igiyar yayi da karfin tsiya, taji makogarinta ya matse.
Wani irin tsoro da fargaba ne ya shiga zuwa mata dan har idanunta sun kasa jajjur.
"Tambaya na karshe ina matana?!"
Sassauta daurin yayi, yana kallonta.
"Wallahi bata nan! Sannan ban san inda take..."
Matse igiyar yayi cikin fusata yace.
"Ki karkashe bayyaninki a can sauka lafiya."
Jan igiyar zai yi tayi maza tace.
"Tana can dokar dajin falgore, zata garin boka kafi Allah, don Allah kiyi hakuri karka kashe ni zan mika kaina ga yan sanda ma."
Kura mata ido yayi tare da zama, yana kallonta.
"Hassanah meye Yumnah tayi miki? Meye ta tsare miki? Anya kece kika haifeta kuwa?!"
Wani irin kuka ne ya kwace mata tana kallon shi, tana girgiza kai.
"Nice? Wallahi sabida son da nake makane nasa na juya mata baya, Halwani tun muna A.t.b.u nake sonka, ka fahimci ne ni!"
Nan ta shiga bashi labarin abinda ya faru, na soyayyar da take mishi, tana kuka tare da gaya mishi sirrin zuciyarta...
"Tabbas! Kinyi ƙoƙari amma ba Ni zakiwa wannan halayen ba, dan haka zan barki nan ki zauna sai naga Matana zan zo na fidda ke, idan ban ganta ba, kiyita zama. Har ki mutu asararriya, Ina sane da kece kika kashi Faruq! Yanzun kuma Yumnah. Na rantse da Allah idan ban sami mata na ba, zaki ga salon kisar da zan miki da ranki zanta yankar namar jikinki."
"Zanyi alfaharin wanda nake so shine ya kashe ni, kasan yadda zan koma!"
Make mata baki yayi, sannan yayi ficewar shi daga gidan,
Waya yayi cikin nutsuwa, can sai ga wasu matasa har su hudu suka iso gidan, bude motar shi suka yi tare da fidda kayan abinci suka shigar dashi gidan, sannan ya kalle su.
"Sau uku bata abinci, sannan karku fara nimanta, dan wallahi kuna ganin yadda take bazata rasa cuta a jikinta ba, idan kuma kuka ki ji babu ruwana."
Yana gama fadar haka yayi tafiyar shi, cikin motar shi. Kifa kai yayi yana mamakin wannan al'amarin, anya akwai muguwa irin Hassanah?!
.... Haka ya gama abinda zai yi ya koma gida, ko cikakken awanni bai yi ba, ya nufi hanyar bai gayawa kowa ba.
Haka ya tafi ya gama yawon shi bai gan me kamar Yumna ba.
Kamar zaiyi hauka, dawo gida cike da bakin cikin rayuwa da Hassanah ta wurga su cikinta.
----
Kwanaki sunyi tafiyar bazata! Sati na kara kutsawa, watanni na kara rubayyawa, haka wannan al'amarin ya kasance, cikin jikin Yumnah ya fito ita kanta tayi mugun rama, sai cikin da ya fito.
Ban da ikon Allah babu abinda yake dawainiyya da rayuwarta, tun daga nesa take hango rugaggen fulani, da sauri takara saurin tafiyar, dakyar ta isa wani ruga matasan Fulani ne a kofar gidan, zama tayi tana kallon yadda suke shan madara, sai had'iye yawu take.
"Zaki sha ne?!"
Gyada kai tayi, suka mika mata, jikin ta na rawa ta shanye, tana zare idanu. Alamun a kara mata.
"Rabi'u karo mata!"
Shiga cikin gidan yayi sai gashi da kindirimo, da ruwa a kwanon sha.
Ya ajiye mata, dauka tayi ta shanye rabin ruwan, sannan ta kuma kafanta a kan kindirimon.
Tana gamawa sha ta kwanta zata yi barci, dayan yace.
"Tashi mu kai ki cikin gidan, ki kwanta."
A hankali ta mike, suka shiga gidan. Tunda aka kaita wani dakin matar dakin farar ce Sosai, amma ta manyanta.
"Zo nan Y'ata, kwanta nan!"
Kwanciya tayi inda aka nuna mata. A hankali barci yayi gaba da ita.
