Showing 99001 words to 102000 words out of 183750 words
tare da saka harshena na lasheta.
Ina kallon yadda yake kallona.
D'aga mishi gira nayi tare da cewa.
"Ba wani abu bane. Allah ya gani bazan iya controlling kaina ba, idan naga Male, kayi tunani yadda zan kasance idan na sami biyar bukata na, Uncle tab'a nan dina wallahi ciwo yak...."
"Kan babban bura uban Bala'i, Keeee!" Ta daka min tsawa, lekowa nayi cikin dakiyar nace.
"Oh! Ashe kin zo? Toh Barka da zuwa. Kin zo ganin ko ya mutu ne? Gashi nan akwance, ba wani abu bane kawai ina gaya mishi gaskiya yadda nake ne. Tunda kin san dai ai shi din namiji ne? Kuma mijin mace hudu harda kai harda concubine wato Kwarkwarah.
Dan haka kiyi aiki da hankali yafi aiki da agogo.
Kamar zata buge ni, haka tayo kaina, a hankali na janyo almakashin da aka mishi gyara d'azun nayi kanta dashi.
Cike da mamaki tayi baya, muna kallon Juna, nuna mata kaina nayi.
"Duba da kyau! Ba Yumnah wacce take shirin nan bace! Wannan Yumnah Omar ce! Wancan ta jima da mutuwa.
Kina kuskura kika tawo min, zan yaga miki fuska."
A tsorace tayi baya, na kuma takawa gabanta, rike hannuna yayi cikin sanyin murya yace.
"Idan an hanani sukuni! Ina zaton ke zaki bani, me yasa zaki fara da haka."
Dawo dani yayi gabanshi, ina dawowa na rungume kanshi, cikin damuwa nace.
"Ba iya yau ba, har karshen rayuwata ina tare da kai."
Kifa kanshi yayi a kan cikina, wayyo Allah na, wani dadi naji, na kuma kwakume shi ina kallon matar shi, dan ina cike da ita, kallon yanzun ba da bane na mata.
Da sauri ta fita daga dakin. Ya kuma rufe ni da fada, wai ai ita ba sa'ata bace, Aunty na ce, tunda ta haifa mishi Baby Yumnah, kuma kanwata ce.
Wani hararar da na maka mishi tare da ture shi a jikina, nace.
"Ko a birnin tubabbun ba za a fara haka ba, balle birnin mutanen da Addini da ilimi ya ratsa su, babu batun Little Yumnah kanwata ce babu wannan batun.
Bayan tun kafin a haifeta kake molest Dina, yau kace min kanwata, sai dai Yar Partner dina Yawwa.
Sake baki yayi, yana kallona.
"Yaushe kika fahimci haka?!"
"Tun ranar da na bar gaban Hajiya! Na kuma kaucewa harin da ka kawo min, na fahimci nice nake maka kallon Uban kai kallon mace kake min! Ka fahimta."
Shiru yayi, yana me janye hannuna daga samar cinyar shi, dan ya fahimci halina daga jiya zuwa yau, ina da matukar jaraba.
"Toh me yasa kike son na kuma Molest dinki." Ya tambaye ni, dai dai na dauki wata mayafi da wata hula zan saka na fita, dan wallahi ina son shan ruwa.
Kallon shi nayi, sannan nace.
"Ka kira matar ka, tasowa yayi ta zauna. Ni zan je Club ne! Na sha ruwa"
"Don Allah ki daina shan ruwa nan babu kyau! Me yasa kike son Allah yayi fushi dake, kinji yadda nake ji kuwa, wallahi zuciyata kamar zata buga, don Allah ki taya ni wannan yakin mana."
Shiru nayi ina kallon shi, can na dawo gabanshi, na ja kujeran na zauna, tare da kifa kaina a bisa cinyar shi, ina jin ba dadi a raina.
Shigowar Yan sanda ya samu d'ago kai, da gaske sune babu wata Magana suka fice dani, duk yadda yaso ya hana amma haka suka fita dani.
Kamar zai yi ihu, can sai ga Matar shi tana dariya tace.
"Bari mu ga yadda zaka kayi idan aka kawo maka ita maza shida sun kwanta da ita ya zaka ji?"
