Showing 24001 words to 27000 words out of 115153 words
kar Driver ya gane me nake nufi na furta Ka Gama facakarka kayi watanda ka balangwaje kace baka tuna ba?Baki ya tabe tare da furta bana gane hausarki ta Yan kauye,Na nuna kaina da yatsa nace Ni,na nuna shi nace Kai na sake nuna cinyoyina nace zafi wannan,abinda ke tsakiya jini,zafi masifa zugi da da balbalin bala'i,Ni kin fadawa kowa,boye sirri Wai Nan fada nake yanda Driver bazai gane ba,Kuma Fu'ad har shi Basu fuskanci kan zancen ba,ya daga Glass dinsa sama yace driver muje,Ina kallo ya tafi na saka kuka ganin Sam Bai gane ba to ko Aljani ne ban sani ba.
Da dare Ina part din Umma Na tayata girki muna Palo Fu'ad ya shigo su Rabi ma suka shigo muna zaune Yana ta Jan Tsaki shi a dole sai Umma ta Kore mu sabo da shi ko kannensa basa zama Inda yake zaune,Ina Zaune Wayata tayi kara,da Sauri na duba ganin Hajara ce kawar mu na daga,Ina cewa Shalo.... Hajara, Fu'ad ya kusa Dariya sabo da shi dai Shalo din Nan tawa tana bashi Dariya,Nace Shalo....Shalo...Hajara...Shaloooo... kina jina? Hajara tace ke shegiya Rumaila Affanki ya zama Dan Daudu wallahi yanzu doya da kaji yake soyawa a Tasha,Kuma Yana Nan Yana daura zani Yana rataya jaka,sunansa Yar Shila,nace Allah Hajara? Hajara tace Alqur'an ki tambaya kiji,tunda naji a bakin Hajara magana ta tabbata,Nace to Allah ya shirye shi na kashe waya jiki a sanyaye na kalli Rabi nace Affa ne ya koma mace,shi yace lallai sai ya koma mace sabo da Haka ya zama Dan Daudu,su Rabi suna tafa Hannaye suka ce Sallallahu sanyi Kalau yanzu Affan naki? Nace sunansa Yar Shila ma,da ace Ina biyewa bacin Rai da tuni na Dade da yin mushe a daki, Ni dai Kwana Nan masifa ce take ta samu na zanje na bawa Fadila Hakuri na Bata dubu biyunta ko hakkinta ne yake tambaya ta, Fu'ad Yana ta kallon kauyencinmu ya gaji yayi fushi ya fita akan Umma Taki korar mu Yana zaune a dakin.
Ai kuwa har Dakin
Fadila naje domin na Bata Hakuri,na sameta a saman gadonta har kasa na durkusa, lokacin Fu'ad yazo zai tambayi Fadila wanne Kalar kayan daki take so sai yaji Ina magana sai ya tsaya a jikin Kofar Yana saurara,nace Anty Fadila Dan Allah kiyi Hakuri ki yafe min abinda na Miki Uwata kika zaga shi yasa nayi Miki Haka Nima sabo da na rama kiji haushi kema Kamar yanda naji,kin San Uwa mahaifiya ba Wasa bace,Babu Wanda za a zagi Uwarsa a zauna lafiya, Mari ta zabga min har biyu Tace ke kin Isa ai Allah ya Toni asirinki kika ce ke Yarinyar Yan fashi ce shi yasa harda fyalle wuka wlh sai an dau mataki a kanki jaka Kawai Yar fashi Yar kidnapping,Wallahi Tallahi Billahillazi la ila ha Illahuwa ko Qur'ani aka bani zan dafa ban taba fashi ba yanda akeyi ban sani ba,Kawai dai Baki shi ke yanka wuya barazana nayi miki kiyi Hakuri....Hannu ta daga zata dukeni Fu'ad ya shigo yace ke mene Haka? Baki da hankali Fadila,Ya....hannu ya daga Mata ban son Jin komai naji komai,ke wacce mahaukaciya ce Fadila? Baki da fahimta ne? Wannan yarinyar ce zata Yi wani fashi,hankali ne da ita? Ki kalle ta shekarunta Nawa? Yarki ce da Zaki dake ta? Wlh kar naji Maganar Nan ta fita sai kin Gane kurenki,Tsawa ya daka min tashi kifita da shegen surutun ku kuke furta Maganar da za a kashe ku, da sauri na Mike na fita ko Maular da Muka ce zamu je tsoron Yan fashi ya jawo mun fasa,Saude ce Tace Wai baza muje Maular ba? Nace ke bala'i Yana ta samu na zanje na karowa kaina masifa gaskiya mu tafi gida na gaji.
