Showing 33001 words to 36000 words out of 115153 words
Yana wani takama ya kwanta a kusa da Umma tare da Dora kansa a Cinyarta.
Ina Yini na gaida shi lfy yace kawai da kyar,Khaleesat Tace kiyi sauri malama,a Dora ruwan zafi kusa sabo da za'a Masa steme (steaming)ake cewa cewar Naila tana dariya nace to,Kitso na Fara zubawa style me Arnen kyau Wanda Basu taba gani ba Allah ya bani basira da kaina nake kirkira,Ai kuwa Suka gigice ganin yanda yake zuba kyau,Naila Tace da an sani Ni aka Fara yiwa,Duk Wanda ya shigo ko mace ko Namiji sai ya yaba,Islam Yana zuwa Yace ah bayan Awarar a kitso ma an kware,Murmushi nayi me kyau fararen hakora na Suka bayyana kanana, Fu'ad kuwa sai Bata Rai yake Yi, Khaleesat tana ta faman kallo a karamin mudubin Dake hannunta,Gani da saurin kitso Haka na yarfa mata shi,da kanta tayi Steaming nasa,Naila ma kalar nata daban Ina Yi Ina ballar Goba ta,gani da saurin Jin yunwa tunda na Fara laulayi,Suhaila Yarinyar Anty Samha Amaryar Abbi na kalla nace ebo min Abinci a kitchen,Da Gudu taje ta ciko min plate da Fried rice harda kaza Ina kitso Ina ci sai gashi na cinye,nace kawo min ruwa taje ta kawo min na Sha sannan naci gaba da cin Goba ta, Fu'ad Yana ta mamakin ci irin nawa,a Haka na gamawa Naila,Ina gamawa na samo kunun gyada na shanye tas, nayi wa Suhaila style na Yara me kyau,tunda wasu kawayensu Suka gani Suka Fara zuwa suna cewa Dan Allah Zaki min Nima ko gobe ne? Nace baza ku samu ba yanzu Haka bayana ciwo yake Yi 12 pm ma tayi,gobe fa? Nace Ina da aiki Mijina zaizo Zan kula da shi,Da sauri Fu'ad ya kalleni irin karyar Dana Yi,Tace laaa kina da aure Yar karama da ke?, Nace Wasa kike a Haka din kuw...kafin na rufe Baki sai wayata tayi kara Ina dubawa Naga Jauro, Jauro Ana Kudu Bai San me ya faru da Ni ba,Wayar na daga tare da kashe murya nace Jauros Wai Ni irin soyayyar Nan, Fu'ad bakinsa ya Danne kar Dariya ta fito ya jawo Laptop dinsa Yana dannawa.
Shagwaba da kukan soyayya na saki Ina buga kafa ni...ni....Allah yaushe zaka dawo Habibi na....ka barni na gaji da jira....Allah zanyi maka kuka na fara wani irin kuka me tafiya da Imanin Wanda ake wa, Fu'ad tsigar jikinsa ce ta tashi Yarrrrrr.....wani Yanayin ya shige shi,Wanda ake wa shagwabar daban me ji a jikinsa daban,Ban dade ba Muka Gama Wayar, Fu'ad a aransa yace na kama Wanda yayi ciki Kawai Jauro ne, Allah yasa tsautsayi ya kawo ka zance live in prison zansa a daure shi daurin Rai da Rai,barin irin wannan a duniya hatsari ne,ban San me yake sakawa ba, Umma tuni ta tafi bacci shima Fu'ad tashi yayi ya wuce,sai wurin 1am na Gama na tafi na wanke Hannu na da sabulu na kwanta sai bacci.
Su Khaleesat da Ya Fu'ad Bai Kore su ba basa Zama idan Yana waje yanzun Nan zai ta masifa Amma yau ya kyalesu har aka musu kitso.