Bayan shi ta koma tai ta fisge bandage din ciwon shi, dakyar ya ture ta, ya fita, tana bin bayan shi ta fara ihu, mijinta ya haukace.
Shi kuma damuwa shi ya nime wani wanda zai bi mishi bayan mu, dakyar ya tsaya yana haki ya gayawa Likitan waya yake so.
Likitan yana bashi yakira gurin aikin su na nan, Tokyo aka shiga bin Address din da ya bada na track device din.
Bayan likitan ya tafi ne, yana juyawa yaji an duke keyar shi da abu, kasancewar gurin babu camaran CCTV.
Janshi suka yi, har dakin shi suka shiga daura mishi wasu magani, kafin wani lokaci ya birkice, ya fita hayacin shi.
Sunyi tambayar duniyar nan yaki ce musu kome, kuma matsala akan Yumnah ce, sun yi maganar sunyi dukar tare da Kafaya, amma yaki magana, asalima kamar hadin baki babu wani likitan da ya kuma zuwa ta wurin.
Azabtar dashi da take akan ciwon shi yayi yawa, dan haka yayi shiru bai mata magana ba, har suka gama suka fita.
---
Tafiya mai nisa suka yi dani kafin suka yanka wani daji mai yawan bishiyoyin, suna zuwa gurin suka shiga cire kayan su, tare da cire min nawa da karfin tsiya,
Sosai suke kokarin keta min alfarma, ina ture su tare da kai musu cizo, burinsu kawai su ai watar da abinda Linah ta sanya su min.
Sai ga karar motar yan sanda, sun yanko dajin, ai jin haka suka fita da gudu babu kaya a jikinsu, nima kayana, na dauka na suturta jikina, ina kuka.
Haka yan sandan suka tafi dani gurin shi, a can asibitin. Ina shiga da gudu nayi kanshi, ina me rungume shi, kuka nake sosai shima Kwalla ce ke bin idanun shi. A hankali na goge mishi tare da cewa.
"Karka yi kuka, idan nayi waye zai rarrasheni." Rike hannuna yayi, cikin jin jiki. Ya gyada min kai,
Yan sanda na fita, naje na rufe kofar, na dawo na kwanta a kusa dashi, sabida ya matsamin.
Yana kife sai pillow da suka sanya mishi a kirjin shi, hannun shi daya yasanya min ya janyo ni jikin shi.
A hankali nake jan zuciya har barci yayi gaba dani, shima haka.
.....
Washi gari a tare muka tashi sakamakon buga kofar da mahaukaciya take, a hankali na sauka tare da gyara rigana da ya yage na bude kofar, d'aga hannu tayi tare da zata kifa min mari, aka rike hannun ta baya, Sarinah ce.
"Akan karuwa zaki hanani ilatata?!"
"Eh ai gwara ita wasu gasu nan da mazajen basu iya tattalin su ba, Kinga ai ba laifi bane dan na bawa karuwa damar ta gwada basirarta ai zama da namiji iyawa ce, idan ka iya ka huta idan baka iya ba kana ji kana gani zaka rasa shi har abada,"
Nan ta nime d'aga murya, Sarinah ta ture ta, tare da gaya mata magana masu zafi, sannan ta shigo.
Nan nake bata labarin abinda ya faru bayan fitarta, tare da nuna mata yaga min rigar da suka yi,......
Paid before read...
a: Sai maganin Gyaran na mata zaku iya tuntubana ta wannan Number! Idan Baki shirya ba karki min magana! Da Manyan mata nake abu na 08130269641
ABU D'AYA.....muke so..
150 singul group! VIP 300 ta bank.Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga
200 singul grp! VIP 400 katin MTN..
Zaku iya tura shaidan biya ta wannan Number Zahran Addah Ramla +2347035133148 only Whatsp.
_ Idan kuma Alhubbih dayyia'n
Shima zaku iya biya ta Number! UmNass_
Acc No: 3051894647
Hajara Ahmad Hussain
Polaris Bank ga book din Alhubbi Dayyia'n zasu biya ta nan ne
3️⃣9️⃣ Yana ji na, ina bawa Aunty Sarinah labari bai ce kome ba, sai sunkuyar da kan shi da yayi cikin damuwa.