Naila ce da Khaleesat suka Tara Mana kwancen Kaya Kudade da Alheri Muka samu iri iri,Ana gobe zamu tafi Naila tazo wajen Nene muma muna palon na Mike nace Bari na tashi naje fatata ta gane kurenta,Nene Tace au wankan ma shine fata zata Gane kurenta? Dariya Muka Yi gaba daya har Naila,Na Mike na tafi abina.
Washe gari da sassafe Muka yiwa Wanda muka samu Sallama Abbi yasa Driver ya kaimu Tasha ya biya Mana kudin mota aka Bamu dubu goma goma ga kayan sawa Dana shafawa da sauran abubuwan mun samo Sha Tara ta arziki,Zamu shiga mota kenan sai ga Fu'ad ansha fited suits Ruwan Toka yayi kyau da alama fita zaiyi,Saude ta rera Wakar Kauye Tace.... munai maka sallama Dan Uwa Dan Uwa a cikin wannan Rana...... .. Ashe Fu'ad a wani Kauye yayi Service yaji Yan matan kauyen suna wannan wakar,hannu muke daga Masa Muna Bye bye da Waka muke hada Baki.... Assalamualaikum Dan Uwa Dan a cikin wannan Rana.....Shima ya dago Mana hannu Yana bye bye yace da wakar.... kar ku barta da yunwa da yunwa a cikin wannan Rana..... Mamaki ya kama mu Yan aiki sai Dariya sukeyi abin mamaki,Rabi Tace da Waka ....mu gidan mu ba yunwa sai Bredi sai shayi sai abincin turawa.....tafiya yayi abinsa ya barmu karshe muma Muka shiga mota Driver ya kaimu tasha ya biya kudin mota lafiyya Inji Abbi.
Sai Da Rana sannan Muka Isa kauyenmu,dama mun sanar da gida zamu dawo,Direct gidan Affa na wuce na ganshi daure da zanin Shadda dark Blue Yana ta karairaya a Kofar gida,a Haka na gaida shi da Maganar matansa yace Oh gantali dadi an dawo Ashe? sai ki koma wajen Uwarki inda kuka Saba yawo,nace dama gaidaka zanyi,yace na gode sai ayi gaba Umma ta gaida Aysha ya furta Yana shanye hannu daya shi a dole mace,tafiyata nayi gidan Iyata,Da murna ta tarbe Ni har kishiyarta da mijinta tare da yaransa suna zamansu lafiya gwanin sha'awa,Bayan na huta na bawa iya kudin tare da nuna Mata kayan da muka samu tana ta godiya,nace Iya kyau dai kiyi zamanki a Nan karki Bari a sakeki kinga Ana zaune lafiya,Baki Iya ta tabe tace wlh sai idan banga harka ba dole na barshi bana son tsimulmula sai dai a baka ci Kawai da Yar sutura Sallah ko anko baza a baka kudi a hannu ba ka fantama bashi da maraba da mazajen Dana aura,Haba Iya Dan Allah ki dinga godewa Allah,da Ubanki nake godewa ke kin Isa kice Zaki min nasiha,Shuru nayi Kawai na kyale Iya.