Da Sassafe a daki nayi Iksasaye (Exercise) kadan na koma Bacci sai 10pm yunwa ta tashe Ni ko wanka banyi ba naje kitchen na ebo abin Kari naci na koshi sannan nayi wanka tare da wanke Toilet din na fito na gyara dakin neat na saka skert din Atamfa Wanda shima a gidan aka dinka Mana zuwan farko Bra na saka purple sannan nasa Vest a sama itama Purple nayi kyau shape komai ya fito,ban Saba daura dankwali ba,gashi na na tafke jelar ta wuce tsakiyar baya na Haka na fita Palo na Iske har an gamawa Umma Lalle suna zaune tare da Fu'ad ya Sha wata sabuwar Gezna Light blue ya gaji da Haduwa sai kamshi yake zubawa,Umma na gaisar da shi Ogan ko kulani baiyi ba sai dai ya kallen sau daya,Goba ta na dakko a Leda na zauna gaban me lalle ta Fara tsara min ita abinka da Fara sai na dauki haske,Hannaye da kafafu aka zana min Baki da ja,tana gamawa na mike tsaye tare da kwaye Yar lukutar Cinyata sumul sumul nace zana min Fuskar Iyata a cinya ta Kamar yanda ake Yi a turai tattoo, me lalle da Umma Suka dinga dariya Banda Fu'ad dake aikin lissafinsa na kudade,Umma Tace in Banda shirmenki Ina tasan Iyan Taki da zata zana Miki ita,nace au sai sunga mutum ma? To wlh anyi asarar Basira a Nan Baki iya komai ba,me lalle tace zancen kike so,Nace to zana min flower me kyau a cinyar Nan tawa na dinga kallonta Ina Jin Dadi,Me lalle ta zage ta Zane min cinya ta Kuma tayi kyau sosai.
Ina sauraron Lissafin da sukeyi na kudi da Baki,idan Sunyi Lissafin abinda aka siya sai ya buga a waya,Ni kuwa sabo da na Saba da Talla munyi mugun iya Lissafin kudi kafin ya Danna a wayarsa na Fadi adadin kudin nace kudi sun Kama kaza mun iya buga Lissafin kudi,idan yayi a waya sai yaga dai dai da abinda nace Amma share Ni sukeyi ko na fada basa yarda har aka Gama min lalle ne ya bushe naje na wanke a toilet lokacin tuni me lalle ta tafi Umma ta fita Itama, Fu'ad ma haka,Yan Matan gidan sai shige da fice suke Yi,wannan ta figi mota ta fita kaga ta dawo wata tayi gaba itama,Hayaniya da Kade Kade a manyan speakers sun dameni Yan Mata ne Suka kunna mayafi na yafa saman vest din na fuce daga part din na koma Garden na Samu bishiya me sanyi na zauna a kasanta Ina zaune Ina cin soyayyar gyada me gishiri.
AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
FREE PAGE
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM
NA KUDI NE
GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE
ACCNT NUMBER
0175487861,ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK
MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER DA ZAKU TURA
08033933642
'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39
21-25
Official
By
AsmaBaffa
Page naku be
Maman Dee
Minerh
Aunty Nurse Zaria
Maryam Barau
Umma Khursum
Fulani Gal Bing
Lawee warra
Mariya Abubakar Gml
Maman Humaira
Azrahh
BB
Matar mijinta
Alhusnah (Mrs Idris)
Mmn Aliyu.
Ina kallon Yan Mata suna ta Hada hada,Dangin Nigeria Dana kasashen ketare duk sun zo,Sai Yamma Kawai aka fara cakarewa masu tafiya make up sun tafi wasu Kuma duk a gidan ake tayi musu,Umma ta Neme Ni har ta gaji ba a San Ina Garden ba,wurin magriba aka fara tafiya Event center inda za ayi wedding Dinner, Ina ta kallon gayu iri iri suna ta birge Ni,duk wacce taci gayu a Yan matan Amarya zata wuce sai na buya a Bayan bishiya suna tafiya Ina cewa ke Siiiiiiiiiiii.....Baki Yi kyau ba,ko nayi ta musu ba'a,idan fara ta wuce nace bature ya daina hada Mai,an rufe kamfanin man Blitching a duniya,Idan baka ce nace ke kuwa duk wayewar Nan da tazo kika tsaya aka barki a baya ga mayuka can sun fito Amma jibe ki kamar Bayan tukunyar Iya ta,idan Siririya ta wuce sai na fara Waka Ina cewa cokali a saka a dadi,idan me kiba ce nace kaga marga margan Toro.