"Ni kam ka sawwake mata mana? Dole ne auren. Sannan taya za ayi haka ya faru, mata tana niman ranka amma still kana zaune da ita, matar nan kashe ka zata yi ni dai ka rabu da ita wallahi na gaji da wannan haukar nata."
Shiru yayi, cikin yanayin shi, na rashin son magana idan bashi yaso yin ta ba, d'ago kai yayi idanun shi cike da kwalla yace...
"Da zan iya saketa da nayi haka tuntuni, Mamie itace ta sayar da kimarta a gurin Linah, Mamie ta maida kanta mabaraciya a gurin Linah.
Wanda har ta kai Linah na gaya min magana akan Mamie ya kuke son nayi Mamie itace ta tun farko ta lalata min gidana,
Ita tayi ta kawar min da duk wata dokar da nasaka a gidana, ita ta janyo min damuwa tasanya Linah ta rena ni.
Duk abinda zan yi akan Linah bani da iko, wannan k'in shayar da yarinyar Mamie na sane asalima sai cewa tayi, bata ga laifin Linah ba ai tayi kokari, tunda. Ta haifi yar aka sanya mata sunan Yumnah toh wallahi ko itace iya abinda zai yi kenan shi yasa taki zuwa sunan ma."
Cikin damuwa da ciwon rai yake fada mana abinda Mamie tayi Mishi, shi yasa linah ma take mishi, wannan abun yayi min ciwo, ashe haka iyaye suke nuna son duniya sama da mu y'ay'an su.
Wannan wacce irin rayuwa ce, son kai ido da ido. Kallon shi nayi sannan nacewa Sarinah.
"Ni kam ina son zuwa gida na sauya kayana?!"
Amsar wayarta yayi sannan ya kira wata layi, magana su kayi kafin ya dube ni yace.
" A 'a zo daukar ki yanzun. Sai ki gaya mishi lokacin da zaki dawo dan ya jiraki ko kuma ya tafi ya dawo."
" Ina sai nayi barci dan har yanzun ban gaji ba, kuma ina son nayi sallah."
Shigowar wani mutum ya mikawa Uncle hannu, sannan yayi mishi ya jikin shi, amsawa Uncle yayi sannan muka fito.
Shiga motar nayi, har gida ya kawo ni, kamar na tsaya nace ya saya min ruwa, amma tunawa da Uncle ya sani fasawa.
Tunda na shiga gidan wanka nayi tare da gyara jikina, Baby Yumnah, kam naji suna cewa an kai ta, wani gidan reno.
Sallah nayi sannan na kwanta. Akan abinci sai na tashi, kawai na shiga barci.
Karfe biyu da rabi, naji an zuba min duka, a firgice na bude idanuna.
Linah da Mamie, tab'e baki nayi tare da mik'ewa na zauna ina sosa inda Linah ta zuba min duka.
"Ki ci Ubanta sosai, ƙaruwar banza" inji Mamie tana huci,
Kallon Linah nayi cikin wani irin yanayi, wanda ita kanta sai da taja baya, mai da hannuna baya nayi, cikin jin dadi nace.
"Toh zoki dake Ni!"
Kamar da gaske tayo kaina, kofin mug din da nasha tea jiya da safe shi na dauka tare da rikewa da kyau, tana kusanto ni burina na buga mata a fuskarta.
Kamar ta fahimci haka, kawai ta fasa tace.
"Mamie yarinyar nan bazata bari na tab'ata ba, Kinga abinda yake hannunta."
A fusace tayo kaina, zata dake ni na dira a gadon, ina kallonta, dan daga ni sai rigar barci, zagayowa nayi na bude kayana na dauki After dress, na daura akai, ina kallon su a hankali.
Sannan na dawo inda suke suna cika suna batsewa nace musu.
"Ba zaku tab'a lafiyata ba! Sabida Yumnah da kuka sani, ba ita bace yanzun, dan haka Mamie ke Uwa ce, kamata yayi ki san abinda yake damun Ahmad bawai ki zauna kina gurbata mishi rayuwar shi ba.
Mamie wacce iri duniya kike bukata? kisan me tayi mishi? Ta fashashen ruwan zafi ta watsa mishi, amma kike son ganin farin cikin ta,.
Meye ma'anar haka? Kin manta da abinda kika haifa kin yarda da."