Yanga Muka dinga Yi a kauyen Muna saka kayan da muka samo na birni,mun zama wasu abin kallo sai kallon mu akeyi kullum muyi ta bawa kawayenmu labarin birni,wani farin jini na Kara samari sai binmu sukeyi,Ina Zaune kusa da Iya da dare Bayan Mun Gama cin tuwonmu yaro yayi sallama,Muka amsa yace Wai Rumaila tazo Inji Jauro,Jauro saurayi nane tin farko ya Dade Yana so na ganin naje birni na Kara gogewa shike Nan ya sake haukacewa a kaina Kuma Jauro kyakyawa ne sannan cirani yake zuwa Ibadan ya waye kamar ba Dan Kauye ba Haka yake,Sai Dana Gama Yanga ta sannan na fita wajensa ya siyo Mana rake muna Sha muna hira,santin rake yasa nace a.a..a Birni ba a shansa Haka sai an yanka da wuka kanana na,Yan gayu ma da cokali me yatsu suke cokala suna sawa a Baki,Jauro yace Gashi rake shi wanke Hanta yake tas Yana Kara karfin gani,Na karasa Masa da karfin ji ma,Wai ya soyayya ta ne?tana Nan kuwa?a wanne mataki Nake? Dake Ina Jin radio idan Ana fadar Yanayin weather kullum da safe,Nan take na bawa Jauro amsa da cewa kana matakin 40°c Selshiyus na furta wani iri sabo da ba Ilimi,Jauro yace gaskiya tayi kadan ko dari ban Kai ba? Nace ae Ina laifi ma kayi Hakuri Haka sabo da akwai samari da yawa Suma Kuma dukan su akwai matakin da suke shine a cikin 100° na Raba muku ka samu 40 ai kafi kowa soyayyarka ai tafi raken Nan Zaki.
Mun Dade muna hira da Jauro sannan ya tafi gida Bayan ya bani dari biyu.
Tunda na dawo bani da Aiki sai tunani da ya zan koma can naji dadi Amma ba dama,Haka idan Ina tuna Fu'ad sai farin ciki ya kamani Ni kadai nake zancen zuci Ina murna cike da farin ciki, lokacin Kuma Fu'ad shi ya Gama Shirin tafiya Germany wata uku zaiyi ya dawo Abbi ne ya tura shi sabo da Haka kwanan mu biyu da tafiya shima ya tafi turai.
Tunda na dawo lafiya Muke zaman mu a gidan Mijin Iya Yana so na sosai,aikin gida Kuma Ina tayasu sosai har wanki da guga nake wa Mijin Iya,na dauke shi kamar Uba na,watan mu Uku da dawowa daga Birni katsam na fara zazzabi Amai tashin zuciya inyi ta zubar da yawu,Kirjina ya sake cikowa nayi mugun haske nayi kiba da kyau,gaba daya kalar me ciki ta bayyana a jikina anyi maganin malaria har an gaji,Iya takan ce Ni dai na gaji da wannan Amai da zubar da yawu gaskiya Rumaila Ina da ja a kanki ,Iya me kike tunani? Dan Allah Iya ki daina zargina Haka nake furtawa Iya kullum, Watarana wata kurma Bata jin magana tazo gidanmu ta shigo da Sauri Ina yiwa iya dakan daddawa naji Kurman Nan ta cikwikwiye Ni tana zancen kurame tana masifa tana Nunawa mutanen gidan Iya da kishiyarta cewa ciki ne dani,duk Basu gane ba sai da me shayi Mijin Iya ya shugo Kurma ta Masa nuni ya fahimta tare da sanarwa Iyata,Iya ta rufe Ni da duka ta ko Ina ta Jani dakinta tana kuka tace fada min waye ya Miki ciki? nace Ni fa Iya bani da ciki ki kaini asibiti ma a gwada ni.
Yamma ta Riga da tayi ba damar zuwa asibiti dole sai gobe da safe,da sassafe Iya ta shirya Nima na shirya har da saka Hijab Kato Muka fita da Iya zuwa Asibiti.
AsmaBaffa
🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
FREE PAGE
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.
NA KUDI NE
GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.
ACCOUNT NUMBER
0175487861, ASMAU GARBA MUHAMMAD,GTBANK
MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER DA ZAKU TURA
08033933642
'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39.