Zama matasan suka yi, sannan Rabi'u yace.
"Ummi! Yanzun zama cigaba da zama anan kenan, kuma kin san yadda kowa ya gama saka ran zamu isa."
Murmushi tayi tare da jan casbi tace.
"Bazan bar yankin nan ba, sai na sadata ga danginta, kasan halin da mijinta yake ciki kuwa, sau uku yana zuwa nan dajin domin ita. Sannan da mun barta haka zata cigaba da tafiya har gurin wancan mushirikin.
Ai ko dan cikin jikinta ya kamata mu taimaka mata, dan haka bana jin zan barta ta salwanta a wannan halin, ka gayawa Karibullah yayi maza ya tafi, zuwa Kisra ya gayawa magaji...."
"Assalamu alaikum"
"Amin wa'alaikimun Salam warahmatullah! Barka da zuwa."
Mik'ewa yaran suka yi, tare da mishi Barka da zuwa, sannan suka fita.
"Zuljah!"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da zabga mishi harara, sannan ta nuna mishi inda Yumnah take kwance.
"Zoben hannunta zaki cire! Don Allah taimaki bawan Allah irina mu koma kisra!"
"Imran bazan koma ko ina ba, aure zaka yi fa, auren ma jikar jikarka, Yo me zance maka, Naje gurin Sadeeq da Amrah, amma ya tabbatar min da aure zaka yi, kuma sai da muka yi alkawarin babu kishiya shine ɗan halinku na wulakancin maza kawai naji labarin aure zaka yi."
Zaro idanu Imran yayi cikin kasuwa ya jero mata tambaya haka.
"Injiwa? Yaushe? A ina matar take?! Don Allah waye ya gaya miki aure zanyi?"
"Waye banda Sadeeq! Kai bana Sadeeq ba, meye nufinka da gyaran gidan nan? Har dakuna sai da aka gyara fa! Wallahi Magaji ka cuce ni! Kaje bani son ganinka!"
"Wai ya kike son Mai da karamin al'amari babban al'amari ne? Na gaya miki ni ba auren zanyi ba, amma dole na zabgawa Sadeeq rashin mutunci, don Allah ko fahimce ni."
"Ka tafi ka bani guri!"
Ta nuna mishi hanya, zama yayi a gabanta, sannan ya fara magana.
"Uku ga watan muharram zaki cika shekaru dari uku da casa'in da tara, wanda yayi dai-dai da cika shekaru dari bakwai da zanyi! Shine yaranki suka ce a shirya miki maulidin karin shekarunki! Ashe ke nan kishi ya gama tafiya da ruhinki! Zuljah yaushe zaki fahimci ke daya nake so? Yaushe zaki gane nauyin soyayyanki a zuciyata.
Sabida son da nake miki, sai da aka kore ni na tsawon shekaru saba'in, don Allah ki bar biyewa Sadeeq, yanzun na yawo na samu ya jirgawa Amrah wannan bayanin itama ya gama turata cikin buhu wai zai kara aure, da jego na samu tana kuka, har tara mutane tayi wai a tambaye shi laifin da tayi mishi, mara kirki .
Ya kafe wai sai yayi auren,wato nima bari ya lalata min rayuwa, ta hanyar cewa zanyi aure."
.dariya ne ya kamata, tana kallon shi sannan tace.
"Toh! Ya zanyi da wannan Yarinyar?!"
"Eh toh ba sai ki kaita gurinsu Amrah, sai a hada mata magani, amma ai ba wani dogon sihiri bane, kawai akwai hatsari ne tab'a zoben, dole sai dan adam ne irinta zai tab'a, sabida asalin zoben na wani kasugurmin aljani ne, kuma boka ne zamanin shi, sace zoben shi aka yi kusan shekaru dari biyar da talatin kenan.
Dashi akayi tsafin, sannan yarinyar takan shagala da addu'a, duk da tana da ibada, Kinga ni ba wannan ba, ya zamu yi dan wallahi nayi hakuri, kuma hakurin ya kare, kisan yadda zaki yi dani!"
"Hmm! Ni fashin sallah nake!" Ta faɗa fuskarta a murtuke.
"Toh wallahi aure zan kara!"
"Ai dama nasan zaka aikata, kaje kuyi ta rashin kunyar ku, a gaban kananun yara,