Wata Yar sukuta tazo wucewa nace Sannu kifi sukunbiya da sauri ta juyo taga ba kowa taja Tsaki tayi gaba,Wata ma lukutar zata wuce nace a dawo lfy Dorinar Ruwa Allah kiyaye,sai Dana gaji na tashi nayi sabo da zanje nayi Sallah,Duk gidan an tafi saura Amarya da wasu tsirari,Har su Rabi sunci gayu an musu kwalliya dake An musu anko ma da wasu kalolin kayan na cin biki,Zasu shiga mota Driver zai kaisu Muka hadu suna ta Iyayi ganin ban shirya ba sun San ma bazan je ba sunyi tunanin ma bani da kayan sawa Dariya suka dinga yimin ko kallonsu banyi ba nayi tafiyata.
Ina Shiga na iske Umma zata tafi tare da Naila sunci gayu karshe,Umma Tace Ina kika tafi Kuma Ana ta tafiya babu Neman da ban Miki ba? Ina wajen Hutawa,je kiyi Sauri kiyi wanka kayanki suna kan gadonki,ga me make up zata Miki,da gudu na fada Bedroom dina naga Kaya kala Uku Shadda lace da Atamfa kalarsu sun birgeni harda mayafai da takalmi na me Dan tudu kadan harda jakarsa da murna na Shiga wanka ba Bata lokaci na fito tare da shafa Mai na zabi lace Dina sky blue and Black na saka sannan na fito aka Yi min kwalliya sama sama nace bana son kwalliyar hauka tana Gama min ta daura min dankwali me kyau, ka Rantse ba Ni bace sai yabawa akeyi,Daki na koma na dauki bakin mayafin da takalmi da jaka bakake Nasha kyau sai da na Dade Ina kallon kaina,su Umma Suka gaji Suka tafi,Islam Umma tayiwa waya yazo ya dauke Ni mu je tare.
Fitowa Nayi Ina taku dai dai zan fita kenan sai ga Fu'ad yasha wata Gezna Yar gaske milk color tana maiko,ba karamin kyau ya zuba ba,kamshi Yana tashi,kallo na yayi sau daya yasan Nayi kyau ba karya a Ransa yace an fara gogewa,Ina Umma? Nace sun tafi,ke Baki da hankali duk kowa ya tafi waye zai tafi da ke? Nace Kai Mana,Baki ya tabe yace kinyi kadan yarinya yayi tafiyarsa,shuru shuru banga Islam ba Ashe Momy ce ta hanashi zuwa Tace Indai ta ganni da shi sai ta Masa Baki,Ni kuwa ganin ba kowa na fita abina na Shiga Taxi dama da gate pass a Hannuna Kuma da Address din wajen,har can me Taxi ya kaini na bashi kudinsa na shiga wajen, kida ne Kawai ke tashi Ana rawa.
Kowa ya hallara aka zuba min Ido kunya ta kamani,duk naga Wanda na sani Amma babu wajen zama kusa da su,ga kida ya cika min kunne,Amarya da Angon ta An Sha kyau shiga na Alfarma, suits ya Sha black ita Kuma white wedding gown Wai su turawa,Fu'ad na hango shi kadai a wajensa ga kujeru har uku ga table a tsakiya an cika shi da abinci iri iri,wajensa na nufa a tsorace Ina Addua Allah yasa kar ya kunyata ni Amma Haka na tafi Ana ta kallon inda na nufa,Momy ta kalli Mama Tace kinga shegu ko gashi can ta tafi wajensa,tayani kallo ai Ina sa Ido sai asirinsu ya Toni Mama ta furta.