11-15
Official
By
AsmaBaffa
PAGE NAKU NE
REAL MAMAN WALEEDA
SAMEERAN GAYA
SADEEYAN GAYA
Ina ta kuka har Muka je asibiti Karami Dake kauyen Iya bako sallama ta fada ciki Tace Likita so nake ki gwada min yarinyar Nan ko ta samu ciki,Likita ta Mika musu Kwalaba Tace tayi fitsari a Nan Hajiya,Iya ta Jani inda aka tanada sabo da hakan a gaban Iya nayi Fitsarin a cikin Kwalaba aka bawa Likita,Nan take ta gwada Tace Alhmdllh Baba kiyi murna yarki tana da ciki na wata Biyu da sati Uku,Nan take na hau kuka Ina rantsuwa Ina karya ne Iyata wlh Karya ne aje asibitin birni a gani,Iya ta fashe da kuka ta fisgi Hannuna muka koma gida,Shima Mijin Iya jikinsa yayi sanyi,washe Gari da Sassafe Iya ta daukeni Muka tafi asibitin cikin garin Jigawa ba Bata lokaci Iya ta bada kudi aka Yi sau uku a asibiti daban daban aka tabbar Ina da cikin Nan,Har scanning aka yi,Iya Bata sake kulani ba har Muka koma gida,da dare nace Iya yunwa nake ji,Iya Tace kije Wanda ya Miki ciki ya Baki mana Yar iska, shegiya,gantalalliya,dama abinda Kika je Yi kenan,duk Tarbiyyar Dana Baki Rumaila,hakazaki min? Yanzu kowa zaice Ni na na lalataki,ga Babanki baya kaunarki bazai iya rike ki ba,Rumaila kin cuce Ni Rumaila Iya ta fashe da kuka Nima na rushe da kuka.
Iya tana kuka Tace fada min waye ya lalata min ke Rumaila? Nace Iya Dan gidan me Gidan da muka je gidansa a birni Fu'ad shine Iya ya sace Ni Ina bacci ban sani ba Nima farkawa nayi na ganni a dakinsa sannan ban sake sanin Ina nake ba sai na sake farkawa na ganni a dakin da aka sauke mu Iya,da zamu taho na Masa magana ya nuna Bai sani ba Sam,Iya Tace Ina zai nuna ya sani tunda ya cuce mu ya Shaka Miki hodar Iblis,nace Iya duk abinda na sani shi na fada Miki wallahi abinda ya faru kenan Dani Iya,Amma Iya abin Haushin idan na tuna shi sai naji Wani sanyi da farin ciki,Iya Masifar sonsa nakeyi Ni abinda ya min ma bana Jin Haushinsa idan naji Haushinsa Ina tuna fuskarsa kyawunsa da dadin muryarsa sai naji farin ciki,Iya Ina sonsa....Mari iya ta dinga watsa min tana kuka sannan ta rufe Ni da duka sai da Kishiyarta da mijinta tare da yaran gida Suka CeCe Ni da kyar,Iya tana Huci Tace gobe da Sassafe idan na ganki a gidan Nan Allah ya Isa ban yafe Miki ba Rumaila,bana kaunar ganinki kusa Dani kiyi nesa Dani tun kafin na Tsine Miki Albarka.
Ina ta kuka duk gidan ba Wanda ya Goya min baya,shima Mijin Iya yace da Baki Kore ta ba ma Wlh sakinki zanyi bazan rike Yar iska ta gurbata min tarbiyar yarana ba,Kishiyar Iya tace wallahi kuwa taje can wajen Ubanta ko ta koma duniya can bariki inda ta kwaso abinta.
Kuka nayi shi har na gaji Haka na kwana a zauren gidan ban iya ko rumtsawa ba,Gari na wayewa na silale da kayana kaf Iya ta Watso min na kwasa, idanuna a kumbure da kyar nake gani na nufi gidan Affa Ashe zance ma tuni ya watsu a Gari Rumaila tayi cikin shege a Birni har Affa yaji labari Yana kofar gida Yana sharewa daure da Zanin Atamfa saman wata jallabiyarsa Yana ta rera wakokinsa Yana hango Ni yace karki karaso kina zuwa Zan karya ki,nasan Halinsa sai na nufi wajen kawuna yayan Iya shima ya Koro ni har gidan su Rabi da Saude naje Suka ce su sun daina kula Yar iska Kar na Jaja musu a Gari a dinga zaginsu,Nace Rabi Dan uwanki ne fa ya min ciki Rabi tayi shewa Tace wannan yan gayun ne zasu rike ko yatsanki Rumaila,kazama talaka irinki me zasu ci da ke,Haka Suka fada min maganganu masu zafi,Manyan mutane sai Tsine min akeyi har a masallatai na Gari sabo da jahilci .