"Toh karuwa! Sai ki dauki bulala, ina ga shi zan fahimci me shi, dan zai shiga jikina. Wallahi idan baki bar min D'ana ba zan sanya a kashe ki!" Inji Mamie,
Zuba mata ido nayi sannan na koma na bude jakata na ciro yar bindigar da Zein ya bani dab kare kaina, na fito dashi, kan Uban can.
Wallahi matan nan matsorata ne, dan sai jin karar fita daga dakin naji, dariya suka bani na shiga ban daki nayi alola, nazo nayi sallah.
Ina idarwa na saka riga da wando, dama rigar ta wuce cinya. Sai dan kwalin dana yane kaina.
Sannan na fito falon, karar waya naji, ina dubawa naga wayar Uncle, a hankali na sunkuya na dauko mishi sannan na mike sai ga Haidar. Tsuke fuska nayi zan fita.
"Lady!"
Ban ko kalli inda yake ba, nayi ficewa ta, daga gidan. Koda na isa asibitin. Aunty Taslima na fara karo da ita tuni na wurga da kome na rungume ta.
Itama cikin kewata ta rungume ni, kuka na saka mata. Sosai.
Rike hannuna tayi muka fita can waje, muka zauna ina kuka sosai. Rungume ni tayi tana rarrashina. A hankali nake bata labarin halin da na shiga, tare da irin rayuwar da na shiga.
Kafin na karshe mata magana da halin da nake ciki, na masifar kaunar namiji ya kasance ni.
Itama kuka tayi sosai, sannan tace min.
"Duk tsannani yana tare da sauki, Insha Allah zaki rabu da wannan matsalar.
Kawai kiyi hakuri tare da azumi, tunda naga Halwani yana sonki."
D'ago kaina nayi cikin sanyin jiki nace mata.
"Ina ganin baku fahimci wani abu bane, tsakanina da Uncle Halwani ba wai soyayya bace.
Abu daya yake nima a tare dani, da zan barshi ya samu zai rabu dani, a halin da muke ciki yanzun bana jin don shi ko na miskala zarra.
Kiyi hakuri! Ina bukatar shi a cikin yanayin da nake ciki ne, amma soyayya ta na Zein Asood ce, kuma daga jiya zuwa yau naga bani da muhalli a cikin rayuwar shi.
Aunty Taslima, mutane dayawa zagaye suke dashi kuma kowa na son ya farmaki duk wanda ya kawo mishi dauki a cikin rayuwarshi, Aunty Mamie! Linah! Uwa Uba mahaifiyar da ta haife ni, tana ji kamar ta cinye shi danye.
Duk da dama, ina yin shi kuma zan cika alkawarin da nayi mishi na tsayawa dashi har karshen rayuwata, bawai na zama a karkashin Inuwar shi bane.
Na fada mishi haka ne a matsayin shi na Abokin Abbanah, don Allah ki ajiye maganar soyayyar da ake tunanin ina mishi."
Jikinta ne yayi mugun mutuwa, kamar zata fasa kuka, take kallona, tace.
"Kina nufin bazaki auri Halwani ba?!".
Girgiza mata kai nayi sannan na ciji lip dina na kasa, kafin na zuba mata ido cikin tausayin a inda zan fada sannan na sunkuyar da kaina kasa,
"Like that!"
Zuba min ido tayi cikin damuwa itama.
"Amma baki san irin wahalar da yasha bane! Da zaki juya mishi baya."
"Ba haka bane! Mahaifiyarsa da matar shi bazan iya zama cikin su ba, sabida ina tsoron abinda zai je ya dawo, sannan kuma taya zan zauna na dinga biye musu muna abin kunya."
"Kenan kin girma kin yi hankali bazaki auri Halwani ba!" Inji Sarinah, juyawa nayi na kalleta sannan na matsa mata ta zauna, suka sani a tsakiyar su.
"Auntys dina ku fahimta mana, Mamie da Surukarta basu da sauki sai ta Allah, sannan kuma, taya zan iya zama naga b'acin rai haka.
Wallahi yadda suka fini shekarun nan sun fini sanin kan duniya zasu iya cutar dani fiye da tunanin ku, kawai zan bar musu Halwani su Ni na Kama Zein."
Tsakanin su da Allah suka takura min,