Kafin na karasa wajen Cikin Sauri Lubna ta koma ta zauna a dayar kujerar tana hararata,Su Rabi Suka saki shewa Ahayyeeeeee lokacin kida aka kashe dif sai ga iya muryar su Rabi a dubban jama'a wajen Yan gayu anji Ahayyeeeeee cassssss......aka kwashe da Dariya gaba daya kallo ya koma kansu Mata da maza,Ni kuwa naja kujera zan zauna wata kawar Fadila da take son Fu'ad Wato Fauziyya itama da sauri ta bangaje Ni ta janye kujerar ta zauna tana cewa me cikin shege,Baki na saki Ina kallon su Kawai na juya zan koma wani wajen,Hannu na naji an rike na juyo da sauri a tsorace sai Naga Fu'ad ne ashe,Lokacin Ido na ya ciki da Hawaye Ni kowa ya tsane ni kenan,Jawo Ni yayi jikinsa sai ji Nayi yayi sama Dani ya Dora Ni a cinyarsa,Kallo ya sake dawowa kaina naji kunya ta masifa Ina nokewa Ina so na gudu Amma sai yace ke dalla zauna ke ba Yan Mata ba kwaila me zakiji Ni ba irin Wanda ya Miki ciki bane,Ni kadai naji Maganar,Nace wallahi Ni ba kwaila bace cab Kaine dai kwaila wanda ko soyayya baka iya ba,ae ai naga alama shi yasa kika Yi ciki ko? Nace ai yaron ma me kama da Kai ne Kuma Ina son dana,Sunanka zan saka Masa idan namiji ne,idan mace ce kuma Sunan Fadila ko Naila,Da kuwa kinci Ubanki a gidan Nan cewar Fu'ad,ki rasa Wanda Zaki sawa sunana sai Dan shege,Murmushi Nayi Ina wul wulla kafafu na Ina Wasa da su by mistake na taba kaurinsa,yace kar ki Bata min Kaya fa,Su Lubna Kawai kallon ikon Allah sukeyi takaici da kunya ya Kama su an disga su,Gashi Basu San hirar da muke ba sabo da kida,tashi sukayi da haushi zasu bar wajen na kalle su Ido cikin Ido na dinga antayo musu gwalo,Ina ta rawa Zaune a cinyarsa har da daga Hannaye sama,Ashe Fu'ad yaji gulmar ance shi yayi min ciki shi yasa ya Nunawa kowa nasa dinne suyi abinda zasu Yi ai Allah ya San gaskiya.
Koma kujera sun tashi kin dameni,na kyalkyale da Dariya sabo da wani irin farin ciki na tsinci kaina ciki na manta duk damuwa ta Baki daya,kafada na makale tare da furta dadi,Momy da Mama tare da sauran Yan gida sai kallon mu sukeyi Kamar idon su zai Fado yau sunga zahiri cikin Fu'ad ne ya ma daina boyewa, Fu'ad duk Yana kallon abinda sukeyi,Amarya sai harara ta takeyi,Umma itama Naila ta fada Mata gulmar da akewa Fu'ad cewar cikinsa ne, Umma taji haushi Amma Bata saurari kishiyoyinta ba,sannan ita abinda Fu'ad yayi Sam Bata ga laifinsa ba,da Hannu Umma ta yafito Fu'ad yazo,Nima na gani sai na koma kujera yaje Kiran Umma,Yana zuwa Tace Ina kudin likina? Ya zaro raper Yan dubu dubu ya Bata Dana Naila,Umma Tace ka bawa Rumaila Bai amsa ba ya tafi ya dawo inda muke Zaune daga Ni sai shi,Yan matan Amarya da dangi Ana ta kiransu suna rawa da liki,Amarya da Angon sun fito fili sai da Fu'ad ya Bari duk an Gama rubibin ruwan liki sannan ya bani Nima Yan dubu dubu yace je ki min liki,na karba tare da Mikewa Yar dagwas Dani Ina tafiya cakwas cakwas Ana ta Yaba kyawu na da kyan surata,Fadila ta balla min harara na share su Waka tana tashi na Balle raper a Raina Ina cewa wayyo Iya ga kudin-Ga kudin a Nan,Iya dadi ya barki,Iya ba Rabo Allah sarki Iyata sai dai ki samu naki a darul salamu, na fara liki far far,Dj ya saki sauti su Rabi sun Ware murya da karfin gaske sabo da karar kida suna cewa wayyooooo Allah Alqur'an Yan Dubu take likawa duf Kake Dj ya tsaya da kida aka sake Jin muryar su Rabi ta cika Hole din suna cewa Alqur'an Yan Dubu dubu take likawa,aka sake kallonsu aka dinga Yi musu Dariya,Hajara Tace yau Bamu da sa'a Kawai mu daina magana idan an koma sai muyi gulmar,Saude Tace tsinannen Dj ne wannan sai kunyata mu yakeyi to wallahi kwandala bazan lika Masa ba Dan ubansa,Rabi Tace wannan kwai jarabar Rumaila tazo dangina daga bakunta tazo ta kwace Mana dangi wallahi da nasan Haka ne wlh bazan zo da ita ba,Kawai na dauki wuka na dabawa kaina.