Duk Sallah idan an Idar sai dai kaji liman yace wannan yarinya Rumaila da tayi abin fada a garin Nan ta kwaso cikin shege a birni Allah ya tsine mata Albarka Ana amsawa da Ameen.
Gidan Iya da Muka Bari Wanda ba kowa ciki sai tsofaffin kayan kitchen na iya sune kawai a gidan ga gidan ya kusa rushewa na tabbata da kyar zai tsallake damunar da zata sauka,Haka na Samu na tura yaro ya kwaso min ragowar kayana tas a wajen iya na share gidan fes na gyara komai na samo wata tsohuwar tabarma na Shimfida a kasan dakin a Nan na kwanta,tun daga wannan Rana na tsaida Sallah naji masifa da jarabta Iriri ai dole na tsaida Sallah ,Addua nake kullum Ina kaiwa Allah kuka na,Abinci ma Sai dai naje nayi bara a makwafta,Haka a zageni a bani na karba na cinye,kudin sabulu Kuma gona nake zuwa nayo ciyawa na siyarwa masu dabbobi Naira Ishirin talatin a Haka nake rayuwa na fita a hayyaci na gaba Daya,Ko Iya ko Affa Babu Wanda ya tausaya min bare Yan Uwa ba Wanda ke kulani har Yara ma jifa na sukeyi suna tsokanata da wakar tayi cikin shege a Abuja,sai gaba Daya sunana ya canja daga Rumaila sai dai tayi cikin shege a Abuja.
Ruwa na fita Ebowa da Botiki na Ina tafiya Ina tofar da yawu,zuwana bakin Rijiyar wani Amai ya taso min na koma gefe na shiga sheka Amai ba ji ba gani,Mutane da Yara suka taru a kaina Ana min ihu tayi cikin shege,na rigada na Saba sannan Ni ba komai ke bata min Rai ba sabo da Haka na share su na ebi ruwa na nayi tafiya ta abina,Su Rabi ma Gaba dayansu sun guje Ni ko a Hanya basa min magana su ma har Tsokana ta sukeyi suna cewa Ashe Yar iska ce Ni Basu sani ba abin da ya kona min Rai kenan Amma bani da bakin magana Babu abinda zan Kare kaina da shi Kuma kowa idan Haka ta faru da shi dole a guje shi banga laifinsu ba,Hajara ce ke Dan sassauta min Watarana har abinci take kawo min daga gidan su.
Bayan Tafiyar Fu'ad Germany Bai dawo Gari ba sai after 3months lokacin bikin Fadila saura 3weeks,ya Kara wani uban kyau yayi fresh,Shima Abbinsu yayi tafiya zuwa Dubai Yana dawowa yace ya kamata mutum ko uku ne a gidan Nan su shirya suje Kauyen Yan uwan mu wato gidan su Rabi,duk sha'ani ko abin bakin ciki suna zuwa Amma su ko mutum Daya Bai taba zuwa ba,Sannan Ina son yarinyar Rumaila mutuniyar kirki me tarbiyya a je a gaisar da iyayenta,Tunda Abbi ke magana ba Wanda ya amsa sai ma kowa cewa yayi bazai iya zuwa kauye ba,yasan dama baza su je ba,Sabo da Haka kawai yace Bari na zabi Wanda zasu je a bisa Umarni na,Yana furta Haka Fu'ad Dake kusa da Abbi ya mike tsam da niyyar barin Palon sabo da Kar ma ace da shi,sai kuwa ya tsinci Muryar Abba yace ka yiwa kanka Dan Momy harda Kai za aje, wani yaji ya sha... shiiiiii Yana tsuke Dan Bakinsa me dauke da jajayen lips masu taushi,Sai Nene,Nene Tace Alherin Allah ya Kai maka Abbin Yara sai tafiya ko da kafar katako,Umma kuwa da kanta tace zanje Abbin Islam mu ukun ma mun Isa,Sai mubi flight Abbi yace akwai Wanda zasu dauke ku da securities har kauyen.
Haka kuwa akayi Bayan An bugo Iv na bikin Fadila da kwana biyu Umma,Nene da Fu'ad Suka Shirya Ranar Saturday da safe