Momy da Mama Suka girgiza Kai tare da kallon juna Suka ce ta Gama tabbata zasu ci ubansu wlh Bari a Gama biki hankali ya kwanta,Ina yiwa Amarya da Angon liki Fu'ad yazo Ni Kuma Yana lika min sai da ya gaji,Ina tsaye Safna ta wuce fuuuu ta fadawa Mc ya min tambayoyi na wulakanci ya kunya ta ni kowa ya min ihu, Amarya akace su koma su zauna,zan tafi Mc yace Yar fillo ga kyau ga kwalliya ya sunanki? Ya Kara min speaker a Baki,Allah sarki ban sani ba nace Rumailan Fu'ad me murmushin Naira,aka kwashe da Dariya har Fu'ad Wanda ya koma tuni ya zauna,Mc yayi Niyyar abinda aka Umarce shi Amma ganin Fuad sai ya Masa kwarjini Yana Tsoronsa,yace waye Fu'ad a wajenki ko kema kanwarsa ce? Nace ka daina rage min daraja mana ai nafi kanwa matsayi a wajensa,Uwar gidan sa Kuma uwar 'yayansa Inshaallah, me Zaki cewa makiyanki? Nace ba abinda zance face na zaro harshe waje na kalli ko Ina a hole din nace wannan gwalon shi zancewa da makiya na, har Yan bakin ciki sai da suka dinga Dariya,Mc yace Dj sa Mata kida Uwar Gidan Fu'ad ce,ai kuwa aka saki kida me shegen dadi ko baka so sai ka taka,Momy na kalla Muka hada Ido na Mata girgiza,Mama ta Bude Baki Tace wannan tsagera ce,Islam ne ya fara zuwa Yana min liki Banda girgizar da nayiwa Momy ba abinda na sakeyi na rawa Ni ba wata rawa nakeyi ba,a wajen na tsaya kawai maza Suka dinga tururuwar Yi min liki, Fu'ad nake kallo Ina masa inkiya da Ido akan yazo ya min liki,Bai taso ba sai da na gaji na fito zan bar wajen rawar sannan ya Iso da Izzarsa ya sake bani sababbin kudi Yan dari biyar shi Kuma ya fito da Yan dubu Yana lika min Nima Ina lika masa,Umma tazo ta Mana liki,Haka Naila,Sai mazan gidan kaf dake maza ba irin Mata bane Basu fiye shiga harkar wani ba bare su suna da aikin Yi gasu da Ilmi,Kamar bikin mu akeyi Haka Muka Sha ruwan liki,Naila ma tazo tayiwa yayanta Ni kuwa hararata tayi Nima na rama.
Muna Gama likin muka koma Muka zauna Yana wani basarwa ya wani Bata Rai nima na share shi na shiga cin abinda aka cika table din da shi,abinka da me ciki sai da na koshi Ina gamawa na Mike tare da daukan jakata na kalli Fu'ad nace na gode Allah ya Kara arziki,Ina Zaki je? Nace gida na Gama biki na ai kasan Dan ciki na kida ya dameshi sai motsi yakeyi Kamar kifi a ruwa,bacci Kuma nakeji,Hade Rai yayi yace ke baza ki Fadi Wanda ya Miki cikin Nan ba ko? Nace Hmm Kawai na juya Nayi tafiyata,Ina fita na tare taxi na shiga sai gida,Ina komawa wanka Nayi na shirya cikin kayan bacci na Bayan Nayi Sallah na kwanta abina bacci yayi gaba Dani.
Sai wurin 3am Yan Biki Suka fara dawowa,Abbi ya Hana ayi Event da yawa yace daya ta isa,washe gari za a daura aure zuwa dare akai Amarya shike Nan an Gama biki.
Washe gari Saturday ranar daurin Aure,da wuri aka fara Shiryawa,Nima Ina jefa gyada a bakina